THE TRAGIC TRUTH
*ƘADDARAR ZUCIYA*
*CHAPTER FOUR: 4*
*THE TRAGIC TRUTH*
*JIDDAAH BARKUM*
———
Adam yana tuƙi da mugun gudun da bai saba yi ba, hannayensa biyu sun manne da sitiyarin motar, idanunsa a kan titi, amma hankalinsa yana can gida, a duk lokacin da ya tuna muryar Mommy Haleema cikin kuka, sai ƙirjinsa ya ƙara bugawa, “Ka taho da sauri…” Wannan kalmar ta ci gaba da maimaituwa a cikin kunnuwansa, tana ƙara tayar masa da hankali, ya matse sitiyarin sosai, sannan ya lumshe ido na ɗan lokaci kafin ya sake buɗe su, “Ya Allah, ka sa ba wani babban abu ne ya faru ba…” Ya furta cikin raɗa, sannan ya ƙara taka accelerator, a gefensa, Abubakar yana zaune shiru, bai iya cewa komai ba, hannunsa ɗaya yana riƙe da wayarsa, yana ta ƙoƙarin kiran Mommy Haleema, amma duk lokacin da ya kira ba a ɗaga ba, sai zuciyarsa ta ƙara tsorata, ya sake duba screen ɗin wayarsa, sannan ya sauke numfashi mai nauyi, “Yaya Adam…” Ya kira cikin sanyin murya, Adam bai ɗauke idanunsa daga kan hanya ba, “Hmm?” “Do you think Inteesar is okay?” Adam ya yi shiru na ɗan lokaci, tambayar ta fi ƙarfin amsar da yake da ita, ya haɗiye yawu, sannan ya ce, “In Shaa Allah, za ta kasance lafiya,” ya yi ƙoƙarin sanya nutsuwa a muryarsa, amma hannayensa da suka ƙara matse sitiyarin sun nuna irin fargabar da yake ciki, Abubakar ya juya kansa ya kalli gefen titi, “Ya Allah, please…” Ya furta a hankali, “Whatever happened, please let them be okay,” babu wanda ya sake magana, sautin injin mota kawai ke cika tsakaninsu, yayin da kowannensu ke fama da nasa tunanin, cikin ƙasa da mintuna goma, Adam ya shigo harabar gidan, ya take birkin motar da ƙarfi, motar ta tsaya, Adam da Abubakar suka buɗe ƙofofin motar lokaci guda suka fito da gudu, amma da suka shiga falon… suka tsaya cak, falon da kullum yake cike da dariya da hayaniya ya rikide zuwa wurin tashin hankali, Mommy Haleema tana durƙushe a ƙasa, tana ƙoƙarin ɗago Inteesar da ke kwance sumammmiya, “Ya Allah… Inteesar!” Hawaye suna zuba mata ba kakkautawa, a gefe guda kuma, Daddy yana zaune a ƙasa, bayansa a jikin sofa, hannunsa manne da ƙirjinsa yayin da numfashinsa ke fita da ƙyar, “Daddy!” Muryar Adam ta fito da tsoro, ya yi saurin nufar wajensa, amma Abubakar ya riga shi kaiwa, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” Abubakar ya durƙusa kusa da Daddy, yana kallon fuskarsa cike da fargaba, “Yaya Adam!” Ya juya ya kalli ɗan’uwansa, “Taimaka min mu ɗaga Daddy da sauri!” Adam ya kalli Inteesar da ke kwance a ƙasa, sannan ya kalli Daddy, a cikin zuciyarsa, tambayoyi sun taru babu adadi, what happened here? Me ya jawo wannan tashin hankalin? Amma babu lokacin yin tambayoyi, ya durƙusa ya ɗaga Inteesar a hannunsa, “Intee…” Ya kira sunanta cikin rauni, “Ki buɗe idanunki…” Babu amsa, ya sake kiran ta, yana ɗan bubbuga kumatunta a hankali, “Inteesar, can you hear me?” Har yanzu babu motsi, ya ɗan matse ta a jikinsa, tsoro ya bayyana a fuskarsa, “Ya Allah…” A gefe guda, Abubakar da Mommy Haleema suka tallafa wa Daddy, “Ah-ah… ku bar ni…” Daddy ya yi ƙoƙarin miƙewa da kansa, amma ƙafafunsa suka kasa, “Daddy, a hankali,” Abubakar ya faɗa cikin tashin hankali, “Please, don’t stress yourself, mu je asibiti,” Daddy ya kalli Inteesar a hannun Adam, “Inteesar…” Ya kira sunanta cikin raunin murya, amma bai iya ƙarasa abin da yake son faɗa ba, Adam ya sunkuyar da kansa, yana ƙoƙarin ɓoye damuwar da ta mamaye fuskarsa, “Za ta samu sauƙi, Daddy, let’s go to the hospital first,” bai san ko yana ƙarfafa Daddy ne ko kuma kansa yake ƙoƙarin ƙarfafawa ba, ba wanda ya sake cewa komai, a cikin mintuna kaɗan suka shiga mota, Mommy Haleema ta zauna a kujerar baya, ta ɗora kan Inteesar a cinyarta, ta riƙe hannunta tana shafa fuskarta, “Intee… ki buɗe ido,” hawaye suka zubo mata, “Don Allah, ƴata…” Ta ɗan matse hannun Inteesar, “Please, don’t do this to me,” muryarta ta karye, “Intee, Mommy ce,” amma Inteesar ba ta amsa ba, a gefe guda, Abubakar yana riƙe da Daddy, wanda ke nishi sama-sama, Adam ya tada motar, gudu kawai yake yi, duk da yana kallon hanya, hankalinsa yana can baya, yana tunanin mahaifinsa da ƙanwarsa, a yau ne ya fara jin tsoron abin da zai iya faruwa a gidansu, da suka isa babban asibitin da ke kusa, ma’aikatan lafiya suka fito da gaggawa, “Quickly!” “Bring the stretcher!” Cikin ɗan lokaci suka karɓi Inteesar da Daddy, Mommy Haleema ta bi su da gudu, “Doctor! Please!” Ta yi ƙoƙarin bin su cikin emergency ward, amma wata ma’aikaciyar lafiya ta dakatar da ita, “Ma’am, please wait here, we’ll attend to her,” Mommy Haleema ta tsaya, tana kallon gadon da aka kwantar da Inteesar a kai har ya ɓace a bayan ƙofar, ta ɗora hannunta a ƙirji, “Ya Allah, ka kiyaye min ita…” A gefe guda, Adam da Abubakar suka tsaya a corridor, dukansu suka yi shiru, a lokacin ne aka kira Mommy ya shiga wajen Daddy, fuskokinsu cike da tsoro, yayin da idanunsu ke ta bin ƙofofin da aka shigar da mahaifinsu da ƙanwarsu, Abubakar ya yi tafiyar ƴan matakai, sannan ya dawo ya tsaya kusa da Adam, bai iya zama ba, bai kuma iya tsayuwa cikin nutsuwa ba, “Yaya Adam…” Adam ya juyo ya kalle shi, “Hmm?” Abubakar ya ɗan haɗiye yawu, “Me Mommy ta faɗa maka a waya game da Ahmad?” Adam ya shafa fuskarshi da palms dinsa, Abubakar ya sauke numfashi, yana jiran bayani daga dan uwansa, Adam ya buɗe baki zai amsa, amma kafin ya furta kalma— wayar da ke hannun Abubakar ta fara ruri, dukansu suka kalli wayar, lambar Ahmad ce, Abubakar ya latsa answer, ya ɗora wayar a kunnensa, “Hello?” Muryar namijin da ya kira Inteesar ɗazu ta sake bayyana, amma wannan karon muryarsa ta fi yin nauyi, “Hello, sir…” Abubakar ya gyara zama, “Eh, I’m listening,” “Ina son sanar da ku cewa an riga an kwashe mutanen da suka rasu a hatsarin zuwa General Hospital mafi kusa,” Abubakar ya daskare, mutanen da suka rasu? A hankali ya sauke wayar daga kunnensa na ɗan lokaci, yana kallonta kamar yana son tabbatar da cewa abin da ya ji gaskiya ne, sai ya sake ɗora wayar a kunnensa, “Sorry… what did you just say?” Mutumin ya maimaita maganar, “An riga an kwashe mutanen da suka rasu a hatsarin zuwa General Hospital mafi kusa,” Abubakar ya ji wani irin sanyi yana ratsa jikinsa, ya kalli Adam, wanda ya lura da sauyin da ya bayyana a fuskarsa, muryar mutumin ta ci gaba, “Kayan mutanen suna hannun jami’an tsaro na wajen hatsarin,” Abubakar ya ji gumi mai zafi ya keto masa a goshi, ya share shi da bayan hannunsa, amma hannun nasa yana rawa, “Don Allah…” Muryarsa ta fara karyewa, “An gano sunan mutumin da yake tuƙin motar?” A ɗayan ɓangaren aka yi shiru na ƴan daƙiƙu, wannan shiru ya sa zuciyar Abubakar ƙara bugawa, sai mutumin ya ce, “Eh,” Abubakar ya riƙe wayar sosai, “Sunansa Ahmad Mai Tangaran,” numfashin Abubakar ya tsaya, ya lumshe idanu a hankali, “Motarsa kuma baƙar Camry ce,” wannan ya isa ya fada masa Ahmad ne tabbas shine, ya ji kamar an cire masa ƙarfin jikinsa gaba ɗaya, Ahmad Mai Tangaran, baƙar Camry, sunayen da bayanan sun haɗu a cikin kansa, suka zama gaskiyar da yake ƙoƙarin ƙin yarda da ita, ya rufe idanunsa, no… no, this can’t be happening, wayar ta yi nauyi a hannunsa, bai jira mutumin ya ƙara wani bayani ba, ya sauke wayar a hankali daga kunnensa, Adam ya ƙaraso, “Me ya ce?” Abubakar bai amsa ba, ya tsaya yana kallon wani wuri, kamar har yanzu yana ƙoƙarin fahimtar abin da ya ji, “Abubakar!” Adam ya ɗan girgiza kafaɗarsa, “Look at me, me ya faru?” Abubakar ya ɗaga ido ya kalle shi, idanunsa sun cika da ƙwalla, “Yaya Adam…” Muryarsa ta karye, Adam ya kama kafaɗunsa da hannaye biyu, “Speak to me, Abubakar, what happened?” Abubakar ya girgiza kai, hawayen da yake ƙoƙarin riƙewa suka zubo, “Ahmad…” Ya yi shiru na ɗan lokaci, yana ƙoƙarin haɗiye kukan da ya taso masa, “Ahmad ya rasu,” Adam ya janye hannunsa, kamar an buge shi, ya yi baya mataki ɗaya, “Me?” Muryarsa ta fito a hankali, cike da rashin yarda, Abubakar ya share fuskarsa da tafin hannunsa, “Ahmad ya rasu, Yaya,” Adam ya girgiza kai, “No…” Ya furta kalmar cikin rauni, “No, Abubakar, are you sure?” Abubakar ya kalli wayar da ke hannunsa, “Sunansa ne suka faɗa, motarsa ma baƙar Camry ce,” Adam ya buɗe baki, amma babu abin da ya fito, ya juya ya zauna a kan doguwar kujerar corridor, hannayensa suka sauka kan kansa, “Ya Allah…” Ya lumshe idanu, a cikin zuciyarsa, wata magana ta zo masa, Inteesar, yaya za su faɗa mata? Yaya za ta iya ɗaukar wannan? Ya tuna yadda take magana game da Ahmad cikin farin ciki, yadda take sa ran zai dawo da manyansa domin neman aurenta, ta yaya za su je su gaya mata cewa mutumin da take jira… ba zai sake dawowa ba? Adam ya dafe fuskarsa da hannayensa, ya kasa tunanin yadda za su fuskanci wannan gaskiyar, kafin su samu damar yin wani tunani, ƙofar Emergency Ward ta buɗe, wani likita ya fito, ya cire tissue daga aljihunsa ya goge gumin goshinsa, sannan ya kalli mutanen da ke corridor, Adam da Abubakar suka miƙe nan take, “Doctor!” Likitan ya tsaya, “Ku kwantar da hankalinku,” Adam ya ƙarasa kusa da shi, “Doctor, mahaifinmu fa?” Likitan ya gyara gilashinsa, “Mahaifinku ya samu matsananciyar tashin hankali, hawan jininsa ya tashi sosai,” Adam ya haɗiye yawu, “Yanzu fa?” “Mun ba shi magani, jikinsa ya fara daidaituwa, amma yana buƙatar hutu da kulawa sosai,” Abubakar ya sauke numfashi, “Alhamdulillah…” Ya ɗan lumshe idanu, yana godiya ga Allah da mahaifinsu ya fara samun sauƙi, amma kafin ya gama samun nutsuwa, sai ya ɗaga ido, “Ita kuma ƙanwarmu?” Fuskar likitan ta sauya, ya ɗan yi shiru kafin ya amsa, “Ita ce take buƙatar kulawa sosai a yanzu,” Adam ya zuba masa idanu, “Me ya same ta?” “Ta shiga shock mai ƙarfi,” likitan ya ɗan sauke numfashi, “Sumewarta ta samo asali ne daga tsananin firgici,” Abubakar ya kalli ƙofar Emergency, “Amma yanzu fa? Is she okay?” “Ta fara motsi,” likitan ya amsa a takaice, Adam ya ɗan sauke numfashi, “Alhamdulillah,” amma kafin su ji daɗin wannan labarin sosai, likitan ya ƙara da cewa, “Amma…” Dukansu suka sake kallonsa, “Ba ta dawo cikin hayyacinta gaba ɗaya ba,” Adam ya matso kusa, “Me take yi?” Likitan ya ɗan yi shiru, “Tana ta kiran wani suna,” Abubakar ya kalli likitan da damuwa, “Wane Abu?” Likitan ya gyara tsayuwarsa, “Heartbeat,” duk suka yi shiru, Adam ya sauke idanunsa ƙasa, Abubakar ya rufe fuskarsa da hannunsa, wani sabon zafi ya ratsa zuciyarsa, ta ko da ba ta san abin da ya faru ba, har yanzu zuciyarta tana neman Ahmad, “Heartbeat…” Ya maimaita kalmar cikin rauni, “Ya Allah…” Adam ya juya kansa gefe, yana ƙoƙarin ɓoye hawayen da suka cika idanunsa, how are we supposed to tell her? Ta yaya za su gaya wa yarinyar da ta kira Ahmad da sunan da ke nuna yadda yake da muhimmanci a gare ta, cewa ba za ta sake jin muryarsa ba? Likitan ya ci gaba cikin nutsuwa, “Ku tabbatar kun kula sosai lokacin da ta farfado, kada ku ba ta labari cikin gaggawa idan tana cikin wani yanayi na rashin nutsuwa,” Adam ya gyada kai, “Mun fahimta, Doctor,” likitan ya juya ya koma Emergency Ward, Adam ya kalli Abubakar, “Dole ne mu kira dangin Ahmad, duk da dare ya yi,” Abubakar ya gyada kai, “Haka ne,” “Mu nemo lambar babban yayansa,” Abubakar ya ɗauki wayar Inteesar, sannan ya buɗe contacts, bayan ɗan bincike, suka gano lambar, Adam ya ɗauki wayar daga hannunsa, ya yi numfashi mai zurfi, yana ƙoƙarin shirya kansa kafin ya yi kiran, sai ya danna kira, wayar ta fara ringing, a karo na biyu aka ɗaga, “Hello, Assalamu alaikum,” muryar Murad ta fito cikin nutsuwa, Adam ya lumshe idanu, “Wa alaikumus salam, Yaya Murad,” ya daidaita muryarsa, “Adam ne, yayan Inteesar,” “Eh, Adam, na ɗauki murya, gida fa? Fatan kuna lafiya?” Adam ya kasa amsa nan take, ya kalli Abubakar, wanda yake tsaye kusa da shi yana jiran jin abin da zai ce, Adam ya haɗiye yawu, amma ya ji kamar wani abu ya toshe masa maƙogwaro, sai ya ce, “Don Allah, Yaya Murad… ku natsu ku saurare ni,” muryar Murad ta sauya nan take, “Me ya faru?” Adam ya runtse idanu, “An kira wayar Inteesar ne daga wayar Ahmad…” Ya yi shiru na ɗan lokaci, yana neman yadda zai gabatar da labarin, “An ce ya yi hatsari a hanyar dawowa Kano,” Murad ya yi shiru, “Wane irin hatsari?” Adam ya share fuskarsa, “An kai mutanen da suka samu accident ɗin General Hospital,” a ɗayan ɓangaren, muryar Murad ta fito cikin tashin hankali, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” Ya yi shiru na ƴan daƙiƙu, sannan ya sake tambaya cikin murya mai rauni, “Ahmad?” Adam ya kasa magana, Murad ya sake kira, “Adam!” Adam ya matse wayar, “Ku zo General Hospital, Yaya Murad,” muryarsa ta yi nauyi, “Ku zo da zarar kun samu damar tahowa,” Murad ya yi shiru na ɗan lokaci, “Okay… za mu taho,” Adam bai iya ƙara wani bayani ba, ya kashe wayar a hankali, ya tsaya na ɗan lokaci yana kallon screen ɗin wayar, sannan ya sauke hannunsa, wannan shi ne karo na farko da ya kira dangin wani mutum da labarin hatsari, amma bai iya bayyana musu abin da ya faru da cikakkiyar nutsuwa ba, domin shi ma har yanzu yana ƙoƙarin yarda da gaskiyar, Adam ya juya ga Abubakar, “Ka zauna a nan,” Abubakar ya kalle shi, amma bai ce komai ba, “Ka kula da Daddy da Mommy da Inteesar,” Adam ya nuna corridor, “Ni zan je General Hospital,” Abubakar ya gyada kai, “Okay,” Adam ya ɗauki numfashi, sannan ya ƙara da cewa, “Kuma… kar ka bari Inteesar ta ji wannan labarin yanzu,” Abubakar ya kalli ƙofar Emergency, “Ba za mu bari ta sani ba har sai mun san yadda za mu yi,” ya yi shiru, sannan ya sauke kansa, “Wallahi, Yaya Adam, I don’t even know how we’re going to tell her,” Adam ya lumshe idanu, “Ni ma ban sani ba,” ya faɗi hakan cikin gaskiya, “Amma dole ne mu kasance masu ƙarfi saboda ita,” Abubakar ya gyada kai, duk da cewa a zuciyarsa yana jin kamar shi ma yana buƙatar wanda zai ƙarfafa shi, ya kasa ƙara magana, sai yaya adam ya ɗauki wayarsa, “Zan kira Khalil,” ya fara neman layin Khalil, sannan ya danna kira, wayar ta shiga, ta fara ringing, a karo na biyu aka ɗaga, “Hello, Yaya Adam!” Muryar Khalil cike take da damuwa, “Yaya, jikin Daddy? Ina kan hanya, zan ƙaraso asibitin yanzu,” Adam ya lumshe idanu, “Khalil…” Muryarsa ta yi nauyi, “Kada ka zo wannan asibitin,” shiru ya biyo baya, “Me ya faru?” “Juya motarka,” “Where?” “General Hospital,” Khalil ya yi shiru na ɗan lokaci, “Can aka kai Daddy ɗin?” Adam ya sauke numfashi, “Ahmad ya yi hatsari,” “Yaya?” Khalil ya tambaya cikin rashin fahimta, “Wane Ahmad?” Adam ya matse wayar, “Ahmad ɗin Inteesar,” ya yi shiru na ƴan daƙiƙu, sannan ya furta kalmar da yake ƙoƙarin kauce mata tun farko, “Ya rasu,” a ɗayan ɓangaren, Khalil ya yi tsit, ya kasa yarda da abin da kunnuwansa suka ji, sai numfashinsa kawai ake ji, “No…” Ya furta cikin rauni, “No, that can’t be true,” Adam ya rufe idanu, “Khalil…” “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…” Muryar Khalil ta karye, “Ahmad?” Adam ya kasa amsawa, kuka ya taso masa, amma ya danne shi, “Ka nufi General Hospital yanzu, mu haɗu a can,” Khalil bai sake tambaya ba, “In Shaa Allah,” kiran ya yanke, Adam ya sauke wayar daga kunnensa, ya zauna a kan kujerar corridor, hannayensa a kan cinyoyinsa, yana kallon ƙofar Emergency Ward, a cikin zuciyarsa, hoton Inteesar ya bayyana, yadda take dariya, yadda take magana game da Ahmad, yadda farin cikinta ya cika gidan tun bayan da Ahmad ya zo musu, sai ya rufe idanu, how will she survive this heartbreak? Ta yaya za ta iya ɗaukar irin wannan rashi? Adam yayi shiru na ɗan lokaci, ya ɗaga kansa sama, “Ya Allah…” Ya furta a hankali, sannan ya juya ya nufi hanyar fita, a gefe guda kuma, Abubakar ya zauna a corridor, ya haɗe hannayensa a kan cinyoyinsa, idanunsa suka tsaya kan ƙofar Emergency Ward, a can ciki… Inteesar tana fama da rayuwar da ba ta san cewa ta canza ba, ba ta san cewa mutumin da take jira ya isa lafiya ba, kamar yadda ta yi fata, ba ta san cewa muryar da take fatan ji ta sake kira ba za ta sake dawowa gare ta ba, har yanzu bakinta yana motsi, har yanzu tana kiran suna ɗaya, “Heartbeat…” “Heartbeat…” Kuma a wajen ƙofar, ɗan’uwanta yana zaune cikin tsananin baƙin ciki, yana ƙoƙarin nemo ƙarfin da zai taimaka masa ya fuskanci abin da ke gabansa, domin nan ba da daɗewa ba… Inteesar za ta buɗe idanunta, kuma gaskiyar da kowa yake ƙoƙarin ɓoyewa gare ta… za ta jira ta a farkawarta.