Chapter 36
by @barista
BIYU A ƊAYA
( Don't judge a book by its cover)
Page 36
Sayyada barrister
***
YOTA 13
The five ink legends
Ta yi tagumi tana tunanin rayuwarta, daga wannan sai wancen, abubuwa da dama suke faɗo mata cikin ranta, tana da tarin tambayoyi amma ta rasa wanda za ta yi wa, duk bautar da ta ke yi wa ALAJA bata gani ba, ta ke ƙoƙarin aura mata Abraham. Mutumin da ba shi da cikakken hankali duk ya fita hayyacinsa saboda shan barasa, to yanzu kuma da wannan abin ya faru wane irin zama za a koma sakaninsu da Alaja. Tana so ta yi magana da Mamanta amma ba hali, wayarta tana gida, kuma a kashe ba lallai ne Mamanta ta buɗe ta ba...
"Angel"
Ta ji muryar Uncle ya kira sunanta, a hankali ta ɗago ta amsa da
"Na'am Uncle"
"Ki rage yawan tunani ko don lafiyar ki"
"To"
"Kowanne ɗan adam yana tare da jarrabawa, babu wanda zai iya gujewa ƙaddarar sa, abu mafi kyau shi ne yadda da ita sannan neman ubangiji ya yaye"
Ta gyaɗa kanta alamun to, sannan ta ce
"Thanks"
Ta faɗa a hankali, sai a lokacin ta ji tana son yin kuka, ta toshe bakinta da hannu tana ƙoƙarin haɗiye kukan, Dr Waahab ya zauna sosai ya ce
"Ki yi kuka ba zan hana ki ba, riƙe shi ma yana illatarwa"
Sosai take kuka, ta jima da sanin rayuwarta a baibai take, ta sadaukar da samun farin ciki. Dr Waahab sai da ya bari ta yi me isar ta sannan ya ce
"Na yi magana da Dr Faisal, wanda ɗakinsa yana kusa da nawa, za ki zauna a bangaren da shi kuma ya dawo nan kafin nan da kwanaki biyu naje mu zauna da Alaja"
Ta tsagaita kuka, ta share hawayenta, a hankali ta ce
"Uncle kuɗaɗen da Alaja take bin Mamata suna da yawa, kada ka ɓata su ta dalilina"
Ya sauke numfashi ya sauƙo ya zauna kan carpet suna facing juna, a hankali ya ce
"Angel kada ki ƙara faɗin haka, koma nawa zan kashe babu damuwa ni dai kawai naga kina farin ciki"
Hawaye suka ciko idanunta, ta ce
"Ban san da wasu kalmomi zan yi amfani wajen gode maka ba, ka yi min abubuwan da ba zan taɓa manta wa ba, a duk lokacin da zan bada tarihin rayuwata da sunanka a ciki"
A hankali ya lumshe idanunsa na wani lokaci sannan ya buɗe su, ya zuba mata su yana jinta har cikin ransa, tabbas yaso Angel ba tare da yasan ita ce Bilqees ba, ya kyautata Bilqees ba tare da yasan cewa ita ce Angel ba, amma a lokacin da ya fahimci su ɗin mutum ɗaya ne yaji wani sabon yanayi tare da shi, tabbas zai auri Bilqees yana ji a jikinsa ita ce rayuwar sa..
"Za ki iya bina Nigeria a matsayin matata?"
Ta ɗan waro idanuwa waje, duk da ba ta yi mamaki ba, tun da ya furta agaban Malliman amma tayi tunanin kawai ya ceceta ne daga auren Abraham, bata yi tunanin har ta kai ya aure ta ya tafi da ita ƙasar sa ba...
"Ko ba ki so?"
Ta sudda kanta ƙasa ta kasa magana, ya ɗan yi murmushi kunya ce ta kamata, ya ci gaba da cewa
"Komai zai zo ƙarshe, ki ci gaba da yin addu'a"
"To"
Ta faɗa...
Aka yi nocking ya bada izinin shigowa, ya mik'e ya dawo ɗaki ya tadda Dr Faisal ne, ya iso tare da cewa
"Har ka shirya?"
"Eh to amma ya za ayi ne? Ka ce Bab da yarinyar nan za su zauna to abin karyawa fah?"
"Ka yi musu order"
"An gama sir"
"Ga card nawa a cire duk abin da zai ishe su"
"Haba Sir muka ci da wasu ma balantana bakin mu"
"Kai ka sani"
Dariya Dr Faisal ya yi, Dr Waahab ya ce Angel ta fito, a lokacin da Dr Faisal ya kalleta ya gane ta, da mamaki yake bin ta da kallo ta ce
"Barka da safiya"
Ya amsa da
"Barkan ki dai da fatan an tashi lafiya"
"Alhamdulillah"
Ba ta sake cewa komai ba, Dr Faisal ya yi mata jagora zuwa side nasu tana riƙe da kayanta wanda Dr Waahab ya saya mata, suna isowa Dr Faisal ya ce da matarsa ga tanan su zauna zai aiko musu da abinci, Bilqees ta zauna, shi kuma ya dawo ɗakin Dr Waahab ya tadda yana kan shiryawa sai da ya kammala suka fito, Dr Faisal ya wuce ALAJA restaurant don yin breakfast sannan ya yi wa su Bilqees order....
Shiru babu hira sakanin Bilqees da matan Dr Faisal, a haka ta dinga janya da hira da kaɗan kaɗan har ta saki ranta, sai dare Dr Waahab ya dawo, ya yi musu siyayya, ya bai wa Dr Faisal ya kai musu, ya karɓa ya kai, zuwa wannan lokacin Angel ta saki jiki da matar Dr Faisal wacce har wannan lokacin bata san sunanta ba, da Aunty take kiranta...
Dr Waahab ya kira Dr Faisal a waya ya ce ya faɗawa matarsa ta turo masa Angel, ta faɗa mata, jiki a sanyaye ta shigo side na Dr Waahab yana zaune a palour yana danna waya da sallama ta shigo ta, ya amsa ta zauna kan carpet, hakan yana nuni da tana girmama shi, cikin sanyin murya ta ce
"Sannu da zuwa Uncle"
Ya sauke numfashi tare da cewa
"Bayan azo mu gaisar ma sai dana roƙa"
"Ka yi hakuri"
Ya ɗan yi murmushi ya ce
"Gobe kada a ƙara"
"In sha Allahu"
"Da fatan ba damuwa"
"Eh babu"
"Yayi kyau, na je wajen yaranki yau"
Ta ɗan dube shi tare da cewa
"Su Aicha?"
"Eh"
Ta yi farin ciki daman tunanin su take ta yi cikin ranta, ko ya suka ji kwana biyu da bata je ba...
"Sun tambaye ki ma, na ce za ki zo"
"Na gode Uncle"
"You deserved it"
Ta sudda kai ƙasa, ya ci gaba da cewa
"Kin chanchanci ayi miki komai"
"Na gode"
"Kun ci abinci?"
"Yanzu za mu ci ka yi kirana"
"To tashi kije ku ci ko"
"To"
Ta mik'e ta fice ta bar shi yana murmushi, Dr Faisal ya shigo ɗauke da ƙaton duvet yana ɗan magana ƙasa² Dr Waahab ya shigo ɗakin tare da cewa
"Cewa aka yi maka nan babu abin rufuwa ne"
Dr Faisal ya turo baki ya haye kan bed tare da cewa
"Allah ba zan kwanta a ƙasa ba"
Girgiza kai Dr Waahab yayi ya hau kan bed ya kwanta daga gefe ya ce
"To waye ya ce ka kwanta a ƙasa?"
"Oho"
Ya faɗa ya lulluɓe jikin sa yana shaƙar kamshin turaren dake jikin, Dr Waahab ya ce
"Kada dai ka suma min"
"Turare Beb ta feshe shi saboda nayi ta tuna ta har nayi bacci"
"To sannunku masoya"
"Wai Sir na tambaye ka mana"
"Za ka iya tambaya ta akan komai da kasu son sani banda akan wannan yarinyar"
"To na yi shiru daman akan ta ne"
"Bani da amsar tambayoyi a yanzu, don ko kaina har yanzu ban baiwa amsa ba"
"Kana cikin ruɗani kenan"
"Eh"
"Ka zauna ka yi nazari"
"Haka ne"
Suna hira a haka bacci ya ɗauke su....
*******************
WASHE GARI
Sanye take cikin riga iya gwiwa da wando ta yi kyau ta yafa mayafin kayan, pitch color, jiki a sanyaye ta fito zuwa ɗakin uncle, bayan Dr Faisal ya sanar mata yana nemanta. A hankali ta turo ƙofar ta shigo tare da yin sallama ya amsa, yana tsaye gaban mirror ya shirya cikin ƙananan kaya, sun yi masa kyau yana ɗaure wrist watch nasa, suka haɗa ido ta cikin madubi, ta yi saurin sudda kai ƙasa, ya feshe jikinsa da turaruka masu sanyin ƙamshi, ya juyo gare ta, ya tako zuwa inda ta ke tsaye ya ɗan matso kusa da ita ya ce
"Yau ba gaisuwa kyakkyawar Aunty"
Ta ɗago ta kalli fuskarsa, taga ya ƙara kyau, ƙamshin Uncle na musamman ne, cikin sanyin murya ta ce
"Barka da safiya Uncle"
"Barka Angel, mu tafi ko?"
Ta ɗan waro fararen idanunta tana kallon sa tare da tambaya ɗauke kan fuskar ta ina za su je...
"Wajen abokan mu mana"
Ta sudda kai ƙasa tana murmushi dimple nata ya lotsa, ya kurawa ramin idanu, abin yana burge shi a hankali ya kai ƙaramin yatsansa kan ramin, ta tsaida murmushi suna kallon junansu, a hankali ya furta
"Ki ci gaba da murmushi"
Za ta sunkuyar da kanta ya yi saurin ɗago da haɓarta ya ce
"A'a"
Yana girgiza kansa, alamun kada ta yi, yana buƙatar kallon fuskar ta, Angel kwarjininsa, ya cikata jikinta ya soma rawa, za ta yi baya ya sake girgiza mata kansa alamun kada ta yi, ta tsaya kamar an shukata, a hankali ya sake cewa
"Yi murmushi"
Ta yi kamar yadda ya ce, dimple ɗin ya sake lotsawa, a hankali ya furta
"Me kyau"
Ta yi saurin juyo masa baya tana sauke numfashi, bata taɓa jin wannan yanayin ba...
"I'm sorry, mu tafi ko"
Ta yi saurin fitowa, sannan ya fito suka wuce wajen yaran, suka tadda suna wasa, suna ganin Uncle tare da wata suka zuba musu idanu da mamaki, Dr Waahab ne ya iso kusa da su ya zauna kan dakali tare da cewa
"Kun gane ta?"
Suna ta kare mata kallo kamar sun gane kamar basu gane ba, Aicha ta ce
"Tattawan (kyakkyawar) Aunty"
Da mamaki suka sake baki, aiko da gudu suka rungume ta, tabbas ita ce duk da tana rufe fuskar ta, ko a lokacin da su kaga fuskar ba sosai ba, yau Kyakkyawar Aunty babu niqabi, sai murna suke yi da kyar ta iya cewa
"Ku cika ni kada ku kadani"
Muneefa da Haneef suka ce
"Ita ce"
Sai murna da tsalle suke yi, ta shafa kansu tare da cewa
"Mu zauna"
Suka zauna, sai dai bata zo musu da komai ba, don bata da kuɗi jakarta na gida, Uncle ya saya musu BOBO da biscuit ya raba musu suna sha suna murna, basu jima ba, suka dawo cikin hotel, sai da ya tabbatar ta shige cikin ɗakinsu Dr Faisal sannan ya juya ya fice ya bar cikin hotel ɗin.
****************
Nocking ƙofar su ya yi, matar Dr Faisal ta bude taga shi ne, suka gaisa yake tambayar ta, Bilqees ta ce tana ciki bari ta yi mata magana, ta koma ta yi mata magana ta fito, ya kura mata idanu, tare da cewa
"Jiya na dawo da daddare ba ki fito mun gaisa ba, haka ma yau da safe har na fice ba ki shigo ba"
Cikin sanyin murya ta ce
"Jiya na yi bacci da wuri, yau da safe kuma na fito ƙofanka a rufe"
"Haka ne, da fatan ba damuwa"
"Babu"
"Ok zan je wajen ALAJA yanzu"
Ta kura masa idanu kamar tayi ƙwalla ya ce
"Da fatan ba za ki yi bacci ba har na dawo?"
Ta gyaɗa masa kanta alamun eh, ya sauke numfashi ya juya ya bar wajen kai tsaye ALAJA SPECIAL RESTAURANT ya nufa, ya iso a lokacin su Dr Faisal suna cin abincin dare, ya wuce Corido ya zauna har lokacin da Alaja tazo giftawa ta ganshi zaune ta iso tare da cewa
"Ah Yallaɓai likita barka da dare"
Da mamaki yake dubanta kamar ba ita ce su ka yi baram baram ba, ta zauna duk da bai amsa mata ba, ta ci gaba da cewa
"Kai ne tafe?"
"Eh ni ne, ya aiki"
"Sai godiya"
"Nazo biyan kuɗin da kike bin Maman Bilqees"
Ta washe baki tana cewa
"To madallah, bari na dubo list ɗin"
Ta mik'e ta shige ɗakin ta bata jima ba ta fito ta miƙa masa, ya duba yaga yawansa bai kai yadda yake tunani ba, ya tura mata kuɗin, ALAJA kamar ta tashi sama, ji ta yi kamar ta taka rawa, ya sauke numfashi ya ce
"Daga yau bana son jin wani abu mara dad'i game da Angel, kamar yadda kika ce ta ƴantu to ki bar ta ta sharara ta samu nutsuwa"
Ta sauke ajiyar zuciya ta ce
"Haka ne amma za ta dawo aikinta"
"Ba za ta yi aikin ba, ta gama aiki anan restaurant ɗin, tun da ba ki dubi ƙoƙarinta kin jinjina mata ba"
"Yallaɓai likita wannan abin da ya faru duk laifin Mamanta ne, mace ce me taurin kai da kafiya...
Ya ɗaga mata hannu tare da cewa
"I didn't asked you about her"
Ta ja bakinta ta yi shiru, ya ci gaba da cewa
"Kamar yadda na faɗa ba za mu wuce 3 weeks nan gaba ba za mu koma ƙasar mu, immediately muna isa zan turo iyayena neman aurenta"
"To ba matsala Yallaɓai, duk yadda kake so haka za'ayi"
"Na hakura da aikin da za ta yi min ta zauna a gida, duk abin da ya dace zan yi"
"To Yallaɓai likita gaskiya kayi ƙoƙari ka kafa tarihin da tun da na buɗe Tumbin Giwa ba ayi irin sa ba"
Bai ce komai ba ya mik'e tare da cewa
"Bana so ɗanki ya kusanci in da take"
"Baka da matsala Yallaɓai likita"
Ya fice ko ta kan su Dr Faisal bai bi ba ya wuce shopping ya lodo mata abubuwan amfanin yau da kullum da kayan sakawa ya dawo hotel ya wuce ɗakinsa...
Angel suna zaune da matar Dr Faisal suna hira ya kira ta ya sanar da ita Dr Waahab yana kiran yarinyar, ta sanar da ita Angel ta yafa mayafi akan doguwar rigar ta, ta fito zuwa side nasa, nocking tayi ya bada izinin shigowa ta shigo, ta tadda shi zaune sanye da jallabiya ruwan madara ta gaishe shi ya amsa, ta zauna ya dubeta sosai sannan ya yi magana
"Ba dai kin kwanta ba?"
"A'a muna hira ne"
"Ok ki shirya gobe zan kai ki gidan ku"
Bata san lokacin da ta yi murmushi ba, shi ma ya yi, ya girgiza kansa ya ce
"Murna kike yi, to za a fasa tafiyar"
Ta ce
"A'a Uncle"
"Eh mana har kin gaji da nan?"
"A'a ina so ne na kalli Mamata"
"Gobe za ki ganta"
"Na gode"
"Mun gama da Alaja kuma na ce kada ta ɗaga muku hankali, sakanin ku yanzu babu rigima"
"Na gode sosai Uncle Allah ya saka da gidan Aljanna"
"Amin ba komai, sannan ba za ki yi aiki a restaurant ba"
Ta ɗago ta dube shi, ya jinjina mata kai alamar eh, ta sauke numfashi ko ita bata son aiki a restaurant amma ya za tayi dole ne sai ta yi ta kula da mamarta...
"Kin yi karatu?"
"Eh na yi"
"Ok ya yi kyau, ki koma ki kwanta zuwa gobe sai na maida ki gida"
"To"
Ta faɗa ta koma side na Dr Faisal suka kwanta shi kuma ya dawo na Dr Waahab yana ta gunaguni ƙasa² Dr Waahab bai ce komai ba, har suka kwanta...
*********************
WASHE GARI
Bilqees ta shirya cikin doguwar riga daga kayan da Dr Waahab ya saya mata, ta yi kyau a kwanaki biyun da ta yi ba tare da ta yi aiki ko fita rana ba, har skin nata yana shaƙi, ta dubi matar Dr Faisal ta ce
"Aunty zan tafi na gode sosai da kulawa"
Murmushi Beb ta yi ta ce
"Ba komai ni ma na gode"
Murmushi Bilqees ta yi ta fito ta tadda Dr Waahab bai fito ba, ta iso ƙofar ɗakin sa kamar ta buɗe amma kuma sai ta dakata ya buɗe ya ganta a tsaye riƙe da ledar kayanta ya yi murmushi gida me daɗi, ta ɗan yi baya tare da cewa
"Barka da safiya Uncle"
"Me zumuɗin zuwa gida"
Ta yi murmushi, ta ce
"A'a"
"Eh mana"
Ya rufe ƙofar suka fito farfajiyar hotel ɗin suka tadda Dr Faisal yana waya, yana ganinsu ya dakata tare da cewa
"Bakuwa har za ki koma?"
"Eh Yallaɓai na gode"
"Ba komai ai"
DR Waahab ya ce
"Zan yi mata rakiya daga cen zan wuce sai mun haɗu"
"Ok ba damuwa, am na ce ba"
Ya matso kusa da Dr Waahab ya yi magana a hankali
"Kuna kama fa sosai, kun dace da juna"
Murmushi Dr Waahab ya yi shi ma ya yi magana a hankali
"Ba za ka ji komai a bakina ba"
Dariya Dr Faisal ya yi ya shige ciki, murmushi Dr Waahab ya yi suka bar hotel ɗin kai tsaye bakin hanya suka nuna ya tara musu mashin guda biyu ya hau ɗaya ita ma ta hau ɗaya ya ce ya kai su Tumbin Giwa...
Suna isowa Bilqees jiki na rawa saboda murna, sai tafiya take tana gaba Dr Waahab yana baya, yana mamakinta yanzu duk wannan rawar jikin akan wannan gidan nasu ne me kamar da club.
Tare suka shigo, har ciki a bakin ƙofar da zata sadasu da side nasu Bilqees ya dakata tare da cewa
"Zan tsaya anan, ki ce da Mama za mu gaisa"
"To bari na faɗa mata sai ta fito ku gaisa"
Ta shige ciki, a palour ta yi sallama Mamanta ta amsa da mamaki suke kallon juna, Bilqees ta iso ta kwantar da kanta a kafadar Mamanta ta sanya kuka, bata hanata ba, ta yi me isarta sannan Mamanta ta ce
"A ina kike a kwanaki biyun nan?"
"Ina tare da Yallaɓai likita, ya ajiye ni a ɗakin matan abokinsa"
"A hotel?"
"Eh Mama"
A hankali ta lumshe idanunta ta sauke numfashi sannan ta buɗe su ta dubi Bilqees tare da cewa
"Me yasa ba ki zo gida ba?"
"ALAJA ce ta ce sai an biya ta kuɗaɗen da take bin mu zan dawo, shi ne Yallaɓai likita ya biya"
A razane Mamanta ta ce
"Ya biya?"
"Eh ya biya"
"Na ji Sadeebaby ta ce Yallaɓai likita ya furta zai aure ki wa Malliman, har ya ba shi damar ya turo iyayen sa"
"Eh Mama, haka ne"
"Da gaske ya faɗa ko kuma so yake ya hana Abraham auren ki"
"Da gaske ne, amma Mama me yasa ba ki hana ALAJA haɗa aure na da Abraham ba?"
Kirjin Maman Bilqees ya buga, bata ce komai ba, Bilqees ta ci gaba da cewa
"Mama ashe babu wata dangantaka tsakanin mu da Alaja, mu su waye ne? Ina ƴan'uwanmu? Me yasa muke cikin wannan gidan? Ina dangin babana? Ina danginki? Me yasa muke ƙarƙashin ALAJA?"
Shiru Maman Bilqees bata ce komai ba, a hankali ta numfasa ta ce
"Waye ya kawo ki?"
"Tare muke da Yallaɓai likita yana bakin kofa ya ce za ki gaisa"
"Menene sunansa daga ina yake?"
"Daga Nigeria yake, sunansa Abdulwahab Waseem KIRAWA"
Wani irin faɗuwar gaba ne ya ziyarci zuciyar Maman Bilqees, ta waro idanuwa waje tana kallon ƴarta a hankali ta furta a wane gari yake a Nigeria?"
"Maiduguri"
"Maiduguri!"
Cewar Maman Bilqees tana waro idanuwa waje, Bilqees ta ce
"Eh amma Mama ba za ki sani ba sai dai ya faɗa miki, ni ma a ID card nasa na gani da tun kwanaki"
A hankali gumi ya soma zubarwa Maman Bilqees shar³ har Bilqees ta ce
"Mama mutumin kirki ne"
"Yana ina?"
"Yana waje"
Ta mik'e da sauri ta ɗauki mayafinta ta fito...
Ayi hakuri da typing errors.
Comment and share fisabilillah