NUFIN ALLAH

43

by @anisamuhammadyah897


💕 NUFIN ALLAH 💕 
By
Anisa Muhammad yahaya 


 YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA


Page 4️⃣3️⃣


Har suka fito ba wanda kema wani magana in ba Radion da yake ta faman zuba ba

Wayar ta kawai take danna wa, gashi su biyu ne kawai a motar, duk a takure take jin ta

Gani tayi ya karya kwana ya bar kan titin, a Valentino taga yayi parking, kallon shi tayi tana son tambayar shi amma ba dama

Ko kallon ta beyi ba, duk da yaji tana kallon shi, ƙara haɗe rai yayi dan baya son ma tamai magana, dan bai san shima dalilin da zuciyar sa ya janyo shi nan ba, 

So yake ya fara gwada abin da Abba yace Mai, so shi yasa ya fara da haka 

Fita yayi daga motan bayan ya kashe, ita dai da kallo ta bishi, har ta kama handle din ya rigata buɗewa yana kallon ta 

Itama kallon shi tayi bata ce komai ba ta fito a hankali kamar bata so, motar ya rufe suka jera suka fara tafiya 

Dan tsayawa tayi saida ya ɗan yi gaba sai ta fara binshi a baya, dan juyawa yayi ya kalle ta bece komai ba har suka shiga 

"Wani flavour kike so" ya tambaye ta yana kallon different varieties na ice creams ɗin
"Ni na ƙoshi"
"Like how, karki ɓata mun rai"

Ganin ya ƙara haɗe ranshi ba kamar sanda suka shigo bane yasa ta pointing chocolate one din

Scooping mata akayi, shima shi yace abashi, zama sukayi a gurin

Cup ɗin ta tusa a gaba da kallo shima ta ɗago ta kalle shi, shan abun shi yake hankalinsa kwance

"Ki sha mu tafi"
Ɗan spoon din ice cream ɗin ta ɗauka tana juyawa amma ta kasa sha

Itafa ba gwanar shan ice cream ɓace dan ba tama so, banda tayar mata da zuciya ba abinda yake in ta sha sai taji kamar zatayi amai

Kallon ta ya ƙarayi yace "so kike in ƙara mai maita miki"

"Yahh Allah na ƙoshi" ta faɗa idonta fal hawaye
Kallon ta yayi yace "abinci ne da zaki ce kin ƙoshi"
"Bana shan ice cream fah"

Irin kallon are you serious ya mata yace
"To yau zaki fara, come on sha"

Kamar zata yi kuka ta ɗauka spoon ɗin takai baki wani kwalla na cika idonta, ita tana ganin ikon Allah, mutum baya son abu amma za'a mai dole, ita tace sai ya siya mata ne da zai saka ta a gaba dole sai ta sha

Tana kaiwa ta haɗuye da kyar ,wani spoon ɗin ta ƙara kaiwa shima kamar ance ta sha flagyl, a spoon na uku ne taji wani amai ya taho mata ai da sauri ta ijje spoon ɗin tayi waje

Saurin tashi yayi shima ya biyo bayanta, tun kafin ta karasa inda sukai parking ta tsugunna a wajen tana kakari, wani me saida pure water ya samu ya bata ta wanke bakinta 

Sai duk yaji be kyauta ba, ta nuna mai bata so amma ya tilasta mata gashi ai ya sakata amai bata shirya ba ba gaira ba dalili, sai sannu yake mata, amma tayi banza ta kyale shi, hankalin sa duk ya tashi amma bazaka ce haka a kan face din shi ba, sannun da yake mata ma kamar wanda aka wa dole amma a ransa kuwa ji yake kamar ya daki kansa

 wani haushi haushin shi take ji ya sakata yin amai a public, 

Suna nufa ya buɗe mata ta shiga tana wani haɗe rai, shima ya buɗe side din shi ya shiga 
"Sannu"

Ji tayi kamar ta gwabe bakin dake mata sannun, se kace bashi ya ja tayi ba hmm 

Kanta ta kwantar kan kujerar ta juya mai baya tana kallon glass din motan ta rufe ido 

Ahaka har bacci ya ɗauke ta, duk bayan mintina sai ya juyo ya kalle ta, yanayin na mai daɗi a hakan dan yama rage gudun motar, ahankali yake tafiya dan kar su ƙarasa da wuri

Har suka isa bata tashi ba, ido ya zuba mata yana jingina kanshi shima akan kujerar sa, yanzu ta juyo tana facing din side din da yake

Face ɗin nata yake bi da kallo, aranshi yace
"You look more innocent and sweet in kina bacci,that baby face of yours, ina son waɗanda tiny lips din da kullum suke gaɓa, dan rigima ayita cuno su" murmushi ya ɗanyi sannan a fili yace
"Matsoraciya, kullum bakida aiki se tsoro kamar wadda za'a sace, farar kura kawai"

Idon ta da ya ɗanyi ja ta bude, bacci take amman tana iya jin yanda idonsa suka hanata sukuni, yana ganin haka yayi saurin kauda kanshi ya zauna daidai kamar ba kallon ta yake ba

Tashi tayi zaune sosai tana salati, ta kalle shi ta kalli kofar gidan, wayar ta da ta faɗar kasa ta dauko dan dama iya abinda ta dauka kenan ba ko jaka a hannun ta

Handle din ta buɗe zata fita ya rufe, bata ce komai ba ta saki handle din, fita yayi ya zagaya ya buɗe mata, kallon shi tayi, sai kuma ta fito ya rufe suka nufi gidan 

A bakin ƙofa suka haɗu da su Nabila da Anty ta aike su suna dawowa, gaishe shi sukayi suna mata kallon Allah yasa mu haɗe zakiyi mana bayani

Binsu tayi suka yi gaba,shima yana biye dasu a baya

Ba kowa a parlourn, Anty na sama, zama yayi su kuma suka yi hanyar stairs Nabila na Jan hannun ta
"Keee ki sake ni ko se kin ɓalla ni tukuna"

Kin sakin ta tayi saida suka je ɗaki sannan tace
"Kaiii kun tafi dani kalla wani match kun wani jero kamar wasu newly Weds"
"To ai sun kusa zama newly Weds din"
"Kin san dan kawai muna gaban sune ba damar yin hoto ai dana ɗan yi capturing moment ɗin nan"
"Keee ashe muna ɗaya nima fa abinda yazo zuciya ta kenan"

Ita dai bata tanka su ba dan tasan so suke su kunna ta, itama dai Fareedah bata ce musu komai ba 

"Kee ba mu kira Anty ba, Anisa kije ki kira anty ai tare kuke" faɗin Jalila 
"To dan tare muk.., ni nasan inda take ne"
Ta gyara zancen ganin kamar har yanzu Fareedah na ciki da ita
"Tana ɗakin ta"

Bata ce komai ba ta fita, tunda dai har tasa aranta zata yarda be kamata ko su ta ringa nuna musu kamar baso take ba dan yanzu ta gane me suke fada mata, ba daɗi taringa hakan a gaban fareedah

Knocking tayi a kofar tace ta shigo, tsaye ta same ta gaban wardrobe tana gyara kaya 
"Anisa kin dawo,yasu Ammi"
"Anty ina wuni, duk suna lafiya sun ce in gaida ke"
"Madallah ya jikin naki"
"Lapiya kalau amm daman tare muke da ya Umar yana parlour"
"Kice Babban yaya ne a gidan, ki faɗa mai gani nan zuwa kar ya jini shiru"

Da Tom ta amsa ta fita tayi ƙasa
Tun ta fara saukowa daga stairs ɗin yake bin ta da kallo, har kusan harɗewa tayi dan daman da sauri take sakkowa 

"Yah tace wai gata nan zuwa tana ɗan abu ne"
Kai ya jinjina mata, ta juya zata tafi yace
"Ke zauna kafin ta sakko"
Kallon shi tayi ta ɗan kwaɓe fuska tace
"Yah ni kuma??"

bayi mata reply ba,sai kallon ta da yake
"Yahh abu nike yi"
Gira ɗaya ya ɗaga mata yana ɗan haɗe rai

Zama tayi a dan nisa dashi tana cuccuno baki, to ita idan ta zauna me zata mai


Follow and like my account on arewapen ba dan halin wannan marubuciyar ba dan Allah 🥹🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏



______________________
By 
Anisa Muhammad yahaya 🌺 
***