42
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA
Page 4️⃣2️⃣
Baki ta cuno tana ƙara kwabe fuska ganin yana ƙara mata alamar tace amma yaki bari taja plate ɗin gaban ta
"Kince you're hungry then maisa bakya ci"
Ɗagowa tayi da niyyar maga amma taga ya haɗe rai kamar bai taɓa dariya ba,
"Na ƙoshi"
"Kin koshi??, ba yanzu kika gama cewa baki ci komai ba"
Shiru ta ɗan yi, da ɗan faɗa faɗa yace
"Am talking to you sa hannu"
Spoon ɗinta dake ciki ta ɗauka ta fara ci kamar wadda ake ba magani a ranta tana faɗin
"Mutum sai yayi ta faɗa yana harhaɗe rai kamar wanda aka ce ga ranar mutuwarsa, se kace wani ke mintsinin shi da ze ringa hucewa akan mutane, anya ma ba aljanu ne dashi ba?" Ta watsa wa kanta tambayar ta na ɗan satar kallon sa ta ƙara cewa a zuciyar ta
'' ba mamaki idan ma yana da su ɗin, ba wuya'' ita ta kasa gane hali irin na ya Umar
Shidai Ahmad tv ya maidasu yana kallon drama, inba karfin hali ba, ka zo kawai kasama mutum hannu a abincin shi dan tsabar neman magana kuma kana wani haɗe rai dan karfin hali
"Allah ya kyauta maka kaidai"Ahmad ya faɗa yana tashi yakai plate ɗin daya gama cin abun shi tun suna dramar su,
Su Batul ne suka fito saboda daura abincin rana,dan ita Ammi bata da mai aiki,haka dai itama Amma, gani take dukan su yara mata ne gwara su koyi aiki tun yanzu, idan ta sabar musu saidai suna zaune a musu ai ba gata bane, duk da dai su they learned the hard way, amma dan tasha wahalar aiki ko rayuwa ba bashi zaisa su sangarta yayan su ba
Tun suka nufo hanyar idon su ke kansu, kallon juna sukayi amma ba suyi gangancin yin wani shirmen ba suka yi kitchen
Saida yaga taci da ɗan yawa sannan shima ya cigaba da ci, a haka har suka gama ta dauki plate ɗin tayi kitchen
"Umm kaga su Julieta" faɗin Batul
"Kee Lailarh dai" Khadijah ta faɗa suna ɗan kwashe wa da dariya
Bata tanka su ba dan bata ma da lokacin shirmen su ta ijje plate ɗin tayi gaba
Tana jin su, amma tayi waje abin ta
"Sai yamma zaki koma ne" faɗin Ammi da ta tashi zata koma ɗaki dan yin sallahn azahar da aka ƙira
"Eh sai irin bayan laasar haka"
"To Allah ya kaimu"
Har lokacin yana zaune a gurin be tashi ba sai aukin danna waya da yake ta faman yi
A ɗan fakaice ta kalle inda yake, tana mamakin wai shi kwata-kwata baya gajiya da danna waya ne, ido suka haɗa tayi saurin dauke wa tayi hanyar daki da sauri, tana shiga itama alwala tayi tayi sallah
Gado ta koma ta cigaba da kallon ta, sai around 3:45 ta tashi ta ƙara wanka ta shirya ta fito, daƙin Ammi tashiga ta mata sallama tace
"Kin ma yiwa drivern magana zai kai ki, kar kije maybe ma ya fita"
"Eh tun ɗazu nace mai wurin 4 zai kai ni gidan Anty"
"To Allah ya tsare sai kun dawo"
Ameen tace ta fita daga ɗakin,
A parlour ta ganshi zaune a zuciyar ta tana faɗin wai bashi da aiki kullum sai danna waya tana yawan yiwa kanta wannan tambayar dan ta lura shi ba gajiya yake ba
Ɗagowa yayi ya kalle ta, atampa ce a jikinta dinkin straight gown ne mara hayaniya, be kamata ba amma ya zauna sosai a jikin nata, sai normal ɗauri da tayi ta yafa veil ɗin akai, tasaka lipgloss dan yau ko lining ɗin ma da ta saba ba tayi ba
"Ke baki da hijab ne wai??"
Kallon shi tayi a zuciyar ta tana tambayar kanta to tayi me da hijab a yanzu
"Ki koma ki saka hijab"
"Hijab!! Kamar wani zanje gidan mutuwa" tayi maganar a ranta, amma a zahiri kawai kallon shi ta ke tana ganin ikon Allah amma ta kasa furta komai
"Didn't you hear me, ki wuce ki saka hijab, ko so kike ki fita haka ko wani banzan ma yayi ta kallon ki"
"Yahh hijab fah!!" Ta faɗa a mugun shagwabe
"Eh"
Juyawa tayi ta nufi hanyar ɗakin, ranta a ɓace, tana cuno baki gaba kamar ze faɗo, abaya ta dauko ta saka ta yapa mayafin abayar ta fito, akan tasaka hijab akan atampa da zafin nan gwara tasaka abayar, ba lokacin sanyi ba ba komai ba ita da zata fita shine zata wani saka hijjab ana zaune kalau
Kallon ta yayi har zai yi magana kawai yayi kwafa ya tashi yayi waje, itama baki ta taɓe tabi bayan shi
Tun fitowar ta driven ya ganta ya taso yana jiran ƙarasowar ta,Inda drivern yaka ta nufa,
Muryar shi ta tsunkaya yace"malam habu kaje kawai ba damuwa zan kaita"
Da toh ya amsa shi ya bar gurin, itama jin hakan yasa ta juya akalar tafiyar tata ba dan taso ba, ranta kuwa kamar ze fashe
Follow and like my account on arewapen ba dan halin wannan marubuciyar ba dan Allah 🥹 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏🙏 🙏 🙏
______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺
***