Furen Zuciya

Chapter 1

by @nasreelml

🌸🌹🌺FUREN ZUCIYA.

 Flower of the heart.


   By Nasreel R.L.

      🤍A hausa love story…….


Chapter 1; 


Riyadh Saudi Arabia.

Wani irin hucin zafi da dakin keyi sakamakon rashin window ko daya, ga wani jarababben yunwa da takejinshi kamar jikinta nacin kanshi yasa Miral mikewa jikinta dayake sanye da wani white cotton sleepwear daya koma creamy brown yayi paci paci a jike da gumi daya sa ya maƙale a jikinta ya fito da Hadadden suffar jikinta. 


Wani layi ne yake dibanta saboda yunwar dake neman hanata neman ma kanta mafita tayi saurin dafa bangon dakin dayake siminti ne kawai babu fenti. Wani irin warin ruma dakin keyi gashi dan karami dan baifi ya dauki mutun daya da kayanshi ba. Babu koda tabarma bare katifa a dakin, wani zanin gado ne daya ji jiki ya yayyage a shimfude dukda bawani fadi ne dashi ba amma ya mamaye rabin dakin. Kasan dakin simintin yadan burma ta wasu yan gurare ga ceiling din wanda ruwa ya dake shi alamun ruwa na zuba ta cikinshi duk ya daddago kamar zai fado kasa.


Dakyar ta samu jirin ya tsaya dukda hakan wani fatsi fatsi take gani. mikewa takarasa yi still hannunta na jikin bangon bata saki ba. 


Doguwa ce ita a cikin mata, dan rigar bata karasa chan kasa ba dukda kuwa full size ne. Batada kiba kokadan dan har wani yawo takeyi a rigan, kirjinta kusan flat yake sai dan tudun da zainuna maka mace ce. Waist dinta so slim tommy dinta is flat kamar wanda bata cin abinci. Hips dinta ne kadai zakace da tsoka dan its wide and nicely shaped saitayi figure 8 shape effortlessly. 


Tanada long oval face dake dauke da manya manyan idanu, eyeballs dinta are a rich shade of brown dayayi enhacing din overall features dinta. Hacinta irin botton nose dinnan ne mai tsawo saidai ba chan chan ba lips dinta are round and medium sized. her face is giving barbie and mulan saboda the eyes makes her look very cute saboda girmansu saidai shape dinsu kuma is upturned ta karshe saiya bata wani fierce no nonsense look dazaka zata irin marasa mutuncin nan ne.


Fatarta dayake mai haske saidai ba chan chan ba irin caramel African glowy skin dinnan. The shade very unique and glowy koda idan kasa ido ka kalla fatar zaka gane bata samun abubuwan dazai gyarata ko ginata. 


Jilbab blue ta dauka da shima ya kode wuyan yadan yage ta nade black curly hair dinta daya sauko har tsakiyan bayanta tasa wani ribon daya gama talewa ta daureshi ta dau wata black cap ta saka sannan tazura jilbab din daya sauka har kasa saidai baija kasa ba ya bayyanar da slender kafafunta dake dauke da zara zaran slim yatsu, faratanta har kyalli sukeyi. 


Kofar dakin ta bude wanda yama sauko daga mazaunin shi saidai ta dagashi gefe ta fita. Long corridor ne gabanta dakinta shine na karshe agurin. Bagu haske kwata kwata a corridor din dan ba windows a bangaren sakamakon duk store rooms ne na ajiye kaya dabasu bukatan iska. Ita kanta dakinta store dinne aka mayar mata dashi daki idan zata kirashi da dakin kenan dan babu koda katifa a ciki. 


Dare ne dan haka gidan tsit bakajin komai sai karan tsintsaye da sautin wakan su ke tashi. Straight part din ta bari ta nufi main part na gidan. Ta kitchen entrance din yake dan haka nan ta shiga kitchen din ya tsaru iya tsaruwa sannan babba ne sosai. Ganin babu kowa a ciki kamar yadda take tsammani yasa ta salallaba a hankali ko takun kafafunta bakaji zuciyanta na bugun uku uku ta nufi wani katon smart double door samsung fridge ta budeshi a hankali.


Fruits ne kala kala a cikinshi sunyi sanyi ga ruwa bottle water a jere a ciki suma sunyi sanyi zuciyanta na ayyana mata karta dauka kada a kamata saidai wani kugi da murdewa da cikinta yayi ya isar mata da sako. Dafe cikin tayi duk wani tsoro na fita daga kanta ganin zata iya mutuwa idan ta zauna haka yasa ta dago tafara daukan abubuwan dazasu kawar mata da yunwar data addabeta.


Apple dayake favorite dinta ta dauka guda daya wanda zata iya irga sonawa a cikin yan shekarun nan taci shi, sai ta hada da banana guda biyu dakuma strawberry biyu ta dauki ruwa guda daya. 


Rufe fridge din tayi tana kallon abubuwan data kwaso, ko kusa bazasu cire mata yunwar dake jikinta da tun jiya da safe babu abunda ya shiga cikinta sai uban Aiki data jibga. Freezer dake gefen fridge din ta bude bayan ta rufe fridge din dan kozataga ragowar abunci. Cikin sa’a saiga wata biryani rice da half chicken a cikin package da alaman takeout ne akayi ordering .

. Ko ba’a fada mata ba tasan na Hanat ne dan ita ta anso mata shi dazu da aka kawo shi delivery. 


Kura ma package din ido tayi tana kallon yanda aka chishi a wulakance, zuciyanta na wani irin ciwo ganin yanda su Hanat suke rayuwarsu yanda sukeso babu wata damuwa bayan ita saidai taci ragowarsu kamar wata mara galihu. Wani murmushin bakin ciki ne ya kufce mata, shin meye marabarta da mara galihun? Masu Aikin gidan sun fita daraja da matsayi. 


Daukar package din tayi hannunta na rawa dukda tanason ta kwantar da zuciyanta ta dauka babu tsoro dan Hanat bazata sake nemanshi ba, batacin abunda ko sanyi yayi bare kuma ace ya kwana. Bazai wuce ma’aikata suci shi gobe ba kokuma a bawa dabbobi. 


Rufe freezern tayi ta juya zata koma dakinta saikuma wata zuciyar tace mata ta tafi laundry room mana yafi dakinta iska. Tasan yanzu kusan karfe 3 ne na dare dan haka tasan Hanat ta kwanta bata wuce 3 na dare. 


Kofar dazata sada ka da main palour ta kitchen din ta bude a hankali ta leka ciki. Duhu na ya sado ta daya tabbatar mata cewa babu kowa dan haka batareda cigaba da sandar datakeyi ba ta shiga tafiya normal ta nufi hanyar laundry room din dake kusan chan karshen falon tana dafa bango dan jirin dake fizgarta. 


Sauke nunfashi tayi tanajin yawunta na tsinkewa rabon dataci abinci lafiyayye bare kuma harda nama ta manta shi, zuciyanta har wani iyo takeyi saboda nishadi. Yau kusan shekaransu biyu kenan a Riyadh tun zuwansu two years ago basu kuma koma GHAIR- MU’ADDAL ba. Tanaso ta tambaya ummi amma tana tsoron masifa, dukda tasan komawar bazata haifar mata da komai ba sai tuna mata wani babi na rayuwarta da batada bukarya tunashi. 


Wani haske ne ya karede palourn dayasa ta datse idanunta dan sam batason haske saidai tuna inda take yasa cikin hanzari ta waro manya manyan brown eyes dinta dake daukeda zara zaran eyelashes dasuka sauka daidai kan Hanat dake mata wani irin kallo kamar zakin dayaga nama. 


Wani baƙin murmushi be ya bayyana akan arab face na hanat, tanada kyau balaifi sannan batada tsawo sosai saidai tanada jiki ba laifi itaba siririya ba bakuma mai kiba ba, saidai tanada bust manya sunso suyima jikinta girma. Tanada irin witch face da kana ganinta kasan bataji, ga yanda tayi da fuska kawai kasan batada mutunci. Gashinta dayake bakikkirin yazubo har tsakiyan bayanta take wasa dashi, hannunta da yasha fake nails kamar zatayi fada da zaki ga wasu rings a jere a yatsunta duka hudu tayi ma Miral alaman tazo da yatsa daya. 


Wani irin bugawa zuciyanta keyi jikinta yafara kyarma kamar wanda aka zubawa ruwan kankara. Lips dinta dake rawa ta bude zatayi magana saikuma ta rufe tama rasa mezatace. Tasan bada hakuri bazai kaita ko inaba duk rokonta dazatayi. 


Tana kallon yanda idanun Hanat ya sauka akan package din abincin kafin ta kara dago idanunta ta sauke su akan face na Miral. Wani bakin ciki ke dirar ma hanat a duk lokacin data kalli fuskar Miral. Face dinta na daya daga cikin abubuwanda ta tsana a duniyar nan. Bataga dalilin da Miral zata mallaki irin wannan kyawu da kallo daya bazakace mutun bace saboda madarar kyau. Sannan duk wanda ta tsaya kusadashi saiya disashe tazama tamkar wata tauraruwa da haskenta ke karuwa kullun akan raguwa. 


Wannan bakincikin yasa batareda tayi wani dogon tunani ba ta daga hannayenta dake dauke da zobuna masu kauri ta kifa ma Miral wani mahaukacin mari da yasa Miral wani irin kara dan saida taji wani abu ya fashe a bakinta. Bata yi wata wata ba ta kara sauke mata wani a dayen side na face dinta wanda saida Miral ta fadi kasa abinci da fruits dake hannunta suka watse a kasan. 


Dafe fuskarta tayi dabama tajinshi a jikinta. Wani irin dau da zugi yake mata ga wani abu nabin hannunta datasan jini ne da ke fitowa daga goshinta daya bugu da kasan,  kunninta yay wani dumm babu abunda takeji daga masifar da Hanat keyi sai kalma daya ‘kaskantacciya’. Wasu hawaye masu zafi ne suka jero daga idanunta suna gauraya da jinin dake fita daga face dinta.


Kafa hanat tasa ta hambareta a hakarkarinta da saida taji nunfashinta ya dauke. Kasa ihu tayi dan azabar daya ziyarceta, dan ciwon da hanat taji mata sakamakon buga mata laptop datayi a daidai gurin ko sati baiyi ba. 


Muryan wata dattijuwa ne ya katse hanat dake Neman cigaba da bugun ta. Wani dogon nunfashi Miral taja jin muryan Ummi, aranta addua kawai takeyi Allah yasa yau ranta ba a bace yake ba ta rabasu da hanat. Karasowa tayi inda suke batada tsawo saidai tanada jiki sosai dan fuskanta a wani chure yake skin dinta wani reddish tana tafiya dakyar tana nunfarfashi jikinta sanye da wani red burgujejen sleeping dress dayaje har kasa.


Daidai inda Miral ke kwance ta tsaya tana bin abincin daya watse a kasa tana kara daure fuska. Miral da jikinta ke rawa tuni ya tsaya chak dan ganin yanda idanun ummi sukayi tasan yau babu sa’a kwata kwata. Yau kashin ta ya bushe yau babu mai chetonta a duniya. 


Kallon yanda ummi ta daura hannu akan kugunta tana mata wani mugun kallo yasa Miral mikewa zaune tana dafe ribs dinta datakejinshi kamar ana zuba mata wutan dalma daga kan gurin har zuwa cikin kirjinta da cikinta. Kasa rike ƙaran daya zo mata makwogwaro tayi cikin zafa ta rufe bakinta da dayen hannunta dan batason wani abu dazai kara harzuka dayansu. 


Hanat ce ta juya ta kalli Ummi da gani bataji dadin zuwan Ummi ba dan tayi niyya cin uban Miral yau, takumasan Ummi bazata barta tayi mata dukan datakeso ba dan zatace tanada aiki gobe karta illata ta. 


“ Meya faru anan daugher?”, Ummi ta tambayi hanat. Kamar wanda take jira hanat ta anshe maganan batareda tajira Ummi takarasa ba a kufule kamar budurwan data kama saurayinta da wata tace “ Ummi wai wannan kazamar yarinyan nan sata tafara? Nadade ina fada miki dama yar iskan yarinyarnan is not innocent tana abubuwa simi simi tasan metakeyi ashe sata takeyi a gidan nan! Yan dauke dauke da akeyi nace miki banga abu kazaba kice maybe nayi misplacing dinsu ne ashe ga barauniyar datake dauka nan. Yau zanci ubanta kuwa”. 


Da fadin haka ta chakuma gilbab na jikin Miral tareda fincikota gaba tahau yi mata ruwan dundu a baya, dum, dum hannu bibbiyu. Miral batayi kokarin matsawa ba dan tasan hakan wani sabon matsalar zaija mata. Inda sabo ta saba da duka saidai sabawar bashi ya hanata jin zafin duka datake mata ba. Hawaye ke fita daga idonta ta rintse su tareda girgiza kanta tanajin yanda dukan ke shiganta har cikin tsakiyar brain dinta. 


Ummi ganin hanat batada niyyan tsayawa yasa ta janyota baya tareda mata alaman ya isa. Umarni tabama Miral akan ta dago idaunta ta kalleta. Jiki na rawa Miral ta dago fuskanta dayake sharkaf da hawaye da jini nabin kusan rabin face dinta daga side dinda goshin ya fashe. 


Wani murmushi Ummi ta saki tana kallon cikin idanuwan Miral dake cike da hawaye sunyi ja jawur. Saurin sauke idanunta Miral tayi ganin irin kallon da Ummi takemata datakasa gane meyake nufi. Alaman ta mike Ummi tamata bata musaba ta mike a sanyaye ribs dinta kamar zasu fizge daga jikinta dakyar ta samu ta tsaya a tsaye tana kara danne ribs din. 


“ cire hijab din malama”, Ummi tafada. Hannu na rawa tayi anfani da hannu daya ta cire jilbab din tana maida kallonta kasa takasa gane meyasa Ummi zatace ta cire hijab. Kodan tanason ganin ko ta dauki wani abune? Tun daga sama har kasa Ummi tabita da kallo kamar yau ta fara ganinta. Idanunta suka tsaya akan kirjinta tawani tabe baki sannan ta karashe kallonta. 


Hanat kamar bakin ciki ya kasheta ganin surar jikin Miral data dade bata ganshi ba dan kullun cikin hijab take. Duk wahala dakuma azabar yunwa da take tabbatar ana mata a gidan amma still jikinta mai kyau ne. Tsaki tayi kawai ta juya fuu tanufi stairs tana hawa bibbiyu tana maganganu ita kadai kamar wata tababbiya. 


Cikin zazzafar murya Ummi tace “ Daga yau idan nasake ji ko ganin irin abunda yafaru yau bazaki so abunda zai faru ba. Miral ni zakima sata a gida? Ni? Meye ban miki bah? Iyayenki sun wurgaki kan titi, ni nice na daukeki na taimaka miki nabaki gata na baki gurin zama, kika ce mun kin dena sata, infact ba cewa kikayi bake kikayi abubuwan dakikayi da ko dabba bazaiyita ga yan uwanshi ba? Cikinsu harda sata shine yau zaki nunamin halinki nanan koh? Toh nima kenan wata ran zama dake zakiyi mun abunda kikayi ma yan uwanki na jini?”. 


Kasa ansa wa Miral tayi jin komai na dawo mata sabo. Nunfashinta na kara karfi kirjinta nawani daurewa tanaji kamar an daure zuciyarta da igiyar dake dauke da kayoyi ana ja. Dafe kirjinta tayi da hannu biyu tama manta ciwon da ribs dinta keyi, kwakwalwanta na neman tunawa da memories dinda ta dade da burne su. Girgiza kai tafara yi kamar tababbiya panic na mamaye ta. 


Wani tsawa Ummi ta sakin mata “ Ba magana nake miki bah? Bude baki ki ansani before i make you regret this”. “ no, no no Miral take maimaitawa tama rasa mezatayi. Saida tadanyi yan mintuna kafin taji memories din na fading hankalinta na dawowa ga Ummi dake mata wani mugun kallo. 


Sauke hannayenta tayi daga kan kunnuwanta, cikin sanyi tafara furta sorry Ummi ta dakatarda ita tana fadin “ rike sorryn ki, bana bukata. Nasan mekike bukata, zamu taimaki juna kinji? Zakiyi mun wata babbar alfarma. Amma yanzu Ki kwashe wannan abuncin dakika zubar ki gyara gurin nan ki wuce ki kwanta kinada aiki gobe ba saurara miki zanyi ba”. Tana fadin hakan ta juya ta hau stairs. 


Kasa ansawa tayi tunaninta ya tafi kan maganan datayi wai zasu taimaki juna. Toh ita metake dashi da zata taimake ta dashi? Ta dade a haka ganin bazata samu ansar tambayan nataba yasa ta dauki jilbab dinta ta mayar tareda bi ta kwashe fruits dasuka watse sannan ta tsugunna inda shinkafar ta watse itama tana kallon yanda ya barbaje gabadaya babu daman ta ci dan idan tasamu food poisoning ba lallai ne a kaita hospital ba gwara yunwa tasan duk yanda za’ayi zata samu ragowar breakfast dinsu hanat gobe.  


Naman kawai ta dauka ta ciccire inda ya taba kasa sannan ta dauki containar tasaka shi a ciki da fruits din ta mike ta nufi kitchen. Kan counter ta ajiye cikin sauri ta chinyeshi duk yunwar datakeji yatafi babu abunda ke yawo a cikin kanta sai maganar Ummi. Shin wani taimako zatayi mata? Meyasa zata sata cire hijab abunda bata taba sata ba? Wani irin kallo ne tabita dashi hakan?