MATAR GIDA PAGE 82
*MATAR GIDA BOOK* 2
*SHUUKRAN*/022
*YOTA ASSOCAITION*
P 82
Anty Aisha bata dauki lokaci mai tsawo ba ta sama masu abin hawa Unaisa na zaune Anty Aisha ta shigo,a tare suka fidda kayayyakin su da babies ɗin Unaisa,daga haka sun shiga mota Anty Aisha na riƙe da baby ɗaya Unaisa na riƙe da ɗaya,sun yi tafiya a ƙallah ta mintina goma tayar motar ta samu matsalah,waje driver ya samu gefen kwalta ya yi parking daga haka ya fara neman masu gyara a ƙallah ya dauki sama da mintina goma tsaya yana waya da mai masa gyara can ya liƙo cikin mota ya kalle Anty Aisha ya ce ''hajiya ku yi hakuri ku fita ku nemi wani,gyarar zata dauki lokaci'' sosai ran Anty Aisha ya ɓaci amma ta daure bata ce komai ba,mayar dubanta ta yi ga Unaisa ta ce da ita su fita,da taimakon driver suka fidda kayayyakin su daga mota,suna tsaye wata motar taxi ta zo har inda suke tsaye,driver motar ya keƙo tare da tambayar su inda zai kai su Anty Aisha ce ta faɗa masa inda za su tafi,sai da suka yi ciniki kafin suka shiga motar,suna cikin tafiya Anty Aisha ta ga driver ya dauki wata hanya,kai tsaye ta ce ''mallam ba ka gane unguwar bane?" hankali kwance driver ya ce ''na gane mana Hajiya hanyar duk ɗaya ce'' Anty Aisha ta taɓe baki kawai bata ce masa komai ba,ita dai Unaisa sai satar kallon babies ɗinta take,daidai juction ɗin gidan Mama mota ta shigo kamar daga sama wata babbar mota ta daki bayan motar cikin ɗan kankanin lokaci motar ta faɗi gefen kwalta nan take ta kama da wuta da wani irin sauri driver ya fito yana ihun neman ceto sosai motar ke ci da wuta driver yana ihu yana faɗin ''jama'a taimako akwai mutane cikin keken mata biyu da jarirai biyu'' cike da firgici da fita hayyaci yake magana cikin ɗaga murya,ganin ɗanyen aiki da ya aikata yasa driver babbar taka mota ya bar wajen da sauri kafin hankalin jama'a ya dawo garesa,sosai mutane dake kaiwa da komowa da wa'inda suka kasa abin sana'a a juction suka yu wajen da gudu cike da tashin hankali suna salati gaba ɗaya driver ya gama fita hayyacin sa sosai ya rikice hakan yasa ya nufi inda jama'a suke da gudu yayin da suma mutanen sun taso da gudu sun nufi inda motar ke ci da wuta,jama'a masu kawo ɗauki suna daf da ƙaraso wajen suka jiyu wata iriyar ƙara kamar tashin bom mota da ke ci da wuta ta yi bindiga sosai motar ke ci da wuta babu yadda za a yi a fidda mutanen ciki saboda yadda wutar ke ci ko da an yi nasarar fitar da su ba lallai su rayu ba,cike da firgice da tashin hankali jama'a dake wajen suke maimaita kalmar innalillahi wa inna ilaihi raji'un wasu ma ƙasa cewa komai suka yi saboda tashin hankali kowa ka gani wajen fuskarsa cike da firgice da tashin hankali wani matashi ne ya yi jarumtar riƙe driver da ya daura hannu a ka jikinsa na rawa sosai yana zare idanu ya ƙasa furta komai sai nuna motar yake da yatsa manuniya,da kyar matashin ya samu ya driver ya amsa masa tambayar da yake masa ''a ina ka dauko passenger shin ko ka san su'' da kyar driver ya iya furta ''ban san su ba ganinsu na yi tsaye bakin hanya da alama daga asibiti suke'' shiru ya yi yana nazari can ya miƙawa matashin wata waya kirar itel ya ce ''daya daga cikin matan ta bani wannan wayar,ina son kiran mahaifiyata sai na ga bana da kati shine na roƙe ta na ce ta ara min wayarta zan yi kira,ta bani wayar kenan na ji mota ta dake bayan motar mu ta baya'' ya kare magana tare da dafe kai a hankali matashin ya kai hannu ya karɓi wayar,cikin sa'a wayar babu password,ba tare da ɓata lokaci ba matashin ya shiga call log nan ya ga wata lamba an yi saving ɗin lambar da Mama,bai tsaya ɓata lokaci ba ya kira layin Mama,Mama na gyaran ɗaki ta ji wayarta ta yi ƙara,Babah Rabi dake zaune gefe saman tafurma ta dauki wayar tare da miƙawa Mama,karɓar wayar Mama ta yi ta amsa kiran,daga ɗaya ɓangaren aka yi sallama jin bakuwar murya yasa Mama cire wayar daga kunnenta tare da duba lambar tabbas lambar Aisha ce Mama ta ƙara wayar kunnenta tana amsa sallamar hayaniyar mutane da ya cika wajen yasa matashin matsawa daga inda mutane suke sai da ya gaida Mama kafin ya ce ''mai wannan layin sun samu hatsari yanzu haka..bai kai ga idah zancen sa ba Mama ta faɗi ta sume,Babah Rabi ce ta yi sauri taro Mama cike da kiɗima ta shiga kiran sunan Mama hannu ta kai ta dauki wayar da Mama ta jefar gefe ta kara wayar kunnenta tare da sallama daga ɗaya ɓangaren aka amsa mata sallamar,kamar yadda wannan matashin ya yiwa Mama bayani haka ya yiwa Babah Rabi bayanin sosai Babah Rabi ta firgita lokaci guda kafarta ya shiga rawa,cikin rawar murya ta tambaye matashin inda hatsari ya auko nan ya yi mata bayani,Babah Rabi ta ƙasa furta koda kalma ɗaya ce kawai ta tashi ta fita daga ɗakin ta diɓa ruwa cikin kofi, hannuta riƙe da kofin ta koma ɗaki inda Mama ke kwance sume,a hankali ta durkusa inda Mama ke kwance ta shafawa Mama ruwa a fuska,a firgice Mama ta farka Babah Rabi ta yi saurin riƙeta tana faɗin ''kwantar da hankalin ki da yardar Allah babu abinda zai samesu'' da kyar Babah Rabi ta shawo kan Mama ta samu Mama ta tsagaita kukan da take,daurewa kawai Babah Rabi ke yi amma sosai hankalinta ya tashi tun sanda ta yi waya da wannan mutumin,a tare Mama da Babah Rabi su ka jera sun nufi inda aka yi haɗarin kasancewar a juction ɗin layin gidan Mama aka yi haɗarin yasa Mama da Babah rabi takawa da kafa tun daga nisa suke jiyu hayaniyar mutane da kyar suka ƙaraso bakin kwalta tun sanda Mama ta yi ido biyu da mota da ke ci da wuta hankalinta ya tashi sosai da kyar take sauke numfashi hakama Babah rabi sosai ta rikice ko magana ta ƙasa sai hawaye dake bin fuskarta,da kyar ta iya kiran layin Aisha bugu ɗaya aka amsa kiran nan Babah rabi ta jiyu muryar wannan matashin ya yi sallama tsabar kiɗima Babah rabi bata iya amsa sallamar ba kawai ta ce ''in ka ke? ina wa'inda suka yi haɗarin?" wata doguwar ajiyar zuciya matashin ya sauke bai san yadda zai sanar wa Babah rabi hasalin abinda ya faru ba saboda bai san matsayin mutanen da suka yi hadari wajen Babah rabi ba,bai sani ba ko ƴaƴanta ne ko akasin haka,hakan yasa ya saita nitsuwarsa kafin ya ce ''ina ki ke Babah?" Babah Rabi ta basa amsa cike da kosawa ta yi masa kwatancen inda suke ita da Mama katse kiran matashin ya yi daga haka ya nufi inda Mama da Babah Rabi suke,harda bakin hanya ce amma saida ya kira layin kusan sau biyu kafin suka haɗu saboda jama'a da suka taro wajen,Babah rabi da Mama suka kafe matashin da ido kowacce daga cikin su Allah Allah take ta je abinda zai faɗa,sai da matashin ya fara gaida su kafin ya ce ''sunana sagir'' Mama da zuba masa ido kawai bata ce komai ba ita ba sunansa take son sani ba,halin da ƴaƴanta suke ciki kawai take son sani,Babah Rabi ta yi sauri tare numfashinsa ta ce ''ina A'isha ina Unaisa?Allah ya sa babu abinda ya same su,matashin da ya kira kansa sagir ya yi shiru na wasu ƴan sakanni can ya ce ''wannan wayar a hannu driver motar na karɓa ya faɗa min wayar ɗaya daga cikin passenger da ya dauko ne,kamar dai yadda ya faɗa mana ya roƙeta wayar ne da niyya yin kira saboda babu kati cikin tasa wayar kuma yana son yi kira a wannan lokacin,kamar dai yadda ya faɗa mana ya dauke mata biyu da jirarai biyu sai dai cikin hukuncin ubangiji bayan aukuwar haɗarin mota ta kama wuta driver kadai ya tsira ya fita yana niman taimakon jama'a kafin jama'a su karaso wuta ta ci motar sosai babu yadda za a yi a fitar da mutanen da ke cikin motar'' tun bai kai ga idah zancen sa ba Mama ta ji kamar mafarki take, gaba ɗaya ta ji duniyar tana juya mata tsabar firgita da fita hayyaci da za a tambayi ta sunanta wannan lokacin baza ta iya amsawa ba,gaba ɗaya bata san inda kanta yake ba,Babah Rabi ce ta yi saurin rike Mama ganin zata faɗi,da taimakon sagir Babah Rabi ta samu waje kofar wani gida ta zaunar da Mama tana kokarin kwantarwa Mama da hankali,har da dai itama daurewa kawai take,bayan Babah Rabi ta zaunar da Mama ta shiga aikin rarrashin Mama,Mama ta ƙasa ko da ƙwawarara motsi sai bin mutane take da ido duk maganganun da Babah Rabi ke yi Mama bata fahimci komai ba sai bin Babah Rabi da ido,ganin mutane ƴan unguwa da wa'inda suke wucewa sun fara taruwa kansu suna masu jaje yasa Babah Rabi raba Mama da wajen,duk wanda ya ga Mama sai ya tausaya mata kamar wata zautattaciya haka Mama ta koma,bayan komawar su gida Babah Rabi ta shigar da Mama daƙi ta zaunar da ita,cike da juriya Babah Rabi ta samu waje ta zauna tana sauke numfashi da kyar,daƙin ya yi shiru baka jin motsin komai,bayan wasu ƴan mintina wani irin hawaye masu zafi suka shiga zubawa daga idanun Mama shiru Babah Rabi ta yi tana kallon Mama bata hanata kuka ba kawai ta kafe ta ido,wani irin ciwo kanta ke mata gaba ɗaya kanta ya kulle tama rasa ta inda zata fara a hankali ta kai hannu ta dafe kai sosai idanunta suka riƙida suka yi ja sosai ta dauki a ƙallah mintina uku a haka can ta yunƙura da kyar ta nufi inda Mama ke zaune,hannu ta kai ta dauki wayar Mama dake saman katifa hannunta na rawa ta shiga wajen lambobi nan ta cire lambar baffa Abubakar bata tsaya ɓata lokaci ba ta kira lambar bugu ɗaya Baffah Abubakar ya ɗaga kiran,bayan Baffah Abubakar ya amsa kiran Babah rabi ta yi shiru ta ƙasa cewa komai Baffah Abubakar yana ta sallama ya ji shiru ba'a amsa ba,can dai Babah Rabi ta tattaro sauran jarumtar da ya rige mata da kyar ta iya buɗe baki da ya yi mata nauyi sosai ta ce ''Rabi'atu ce'' nan dai suka gaisa bayan sun gama gaisawa ne murya can ƙasa cikin rawa murya Babah Rabi ta ce ''Allah ya yiwa Aisha da Unaisa tare da jariran Unaisa rasuwa,haɗari suka yi mota ta kama da wuta'' wani irin kuka ne ya kwafce mata sai yanzu ta samu damar kuka,kuka take sosai bil hakki da gaske har sannan waya na kare kunnenta a hankali ta zame jiki ta zauna,daga ɗaya ɓangaren baffa Abubakar yana jin yadda take kuka sai dai ya kasa cewa komai sun dauki sama da mintina huɗu a haka can baffa Abubakar ya katse wayar Babah Rabi ta shiga rera kuka,bayan Baffah Abubakar ya katse wayar ƴar danne danne ya yi cikin wayarsa ya ciro lambar Ɗalha nan take ya rubuta masa sako kamar yadda Babah Rabi ta faɗa masa haka ya rubutawa Ɗalha ya tura masa,bayan ya turawa Ɗalha sako nan ya shiga kiran ƴan uwa da abokan arziƙi musamman ɗangi mahaifin Unaisa,Ɗalha na zaune opis sako ya shiga wayarsa ganin sunan Baffah Abubakar yasa bai duba sakon ba a tunaninsa kan maganar aurensa da Unaisa baffah Abubakar ya tura masa saƙo hakan yasa bai buɗe sakon ba,cikin ɗan kankanin lokaci labarin hadari ya yaɗa unguwar su Mama da ma gari baki ɗaya, Rumaisa na kitchen tana shirin daura girkin rana Fadeelah ta shiga gida a rikice tana kiran sunan Rumaisa cikin ɗan ɗaga murya da kuma firgice take faɗin ''anty Rumaisa.. Anty Rumaisa..'' da sauri Rumaisa ta fito daga kitchen tana ƙarewa Fadeelah kallo sosai ta firgita ta buɗe baki da niyyar magana Fadeelah ta ce ''rasuwa aka yi Unaisa ce sun yi haɗari ita da yayarta da twins ɗinta mota ta kama da wuta babu wacce aka cire da rai driver ne kaɗai ya tsira'' galalah Rumaisa ta yi na wasu ƴan sakanni ko kaɗan bata yarda da labarin da Fadeelah ta faɗa mata kawai ta taɓe baki ta ce ''kai amma Fadeelah kin iya tsiya wacce Unaisa ki ka magana a kai wai kishiyar Amirah ki ke nufi?" Fadeelah da ta gama kiɗima ta ce ''eh ita'' ta faɗa tare da ciro wayarta daga aljihun wando Uniform ɗin islamiyya da take sanye da shi ta ce ''kalli nan Anty wallahi ɗazu wata ƴar unguwar su da muke zuwa islamiyya tare ta tura a group'' ta kare magana tana nunawa Rumaisa vidoe motar da ke ci da wuta zuwa yanzu Rumaisa ta fara yarda da maganar Fadeelah ganin da gaske Fadeelah take kuma babu alamar wasa tare da ita hakan yasa kai tsaye Rumaisa fadin ''a ina ta san Unaisar ita yarinyar?wai ki kam anya kuwa Unaisa kishiyar Amirah ki ke nufi?" Fadeelah ta ce ''Anty karfa ki manta kafin Unaisa ta yi aure islamiyyar mu ɗaya ita kuma yarinyar a unguwar su Unaisa take'' Rumaisa ta zaro ido waje tana salati tare da ajiye ludayin miya a kasa tana salati,bayan wasu ƴan sakanni ta shiga ɗaki tare da daukar wayarta ta kira layin Amirah,har kiran ta katse Amirah bata ɗaga kiran ba hakan yasa Rumaisa tura mata saƙo a whatsapp tare da vidoe da Fadeelah ta nuna mata bayan ta sa Fadeelah ta tura mata vidoe,Dalha na zaune opis kiran Amirah ta shiga wayarsa amsa kiran ya yi tare da kara wayar kunnensa daga ɗaya ɓangaren Amirah ta yi shiru ta ƙasa cewa komai sai shassaƙar kuka take,shima shiru ya yi na wasu ƴan mintina can ya ce ''ya aka yi queen? me ke faruwa? mutawa aka yi ne?" ya ƙare magana idanunsa kan kamputa yana typing daga ɗaya ɓangaren sosai Amirah ke kuka jin yadda take kuka yasa Ɗalha fahimta da akwai abinda ya faru,a natse ya dakatar da rubutu da yake cikin kamputa ya ƙara mayar da hankali sosai ya buɗe baki ya ce ''please talk to me,me ke faruwa?'' Amirah da kuka ya gama cin karfin ta da kyar ta iya buɗe baki ta ce ''Unaisa ce'' wani irin bugu zuciyar Ɗalha ya yi harda baya tare da Unaisa kuma bai da niyyar maida aurensu ya ji hankalin sa ya yi mugun tashi zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri amma sai ya dake ya yi ta maza cike da juriya da son ɓoye yanayin da yake ciki ya buɗe baki da kyar da niyyar magana bai san dalili ba ya ji bakinsa na masa rawa sai ya daure ya ce ''me ya sami Unaisar?" cikin kuka Amirah ta ce ''Allah ya mata rasuwa'' daga haka bata sake iya furta komai ba sai kuka,wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa Ɗalha ya shiga lokaci guda,jikinsa ya yi sanyi sosai,ya dauki a ƙallah sakan goma a haka gaba ɗaya jikinsa ya shiga wani irin rawa a hankali ya cire waya daga kunnensa ya daura shi kan tebur yana jin yadda Amirah ke kuka
*SHUUKRAN*