Riya

Riya Chap 3

by @001295.2176ade97405411783bc1e628a01ecd2.0018

BAYAN WASU SHEKARU ……. 
 Yarinya ce karama zaune ah bakin runfa irin ta buzayan dajin nan dan ah lokacin da akoy masu yin irin wanan rumfar cikin garin koda koh kana da arziki idan asalin kaneh toh zakayi…….
Yarinya ce da bazata huce 6 year amma girman da take dashi zakace yar shekara 10 ce koh 11 , Dan Yarinyar nada jiki sosai, farace mai matsakaicin farin sanan tanada kananun idanuwa, Zaune take tana wasa da wata yar karamar yar tsana, sai taji ance 
….. Kehh mai baban suna tashi ki tafi gidanku maghrib tayi… ta fada cikin tsokana !!!
 Sai yarinyar tace toh mama barin papa ya dawo 
Mamar ta fada cikin kulawa tace a’a tashi kije kaway gobe kin dawoo, bari Rumana ta Rakaki kan hanya… 
Yarinya da aka kira da mai baban suna ta dawku hidjab dinta ta saka … sanan ta kamo hanya ta baro gidan koh jiran Wace , akace zata raka batayi bah ….. 

Tafe take cikin bakincikin  rai duk da karanci shekarunta tasan tana tunanin, irin abunda zata tarar ah gidan kankar ta ta……
    Riya kenan yar Aziz da Djamila !!! Bayan wasu shekaru da suka yuce mamar su Aziz ta nemi da ya bata Riya ta rike dan a , Cewar tah tana son Yarinyar !!!! Nan kuwa so take ta huce haoushi uwar Yarinyar ah ranta….. 
Bayan Riya Djamila ta kuma haifar wata ya mace aka saka mata suna Naja’atu…
tun wanan lokacin zaman Riya yayi karanci ah gidan su kullin tana gidan kakar ta , da yake Aziz 
yasamu aiki ah Ma’aikatar hakar uraniums inda , Baba sa’idu yake aiki, so bah nisa da gidan su Riya da gida baba sa’idu !!!!!! 

Tunda Riya ta fara dan wayo tasan mai kyau da marar kyau , ta gane cewa kakar ta bata santa..
Dan kiri kiri take nuna mata kyama … 
Dayake yarinyar nada Wayo sosai tasan komai 
Tanasha azaba daga gun kanwar Aziz wato , Autar su dan babu irin dukan da batama riya..

Har ta karaso cikin gidan kankan nata batabar bacin rai da take bah… ta zawna kofar dakin kakar ta da dakin ah kulle, tana kwallon dakin kishiyar kakar ta wato mama ussaina , Tana so taje gurin anty ta Aysha amma tana gudin kar , tsohuwar nan ta isketa… Bata mantawa dukan da tasha watarana akan duk sadda ta kuma ganinta dakin su Aysha saita yanka mata yuwa… 
Tana nan zawne har kakarta ta dawo sanan ta shiga Dakin tayi zawne kan ledar dakin , ga sanyi sosai dan ah lokacin akoy AC !!!!
Jakar ta dan dubeta tace…..
“ Munafuka kin dawo daga munafircin koh ”
Sai tace …. 
    A’a wallahi ganin ammy na naje gida kuma naga Naja !!!!!  … Sai kakar tace 
« Tsusssssss » 
Dan ubanki tashi kije ni ki sayomin icen da zan girka abinci… Ta yurga maka kudin sanan tace 
sawra kitsaye shegen surutu kan hanya kafin ki dawo…. 
ta mike tafita daga dakin… 
Har taje ta sayo icen ta dawo kakar ta na dakin, Tayi tsaye bakin murhun hutar tana tunanin inda zata samo abin kunna hutar, dan koda taje ta fadawa kakar tace mata ta kayo icen cewa zatayi ta dawra mata ruwan zafin tuwo cikin tukunyar !!!!
Ah haka har ta kunna hutar ta , Ta kinkimo wata katuwar tukunya ta dawra kan hutar daje ci … 
ah dedenan Baba Sa’idu ya shigo cikin gidan da sallama … 
« Assalamu Alai’ku » ….
Mama Ussaina dake kofar Dakinta zawne tun dazun dan duk abinda Riya take na kwallon ta , Tace … « wa’alaikum Sallam »…
Ayy da sawri Mamar su Aziz ta futo daga dakinta 
Dan gudan daki 5 ne , Kuma gidan ma’aikata ne bawani girma ne dashi bah , dakin mamar su Aziz shine daki na farko kana  shigowa gidan ah gefen dakinta akoy wata yar store karama ta runfa, toh tata ce sai dakin mama ussaina tanada yara 4 duk manya ne Aysha ce ta fari sai Indo , Da illa sai wasila karamar !!!! 
sanan dakin malama,  dan malamar makarantar uwaye ta unguwar ce , yaranta biyu mace da namiji 
sai daki na karfen gidan dakin mazan gidan ne , 
dakin Bava sa’idu nadaga gefe cen , akoy bayi biyu daya na wanka daya na bayan gida sai kichten daya …. 


Tana karasowa sai tace sanun dazuwa dan ranar ita keda girki … 
Tayi sawri ta karasa bakin murfun nan ta bude tukun yar dan bata so Baba sa’idu yasan Riya ce ta dawra tukunyar, 
Duk irin wahalar da takewa Riya Baba sa’idu bai sani bah dan yana mugon son yarinyar… 
Sai Riya ta karaso kusa dashi tace “Baba !!! 
Sai ya kwalle yace ..
       Na’am uwar masu gida ya kike ya gidan ..
tace … Alhamdulilah Baba , ta dan kwalleshi tayi fadada murmushin ta tana cewa !! Ina abinda nace kah sayamin… Yayi murmushi yace !!! 
Nidai tunda nake ban taba ganin yarinya mai son cin dadi kamar kibah … Tayi dariya mai sauti tace !!  Nidai kaway bani in kah sayomin…
ya saka hanunshi cikin aljuhu ya dawko wata chocolat mai dan girma, ya nuna mata , Takaï hannun kamar zata karba sai ya dawke hanun sa , Tare da chocolate din yace… « bazaki ci chocolate dinnan bah sai kinmin karatun makarantar ku»….   
 ayy da sawri cikin zumudi bema gama karasa maganar sa bah tace cikin muryar ta , mai zaki da yarinta … Alif , Bâ , Tâ, sâ … har zuwa kashe tace toh Dan Allah bani, tana kare shagwabewa yace…..
        ungo nan ta karba da sawri tace , Nagode Baba … cikin farincikin ta … 

haka rayuwa taci gaba da tafiya , yau fari gobe baki, Riya na zuwa gidan su lokaci zuwa lokaci zuwa lokaci ganin papa da ammyn ta sa yar karamar kanwar Naja har lokacin Rumana na gidan su dan ta zama yar Djamila itama … 
zuwa wanan lokacin Riya ta dan kara girma kuma har yanzu tana gidan kakarta   , Kuma babu abinda ya cenza daga tsanar da take mata.. har lokacin nan Baba sa’idu  besan komai bah akan rayuwar da Riya take ah gida bayan ammyn ta , sai sawran kishiyoyin da suke gidan kaway suka sani !!!! 
wata rana ,,  yayar su Aziz baba tazo gidan Da yaran su 3 duk  mata ne dayar karamar sa’ar Riya ce … !!! 
babar yar tace ayi mata kitso hanun amma za’a yi mata kari da na doki …
Duk yan matan gidan na zawne , !!!  
Aysha , Indo wasila yar malama Rayyanatu sai Ayshatuwa autar su Aziz , Riya kuma da Cousin dinta yar yaya baba mai suna mimi suna zawne , ah gefen su !!! indai riya zata hadu da mimi sai sunyi fada kuma ah haka suke abota duk, da busu cika haduwa bah … 
Suna nan zawne anga kitsen nan an kawo ruwan masu zafi za’a saka bakin gashin karin da akayi dan ya kwanta … 
kaway Riya da mimi suka fara fada fada sosai sukayi harda dembe kafin yan mata su tashi rabasu har mimi ta dawku kasar toka ta watsawa Riya , ah jiki 
kaway Riya taji zafin abin nan ta rasa me zatayi kaway ta dawko kasa cike da hannun ta tana ta wasawa mimi ta gama harda yayar ta Hadiza dake rike da mimi !!!!  Daker aka Raba fada dan Aysha rungume Riya tayi tsam ah jikinta … Yarinyar nada wata irin zuciya sosai dan bata jin rarrashi idan ranta ya bace !!!! 
Sai kuma ah lokacin ne matan gidan suka fitu waje dan jin ba’asin meke faruwa ??? 
    
   Ganin Riya a jiki Aysha ga kuma mimi nata lalube, dan idonta cike da kasar da Riya ta zuba mata , ga kuma hadiza kaii  da sabon kitso duk cike da kasa !!!!  sai suka rude suna tambaya meye ya faru…. 
Rayyanatu ce yar mallama ta fada musu komai duk da cewa suma busu cen mafarin fadan ba … yaya baba tace « Toh  koyi hakuri !!!
 mamarsu Aziz ta fara wege wege tana neman abinda zata doki Riya dashi ta rasa … Babu wanda ya lura da ita balle ya hanata kaway saii muyar Riya sukaji ah gefe ta kwalla wani irin ihuuu….!!! tana cewa 
>>> Innalilahi wa’innalaihi raji’un wayo jikina zafi .. Zafi wayo kafata 😭😭😭😭😭 Kuka taje sosai dan ta rude … idon kowa kan hannun malar su Aziz ???
« Ruwa ne !!! Ruwan zafin da aka dafa za’a kwanta da gashin karin da hadiza tayi » 
kowa na yurin ya fara sallalamin yana cewa 
… Innalilahi… Innalilahi 
mamarsu Aziz koh koh dar batayi dan kama hannun Mimi tayi da hadiza sai kanwar hadiza wato Ramatu suka huce daki !!!! 
Aysha kaway ita sai ta fashe da kukan ta tafi da sawri gurin Riya tana tatabata tana kuka … 
tace !! yi  hakuri ummi na sanun sannun … 
Allah yasa ruwan zafin sun fara hucewa , So yurin data kunan bawani sosai bane !!!
Har akayi wanan abu aka gama Allah besa Baba Sa’idu koh Aiz sun sanin bah !!! Amma ammy Riya ta sanin da washe gari ta tafi gidan su sai malar ta taga tana ta , nuku nuku … tace  Ke eo nan ..
Meye ??? sai tace >>  Bakomai, kaway ta cire hijab in yarinyar ta kara ware ido , dan gani take kamar gizo abun take mata … tace Innalilahi 
Rumana dake gefe ta karasu itama ta ware ido tace meue wanan Riya ????
Kaway sai ta fashe da kuka 😭😭 
Yuwan yarinyar duk ya salube dan ana ganin asan wanan yuta ce koh abu me zafi …
gashi konuwar har cikinta da cinyoyinta …
ta cinyar tafi yi mata zafi sosai ..
haka Riya ta fada komai daya faru !!! 
Djamila taji zafi sosai dan batata ba jin haoushi sirikar ta ta ba kamar na yau!!! 
tace kin zawna kiyi kwana biyu sanan ki koma 
Tasan koda tayiwa Aziz magana toh abun da lefin kanta zai dawo kaway tayi shuru.. Ta barwa ranta , Ta tashi tayi Alwala ta shige dakinta yin sallah …



Haka aka cigaba da Rayuwa daga kwanaki, Zuwa satiti kah , Zuwa watan ni , !!!!
     Riya ta warke sosai dan yanzu har school take zuwa … Anty ta Aysha na kulla da ita sosai duk da hattarar da malar su Aziz take mata a cewar ta babu ruwanta da jikar ta …. 
ita koh Aysha koh ah jikinta dan tana son Yarinyar !!! 
haoussawa nacewa rana dubu  ta barawo daya kuma ta me kaya..
wata safiyar litinin Ayshatuwa autar su Aziz ta aiki Riya debo mata ruwansha  , sai Riya tatafi cikin sawri ta dawko ruwa ta kawo , dan ah lokaci ta karatu ne tare da anty ta Aysha !!!
tana shigowa dakin cikin hanzari kaway ta kife ta fadi ah kasa , Ruwan suka zube kan Ayshatuwa gasu da sanyi … !!!!
Riya bata gama gane abinda ya fatu bah dan zaji ciwo ah giwa sosai har ta dan rude !!! Kaway taji mari « Tassssss» takuma kifamata wani marin «Tassssss» … tajawota wajen dakin ta rufeta da duka hakkun kamar ta samu jaka !!! 
da taga dukkan bazeyubah , kaway tah dago kan Riya , ta buga goshinta jikin bangon  dakin su   … 
Sai ga jini na mala lowa daga fuskarta goshin ya dan tsage … 
ah dede nan baba Sa’idu da Aziz suka shigo gidan !!! sawran matan da yan yan su duk suka fito waje …. 
      kowa yayi cirko cirko !!! ga goshin riya na zubar da jini , Baba sa’idu na kwallon Ayshatuwa cikin wani irin yanayi … Aysha na gani Riya cikin halin nan kaway sai ta ruga tah saka hijab dinta 
ta kinkimi Riya ta fita daga cikin gidan ta barsu cikin tsananin mamaki ah tsaye !!!!  
…..    
To be continued….