FACING THE DESTINY
*ƘADDARAR ZUCIYA*
*CHAPTER FIVE: 5*
*FACING THE DESTINY*
*JIDDAAH BARKUM*
———
Tafiyar tsawon kilomitoci kaɗan daga Katsina zuwa General Hospital ta yi wa Adam tsayi kamar ta shekara guda, duk da cewa dare ya yi, kuma babu yawan cunkoso a hanya, tafiyar ta masa nisa fiye da yadda ya zata, hannayensa suna kan sitiyarin motar, amma hankalinsa ya yi nisa da inda yake tuƙi, zuciyarsa cike take da ɗaci, damuwa da fargabar abin da ke jiransa a gaba, duk lokacin da tunanin Ahmad ya faɗo masa a rai, sai ya ji wani irin nauyi ya sauko masa a ƙirji, Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, ya maimaita kalmar a cikin zuciyarsa, yana ƙoƙarin danne damuwarsa ta hanyar ambaton sunayen Allah, ya san cewa mutuwa ƙaddara ce da babu wanda zai iya tserewa daga gare ta, amma sanin hakan bai sa karɓar wannan labari ya zama mai sauƙi ba, musamman idan wanda ya rasu matashi ne, mai rayuwa a gabansa, mai burin gina rayuwarsa da kuma iyalin da yake fatan kafa wa, Ahmad ma yana da irin waɗannan burukan, amma yanzu… komai ya tsaya, Adam ya sauke numfashi mai nauyi, sannan ya ɗan gyara zamansa, “Ya Allah, ka ba mu ƙarfin zuciyar karɓar wannan ƙaddara,” ya furta cikin raɗa, kafin ya ci gaba da tuƙi, da ya isa babban asibitin, ya datse birki a parking lot, inda ya hango motar Khalil har ta riga ta faka a wajen, ya kashe injin motar, ya zauna na ƴan daƙiƙu yana kallon gabansa, ya san cewa daga lokacin da ya fito daga motar, ba za su sake kasancewa kamar da ba, domin a wannan daren, sun zo ne domin karɓar gawar mutumin da har yanzu zuciyar wata yarinya take jira, ya buɗe ƙofar motar ya fito, Khalil, wanda yake tsaye kusa da motarsa, ya hango shi ya ƙaraso da sauri, fuskarsa cike take da damuwa, amma babu alamun kuka, ya danne komai ne a cikin zuciyarsa, yana ƙoƙarin kasancewa mai ƙarfi duk da irin labarin da ya ji, “Yaya Adam…” Ya tsaya a gabansa, yana ƙoƙarin daidaita numfashinsa, “Yayan Ahmad ya kira ni, ya ce ya kasa samun wayar Intee da ke wajenku, ƴan uwansa sun taso tun ɗazu, sun kusa ƙaraso wa,” ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ƙara da cewa, “Jami’an tsaro suna can suna jiranmu domin su miƙa mana kayansa,” Adam ya jinjina kai a hankali, “Okay,” ya kalli ƙofar asibitin, sannan ya mayar da dubansa kan Khalil, “Muje, Khalil,” ya yi ɗan shiru kafin ya ci gaba da magana cikin murya mai nauyi, “Dole ne mu kasance jarumai a wannan lokacin, our families need us to be strong,” Khalil ya haɗiye yawu, sannan ya gyada kai, “In Shaa Allah,” amma yayin da suke tafiya tare, babu wanda ya yi magana, kowannensu yana fama da nasa tunanin, suna isa corridor na ɗakin ajiyar gawarwaki, wato mortuary, sai ga motoci guda biyu sun faka da sauri a wajen, ƙofofin motocin suka buɗe, Yaya Murad da sauran ƴan uwan Ahmad maza suka fito, fuskokinsu cike suke da damuwa da tashin hankali, akwai wadataccen haske a wajen, wanda ya sa ake iya ganin yanayin fuskokin kowa sosai, wasunsu sun yi shiru, wasu kuma suna ta kallon ƙofar mortuary, kamar suna fatan za a fito a ce musu an yi kuskure ne, amma babu wanda ya ce komai, kowa yana ƙoƙarin haɗiye damuwar da ke cikin zuciyarsa, Murad ya hango Adam, sai ya ƙaraso da sauri ya miƙa masa hannu, Adam ya karɓa, suka yi musabaha cikin yanayin juyayi, Murad ya riƙe hannunsa na ɗan lokaci, idanunsa suna kallon fuskarsa, “Adam…” Muryarsa tana rawa kaɗan, amma ya yi ƙoƙarin daurewa, “Ashe ƙaddarar da ta same mu kenan?” Ya ɗan juya kansa zuwa ƙofar mortuary, sannan ya sake kallon Adam, “Ina Ahmad ɗin yake?” Adam ya matse hannun Murad cikin tausayawa, ya fahimci irin wahalar da ke tattare da wannan tambaya, duk da cewa Murad ya san an yi hatsarin, zuciyarsa har yanzu tana neman wata alamar cewa akwai yiwuwar komai ya zama daban, Adam ya sauke numfashi, “Yaya Murad, ƙaddara ta riga ta gabata,” ya yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya ci gaba, “Ahmad ya cika a matsayin shahidi, in Shaa Allah, tunda yana kan tafiya ne, yanzu haka likitoci da jami’an tsaro suna ciki, suna jiranmu domin karɓar gawarsa da kayayyakinsa,” Murad ya lumshe idanu, Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, ya furta kalmar a hankali, sannan ya ɗaga kansa sama, “Allah ya jiƙansa da rahama,” “Ameen,” Adam ya amsa, daga nan Murad ya juya ya kalli sauran ƴan uwansa, wasunsu suka sunkuyar da kawunansu, yayin da wasu suka share idanunsu a ɓoye, babu wanda yake son ya zama na farko da zai fashe da kuka, ba don baƙin cikin bai yi musu yawa ba, sai don kowa yana ƙoƙarin ƙarfafa ɗan uwansa, a wannan lokacin, baƙin cikin ya zama nasu baki ɗaya, cikin ikon Allah da dauriya irin ta maza, suka nufi wurin da jami’an tsaro suke domin karɓar gawar Ahmad da kayayyakinsa, ambulance tana jiransu a waje domin ɗaukar gawar zuwa Kano, inda za a shirya jana’izarsa bisa koyarwar addinin Musulunci, kowannensu yana tafiya ne da wani irin nauyi a zuciya, domin duk wanda ya shiga wannan wuri, zai fito da gaskiyar da babu wanda yake son ya gaskata, Ahmad ba zai dawo gida da ƙafafunsa ba.
A daidai wannan lokacin kuma, a wani asibiti da ke Katsina… ɗakin jinyar da Inteesar take ya yi tsit, Mommy Haleema tana zaune a gefen gadon, tana kallon fuskar Inteesar da ke cike da alamun gajiya, Abubakar kuma yana tsaye nesa kaɗan, yana kallon titi ta window ɗin ɗakin, fuskokinsu babu alamun kuka, ba don ba sa jin zafin abin da ya faru ba ne, sai don sun san cewa a wannan lokacin Inteesar tana buƙatar su fiye da kowane lokaci, sun yanke shawarar danne damuwarsu domin su zama garkuwa ga zuciyarta, Mommy Haleema ta gyara zaman Inteesar a hankali, sannan ta ja bargon da ke jikinta sama kaɗan, ta kalli fuskarta cikin tausayi, “Innalillahi…” Ta furta a hankali, “Ya Allah, ka ba ta lafiya,” a gefe guda, Abubakar ya juya daga window ya kalli ƙanwarsa, ya tuna yadda likitan ya ce tana ta kiran suna ɗaya, Heartbeat, ya lumshe idanu, sannan ya sauke numfashi, how are we going to tell her? Tambayar ta ci gaba da maimaituwa a cikin zuciyarsa, amma babu amsar da yake iya samu, a hankali, yatsun hannun Inteesar suka fara motsi, Mommy Haleema ta lura da hakan, sai ta matsa kusa da ita, “Intee?” Ta kira sunanta cikin sanyin murya, Inteesar ta saki wani nannauyan nishi, sannan idanuwanta suka buɗe a hankali, hasken ɗakin ya ɗan haska ta, sai ta lumshe idanunta kafin ta sake buɗe su, ta ɗan yi ƙoƙarin fahimtar inda take, idanunta suka fara yawo a cikin ɗakin har suka sauka kan fuskar Mommy Haleema, “Mommy…” Muryarta ta fito ƙasa-ƙasa, cike da disashewa, Mommy Haleema ta matso da sauri ta kama hannunta, “Inteesar, kina jina?” Ta ɗan shafa hannunta, “Sannu, kin ji? A hankali, you’re safe, my daughter,” Inteesar ta yi ƙoƙarin tashi ta zauna, amma jikinta ya yi mata nauyi, Mommy ta taimaka mata ta kwanta da kyau, “Ki kwantar da hankalinki, Intee, kada ki yi sauri,” amma Inteesar ba ta amsa tambayar Mommy ba, a hankali, hankalinta ya fara dawowa jikinta, sai kuma tunawa da kiran wayar da ta yi kafin ta sume ya faɗo mata a rai, fuskarta ta sauya, ta juya kanta da sauri tana kallon ɗakin, har ta hango Abubakar, “Yaya Abubakar…” Abubakar ya juyo nan take, “Intee?” Ta ɗaga kanta kaɗan, tana kallonsa da idanun da suka fara nuna fargaba, “Ina wayata?” Abubakar ya tsaya cak, ta sake tambaya, wannan karon da sauri, “Yaya, ina wayata? Heartbeat ya sake kira?” Mommy Haleema ta matse hannunta a hankali, “Intee, ki kwantar da hankalinki tukuna…” Amma Inteesar ta girgiza kai, “Don Allah, Mommy, ku faɗa mini…” Ta kalli Abubakar, sannan ta mayar da dubanta kan Mommy, “Mafarki nake yi ko kuwa?” Muryarta ta fara rawa, “Na ji wani mutum yana magana a wayar Ahmad, ya ce sun yi accident…” Ta haɗiye yawu, “Please, tell me it was just a dream,” Abubakar ya juyo gaba ɗaya ya fuskance ta, ya ji kamar zuciyarsa za ta tsage, ya ga irin fargabar da ke cikin idanunta, kuma ya san cewa ƙarya ba za ta iya kawar da abin da ya riga ya faru ba, amma ta yaya zai gaya mata? Ta yaya zai faɗa mata cewa mutumin da ta yi sa’o’i tana jiran kiransa ya rasu? Ya haɗiye wani ɗaci da ya makale a maƙogwaronsa, sannan ya matso kusa da gadon, ya daidaita fuskarsa, ya yi ƙoƙarin sanya murmushi a fuskarsa, “Inteesar, kwantar da hankalinki,” ya zauna a gefen gadon, yana kallonta cikin tausasawa, “Komai yana ƙarƙashin ikon Allah,” ya ɗan yi shiru kafin ya ci gaba, “Jikin Daddy ya tashi, shi ya sa muke asibiti tare da ke, amma yanzu duka kun fara samun sauƙi,” Inteesar ta zuba masa ido, da farko ta yi shiru, kamar tana ƙoƙarin fahimtar maganarsa, sai ta girgiza kanta a hankali, “A’a, Yaya Abubakar…” Hawaye guda ɗaya ya zubo mata ta gefen ido, duk da cewa tana ƙoƙarin daurewa, “Ba maganar Daddy nake yi ba,” ta matse hannunta cikin na Mommy, “Ahmad fa?” Muryarta ta yi ƙasa, “Mutumin da ya kira a wayarsa ya ce sun yi hatsari…” Ta sake kallon Abubakar, “Me ya faru da shi?” Abubakar ya kasa kallonta na ƴan daƙiƙu, ya sauke idanunsa ƙasa, sannan ya sake ɗaga su, “Inteesar…” Ya kira sunanta cikin tausasawa, “Kina da rauni a jikinki yanzu, kuma babban abin da muke buƙata daga gare ki shi ne addu’a da kuma amsar duk abin da Ubangiji ya ƙaddara mana,” ya riƙe hannunta cikin natsuwa, “Rayuwa tafiya ce, Intee, Allah Shi ne ke tsara lokacin da kowanne bawa zai kammala tasa tafiyar,” Inteesar ta zuba masa ido, zuciyarta tana bugawa da ƙarfi, ta san cewa akwai wani abu da suke ɓoyewa gare ta, ta ga yadda Mommy ke kallon Abubakar, da yadda Abubakar yake ƙoƙarin kauce wa idanunta, something is wrong, wani abu ya faru, kuma babu wanda yake son ya faɗa mata, “Yaya Abubakar…” Ta kira shi a hankali, “Look at me,” Abubakar ya ɗaga idanunsa, ta matse hannunsa, “Kana nufin da gaske ne?” Hawaye suka fara taruwa a idanunta, “Ahmad ya rasu?” Tambayar ta fito cikin rauni, amma ta cika ɗakin da wani irin shiru mai nauyi, Abubakar ya buɗe baki, amma babu amsar da ta fito, sai ya juya kansa gefe, wannan kaɗai ya isa ya ƙara tayar wa Inteesar da hankali, “Yaya…?” Muryarta ta karye, “Why aren’t you answering me?” Mommy Haleema ta matso ta dafe kafaɗarta, ta yi ƙoƙarin sanya nutsuwa a muryarta, duk da cewa zuciyarta tana ciwo, “Inteesar…” Ta shafa kanta a hankali, “‘Innalillahi wa inna ilaihi raji’un’ ita ce kalmar da ta dace da mu a halin yanzu,” Inteesar ta tsaya cak, Mommy ta haɗiye yawu, sannan ta ci gaba, “Ahmad ya riga mu gidan gaskiya,” ta ɗan matse kafaɗarta, “Kuma yanzu haka su Adam suna can domin karɓar gawarsa,” shiru ya mamaye ɗakin, Inteesar ta zuba wa Mommy ido, ba ta motsa ba, ba ta yi magana ba, kamar kalmomin sun isa kunnuwanta ne, amma hankalinta ya ƙi fahimtar ma’anarsu, Ahmad ya riga mu gidan gaskiya, ta girgiza kai a hankali, “A’a…” Ta furta cikin rauni, Mommy Haleema ta matso kusa, “Intee…” “A’a, Mommy,” ta sake girgiza kai, wannan karon da sauri, “No… no, that can’t be true,” hawaye suka fara zuba mata, “Ahmad ya ce zai dawo…” Ta kalli Mommy, kamar tana neman ta gyara maganar da ta faɗa, “Ya ce zai dawo next week, ya ce zai zo da manyansa…” Muryarta ta fara rawa, “Ya ce za mu yi aure…” Ta ɗora hannunta a ƙirji, “Mommy, ya ce zai dawo!” Hawaye suka zubo mata ba kakkautawa, jin waɗannan kalmomi daga bakinta ya sa Mommy Haleema ta kasa riƙe nata hawayen, ta jawo Inteesar jikinta a hankali, ta rungume ta, “Intee, my daughter…” Ta shafa bayanta, “Ki yi haƙuri,” amma Inteesar ta kasa karɓar maganar, ta dafe rigar Mommy da hannayenta biyu, tana kuka cikin rauni, “Please, Mommy… tell me this isn’t happening,” ta girgiza kanta a jikinta, “I was waiting for his call, I thought he had reached home…” Ta yi shiru, tana ƙoƙarin ɗaukar numfashi, “Na yi tunanin zai kira ni ya ce ya isa lafiya,” muryarta ta ƙara karyewa, “Ban san cewa…” Ta kasa ƙarasa maganar, hawaye kawai suka ci gaba da zuba mata, Abubakar ya juya kansa gefe, yana share hawayen da suka zubo masa, ya kasa jure kallon yadda ƙanwarsa take karyewa a gabansu, Mommy Haleema kuwa ta ci gaba da rungume Inteesar, tana shafa kanta da bayanta, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…” Ta maimaita cikin rauni, “Kuka ba zai dawo da shi ba, Intee, ki yi masa addu’a,” ta sumbaci kanta, “Allah ya jiƙansa da rahama,” Inteesar ta lumshe idanu, amma hakan bai hana hawayenta zuba ba, zuciyarta ta shiga wani irin zafi da ba ta taɓa jin irinsa ba, kamar an ɗauke mata wani ɓangare na rayuwarta, kamar an rufe ƙofar farin cikin da take tsammanin za ta shiga, a cikin ’yan awanni kaɗan… mutumin da ta yi bankwana da shi cikin murmushi ya zama wanda za ta riƙa tunawa da shi cikin hawaye.
A babban asibitin Malumfashi, Adam da Khalil suna tsaye tare da Yaya Murad a gaban jami’an tsaro, bayan kammala bayanan da suka dace, wani jami’i ya matso kusa da su, yana riƙe da ƙaramin akwati, ya miƙa shi ga Adam, “Wannan shi ne jakarsa, da wayoyinsa,” Adam ya kalli akwatin, na ɗan lokaci, ya kasa miƙa hannu ya karɓa, ya tuna yadda Ahmad ya zo gidan su cikin farin ciki, yana shirin gina rayuwa da Inteesar, yanzu ga kayansa suna gabansu, amma mai su ba ya nan, Murad ya lura da yadda Adam ya tsaya, sai ya matso ya karɓi akwatin tare da shi, Adam da Murad suka riƙe akwatin, kowannensu yana jin wani sabon ɗaci a zuciya, Khalil ya juya kansa gefe, yana ƙoƙarin danne hawayensa, Murad ya ɗaga kansa ya kalli jami’in, “Mun gode sosai,” jami’in ya jinjina kai, “Allah ya ba ku haƙuri,” “Ameen,” Murad ya amsa a hankali, suka ɗauki akwatin, suka nufi wajen da ambulance take, a waje kuwa, an riga an sanya gawar Ahmad a cikin motar gaggawa, Murad ya tsaya kusa da ambulance, ya kalli ƙofar motar na ɗan lokaci, fuskarsa ɗauke da tsantsar jimami, “Adam…” Ya juyo gare shi, “Mun gode ƙwarai da taimakonku da ƙarfin halinku,” Adam ya girgiza kai a hankali, “Ba komai, Yaya Murad, wannan ƙaddara ce ta Allah,” Murad ya sauke numfashi, “Za mu wuce da shi Kano yanzu domin a yi masa sutura kamar yadda addini ya tanada,” Adam ya gyada kai, “Za mu biyo bayan ku, Yaya Murad,” sai ya juya ya kalli Khalil, “Khalil, kira Abubakar a waya ka shaida masa cewa muna kan hanyar Kano yanzu, su kuma su kula da lafiyar Inteesar da Daddy,” Khalil ya gyada kai, “Okay, Yaya,” Murad ya sake kallon ambulance, sannan ya shiga motarsa, sauran ƴan uwan Ahmad suka bi shi, ba da daɗewa ba, motocin suka fara tafiya a jere, suka ɗauki hanyar Kano, shiru ya mamaye su, babu dariya, babu hirar da aka saba yi a cikin mota, sai sautukan injuna da kuma addu’o’in da kowannensu ke yi a cikin zuciyarsa, kowannensu yana fuskantar wannan ƙaddara ne ta hanyar da zai iya, amma dukansu suna da abu ɗaya a zuciyarsu, Ahmad, matashin da ya bar gida yana fatan dawowa, matashin da yake da buruka da tsare-tsare, matashin da bai san cewa wannan tafiyar za ta zama ta ƙarshe ba, yanzu dai… Allah ne kawai Ya san sirrin abin da Ya ƙaddara, kuma ga waɗanda suka rage a baya, rayuwa ta fara ɗaukar wani sabon salo, wani salo mai cike da rashin fahimta, baƙin ciki da tambayoyin da ba za a iya samun amsarsu cikin sauƙi ba.