SARƘAƘIYA

07

by @umaimahadogaya905

Chapter 07 page 13

***ABUJA CAPITAL STATE (VILLA)***

Washe gari da misalin ƙarfe takwas na safe.

A ofishin Chief of Staff, tun da wuri ana ta kai da kawo wa . Manyan fayiloli ne aka shimfiɗa a kan babban tebur, yayin da sakatarori ke karɓar takardu daga jami'an ma'aikatu daban-daban.

Chief of Staff ya zauna a kujerarsa, yana nazarin rahoton farko da Ma'aikatar Ayyuka ta aika masa dangane da manyan hanyoyin gwamnatin tarayya da suka lalace.

Ya buɗe shafi na gaba, sai ya ɗan haɗe gira.

Akwai wasu ayyuka da aka fara tun shekaru da suka gabata, amma har yanzu ba a kammala su ba. Wasu an sake ba su ƙarin kuɗi fiye da sau ɗaya, yayin da wasu rahotannin ke nuna cewa ana ci gaba da aikin duk da cewa babu wani gagarumin ci gaba da ake gani a zahiri.

Ya ɗauki alƙalaminsa, ya yi wa wasu sassan rahoton alama.

A dai-dai lokacin ne wayar ofishinsa ta yi ƙara.
Ya miƙa hannu ya ɗaga wayar.
"Good morning." Ya faɗa still idanuwansa akan takardar.

Daga ɗayan ɓangaren, sakataren Ministan Ayyuka yayi saurin faɗin "Good morning, Sir. Honourable Minister yana son tabbatar da lokacin da Mr. President zai karɓi rahoton farko."

Chief ya kalli agogon da ke bangon ofishinsa.

"Tell him I expect the preliminary report before the end of today. Kuma ina son a haɗa bayanan kuɗin da aka ware wa kowane aiki da kuma adadin aikin da aka kammala zuwa yanzu."

"Okay, Sir."

Ya katse wayar, sannan ya miƙe ya ɗauki rahoton.

Bai so ya kai wa shugaban ƙasa takardun da ke cike da alƙaluma kawai ba. Yana son a samu bayanan da za su nuna ainihin halin da ayyukan suke ciki.

Ya san Mr. President ba zai gamsu da bayanin da ba shi da hujja ba.

Ofishin Mr. President

Mr. President yana zaune a kujerarsa, yana sauraron bayanin da National Security Adviser (NSA) yake yi masa dangane da yanayin tsaron ƙasar.

A gabansu akwai rahotannin tsaro daga sassa daban-daban na ƙasar, musamman yankunan da hare-hare da satar mutane suka addaba.

NSA ya buɗe wani fayil. "Your Highness, daga bayanan da muka tattara, akwai wasu yankuna da ke buƙatar kulawa ta musamman. Matsalar ba wai ƙarancin jami'an tsaro kaɗai ba ce. A wasu wurare, rashin kyawun hanyoyi yana hana jami'an tsaro isa inda ake buƙatar su cikin gaggawa."

Mr. President ya ɗago kai. "Are you saying the condition of our roads is also affecting security operations?"

"Yes, Your Highness." NSA yayi saurin amsa wa kafin ya cigaba da crwa "A wasu yankuna, motocin sintiri suna fuskantar matsala wajen isa ga al'ummomin da ke cikin haɗari. Idan hanya ta lalace sosai, lokacin da ya kamata a yi amfani da shi wajen ceton rayuka yana ɓacewa a kan hanya."

Mr. President ya yi shiru, yana nazarin maganar.A hankali ya jingina bayansa da kujera.

"Then we need to stop treating these problems as if they have nothing to do with one another." Ya ɗauki alƙalami, ya rubuta wasu bayanai.

"Ina son a haɗa bayanan tsaro da na hanyoyin da za a gyara. Ba wai duk hanyar da ta lalace tana da matsalar tsaro ba, amma ina son mu tantance wuraren da gyaran hanya zai taimaka wajen sauƙaƙa aikin jami'an tsaro da kuma rayuwar jama'a."

NSA ya jinjina kai. "Understood, Your Excellency."

Mr. President ya ci gaba. "Sannan ina son a tabbatar cewa wannan shiri ba zai zama na gyaran hanyoyin birane kawai ba. Mu duba yankunan karkara ma. Akwai al'ummomin da suke fama da matsalar kai kayayyakin amfanin gona kasuwa, samun asibitoci da kuma kai yara makaranta saboda rashin hanyoyi masu kyau."

Ya ɗan dakata sannan ya cigaba "Idan muna son gyara ƙasa, dole mu fara da fahimtar irin wahalar da jama'armu suke sha."

NSA ya rufe fayil ɗinsa. "Your Highness, wannan zai buƙaci haɗin gwiwar hukumomi da dama."

Mr. President ya kalle shi. "Then let us coordinate them properly. Ba na son kowace ma'aikata ta yi aikinta ita kaɗai, ba tare da sanin abin da sauran suke yi ba."

A dai-dai lokacin ne aka kwankwasa ƙofar ofishin.
PA ya shigo bayan ya samu izini.Sai da ya russuna sannan yace "Your Highness, Chief of Staff yana waje. Ya ce yana da rahoton farko daga Ma'aikatar Ayyuka."

Mr. President ya gyara zamansa.
"Let him come in."

Bayan ɗan lokaci, Chief of Staff ya shigo da fayil ɗin da yake riƙe da shi.Ya gaishe da shugaban ƙasa, sannan ya zauna bayan an ba shi izini.

Mr. President ya dubi fayil ɗin. "Is this the report we requested?"

"Yes, Sir. Wannan rahoto ne na farko, amma har yanzu muna jiran cikakkun bayanai daga wasu sassan ma'aikatar. Na ga ya dace in fara kawo muku abin da muka samu zuwa yanzu. ne"

Mr. President ya karɓi fayil ɗin, ya fara duba shafukan da ke ciki.Bayan wasu mintuna, ya ɗaga kai. "Chief, ina son a yi wannan aikin cikin gaskiya. Kada mu zaɓi hanyoyin da za a gyara saboda kawai suna kusa da manyan birane ko kuma saboda wasu mutane suna da murya mai ƙarfi."

"Understood, Sir."

"Sannan duk wani kamfani da zai shiga wannan gasa, ina son a tantance shi bisa ƙwarewa, ingancin aikin da zai gabatar, kuɗin da ya nema da kuma damar kammala aikin cikin lokacin da aka tsara. Ba za mu yanke hukunci bisa suna ko alaƙar wani da gwamnati ba."

Chief of Staff ya rubuta umarnin.

"Zan tabbatar da hakan, Sir."

Mr. President ya rufe fayil ɗin. "Good. Ina son jama'a su fara ganin sakamako. Amma ba zan bari gaggawar nuna nasara ta sa mu yi kuskuren da zai jawo mana matsala nan gaba ba."

Ya miƙa fayil ɗin ga Chief of Staff.

"Ka ci gaba da aiki tare da Ma'aikatar Ayyuka. Kuma ka tabbatar an shirya cikakken tsarin tantance kamfanoni kafin a fara karɓar tayin kwangila."

Chief ya karɓi fayil ɗin.

"Yes, Your Highness."

Da ya miƙe domin fita, Mr. President ya ƙara da cewa,

"Chief..."

Ya tsaya ya juyo.

"Sir?"

Mr. President ya kalle shi da natsuwa.

"Ka tuna, babban nasarar wannan gwamnati ba ita ce yawan ayyukan da za mu sanar a jaridu ba. Ita ce yawan ayyukan da za mu kammala, da kuma yadda za su sauya rayuwar jama'a."

Chief of Staff ya jinjina kai.

"I understand, Sir."

Ya fita daga ofishin, ya bar Mr. President yana cigaba da tattaunawa da NSA game da matsalar tsaro Tabbas duniya na gab da shaifa cewa Nigeria ta samu canjin shugaba na ƙwarai.

A wajen ofishin kuwa, sabon shirin gwamnatin ya fara ɗaukar salo. Sai dai har yanzu akwai tambayoyi da dama da ba a samu amsarsu ba.

Waɗanne hanyoyi ne za a fara gyarawa?

Waɗanne kamfanoni ne za su shiga gasar?

Kuma shin duk masu ruwa da tsaki za su amince da sabon tsarin da shugaban ƙasa yake son kafawa?

**** MASARAUTAR AGADAS****

### GIMBIYA HADIZA ###

   Kishingiɗe take a cikin ɗakin hutunta na musamman, wani katafaren ɗaki da aka ƙawata shi da kayan alfarma irin na sarauta. Babu hayaniya ko motsin da zai katse nutsuwar da ke cikinsa, sai dai sautin numfashin waɗanda ke wurin da kuma motsin ƙaramar iska da ke ratsawa ta labulen tagogin ɗakin.

A tsakiyar ɗakin an shimfiɗa wata katuwar sallayar alfarma, mai laushi da tsada, wadda aka yi mata ado da zubin sarauta. A kanta ne Gimbiya Hadiza take kishingiɗe, bayanta a jingine da wasu manya-manyan filo masu kayatarwa, yayin da ƙafafunta suke kan wasu ƙananan filo da aka tanada musamman domin hutunta.

A gab da ƙafafunta kuwa, wata hadima ce take yi mata tausa cikin nutsuwa da taka-tsantsan, tana ƙoƙarin tabbatar da cewa ba ta aikata ko da ƙaramin kuskuren da zai iya jawo mata fushin uwargijiyarta ba.

A gabanta kuwa, wani ƙayataccen faranti ne na azurfa, cike da nau'ikan kayan marmari, ciki har da inibi, tuffa da sauran 'ya'yan itatuwa masu ƙamshi da armashi.

  Idanun Gimbiya Hadiza a lumshe suke, tamkar mai bacci. Sai dai duk wanda ya san halinta zai fahimci cewa ba baccin take ba. Wata irin damuwa ce take ta kai kawo a cikin zuciyarta, duk da cewa a zahirance ba za ka ga alamar hakan a fuskarta ba.

Tana ƙoƙarin nuna cewa komai yana tafiya yadda take so, amma a can cikin zuciyarta, wani abu yana ta cin karo da tunaninta, yana hana ta samun cikakkiyar nutsuwa.

Tun bayan samun labarin wasu sauye-sauye da suka shafi Yarima Iqbal, hankalinta bai kwanta yadda ya kamata ba. Tana jin kamar akwai wani abu da yake shirin faruwa, wani abu da zai iya tarwatsa dukkan tsare-tsaren da ta ɗauki tsawon lokaci tana ginawa.

“Assalamu alaikum, ranki ya daɗe.” Muryar Jakadiya ce ta ratsa ɗakin, cikin ladabi da neman izinin shigowa.

  Sai dai Gimbiya Hadiza ba ta amsa nan take ba.Sai da ta bar wasu 'yan daƙiƙu masu nauyi suka shuɗe kafin ta buɗe idanunta a hankali, sannan ta juya kanta zuwa ga hadimar da take yi mata tausa.

Ta yi mata wata alama da hannunta, wadda ta fahimta nan take. Hadimar ta dakatar da aikin da take yi, ta miƙe cikin ladabi, sannan ta nufi ƙofar ɗakin domin buɗe wa Jakadiya.

Jakadiya ta shigo da taku mai nauyi, fuskarta cike da wani irin yanayi da ya nuna cewa ba ƙaramin saƙo ne ya kawo ta ba. Da isowarta gab da Gimbiya Hadiza, sai ta durƙusa ƙasa cikin ladabi, ta sunkuyar da kanta.

“Allah Ya ƙara miki tsawon rai, sarauniyar sarakai. Ki gafarce ni da saƙon da na zo sanar miki. Allah Ya huci zuciyarki.”

Gimbiya Hadiza ta buɗe idanunta sosai, ta zuba mata wani irin kallo mai nauyi.

“Jakadiya, me ya faru? Ki yi magana kai tsaye. Ba na son wani kwana-kwana. Idan akwai abin da ya faru, ina so in ji shi yadda yake, ba tare da ɓata lokaci ba.”

Jakadiya ta haɗiye yawu. Hannayenta suka fara rawa a hankali, yayin da ta ƙara sunkuyar da kanta.

“Ranki ya daɗe... Yarima Iqbal ne...”

Ta dakata na ɗan lokaci, kamar tana neman ƙarfin halin furta abin da ke bakinta.

“Yarima Iqbal ne ya sake yanke jiki ya faɗi. Likitoci sun zo sun duba shi, amma... amma sun tabbatar da cewa ya amsa kiran Mahaliccinsa.”

Ta ƙara sunkuyar da kanta.

“Ki yi haƙuri, ranki ya daɗe. Allah Ya huci zuciyarki.”

Kafin Jakadiya ta ƙarasa maganarta, Gimbiya Hadiza ta zabura daga kishingiɗarta ta miƙe zaune zumbur, kamar wadda aka soka wa allura.

“Me kika ce?!”

Ta zuba wa Jakadiya ido, fuskarta cike da rashin yarda.

“Jakadiya, me kike faɗa? Maimaita abin da kika ce, ina so in ji shi da kyau! Ko dai kunnuwana ne suka fara jiye-jiye saboda sun saba jin labaran da ba su da tushe?”

Jakadiya ta kasa ɗaga kanta. Ta ji kamar ƙasa ta tsage ta haɗiye ta.

“Ki yi haƙuri, ranki ya daɗe. Yarima Iqbal ya rasu.”

Gimbiya Hadiza ta yi saurin miƙewa tsaye gabaki ɗaya. Ta fara kai wa da kawowa cikin ɗakin, tana girgiza kai kamar wadda aka sanar da ita wani abu da ya saɓa wa dukkan abin da ta sani.

“Ba zai yiwu ba! Ba zai taɓa yiwuwa ba!”

Ta tsaya cak, sannan ta juya ta kalli Jakadiya.

“Iqbal ba zai mutu yanzu ba! Ba zai mutu ba, Jakadiya! Ai sai da na tabbatar cewa shi ɗin mai tsawon rai ne kafin na sako shi cikin tsarina. Sai da na tabbatar da hakan kafin na fara aiwatar da abin da na fara tun kafin ma a haife shi!”

Muryarta ta fara ɗagawa, fuskarta ta sauya.

“Jakadiya, ba na jin ƙamshin rashin nasara a rayuwata. Dole ne mulkin Agadas ya dawo ƙarƙashin tafin hannuna! Dole ne wannan masarauta ta dawo ƙarƙashin jinina! Ba zan yarda wani abu ya rusa mini burina ba, bayan duk abin da na sadaukar domin cimma shi ba!”

Jakadiya dai ta ci gaba da kasancewa a durƙushe, kanta a sunkuye, jikinta ya yi laushi tamkar nunanniyar gwanda.Amma a cikin zuciyarta, wani sabon tunani ya fara tasowa.Ya Allah, me ya sa na bari aka jawo ni cikin wannan mugun aiki?

Ta tuna dukkan abubuwan da suka faru, yadda ta bi umarnin Gimbiya Hadiza tana tunanin cewa biyayya ga uwargijiyarta ita ce mafi muhimmanci a rayuwarta.Amma yanzu fa?Idan har ita ce ta rasu a wannan lokaci, tare da tarin zunubai da alhakin cutar da bayin Allah a wuyanta, da wace hujja za ta tsaya a gaban Mahaliccinta?Hawaye ya silalo daga gefen idonta, ta gaggauta share shi kafin Gimbiya Hadiza ta lura.

Sai ta ɗago kai a hankali, ta saci kallon gimbiya.
Abin da ta gani ya ƙara firgita ta da Gimbiya Hadiza.Ko kaɗan Gimbiya Hadiza ba ta nuna alamar alhinin rasuwar Yarima Iqbal ba. Hankalinta gaba ɗaya yana kan mulki da kuma yadda za ta tabbatar da cewa burinta bai tarwatse ba.

A lokacin ne Jakadiya ta tuna wani abu,tabbas hhausawa sun yi gaskiya da suka ce Gurbin Ido ba ido ba ne. Wannan kaɗai ya isa ya tabbatar da cewa babu ko ɗigon jinin Gimbiya Hadiza a jikin Yarima Iqbal!

   Duk da cewa shi ne ɗan da take kallo a matsayin tsanin cikar burinta, ba wani abu na jini da ya haɗa su. Wataƙila wannan kaɗai ya isa ya bayyana dalilin da ya sa mutuwarsa ba ta girgiza ta kamar yadda ya kamata ba.

Jakadiya ta runtse idanunta na ɗan lokaci, tana jin wani irin tsoro da nadama suna ƙara mamaye ta.Sai kuma kwatsam, tunanin Fulani Fadime ya faɗo mata a rai.Ta san halin da matar take ciki a yanzu, bayan samun labarin rasuwar ɗanta tilo da take matuƙar ƙauna.

Fulani Fadime, wadda ta daɗe tana rayuwa cikin zalunci da ƙuntatawa a hannun Mahaifiyarta akan son ranta. Wadda ta mayar da rayuwarta tamkar rayuwar baiwa, duk da cewa ita matar sarki ce.

A gefe guda kuwa, Gimbiya Hadiza ta tsaya gaban wata katuwar taga, ta zuba ido cikin sararin samaniyar masarautar, kamar tana ƙoƙarin hango abin da zai biyo bayan wannan mummunan labari.

Chapter 07 page 14
### DAKIN FULANI MAIRAMA

Tun bayan da labarin rasuwar Yarima Iqbal ya bazu a cikin masarautar Agadas, ɗakin Fulani Mairama ya zama tamkar wurin taron murna ga wasu, amma ga ita kanta kuwa, ya zama ɗakin da take jin kamar za ta rasa hankalinta a cikinsa.

Kamar yadda ta saba, tana zaune tare da aminanta, Hajiya Lubba da Hajja Asime. Sai dai a wannan karon, yanayin da ya mamaye ɗakin ya bambanta da yadda yake a baya.

Hajiya Lubba da Hajja Asime suna ta shewa da nuna farin cikinsu, suna kallon rasuwar Yarima Iqbal a matsayin babban sauƙi da ya samu rayuwarsu. A ganinsu, wani babban shamaki ne ya kau daga gabansu, kuma yanzu babu abin da zai hana cikar burinsu.Amma Fulani Mairama ba ta cikin wannan farin ciki ko kaɗan.

Ta yi shiru, ta nutsu cikin tunaninta, tana jin wani irin nauyi a kirjinta da ba ta iya bayyana wa kowa ba. Duk lokacin da ta tuna cewa Yarima Iqbal ya mutu, sai zuciyarta ta yi wani irin harbawa, kamar wani abu ya tokare mata maƙogwaro.Ta kasa samun sukuni.A duk lokacin da ta lumshe idanunta, sai hoton Yarima Iqbal ya bayyana a cikin tunaninta, yana ƙara tunasar da ita abin da ta aikata.

Me ya sa na yarda na aikata wannan mummunan abu?Me ya sa na bari aka jawo ni har na zama sanadin mutuwar wanda bai yi mini komai ba?

Nadama da kaɗuwa sun yi mata katutu. Ta fara fahimtar cewa akwai laifukan da mutum zai iya aikatawa cikin 'yan mintuna, amma ya shafe tsawon rayuwarsa yana ɗauke da nauyin su.Sai dai abin takaici, komai ya riga ya faru.Yarima Iqbal ya amsa kiran Mahaliccinsa, kuma babu wani abu da za ta iya yi a yanzu da zai dawo da shi.

Hajiya Lubba ta ɗago kai, ta kalli Fulani Mairama da ta yi tsit, kamar ba ita ce take zaune tare da su ba.

“Asime, don Allah ki dubi matar nan mana! Ki ga yadda ta ɗora wa kanta damuwa a kan abin da bai kai ya kawo ba.”

Ta juya zuwa ga Fulani Mairama.

“Fisabilillahi, ke Mairama, wannan ba abin farin ciki ba ne a gare ki? Ai shamakin da ya gitta tsakanin ki da cikar burinki ya kau. Kin samu nasarar kawar da abin da yake hana ki cimma abin da kike so. To me ya rage?”

Fulani Mairama ta ɗago idanunta a hankali ta kalle ta. Idanunta sun yi ja, duk da cewa hawaye bai zubo ba.

“Ba za ku fahimci yadda nake ji ba,” ta furta cikin muryar da ta yi rauni.

“Wallahi, tun lokacin da labarin mutuwar nan ya shiga kunnuwana, ban sake samun sukuni ba. Wani irin abu ne ya tokare mini maƙogwaro, har yanzu ban ji ya sauka ba. Zuciyata kuwa kamar tana son ficewa daga ƙirjina.”

Ta ɗora hannunta a kan ƙirjinta, tana girgiza kai.

“Ban taɓa tunanin cewa zan ji haka ba. Na yi zaton idan wannan ranar ta zo, zan ji daɗi ne, zan samu salama a raina. Amma yanzu... yanzu abin da nake ji ya fi ƙarfin bayani.”

Hajja Asime ta ja dogon tsaki, ta gyara zamanta kafin ta yi magana.

“Ke Mairama, ai sa rai da ƙoshi shi ne yake kawo yunwa! Dama tun farko ba ki gama sakin jikinki da wannan aikin ba. Kina ta tunanin ko abin da muka yi zai yi nasara, ko kuma zai dawo ya same mu. Shi ya sa yanzu kika kasa samun nutsuwa.”

Ta yi ɗan shiru, sannan ta ƙara da cewa:

“Da kin kwantar da hankalinki tun farko, da yanzu ba kya cikin wannan halin ba. Amma na gaya miki, babu wani abu da zai sake faruwa. Abin da ya faru ya riga ya wuce, kuma babu wanda zai iya sauya shi.”

Hajiya Lubba ta gyaɗa kai cikin gamsuwa.

“Kwarai kuwa! Abin da Asime ta faɗa gaskiya ne. Mairama, ki daina ɗora wa kanki nauyin da ba zai amfane ki da komai ba. Mutuwa ƙaddara ce, kuma kowa yana da ranar da zai bar duniya,kawai dai mun rage masa nauyi ne.”

Ta ɗan karkata kanta, ta ƙara da cewa:

“Abin da ya kamata ki yi yanzu shi ne ki mai da hankali kan rayuwarki da abin da ke gabanki. Kada ki bari tsoron abin da ya wuce ya hana ki cin moriyar abin da zai zo.”

Fulani Mairama ta girgiza kai a hankali.

“Ba ku fahimta ba...”

Muryarta ta yi sanyi, kamar za ta fashe da kuka.

“Ba mutuwa kaɗai nake tunani a kai ba. Ina tunanin yadda aka yi na yarda zuciyata ta kai ni ga wannan mummunan aiki. Ina tunanin yadda wani mutum ya rasa rayuwarsa alhali ban san ko ya taɓa yi wa wani laifin da ya cancanci haka ba.”

Ta runtse idanunta, tana ƙoƙarin danne wani irin zafi da ya taso daga cikin zuciyarta.

“Idan har zan ci gaba da rayuwa da wannan abin a raina, to wace irin rayuwa ce zan yi?”

Hajiya Lubba ta kalli Hajja Asime, sannan suka yi musayar kallon da ya nuna rashin jin daɗinsu da kalaman Fulani Mairama.

“Ke dai ki yi shiru da wannan maganar,” Hajja Asime ta faɗa cikin kakkausar murya. “Ba mu zo nan domin mu riƙa tuno abin da ya wuce ba. Mun yi abin da muka ga ya dace, kuma yanzu abin da ya rage shi ne mu tabbatar da cewa komai ya tafi yadda muka tsara.”

Fulani Mairama ta zuba musu ido.

A karon farko, ta fara jin tsoron waɗannan mata da ta daɗe tana kira da aminanta.Domin idan har za su iya ɗaukar mutuwar ɗan wani mutum a matsayin abin murna, to mene ne zai hana su cutar da ita idan wata rana ta zama shamaki a gabansu?
Wannan tunanin ya sa ta yi shiru.Ta karkata kanta gefe, tana ƙoƙarin ɓoye tsoron da ya fara bayyana a idanunta.Amma a can cikin zuciyarta, wata tambaya ta ci gaba da maimaituwa:Shin akwai hanyar da zan bi in gyara wannan kuskuren, ko kuwa zan ci gaba da rayuwa cikin wannan nadamar har ranar da ni ma zan amsa kiran Mahaliccina?Ba ta da amsar tambayar.Abin da kawai ta sani shi ne, tun daga wannan rana, babu abin da zai sake zama yadda yake a da.

### DAKIN FULANI FADIME ###

Tun lokacin da labarin rasuwar Yarima Iqbal ya isa kunnuwanta, Fulani Fadime ta zama tamkar mutum-mutumin da aka cire masa rai.Zaune take a kan gadonta, idanunta a buɗe, amma kamar ba ta ganin abin da ke gabanta. Babu magana, babu kuka, babu wani motsi da zai nuna cewa har yanzu tana cikin duniya mai rai.

Mutanen da suka shigo domin jajantawa sun yi ta magana, sun yi ta rarrashinta, wasu ma suka yi ƙoƙarin riƙe hannunta suna ambaton sunan Allah. Amma duk abin da suke faɗa ya zama kamar sautin da yake zuwa daga nesa, wanda kunnuwanta suke ji amma hankalinta ba ya iya fahimta.

Abin da take gani a cikin tunaninta shi ne Yarima Iqbal kaɗai.Fuskarsa tun yana ƙaramin yaro,Murmushinsa,Yadda yake bin ta da ƙananan ƙafafuwansa a lokacin yarintarsa,Yadda yake neman ta idan ya ji wani abu ya dame shi,Yadda yake zama kusa da ita yana ba ta labaran abubuwan da suka faru da shi, yana mai kallonta da idanun da ke nuna cewa ita ce mafakarsa.

  Duk waɗannan abubuwan sun dawo mata a lokaci guda, suna wucewa a cikin tunaninta kamar fim da aka kunna ba tare da an nemi izininta ba.Wani lokaci tana jin kamar tana mafarki ne kawai. Kamar za ta lumshe idanunta ta ɗan huta, idan ta sake buɗe su sai ta tarar Yarima Iqbal ya dawo ya zauna kusa da ita, yana yi mata murmushinsa na musamman.Amma duk lokacin da ta dawo hayyacinta, sai gaskiyar ta sake fuskantarta.

IQBAL YA MUTU!

  Ɗanta tilo, wanda ta ɗauki cikinsa, ta haife shi, ta raine shi, ta yi ta addu'o'i a kansa tun yana ƙarami har ya girma ya zama babban mutum,ta ɗora manyan buruka akansa.Ta so ta ga aurensa,ta ga yaransa har ma da jikokinsa.Sai dai hakan ba za ta faru ba. Ya tafi in da ba a dawowa. 

Ba za ta sake ganin sa ba,ba zai sake kiranta da sunan da ya saba kiranta da shi ba.Ba zai sake zama gabanta yana ba ta labari ba.Ba zai sake riƙe hannunta yana tambayarta ko tana lafiya ba.

Wani irin raɗaɗi ne ya mamaye zuciyarta, raɗaɗin da ba ta taɓa sanin cewa mutum zai iya ji ba tare da ya mutu ba.Hawaye kuwa, ko kaɗan ba sa zubowa.Idanunta sun yi ja, jijiyoyinsu suka fito fili saboda irin matsin da suke ciki. Amma ko da ta so yin kuka, sai ta ji kamar wani abu ya toshe mata hanyar numfashi. Maƙogwaronta ya bushe, harshenta ya yi nauyi, kamar dukkan ƙarfinta ya tattaru ne a cikin wani wuri guda a ƙirjinta.

Wata mata da ke zaune kusa da ita ta matso, ta riƙe hannunta cikin tausayi.

“Fulani, ki yi haƙuri. Allah Ya jiƙan Yarima Iqbal. Allah Ya ba ki haƙurin wannan babban rashi da kika yi.”

Fulani Fadime ba ta amsa ba.Ta ci gaba da kallon gabanta, amma a zahiri ba ta ganin komai.

Matar ta sake matsa wa kusa da ita.

“Fulani, ki yi magana mana. Kada ki bar kanki a cikin wannan halin. Ki yi kuka idan kina so, ko da kalma ɗaya ce ki faɗa, za ki samu sassauci,ki ambaci sunan Allah, ki ce innalillahi wa'inna ilaihirraji'un.”

Amma har yanzu shiru.Fulani Fadime ta kasa ko motsa leɓɓanta.

A cikin zuciyarta kuwa, tana ta maimaita kalma guda:

Iqbal...Ɗana...Me ya sa ka bar ni? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. 

Sai tunanin mintuna talatin da suka gabata ya dawo mata, ya ƙara jefa ta cikin wani irin yanayi na rashin yarda.

Mintuna talatin kacal!Mintuna talatin ne kawai suka shuɗe bayan fitar Yarima Iqbal daga wurinta. A lokacin, babu wani abu da ya nuna mata cewa wannan shi ne karo na ƙarshe da za ta gan shi a raye.Ta tuna yadda ya kalle ta.Ta tuna muryarsa.
Ta tuna yadda ya yi mata sallama kafin ya tafi.

Ta tuna yadda ta kalle shi yana tafiya, ba tare da ta san cewa a cikin waɗannan 'yan mintunan ne ƙaddara za ta sauya rayuwarta gaba ɗaya ba.
Ta girgiza kanta a hankali.Ba zai yiwu ba.Ta yaya za a ce mini Iqbal ya mutu?Bayan bai daɗe da barin wajena ba,kuma lafiya lau ko ciwon kai ba ya yi. Me ya faru a cikin wannan ɗan lokacin?

  Ta so ta yi tambayar da ƙarfi, ta nemi a bayyana mata abin da ya faru, ta nemi wanda zai ba ta amsa mai gamsarwa. Amma bakinta ya kasa buɗewa.Kamar an ɗaure harshenta.Kamar an ɗora mata dutse a kan ƙirjinta.Sai ta sake lumshe idanunta.A wannan karon, hoton Yarima Iqbal yana tsaye gabanta, yana murmushi kamar yadda ya saba yi mata.Amma da ta buɗe idanunta, sai ta tarar babu kowa a gabanta.Sai gadon da take zaune a kai.Sai kuma mutanen da suke ta rarrashinta.Sai wannan mummunar gaskiyar da take ƙoƙarin guje mata.Ɗanta ya tafi, kuma ba za ta sake ganinsa a wannan duniya ba.

A hankali, wani ɗigon hawaye ya fara taruwa a gefen idonta, ya tsaya na ɗan lokaci kafin ya gangaro bisa kumatunta.

Hawaye guda ɗaya ne.Amma a cikinsa akwai tarin baƙin cikin da kalmomi suka kasa bayyana wa, da ƙaunar uwa ga ɗanta, da kuma radadin rabuwa da wanda ta ɗauka a matsayin wani ɓangare na rayuwarta.Ta ɗaga hannunta a hankali, ta goge hawayen.Sai kuma ta sake zuba ido cikin sararin ɗakin, kamar tana neman wani abu da ta rasa.

A wannan lokacin, ba ta damu da masarautar ba,Ba ta damu da sarauta ko dukiyar duniya ba.
Ba ta damu da abin da zai faru gobe ba.Abin da kawai take so shi ne ta sake ganin Iqbal, ko na minti ɗaya ne.Ta sake jin muryarsa.Ta sake riƙe hannunsa.Ta sake kiran sunansa ta ji ya amsa mata.Amma burinta ya tsaya a matsayin buri kawai.Domin a yanzu, Fulani Fadime ta fara fuskantar gaskiyar da babu wani mutum da zai iya sauya mata ita:Wani babban ɓangare na rayuwarta ya tafi tare da Yarima Iqbal.

Kuma yayin da take nutsewa cikin wannan baƙin ciki, ba ta san cewa a wasu ɓangarorin masarautar, akwai waɗanda suke murnar mutuwar ɗanta ba, wasu kuma suna ƙoƙarin ɓoye sirrin da zai iya sauya komai.

Sirrin da idan ya bayyana, ba Agadas kaɗai zai girgiza ba, har ma da rayuwar waɗanda suke tunanin cewa sun riga sun yi nasara.