Chapter 37
by @barista
BIYU A ƊAYA
( Don't judge a book by its cover)
Page 37
Sayyada barrister
***
YOTA 13
The five ink legends
Bilqees ta yi kewar gidansu, ta mik'e ta shige ɗaki ta hango tulin birthday gift ɗin da aka bata, ta ƙaraso ciki tana sake dubawa ita tama manta dasu, ta hango envelope ɗin da Uncle ya bata ta buɗe taga kuɗaɗe ne a ciki, a hankali ta furta
"Allah sarki Uncle, ɗawainiya bata yi masa yawa"
Tana buɗe su ɗaya bayan ɗaya tana dubawa...
Maman Bilqees ta baya ta hango shi yana kallon ƙofar gida, yana waya, ta ɗan yi mintina kaɗan sannan ta jiyo ta dawo ciki, ta tadda Bilqees tana duba gift nata, ta ce
"Mama har kun gaisa?"
"A'a, yana waya kuma kaina ke min ciwo shi ne na dawo"
"To bari naje"
"A'a yi zaman ki"
Bilqees bata so haka ba, bai dace ta bar shi a tsaye ba, ta sauke numfashi ta ci gaba da duba gift ɗin...
****
Dr Waahab ya gama wayar sa ya juyo bai ga kowa ba, da farko ya yi tunanin Angel ce amma kuma sai yaga bata nan, har zai juya ya fice yaga an tokare masa ƙofar fita, ya ɗan yi bata ta ce
"Hey handsome man"
Ya ɗaure fuska kamar bai taɓa dariya ba, ta ci gaba da cewa
"Sauƙan yaushe?"
"Ke bani hanya na wuce"
"Kaga ɗakina cen mu je ka huta gajiya, zuwa anjima sai ka wuce"
Ya ɗan ja tsaki, ko kallon inda take bai sake yi ba, ya fice ya bar cikin Tumbin Giwa...
*****
Sai dare ALAJA ta dawo, tun daga bakin gate ake mata gulmar Bilqees ta dawo, tana shigowa ta iso ɗakinsu ta bankaɗa labule tare da cewa
"Ah my Angel ashe ta dawo"
Babu wanda ya tanka mata, tana ci gaba da magana
"Wai fushi ku ke yi da ni ne, to ai komai ya wuce an rigada an raba gardama"
"ALAJA ko an raba ba za ki ga fuska ba, don kin yi mana abin da ba za mu manta ba"
Cewar Maman Bilqees, ALAJA ta ce
"To ke in ba ni SA'ADEEY ba waye zai yi miki kara kamar yadda na yi, shekaru nawa kike riƙe da kuɗaɗena, ban yi magana ba sai wannan lokacin"
"Duk da haka ai na ce zan biya ki ba wai sai kin yi min shela ba"
"Kin ga kada ki ɓata min rai ke kan ki kin san irin halaccin da nayi miki in ba so kike yi na yi suɓul da baka ba"
Maman Bilqees taja baki ta yi shiru, Bilqees ta ce
"Sannu da zuwa"
"Yawwa sannu Angel, Yallaɓai likita ya maida min kuɗaɗena sannan ya ce ba za ki yi aiki a restaurant ba"
"To mun gode"
Cewar Maman Bilqees, Angel ta ce
"Ya faɗa min"
"To sai ku shirya nan da wani lokaci zai turo iyayen sa neman auren Angel"
"Da kamar wuya na aura masa Bilqees"
Da mamaki Alaja da Bilqees suka kalli Maman Bilqees, suna mamakin maganarta, ko me yasa, ALAJA ta ce
"Kada ma ki fara, tun da dai yana so a ba shi kawai"
"Yana da nisa, bana so Bilqees ta bar wannan ƙasar"
"To menene a ciki, don ya tafi da ita, ai za ta kawo miki ziyara"
"ALAJA zan shigo mu yi magana"
"To shi kenan, na wuce ciki"
Bilqees bata ce komai ba har Mamanta ta kwanta, taji wayarta tayi ƙarar shigowar saƙo, ta duba taga Yallaɓai likita ne, ta sauke numfashi ta buɗe...
_Barka da dare Cutie_
Ta mai da masa da
_Barka dai Uncle_
_You didn't sleep?_
_Yeah_
_Ok ɗazu na jira mom bata fito ba har na tafi_
Ta ɗan runtse idanunta na wani lokaci sannan ta tura
_Ya fito kana waya shi ne ta dawo ciki saboda ciwon da kanta ke yi mata._
_Subhanallah Allah ya sawwaƙa, gobe zan dawo da daddare_
_Ok amin_
Shiru bai sake turowa ba har bacci ya ɗauke keta...
**********
"Maman Bilqees ba zai yi ki hana wannan auren ba, tun da nayi alkawarin duk wanda ya biya ni bashin da nake bin ki shi ne mijin Angel"
"Wannan ba hujja bace, ba zan bar Bilqees ta tafi Nigeria ba"
"Dole ki barta"
"Ki je ki sami Malliman ki faɗa masa wannan abin ba zayyu ba"
"Ni ALAJA ba zan je ba, kuma an gama magana yaro zai turo iyayen sa su nema masa auren ta a wajen Malliman"
"Da ta auri wannan mutumin gwanda ta auri Abraham"
"A'a Mama, bana son Abraham kada ki yi haka don Allah"
Cewar Bilqees dake zaune a palourn ALAJA, tun ɗazu ake abu ɗaya Dr Waahab yazo unguwar su ya yi kiranta a waya Maman ta ji, ta tambaye wane ne ta sanar da ita Yallaɓai likita ne yazo shine Maman ta hana, Bilqees ta ce ko ba komai su gaisa ai ya yi musu halacci, fir Maman taƙi sai da Alaja ta shigo ta saka baki, ta fito da Bilqees zuwa bangaren ta Maman Bilqees ta bisu akan ba zayyu Bilqees ta fita wajen mutumin ba...
"Maman Bilqees kin manta tarin kuɗaɗen da ya biya domin ƴarki kuma ki ce ba za ta fita ba"
"Ai don Allah ya yi, kuma mun gode Allah ya bada lada"
Kuka Bilqees ke yi ba don Mamanta ta hanata zuwa wajen Uncle bane a'a cewa da ta yi da Yallaɓai likita gwanda Abraham, ta mik'e tana ƙoƙarin barin palour ALAJA ta ce
"Angel ki je ku gaisa zan yi magana da Maman ki"
"To"
Ta fice zuwa bakin gate ta iso dakalin da Yallaɓai likita ke zama ta tadda shi zaune yana danne danne a wayarsa, ta iso tare da yin sallama cikin sanyin murya, ya ɗago tare da cewa
"Wannan duk jan aji ne?"
Ta sudda kai ƙasa ta ce
"A'a
"To zauna mana"
Ta zauna, still kanta na ƙasa tana wasa da siraran yatsun hannunta, ya dawo kusa da ita sai ƙamshi yake yi, ya ce
"Ba haka na saba ganinki ba, me yake faruwa ne?"
"Babu komai Uncle"
"To ki ɗago mu yi hira"
A hankali ta ɗago ya kalli ƙwayar idanunta da suka rine da hawaye ya ce
"Kuka ki ka yi"
"A'a idanuna ke yi min ciwo"
"Oh sorry, mu je na saya miki magani"
"Mama ta saya min"
"Ok sannu"
Tausayi uncle ya bata, ace mutum kamar sa yake damuwa da rayuwar ta, yana da abubuwan yi, amma yake bari ya zo yaji damuwar ta, me yasa Mama bata son shi? Me yasa ta dage da bata son alaƙar su...
Sauƙan hannunsa taji kan nata, duk da hannun namiji ne amma sai taji da laushi, ta ɗago suna kallon juna, ta kasa jurewa ta sudda kai ƙasa a hankali ya ce
"Angel ba ki son haɗa alaƙa da ni ne?"
Ƙirjinta ya buga, jikinta ya soma rawa, ta girgiza masa kanta alamun a'a, tana ji ya sauke numfashi tare da cewa
"Mama ba ta yi maraba dani bane?"
Ta ɗago tana kallon sa, jikinta yayi sanyi ta furta
"Ta yi"
"Za ki iya rayuwa dani?"
"Kai mutumin kirki ne"
Ta faɗa a hankali, ya sauke numfashi ya riƙe hannunta sosai ya ce
"Ba haka nake nufi ba"
Tana kallon shi, ya ci gaba
"A matsayin matata"
Bakinta ya yi mata nawi kunya ta kamata, ba zata iya amsa masa ba...
"Kina jin tsoro ne"
"A'a Uncle"
Ya fahimci tana jin nauyin sa ne, ba za ta iya jira sosai da shi ba, amma ya zama dole ta saki jiki da shi su fahimci juna, ya kasa gane rayuwarta sai kusan uku yake son haɗuwa da Mamanta amma bata haɗa su ba, ko menene dalili?
"Look at me cutie"
Ta ɗago ya yi magana a hankali
"Ki saki jiki dani da kyakkyawar manufa nazo"
"Uncle kana da kirki"
"Ba haka nake nufi ba, ba zan cutar dake ba, auran ki zan yi, zan cika alkawari"
"To"
Ta faɗa, ya fahimci Angel ba gwana bace ta fannin soyayya, kuma shima haka, kwata kwata bai bawa soyayya muhimmanci ba, sai dai a lokacin da ya faɗa a sonta yake jinsa ya canza ba ki ɗaya, kuma ita ma zai yi ƙoƙarin sauya ta, taji abin da yake ji...
"Ki rufe idanunki"
A hankali ta rufe, ya yi magana
"Wa kike gani?"
"Banga komai ba"
"No ki dai duba"
Tayi ta duba wa cikin duhu ba wanda ta gani, ya ce
"Buɗe"
Ta buɗe, ya yi mata murmushi tare da cewa
"To ni bari na rufe"
Tana kallo ya rufe, tana kallon fuskar sa, ya ce
"Ki tambaye ni, wa na gani?"
"Waye ka gani?"
"Cute, Angel, Bilqees, kyakkyawar Aunty"
Ta yi murmushi, ya buɗe idanunsa suna murmushi, daman haka yake son ganinta, ya sake hannunta ya ce
"Zan koma hotel"
"To Uncle sai da safe"
"Thanks, take care"
"Na gode"
Ta mik'e ta dawo cikin, ya tashi ya iso bakin titi ya tari mashin ya kawo shi hotel...
*************
*Bayan sati biyu*
Alhamdulillah Dr Waahab suna shirye-shiryen kammala training da suke yi, kuma suka soma shirin komawa ƙasar su, sosai yake baiwa Angel time na shi, yawanci su kan haɗu a wajen yara marayu wani lokacin yana zuwa Tumbin Giwa. Duk da Maman Bilqees tana hanata fitowa ALAJA ke sanya baki ta barta.
Kasancewar yau Sunday ne, Dr Waahab yana gida, shi da kansa ya gyara side nasa, ya tsaftace ko'ina sannan ya watsa ruwa ya sanya kananan kaya, sun yi masa kyau musamman yellow rigar da ya saka, yana zaune bakin bed yana gyara wrist watch nasa, watarsa ta yi ringing ya ɗauka ganin sunan Daddyn sa ne ya ce
"Daddy an tashi lafiya"
"Lafiya kalau son, ya shirye-shiryen dawowa"
"Alhamdulillah ina kan yi Daddy"
"To ya yi kyau"
"Ina Mamie?"
"Ga ta nan yanzu ta shigo"
"Ok ka bata na gaishe ta"
"Ah Babangida ana ta shirye shiryen dawowa?"
"Eh Mamie satin sama in sha Allahu"
"To ubangiji ya nuna mana, muna ta kewarka"
Murmushi ya yi ya ce
"Ni ma ina kewarku"
"To ya dawo da kai lafiya"
"Amin Mamie, ina Hauwa"
"Tana kitchen"
"Ok a gaishe da Ammie"
"Za ta ji"
Daddy ya karɓi wayar suka tattauna sannan su ka yi sallama. Dr Waahab ya mik'e ya fito, ya wuce in da suke samun yaran, ya tadda har Angel ta iso, ta yi kyau sosai cikin doguwar riga ta Abaya maroon color, suna haɗa ido ya sakar mata da murmushi, ita ma ta mayar masa, tare da cewa
"Barka da safiya Uncle"
"Ba zan amsa ba"
Ta ɗan waro fararen idanunta ta ce
"Saboda meye?"
"Kin zo har nan ba ki ƙarasa mun gaisa ba"
"Yi hakuri ni ma yanzu na ƙaraso"
Ya zauna ta raba musu Alawa da biscuit, sannan uncle ya sallame su, ya dube ta sosai ya ce
"Na saka yaran a makaranta"
Da mamaki ta tambaye shi
"Wasu yaran Uncle?"
"Abokan ki"
Idanunta suka ciko da ƙwalla, a hankali ta ce
"Ta yaya?"
"Ya kwana biyu naje gidan marayunsu tare da hukuma akan yadda suke barin yara suna nema da kansu bayan sun san cewa marayu ne, ko a sanya su a makaranta ko su daina zuwa bakin hotel...
Ya ɗan yi shiru ganin Angel sarkin tausayi tana hawaye, sannan ya ci gaba
"Sun amince na biya musu komai da komai, sannan na nemi taimakon wasu organisations akan ilimi su tallafa musu har su kammala karatu, a takaice ma an gama komai yanzu"
Ji ta yi babu kamar Uncle a duk mazan dake cikin duniya, a hankali ta sudda kanta ƙasa tana hawayen farin ciki, Yallaɓai likita ya cika mata burin da take da shi akan yaran nan...
"Angel farin ciki za ki yi ba kuka ba"
Ta share hawayenta ta sauke numfashi ta ce
"Uncle na gode sosai"
"Kada ki damu kin ji, ta shi ki yi min rakiya"
Ta mik'e ta yi masa rakiya zuwa babban shop ya dinga siyayya har da tsara, sannan ya yi mata siyayya, suka dawo hotel ta taimaka masa suka shigar ɗakinsa, ya miƙa mata nata siyayyar ya ce
"Ke ma ga naki"
Ta zuba masa fararen idanunta, tana mamaki yadda yake kashe kuɗaɗe ko a jikinsa...
Ya sanya mata ledar a hannunta sannan ya ce
"Kin san menene?"
Ta girgiza kanta alamun a'a, ya ci gaba da cewa
"Nan da next week zan koma Nigeria"
Ƙirjinta ya buga, tana duban sa, zai koma Nigeria shi kenan ta daina ganin Uncle...
"Ba ki ce komai ba"
"Har lokacin komawar ku ya yi?"
"Eh amma zan dawo don ke"
Jikinta yayi sanyi, ta ce
"Allah ya nuna mana"
"Amin, yawwa ban faɗa miki ba, yaran nan ba za su sake zuwa nan ba, ki yi zaman ki a gida, ni zan din ga zuwa muna gaisawa"
Ta jinjina kai, ya yi mata rakiya ta koma gida...
Tana shiga ta tadda ana ƙaramin yaƙi sakanin Zee Dollers da me bakin sigari, sanye yake da gajeren wando da vest ita kuma ɗaura ƙirji tayi Iya zani ne a jikinta, ta yi kansa tana cewa
"Ban ƙi nayi zigidir haihuwar uwata ba, ta ci ubanka mara kunya"
Ya kalle ta sama da ƙasa ya ce
"Idan ban yi miki ciki anan ba shege nake, ki zigidir ɗin muga wa ya fi iskanci"
"Shashasha har ka isa ka taɓa jikina ɗan shaye-shaye irinka"
"Ke ma ƴar ƙwaya ce ai, waye bai sani ba, karuwa kawai"
Tayo tsalle zata faɗa masa Sadeebaby ta riƙo ta tana cewa
"Ki ci gaba da biye masa ya maida ke mahaukaciya, ba ki ga yanayin da yake ciki bane"
"Barni da ɗan iskan nan na koya masa hankali, ya daina shiga harkokina"
"Wacce harka kike da shi, ke kuma Sadeebaby yanzu sai na ɗura miki ashar"
"Ka jima baka ɗura ma, in kafasa Allah ya tsine maka...
Nan dai ƙaramar yaƙi ya koma babba, don Sadeebaby ta karɓi faɗan, nan dai hayaniya ya cika gidan, Bilqees ta gifta ta wuce ciki, ta tadda Mamanta zaune a verender tana yanka danye, ta zauna tare da karɓa ta ci gaba da aikin...
******
Dr Waahab yana zaune a cikin ɗakinsa yana kimtsa kayansa wayarsa ta yi ringing ya duba yaga Ashfat ce, kamar ba zai ɗauka ba, amma ya ɗauka ta yi sallama ya amsa ta ce
"Ya Waahab barka da warhaka"
"Ashfat sannu"
"Ɗazu nake jin labarin lokacin dawowarka ya yi"
"Um haka ne"
"To Allah ya nuna mana, muna nan muna jiran ka"
"Na gode"
"Ba komai yaya, Allah ya nuna mana ranar"
"Amin"
"Bye Yayana"
"Thanks"
"Take care"
Ta faɗa ta kashe wayar ya zubawa wayar idanu, sannan ya ajiye wayar...
______________________
To fah ku shirya lokacin komawar mu ƙasar mu tayi da fatan kun fara shirye-shirye. Ni kam babban bacco na samu sai loda kayan abincin ALAJA SPECIAL RESTAURANT nake yi na yo tsaraba wa cikina😂 babu a house😂😂
To ma sha 🥰 a ci gaba da hakuri da typing errors zan iya ce muku yanzu za mu shiga kan labarin BIYU A ƊAYA kai tsaye in sha Allahu
Comment and share fisabilillah