KADDARAR ZUCIYA

THE CALL

by @jiddaahbarkum

*ƘADDARAR ZUCIYA*

*CHAPTER THREE: 3*

*THE CALL*

*JIDDAAH BARKUM*

———

Har motar Heartbeat ta ɓace daga idona, amma har yanzu ban iya barin wajen gate ɗin ba, na tsaya ina kallon hanyar da ya bi, kamar ina tsammanin zai dawo ya sake yi min horn, ko kuma ya sauke gilashin motar ya ce min wani abu, amma babu komai, hanyar ta yi shiru, na share hawayen da suka taru a gefen idona da bayan hannuna, sannan na sauke numfashi mai nauyi, “Ina maka addu’ar Allah ya tsare hanya, Heartbeat…” Muryata ta fito kamar raɗa, na sake kallon hanyar, “Ka isa lafiya, please…” Sai na juyar da kaina a hankali, na nufi cikin gidan, amma ban san dalilin da ya sa ƙafafuna suka yi min nauyi haka ba, kamar wani abu yana damun zuciyata, wani abu da ban iya bayyana shi ba, na shiga babban falon cikin nutsuwa, da na ɗaga ido, sai na hango Daddy zaune a kan sallaya, hannunsa ɗaya yana riƙe da carbi, yana jujjuya ƙwayoyin carbin ɗaya bayan ɗaya, yayin da bakinsa ke motsawa cikin zikiri, na tsaya na ɗan kalle shi, sai na ƙarasa kusa da shi, na zauna a ƙasa, Daddy ya dakata da jujjuya carbin, ya kalle ni daga gefen idonsa, “Har ya tafi?” Na gyada kai a hankali, “Eh, Daddy,” muryata ba ta da ƙarfin da take da shi da farko, Daddy ya jinjina kai, sannan murmushi ya bayyana a fuskarsa, “Mutumin kirki ne Ahmad,” na ɗago ido na kalle shi, “Yaro ne mai tarbiyya da sanin ya kamata, Allah ya tabbatar mana da alheri,” wata irin daɗi ta mamaye zuciyata, na sunkuyar da kaina cikin kunya, “Ameen, Daddy,” ya sake fara jujjuya carbin, ni kuma na zauna kusa da shi na ɗan lokaci, amma hankalina… ba ya nan, yana can, a kan hanyar Kano, a tare da Ahmad, kusan mintuna goma suka wuce, na miƙe na gyara wasu cushions a kan sofa, sannan na koma na zauna, bayan wasu mintuna sai na sake miƙewa, na gyara labulen falon, na sake zama, na ɗauki wayata, na kalli screen ɗin, babu saƙo, na sauke numfashi, “Ya kamata ya kusa isa…” Na faɗa wa kaina a hankali, na sake ajiye wayar, amma bayan wasu mintuna kaɗan, sai na sake ɗauka, har Daddy ya lura da ni, ya ɗan yi murmushi, “Me ya sa kika kasa zama wuri ɗaya yau?” Na yi kamar ban damu ba, “Ba komai, Daddy,” ya ɗaga gira, “Ba komai?” Na yi murmushi, “Eh,” ya girgiza kai yana dariya ƙasa-ƙasa, “Allah ya sa ba komai ba ne,” na yi masa murmushi, amma zuciyata ta ci gaba da yin wani irin bugawa, lokaci yana tafiya, agogo ya nuna ƙarfe shida da rabi na yamma, sararin sama ya fara yin duhu, hasken rana yana dusashewa a hankali, alamar magariba ta kusanto, na zauna a gefen sofa ina kallon screen ɗin wayata, sai kawai— TRRRRINNN! Sautin wayar ya cika falon, na ɗan firgita, sannan hannuna ya miƙe da sauri na ɗauki wayar, na kalli screen, My Heartbeat, zuciyata ta yi wani irin tsalle, “Oh…” Na yi murmushi ba tare da na sani ba, “Ya isa kenan,” na danna amsa cikin sauri, na ɗora wayar a kunnena, “Hello, Heartbeat!” Muryata cike take da farin ciki, “Har ka isa—” Ban ƙarasa ba, domin muryar da ta amsa min… ba ta Ahmad ba ce, muryar wani namiji ce, mai nauyi, mai saurin magana, kuma akwai wani irin tashin hankali a cikinta, “Hello?” Na ɗan daure fuska, “Eh…” Na gyara zama, “Wane ne?” Muryar ta sake magana, “Please…” Ya ɗan yi shiru, kamar yana neman kalmomin da zai yi amfani da su, sai ya ce, “A serious accident just happened along the highway,” na tsaya cak, murmushin fuskata ya fara dusashewa, “Accident?” Na maimaita kalmar a hankali, “Me… me kake nufi?” Mutumin ya ci gaba da magana cikin ruɗewa, “The owner of this phone is involved in the accident,” zuciyata ta buga da ƙarfi, na ɗan yi dariya cikin rashin fahimta, ina ƙoƙarin shawo kan kaina cewa wataƙila ban ji abin da ya faɗa daidai ba, “Ban fahimta ba,” na matse wayar a kunnena, “Wane phone?” Ya sauke numfashi, “This phone, ma’am,” na yi shiru, jin daɗin da ke cikina ya fara gushewa, ya maye gurbinsa da wani irin fargaba da ban taɓa ji ba, “Wannan…” Na kasa kammala maganar, sai muryar mutumin ta sake zuwa, “Please, is he your relative?” Na ji kamar duniya ta tsaya, relative? Na kalli screen ɗin wayar, My Heartbeat, na sake kallon sunan, kamar idan na ci gaba da kallonsa, zan ga Ahmad ya kira ni da kansa ya ce min komai lafiya, sai na ji ƙirjina yana bugawa da wani irin ƙarfi, “Ahmad…” Sunansa ya fito daga bakina a raɗe, muryar mutumin tana ci gaba da magana a ɗayan ɓangaren, amma ban ƙara jin kalmomin ba, komai ya fara yin nesa, sautin muryarsa ya rikide ya zama kamar ana magana daga wani wuri mai nisa, idanuwana suka fara yin nauyi, wayar ta fara rawa a hannuna, “Me… me ya same shi?” Na tambaya cikin murya mai karyewa, “Please…” Na haɗiye yawu, ina ƙoƙarin hana muryata karyewa, “Tell me what happened to him,” amma kafin in samu amsar da zan iya fahimta— ƙafafuna suka kasa riƙe ni, na ji jikina ya yi sanyi, sai na sulale a hankali zuwa ƙasa, wayar ta kubuce daga hannuna, ta faɗi a ƙasa, har yanzu kiran yana kunne, “Hello? Ma’am? Hello?” Ban amsa ba, na kasa jin komai, na kasa ganin komai, sai duhu.

“Inteesar!” Muryar Daddy ta fashe da tsoro, ya ƙaraso da sauri daga bathroom ɗin falon, inda ya je ɗauro alwalar magariba, carbin hannunsa ya zube a ƙasa, ƙwayoyin carbin suka watse a gefen ƙafafunsa, “Inteesar!” Ya ƙaraso inda nake kwance, jikinsa yana rawa, “Ya Allah!” Ya sunkuya yana ƙoƙarin ɗaga kaina, amma ban motsa ba, wayar da ke ƙasa ta ci gaba da yin magana, “Hello? Sir? Can you hear me?” Daddy ya kalli wayar, ya miƙa hannu cikin rawar jiki ya ɗauke ta, sannan ya ɗora a kunnensa, “Hello?” Muryarsa ta fito a hankali, “Wane ne wannan?” Ya kalli Inteesar da ke kwance a gabansa, “Me ya sami mai wayar?” Mutumin da ke ɗayan ɓangaren ya fara magana cikin sauri, “Sir, there has been a terrible accident,” Daddy ya matse wayar a kunnensa, “Accident?” Ya maimaita kalmar kamar bai yarda da abin da kunnuwansa suka ji ba, “Yes, sir,” muryar mutumin ta yi nauyi, “The car had a head-on collision with a heavy truck,” Daddy ya lumshe idanu, a take, jikinsa ya yi sanyi, “Please…” Muryarsa ta fara rawa, “Me kuke nufi?” Mutumin ya ci gaba, “We are at the scene right now, we are trying to move the victims to the nearest hospital,” Daddy ya kasa magana, ya buɗe bakinsa, amma babu kalma da ta fito, idanunsa suka koma kan Inteesar, yarsa, ƙaunarsa, rayuwarsa, ta kwanta a ƙasa ba ta san abin da ke faruwa ba, hannunsa ya fara rawa sosai, ya dafe ƙirjinsa, kamar yana ƙoƙarin hana wani abu mai nauyi da ya sauko masa ya murƙushe zuciyarsa, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…” Numfashinsa ya fara nauyi, wani irin jiri ya turnuke shi, ya yi ƙoƙarin miƙewa, amma ƙafafunsa suka kasa riƙe shi, ya kama gefen sofa domin kada ya faɗi, “Ya Allah…” Ya sake maimaitawa cikin rauni, sai ya katse wayar, “Mommy!” Muryarsa ta fito da ƙarfi, “Haleema!” Ya sake kira, “Haleema!”

Daga kitchen, Mommy Haleema ta ji muryarsa, ta fito da sauri, tana riƙe da ludayi a hannunta, “Alhaji?” Da ta shiga falon… sai ta tsaya cak, idanunta suka sauka kan Inteesar da ke kwance a ƙasa, sannan suka koma kan Daddy, wanda yake jingine da sofa, hannunsa a ƙirji, fuskarsa ta sauya gaba ɗaya, ludayin hannunta ya faɗi ƙasa, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” Ta ruga zuwa Inteesar, “Inteesar!” Ta durƙusa kusa da ita tana girgiza kafaɗunta a hankali, “Intee! Ki buɗe ido!” Babu amsa, ta sake kiran sunanta, wannan karon muryarta tana rawa, “Inteesar, don Allah ki buɗe ido!” Amma har yanzu babu motsi, ta ɗaga kanta ta kalli Daddy cikin tsoro, “Alhaji, me ya faru?” Daddy ya buɗe baki, amma muryarsa ta ƙi fitowa, “Haleema…” Ya haɗiye yawu da ƙyar, “Kira…” Ya yi shiru yana ƙoƙarin samun ƙarfin magana, “Kira Adam,” Mommy Haleema ta kalle shi cikin ruɗewa, “Adam?” Ya gyada kai, “Yanzu…” Muryarsa ta ƙara rawa, “Ki kira shi ya taho,” ta ɗauki wayarta da hannayen da ke rawa, “Me ya faru, Alhaji?” Daddy ya lumshe idanu, “Ahmad…” Kalmar ta fito daga bakinsa da ƙyar, Mommy Haleema ta tsaya cak, “Ahmad?” Daddy bai iya ci gaba ba, hawayen da yake ƙoƙarin riƙewa suka taru a idanunsa, “Accident…” Mommy Haleema ta rufe bakinta da hannunta, “Ya Allah…” Ta fara kiran Adam cikin kuka, “Adam… ka taho gida yanzu!” Muryarta tana rawa, “Ka taho da sauri… don Allah,” a ɗayan ɓangaren, Adam ya fara tambayar abin da ya faru, amma Mommy Haleema ba ta iya bayyana komai, “Ka zo kawai!” Ta katse wayar, sai ta koma kusa da Inteesar, ta riƙe hannunta cikin nata, tana shafa shi a hankali, kamar tana ƙoƙarin dawo mata da nutsuwarta ta hanyar taɓawa, hawaye suka fara zuba daga idanunta, Daddy kuwa ya zauna a gefen sofa, hannayensa biyu a kan kansa, carbin da ya zube a ƙasa yana nan a warwatse, gidan da ya saba cika da dariya… gidan da kullum yake cike da muryoyin iyali, barkwanci da fara’a… ya yi shiru, shiru mai nauyi, shiru mai firgita, shiru wanda babu wanda ya san abin da zai biyo bayansa.