Zaren Rayuwar Mu

BABI NA ASHIRIN DA HUƊU

by @zainabb

Zaren Rayuwar Mu 

A KWANA A TASHI, su Ahmad suka yi hutun semester. Ahmad ya dawo gida domin yin hutu a gida amma Baffa be dawo ba. Nayi mamaki sosai saboda ba abinda ya saba yi bane. Zama kawai Ahmad yayi nasa waya na kira Baffa. 
    “Me kake a makarantar Baffa? Ahmad fa yace min wani session zaku shiga. To kana iya zaman makaranta har wata uku? Ka faɗa min ma dalilin da yasa zaka zauna makaranta a irin wannan hutun. Ko wanda ba gari suke ba sun je gida bale kai Baffa. Kuma naga makaranta rufewa za'a yi har hostel ɗin ma. Kana ji bana son shashanci ka tattara kayan ka ka dawo gida” Tunda na fara magana har na gama Baffa be ce komai ba. Kashe waya ta nayi tunda nasan yaji abinda nace kuma nasan ze dawo gida. 
Ranar da marece ya dawo gida riƙe da akwatin shi. 

Baffa ya zama wani iri amma ba wanda na kasa ganewa ba. Baya da annuri ko kaɗan akan fuskar shi. Ba kuma fushi ne akan fuskar tashi ba ko jin haushi amma de baya cikin farin ciki kamar wani wanda yake cikin damuwa fuskar shi ta zama neutral. 
Zama nayi daura dashi “Baffa me yake damun ka? Kodai ka je kana soyayya da wata yarinya ne ta karya maka zuciya ne?” na tambaye shi cikin wasa ina ɓoye nawa baƙin ciki da damuwa saboda kawai kar yarana su san abinda yake faruwa a gidansu, tsakanin mahaifin su da mahaifyyar su. 
Baffa be yi murmushi ba, fuskar shi na neutral kamar yadda take yace “A'a Umma. Ina kawai tunanin abubuwan da suke faruwa a duniya ne”
   “Kamar me Baffa?”
“Babu komai Umma” Baffa yace tare da tashi tsaye ya wuce. Da kallo na bi shi na kasa gane abinda yake faruwa dashi. 
Ahmad na shigowa cikin gida bayan ya zauna nazo na same shi ko yasan abinda yake faruwa da Baffa. 
  “Nima na sha tambaya duk lokacin da muka haɗu dashi muna makaranta amma cewa yake babu komai. Idan yaji na takura mishi da tambaya tashi yake ya wuce baya tsayawa saurare na”
   “Kuma baka san ko wani abu ya faru dashi a makarantar ba? Ko dai Baffa ya faɗa ƙungiyar cultism ne kasan irin waɗannan makarantun na Kudu suna da irin waɗannan matsalolin na kungiyoyi amma kuma bana tunanin Baffa yayi wa kanshi irin wannan abu”
“Nima bana tunani Umma. Yana yiwuwa wani abu ne ke faruwa dashi. But i definitely don't know what it is and I can't think of any possible thing. He just change suddenly”
Ban sake cewa Ahmad wani abu ba. Amma nasan zuwan da yayi na karshe kafin wannan ne ya chanjar dashi. Ko dai yaji abinda yake faruwa tsakanina da mahaifin shi?
Ina cikin tunanin abinda yake iya faruwa naji Ahmad yace “Gidannan yanzu....ban san ya zan bayanin shi Umma. Amma baya da atmosphere da yake da irin shi a da. Inaji a jikina duk ya chanja kamar harda mutanen dake ciki. Dan Allah idan har akwai wani abu da yake faruwa tsakanin ki da Daddy, kuyi ƙoƙari ku gyara shi. Gidannan ba haka yake daa ba. It was full of love and peace and mercy and laughter”
Hawaye naji na ƙoƙarin sauko min yasa nayi sauri na tashi daga wurin Ahmad. Duk iya kokarina na ɓoye abinda ya dameni nasan zasu iya ɗago akwai wani abu tunda yanzu gidannan ba yadda yake a da yake ba kuma yarana sun girma zasu iya gane duk abinda yake faruwa. Dole ma zasu gane akwai wani abu saboda idan har mahaifin su yana nan baya kan aiki, a kodayaushe muna tare dashi yana bamu labarin abubuwan da suke faruwa idan yana wurin aiki. Kowa ma yana bada labarin abinda ya faru da abinda yake faruwa a rayuwar shi. Mun kasance wani ƙaramin family masu haɗin kai da jin ƙan juna da murna a kodayaushe. 

Kafin su Ahmad su koma hutun su, watarana Ahmad da Farida sun shiga cikin gari. Baffa na ɗakin su yana bacci saboda Ahmad yace yazo su tafi yace mishi ba ze samu zuwa ba bacci ze yi. 
Har na shiga ɗakin Farida na zauna se kuma na tashi na wuce ɗakin mu. Ina cikin gyara kayana wanda Ahmad ya wanke min dake cikin wardrobe Ibrahim ya shigo. Be tsaya ko ina ba se daura dani a kusa dani sosai. Ban kula shi ba se cigaba da gyaran kayana da nake. 
  “Maryam” ya kira sunana.
Cigaba da gyaran kayana nayi ban amsa shi ba. 
  “Maryam haka zamu cigaba da zama dake a cikin wannan yanayin a cikin gidannan yaran nan na gani? Baki tunanin wannan dabi'un zasu taɓa mana yara? Ahmad har ya gano da akwai wani abu ya min magana mu sasanta kanmu. Dan Allah kiyi haƙuri mu dawo kamar yadda muke”
Hannuwa na na cire a cikin kayana, ina kallon shi cikin idanu nace “Kasan ɗaya daga cikin abinda yafi min zafi akan dukkan wannan abubuwan? Baka yi ƙoƙarin kare kanka ba, baka yi ƙoƙarin cewa baka aikata ba, ka yarda kayi abinda nake tunanin kayi da wata mace. Shine ɗaya daga cikin abu me zafi a wurina”
    “Maryam“ yace tare da ƙoƙarin riƙe hannuwana. Da sauri na janye hannuwana. “Maryam kiyi haƙuri dan Allah Maryam. Wallahi ba zan sake ba sau ɗaya ya faru. Ban san amfanin ce miki a'a ga abinda ya faru da gaske ba kuma kika sani Maryam. Ki duba Baffa yadda ya zama distant a cikinmu. Ba zan ce kiyi haƙuri saboda ƴaƴan mu ba saboda ba su suka haɗa mu ba. Ƙaunar da nake miki ne ta janyo ni a wurin ki har muka yi aure, idan zan baki haƙuri zan baki ne kiyi saboda mu ba saboda ƴaƴanmu ba, amma tunda suna ɗaya daga cikin albarkar aurenmu Maryam, dan Allah kiyi haƙuri saboda soyayyar mu da kuma ƴaƴan da muka samu ta hanyar ƙaunar junanmu”
    “Ko gobe za'a iya deploying naka a wani gari kuma zaka je ka sake yin abinda yafi maka daɗi, Ibrahim. Ni ban san ko saboda wannan abun kake son wannan baƙin aikin soji ba”
   “Kar ki zage aikina Maryam” yace ahankali.
Cikin ɗaga murya nace “Idan na zaga me zaka yi Ibrahim? Zaka sake ni ne? Ka faɗa min abu guda me kyau that comes out of this work. Ba tafiya kuke ana kashe ku ba? Ba tafiya kuke kuna sadaukar da duk wani abu naku ba? Ba tafiya kuke kuna yaƙar ƴan ta'addan da suka fi ku makamai ba? Me kuke dashi Ibrahim? Kayan da kuke sawa se kun siya da kuɗin ku Ibrahim. Bindigar da kake amfani da ita, tun wane lokaci take? Allowance ɗin ka ake baka a lokacin da ya kamata ko kuwa albashin da ake baka wani abun azo a gani ne? Yau idan akace ka mutu, zamu ɗauki lokaci a cikin bariki ba'a tashe mu ba? To menene amfanin wannan aiki? Menene amfanin sadaukarwar ku? Me kuke zuwa kuyi a deployment ɗin ku idan ba zinace zinace ba?”
  “Maryam kece kike magana irin haka?” yace idanun shi na chanja kala 
 “Me zaka yi?”
  “Kina da hankali Maryam? Bana son ki ɓata min rai na miki abinda baki tsammani”
Baffa komawa yayi zaune yana jin duk abinda mahaifan shi ke faɗa. 
  “Me kake iya min idan ranka ya ɓaci Ibrahim? Saki na kawai zaka iya yi amma babu wani abu wanda ka isa ka min. Idan kuma duka na zaka yi, bismillah”
Baffa na jin an faɗi duka ya tashi tsaye. Be tsaya ko ina ba se ɗakin mahaifan shi. 
 “Idan na dake ki, me zaki yi Maryam?”
Hannuna Baffa ya jawo ya maida ni gefen shi. “Umma ce zaka duka? Bayan irin haƙurin da tayi da kuma zama a cikin wannan baƙin cikin da ka sanya mata? Wallahi da nine ita, ko duk duniya na haifa tare da kai se na rabu da kai kuma duk ranar da ka ɗauki hannu domin dukan ummanmu, ni ne na farko a cikin ƴaƴan ka da zasu juya maka baya”
    “Baffa......” na kira sunan shi. Yanzu nasan yasan abinda yake faruwa tsakanina da mahaifin shi. Nasan shine sanadiyyar halin da yake ciki. 
   “Umma dan Allah kiyi shiru”
  “Kin faɗa wa ɗan ki abinda yake faruwa saboda yaci min mutunci?”
Ban san yadda akayi yanayin fuska ta ya chanja nan take ba “Ni zan sa Baffa yaci maka mutunci?”
Muryar Baffa naji ya fara magana “Babu wani abu wanda Umma ta faɗa min. Duk abinda yake faruwa da kunnuwana naji”
Da sauri na juyo ga Baffa na riƙe mishi hannu. Hannun shi ya cire ya fice daga ɗakin mu. Da sauri na bi bayan shi zuwa ɗakinsu.
   “Umma me yasa zaki yarda ki zauna cikin irin wannan baƙin cikin? Baki taɓa zama kanki ba tun lokacin da wannan abu ya faru. Idan ba zaki iya ba, me yasa ba zaki ce ya rabu dake ba? Is it compulsory for you to be married to him? Why don't you go away? You have your reason”
Shiru nayi ina baƙin cikin sanin da Baffa yayi wa wannan al'amari. 
  “Umma dan Allah kar ki ƙarar da rayuwar ki a cikin wannan zaman. Idan ba zaki iya ba ki tafi. Zamu iya kulawa da kanmu. Farida ma zamu kula da ita”
  “Yi min shiru Baffa bana son maganar shashashu. Yi min shiru. Bana son sake jin irin wannan maganar daga wurin ka. Kai ka haɗa ni dashi ne zaka ce na rabu dashi?”
Hawaye ne suka fara zubowa a idanun Baffa wanda ya ba Maryam mamaki sosai. Buɗe idanun ta tayi tana kallon shi “Kuka kake Baffa?”
   “Idan ba zaki iya zama dashi ba ya sake ki ki tafiyar ki Umma. Nasan duka sacrifices naki a wurin mu ba zamu mance ba. Menene amfanin zama haka Umma? Zaki sadaukar da rayuwar ki ne akan abinda be cancanta ba?”
  “Baffa dan Allah kayi shiru kuma kayi haƙuri. Kar mu sake wannan maganar. Bana so na sake jin kayi wannan maganar. Bana son ganinka haka yadda nake ganinka. Ka dawo yadda kake a da mu cigaba da rayuwarmu. Zan ajiye komai a bayan zuciyata muyi haƙuri da junanmu Baffa. If you have to shed tears before you get this, then continue shedding tears but after this, I don't want to see you so distant”
Wurin window Baffa ya tafi ya tsaya zuciyar shi cike da abubuwa mabanbanta. Yana so ya sake wata magana amma baya so ya tunzura mahaifyyar shi. 
  “Idan ka fito kaje ka ba Daddyn ku haƙuri”
Baffa be ce komai ba hawaye suka cigaba da zubowa a idanun shi.

~~~~~~~

Do you know how a child can get affected by his parents fights?