FADIANA

Chapter 3: Trapped beside my worst enemy

by @hauwajaywrites

"Kaɗan?"


"Eh kaɗan, amma ba kaɗan sosai ba"


"Meye ma'anar hakan?"


Rahma ta rufe ido ɗaya tana murmushi "Mammy, you understand me"


"A'a ban gane ba, ki gaya min yawan yajin da kike so"


"Toh dai dai, sai kuma jollof rice, amma ina son wanda aka yi da kayan lambu, sannan a yi min soyayyen kaza. Ba sai kin yi mai yawa ba, saboda na san za ki ce na cika cin abinci"


Mammy ta yi wata dariya "Yarinyar nan! Sannu ko? Irin gashi kin samu chef harda fadin yadda kike so”


"Wallahi Mammy, na cancanci hakan. I've suffered enough!"


"Eh lallai, sai ka ce wanda ta tafi aikin wahala"


"Eh mana! Exams, assignments, projects, lecturers, presentations... Mammy, you have no idea!"


"To yanzu kin gama, Alhamdulillah! Allah ya sa abin da kika karanta ya amfane al’umman Annabi"


"Ameen, Mammy"


Tayi shiru sai kuma ta ɗaura "Wallahi I'm so happy, har yanzu nakan tuna ranar da na fara zuwa school, ina mamakin yadda na kai wannan matakin. Alhamdulillah, Mammy Allah ya ƙara miki lafiya, da ba don addu'arki da goyon bayan Abbah ba, da ban san yadda zan yi ba”


A ɗayan ɓangaren, Mammy ta yi shiru na ɗan lokaci, sai ta amsa cikin taushin murya


"Allah ya yi miki albarka Rahma, mu dai muna addu'ar Allah ya ba ki ilimi mai amfani, ya buɗe miki ƙofofin alheri, ya kuma sa ki zama mace ta gari, wannan shi ne abin da muke so"


Rahma ta yi murmushi, idanunta ta lumshe "Ameen! I promise I'll make you proud"


"Kin riga kin sa mu alfahari, my baby”


Wata ƙwalla ta taru a idanun Rahma, sai dai ba ta goge ba, murmushi ta yi kawai, tana jin wani irin sanyi a zuciyarta


Sai kuma ta tuna da main abunda ke ranta

"Amma Mammy, don Allah ki tabbatar kin dafa min su duka, kar ki ce wai saboda kin san ina zuwa, sai ki yi min shinkafa da stew kawai"


"Toh na ji, zan dafa miki amma idan kika dawo kika ga ban dafa komai ba fa?"


Rahma ta buɗe baki da sauri "Mammy!"


Mammy ta fashe da dariya “Alright, wasa nake yi dear, zan dafa miki abincin da kike so”


"Okay. Then I love you more!"


"Toh yanzu ki ajiye wayar ki huta, Idan aka kira jirginku, ki saurara sosai, kada ki zauna kina waya har su tafi su bar ki"


Rahma ta yi dariya "Mammy, I'm not a child"


"Eh sannu fah, ai sanin hali ne, kuma kin fi kowa sanin ba Yau aka fara ba”


"Mammyyyy!"


"Toh na ji, Allah ya kiyaye hanya ki kira ni idan zaku shiga jirgi”


"Ameen! Bye Mammy, tell Abbah I said hi”


"Zan gaya masa, bye my baby”


Ta kashe wayar, ta riƙe ta a hannunta tana murmushi, wannan shi ne farin cikin da ta fi so a duniyarta wato kasancewa da Iyayenta


Ta kalli screen ɗin wayarta, ta buɗe wani chat da ƙawarta ta aiko mata da hotunansu na ranar kammala karatu, ta fara duba hotunan ɗaya bayan ɗaya, tana murmushi idan ta tuna abin da ya faru a kowannensu


A ƙarshe, ta yi wata ƙaramar kara tana dariya "Alhamdulillah for everything”


Meanwhile kafin gama wayanta da Mammy abun daya faru shine…. A dan gabanta wannan saurayin da ta buge ne zaune a kan kujera


Ya jingina bayansa da kujerar, yana riƙe da wayarsa a hannuns, ya sake duba tsagu-tsagun da ke fuskar screen ɗin, sannan ya yi wani irin tsaki


"Unbelievable” Ya ɗaga kai ya kalli mutanen da ke wucewa a gabansa


Yau dai kamar bai fito a sa’a bane, tun da ya shigo airport ɗin, hankalinsa bai samu nutsuwa ba, bayan wata stranger da ta zo ta buge shi, ta fasa masa waya, sannan ta tsaya tana masa bayanin cewa shi ne ya tsaya a hanya


Wani irin fushi ya ji ya sake taso masa

What kind of people are these?


Ya yi ƙoƙarin mayar da hankalinsa kan abin da yake yi, amma ya kasa, bcos duk lokacin da ya tuna fuskar Rahma da yadda ta tsaya tana kallonsa bayan ya kira ta dabba, sai ya ji kamar ya sake fusata


Ba wai don kalamanta sun dame shi ba ne, A'a. Abin da ya fi ba shi haushi shi ne yadda ta yi masa magana kamar ba ta san girman laifin da ta aikata ba


Ya girgiza kansa, sannan ya saka earpods ɗinsa a kunnensa


Ya fi son zama wajen da babu hayaniya, ba ya son surutu marar amfani, ba ya son mutane masu yawan magana, kuma musamman ma ba ya son matan da suke nuna rashin kamun kai a duk inda suka samu kansu


A ganinsa, nutsuwa da mutunta mutane abubuwa ne masu muhimmanci


Amma yarinyar da ya haɗu da ita yau kamar ba ta san ma'anarsu ba, ya buɗe wayarsa ya fara duba wani abu, yana ƙoƙarin manta da ita

Sai dai ba a daɗe ba, ya ji wata murya a kusa da shi "...wallahi Mammy, na gaya miki, ina son miyar kukar nan da nama sosai..."


Ya dakata, a hankali ya ɗago kansa, wace ce kuma mara kamun kan nan?


Idanunsa suka fara bin muryar, har suka tsaya kan fuskarta, quite sure ya gane ta, ita ce dai ta buge shi

Rahma ce zaune a kujerar da ke bayansa, tana waya da wani irin farin ciki a fuskarta. Hannunta ɗaya na riƙe da wayar, ɗayan kuma tana amfani da shi wajen yin gestures kamar wadda take magana da mutum a gabanta


"...sannan ki yi min jollof rice, Mammy, amma kada ki manta da kazar…"


Saurayin ya lumshe idanunsa Ya Allah, not again, ya ja wani irin tsaki mai ƙarfi


Rahma ta dakata a tsakiyar magana, a hankali ta ɗago kai, Idanunta suka sauka Kansa

Rahma ta gane shi nan take ita ma ‘The airport animal man’ Ta lumshe ido, sannan ta ɗan karkatar da kanta


Shi kuma ya zuba mata ido kamar ya kasa yarda da abin da yake gani ‘Of all the seats in this airport, she had to sit here?’


Ya cire earpods ɗin da ya saka, ya sake saka su a kunnensa, kamar yana nuna mata cewa ba ya son jin muryarta


Rahma ta ji wani irin haushi ya taso mata ‘Oh, so yanzu ni ce na dame ka?’


Ta juya fuskarta daga gare shi, ta ci gaba da magana da Mammy


Ta sake dariya. Saurayin ya buɗe idanunsa a hankali ya kalli gabansa, sannan ya kalli Rahma


Ta ci gaba da magana, yaja dogon numfashi, ya ɗaga hannunsa ya cire earpods ɗin


Rahma tana cikin bayani game da yadda tasha wahala ba ta ma lura da yadda yake kallonta ba


Ya tsaya na ɗan lokaci yana sauraron ta, har ya fara jin haushin kansa saboda bai bar wurin tun da farko ba


A ƙarshe, ya miƙe, ya ɗauki kayansa, ya gyara rigarsa, sannan ya nufi wani wuri dabam ba tare da ya ce mata uffan ba

Rahma ta harareshi ta gefen ido "Mtcheew! As if I care” Ta mayar da hankalinta kan wayarta


"Sorry, Mammy. Akwai wani mutum ne a nan yana nuna kamar shi kaɗai ne aka haifa a duniya”


Mammy ta yi dariya a waya "Rahma, ki daina faɗin haka, wataƙila yana da damuwa ne"


Rahma ta buɗe baki "Mammy! Ki ga dai wannan mutumin ya kira ni dabba saboda na buge shi bisa kuskure. Dabba fa! Ni!"


"Subhanallah! Ya kamata ki yi haƙuri, kada ki bari fushin wani ya ɓata miki farin ciki”


Rahma ta yi shiru na ɗan lokaci, sai ta sauke numfashi "Okay Mammy, zan yi ƙoƙari”


Shine har lokacin da suka yi sallama da mahaifiyarta..


 Can aka fara sanar da fasinjojin jirginsu cewa lokaci ya yi da za su shirya shiga jirgi


Rahma ta duba boarding pass ɗinta, sannan ta tabbatar da cewa jirgin ne ake kira,ta saka ta a handbag, sannan ta ɗauki kayanta


A wurin shiga jirgin, ma'aikatan suka fara duba boarding pass ɗin fasinjoji da tabbatar da cewa sun shiga jirgin da ya ke nasu, Rahma ta bi jerin mutanen da ke gabanta, ta miƙa boarding pass ɗinta ga ma'aikaciyar da ke karɓa, sannan ta bi hanyar da aka nuna mata zuwa jirgin


Da ta shiga, wata flight attendant ta gaishe ta cikin murmushi, ta nuna mata hanyar da za ta bi domin isa kujerarta


Rahma ta duba lambar kujerar da ke boarding pass ɗinta, sannan ta bi layin kujerun har ta isa wurin da aka ware mata


Kujerar tana gefen window, murmushi ya bayyana a fuskarta "Perfect!"


Ta fi son zama a gefen window saboda tana jin daɗin kallon gajimari, filayen sama da yadda abubuwa suke bayyana ƙanana yayin da jirgi yake tashi


Ta ajiye handbag ɗinta a inda ya dace, sannan ta zauna ta daidaita veil nata


Bayan wasu lokuta, fasinjoji suka ci gaba da shiga jirgin har aka fara samun nutsuwa. Flight attendants suka fara zagayawa suna tabbatar da cewa kowa ya zauna a kujerarsa


Rahma ta jingina bayanta da kujerar, tana kallon waje ta taga, tana jin wani irin farin ciki da ba ta iya bayyana shi


Finally, I'm going home… Ta lumshe idanunta na ɗan lokaci, tana jin daɗin tunanin cewa nan ba da daɗewa ba za ta ga iyayenta


Murmushin fuskanta yayi fading nan take.. Domin da ta juya kanta daga window sbd ta ɗauki handbag ɗinta ta cire wayarta, sai ta lura da mutum dake zaune a kujerar gefenta, fuskarsa a ɗaure, kuma wayarsa a hannunsa yana daddannawa

Rahma ta tsaya cak, a hankali ta ɗaga idanunta daga wayar zuwa fuskarsa

Shi ma ya ɗago kansa a daidai lokacin, Idanunsu suka haɗu

Wani irin shocked dukkansu biyu suka shiga, sai saurayin ya ɗan karkatar da kansa, ya zuba mata ido


Rahma ta buɗe baki a hankali "No way"

Ya lumshe idanunsa, ya sauke numfashi mai nauyi "Are you serious?"


Rahma ta mayar da kanta window da sauri, tana jin haushinsa ya sake tasowa a zuciyarta ‘This cannot be happening’


A gefe guda, saurayin ya mayar da wayarsa gefe, yana kallonta daga gefen ido ‘Out of all the people in this world, why her?’ Ya yi tsaki a hankali

Rahma ta ji kuma a duniya babu abun data tsana kamar tsaki, dan tun tana yarinyar idan ana son sata kuka tsaki ake yi


Ta juya ta kalle shi "Can you stop that?"

Ya ɗago kansa "Stop what?"


"That irritating thing you keep doing with your mouth, ko ya kuke yi bakin ma oho”


Ya ɗan daga gira, kamar bai yarda da abin da ya ji ba “Kee kinga nayi Kama da sa’anki ne?”


Rahma ta yi murmushi mai ɗan zafi "Oho"


Ya girgiza kansa, sannan ya mayar da hankalinsa ga wayarsa, ta juya kanta ta window, tana jin wani irin haushi da ba ta iya boyewa


Bayan an gama shigar da fasinjoji, flight attendants suka fara sanar da su abin da ya kamata su yi kafin jirgin ya tashi. Aka umurci kowa ya zauna, ya ɗaura seat belt, sannan ya tabbatar da cewa wayoyinsa suna cikin airplane mode ko kuma a kashe su yadda aka buƙata


Rahma ta ɗaura seat belt ɗinta, sannan ta mayar da kanta zuwa window 


Jirgin ya fara motsawa a hankali


Ta ji wani irin farin ciki ya cika zuciyarta yayin da take kallon yadda filin jirgin yake ja da baya a ta window ɗin


Da jirgin ya fara tashi, sai ta ɗan riƙe gefen kujerarta, tana murmushi "Alhamdulillah," ta furta a hankali


Da jirgin ya daidaita a sama, aka sanar da fasinjoji cewa za su iya ci gaba da zaman su bisa umarnin ma'aikatan jirgin


Rahma ta cire wayarta, ta buɗe camera, ta fara ɗaukar hotuna ta window, ta ɗauki hoton gajimari, ta ɗauki hotar kujeran jirgin, sai kuma kanta da take selfie, sai ta mayar da wayar window

Ta yi murmushi, tana ƙoƙarin samun hoton da zai nuna yadda rana take haskakawa a kan fararen girgije


Ta ɗan karkatar da wayar, ta ɗauki hoto ɗaya, sannan ta duba hoton tana murmushi "Beautiful," ta furta


Shi dai saurayin ya yi ƙoƙarin yin watsi da ita, amma duk lokacin da ta ɗaga wayarta ko ta yi wata ƙaramar dariya, sai ya ji wani irin haushi yana tashi a ransa


Ya juya kansa ya kalle ta


Rahma tana cikin ɗaukar wani hoto, fuskarta cike da farin ciki, kamar babu abin da ya faru a airport


Ya ɗan daure fuska ‘How can someone be this carefree?’


A ganinsa, tana ɗaya daga cikin matan da ba sa damuwa da yadda halayensu suke shafar wasu. Ta yi kuskure, ta ɓata masa waya, sannan ta ci gaba da rayuwarta kamar ba wani abu ba


Ya juya kansa zuwa gabansa ‘Whatever. I don't care’

Rahma ta ɗauki wasu hotuna, sannan ta gaji, ta kashe camera, ta saka wayarta a cikin handbag, ta gyara veil, sannan ta jingina kanta da kujerar


Ta kalli gajimarin da ke waje na ɗan lokaci, kafin ta sauke idanunta


Wani tunani ya fado mata a rai ‘wannan mutumin dai Allah ya shirya shi’ Ta ɗan yi murmushi

Amma wallahi, idan wani abu ya sake haɗasu, ba zan sake barin sa ya yi mata irin wannan cin mutuncin ba, ta lumshe idanunta, tana ƙoƙarin samun hutu

A gefenta, saurayin ya ci gaba da duba wayarsa, yana ƙoƙarin mantawa da ita