BA NI DA MADOGARA

Chapter 4

by @narrnarhhbukar00

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*








  


*Bani da Madogara*
  (Sai Allah...)




 







004

Tana a maɓuyanta ne ta ji abu mai sanyi ya taɓa mata ƙafafu,daga ji abun mai girman gaske ne saboda sanyi da abun ya ke dashi da kuma nauyinsa, kamar daman jira ake sai ga walƙiya ta haskake ilahirin dajin kamar rana, karaf!  Idanun Hujayrah su ka yi arba da ƙasurgumin maciji baƙi siɗik! Sai faman huci ya ke yana fito da harshensa waje, ba tare da tsoro Hujayrah ta kafe macijin da dara-daran idanunta babu ko ƙyaftawa, kallan-kallo su ka shiga yi da macijin sai can ya sauka daga ƙafafunta sululu ya wuce abinsa, sauke ajiyar zuciya tayi a ranta tana ƙara godema kakarta domin da ba ɗan ta sha maganin maciji ba da wannan kumurcin macijin ya hallakata.Su Eze ne da mai gadi suke ta haske-haske tare da ƙara jaddada mata idan bata fito daga maɓuyarta ba har ta bari suka nemota da kansu to ta tabbata a yau ɗin nan za ta baƙunci lahira, su Eze sai ƙara kusanto inda ta ɓoye suke suna haska wurin duhu-duhun ciyayi ko a nan ta ɓoye.

Da wani irin ƙarfi mai gadi ya saƙi ƙara yana cewa

"Wayyo ƙafana maciji! Wayyo! Wayyo!"

Da sauri Eze ya dawo baya daman shi ne a gaba mai gadi na biye dashi, sosai hankalin Eze ya tashi ganin mai gadi kwance a ƙasa yana riƙe da ƙafa yana ihu, shi kuma macijin kamar walƙiya ya sulale yabar wurin. Da sauri Eze ya nufo inda mai gadi ya ke don ya taimaka masa,ciro belt ɗin wandonsa ya yi sai ya ɗaure saman cinyar mai gadi wanda ya ke kyautata zaton a ƙafarshi macijin ya sare shi, abu goma da ashirin,Eze ya rasa mai zai yi shin ya taimaki  mai gadi ne wanda ya ke cikin halin taimako ko kuma ya ci gaba da neman wannan yarinya saboda yasan waye mai gidansa mugu ne sosai don zai iya hallaka rayuwar shi akan cimma burinsa,waswasi ya ke akan ya taimaki mai gadi ko kuma ya ci gaba da neman yarinyar,wani ɓangare na zuciyarsa ta bashi zaɓin ya taimaki mai gadi in yaso daga baya ya dawo ya nemeta don yasan bazata taɓa fita daga dajin ba. Haka ya miƙar da mai gadi wanda sai lumshe idanu ya ke suka bar wajen sai ya wuce dashi zuwa gida. Sai a sannan ne Hujayrah ta saki ajiyar zuciya daman tana jin duk abinda suke cewa kasancewar suna kusa da inda ta ɓoye.

Bayan tafiyarsu bata taso daga maɓuyarta ba saboda Ruwan da ake mai ƙarfi ne, sai rawar sanyi ta ke tana riƙe da jakarta,wasu zafafan hawaye ne masu ɗumi suka gangaro bisa kuncinta a zuciyarta tana cewa 'Allah ka dubeni da idon Rahma ka kawomin ɗauki tare da sanyaya zuciyata daga ƙuncin da ta ke  ciki,mai nayi ma Baba Zakari da ya zaɓi Kaini ga halaka, a matsayinsa na ɗan uwan mahaifina uwa ɗaya uba ɗaya amma ya zaɓi cutar da rayuwata saboda son abinda duniya, in shaa Allah bazaka Taɓa ganin daidai a rayuwarka ba,muguntar da kaso kamin ta hanyar siyar dani da yardar Allah akan ƴaƴanka za ta koma, Allah sarki Abbuna... ' kuka ta saki mai ratsa jini da ɓargon duk wani mai sauraronta,sosai ta ke kuka tana tausayawa kanta akan halin da ta ke ciki duk yayan babanta ne ya ja mata,bata da mai lallashinta gashi ruwa yaƙi tsayawa sai tsawa da walƙiya ake da ya ke an shiga watan malka-malka. A haka ta ci gaba da ɓoyewa har ruwan ya yi sauƙi garin ya ɗan fara haske,miƙewa ta yi daga duƙyen da ta ke a hankali saboda ƙafarta tayi tsami sosai dalilin daɗewar da ta yi a duƙyen, jakarta ta sake gyara mata zama duk da a jiƙe ta ke,Allah yasa da hijab a jikinta ƙafarta ma da takalmi, fitowa tayi daga maɓuyanta, a hankali ta ke taka ƙafarta saboda tsamin da ta yi,abinka da mutumin ƙauye wanda ya taso a cikinsa musamman ma Hujayrah da ta saba shiga daji ita da Kakulle, duk wani sirri da abinda dazuzzuka suka ƙunsa kakarta ta sanar mata babu laifi tanada ɗan saninki akan daji da wasu sirrikan cikinsa . Sosai ta ke tafiya cikin daji babu alamun tsoro ko firgici a tattare da ita, garin sai ƙara haske ya ke tana ganin dajin dakyau a haka har ta fito daga dajin zuwa cikin wani layi, sabon layi  ne saboda akwai gine-ginan da ba a ƙarasa ba,wani tunani ne ya faɗo mata kar dai ace wannan ne layin da Alhaji Sambo Dala ya kawota,da sauri tacanja tafiyar ta zuwa ɗan sauri-sauri tsoran kar mugayan nan su fito nemanta su sameta a layin, daga sauri ta koma gudu, abinka da layinmasu kuɗi akwai wadataccen hasken solar wanda kusan kowani gida yanada guda ɗaya, titinsu lafiyayye ne ya sha kwalta, baka jin motsin komai a Layin sai kukan karnuka, sai gudu ta ke babu full stop har Allah ya bata ikon fita daga layin baki ɗaya lokacin masu tafiya sallar asuba suna fitowa daga gidajensu zuwa masallaci,tunda tabar layin sai ta canja salon tafiyar daga gudu zuwa tafiyar sauri,layin da ta shiga shima mai kyau ce kusan yana ɗan yanayi da ɗayam layin. 

Gari ya waye sosai domin haske ya bayyana mutane sun fara kai-kawo a unguwar musamman ma'aikata da masu kai yaransu makaranta duk a lokacin kayan Hujayrah suna a jiƙe, nan ta bar unguwar, ahaka-ahaka har ta fito daga unguwar complete sai ta tsaya wuri ɗaya tana tunanin wace hanya ya da ce ta bi,tuno da kacinci-kacinci da suke lokacin suna yara idan za su yi wasa ko kuma za su zaɓa abu. Gyara tsayuwarta tayi ta fara waƙar tana cewa

"Kacinci-Kacinci,Kacinci gizo da koɗi in ba koɗin ba a ina wutar ta kama a gidan Audu maƙerisss!" (Su Hujayrah babu kara 🤭ace kina kiran sunan Abbunki gatse wai Audu maƙeriss,a'a ba Audu maƙeriss ba Sai dai Audu manomi😂) 

Cak hannunta ya tsaya a gefan damanta sai kawai tabi hanyar tana addu'ar Allah ya tsareta daga sharrin yaran Alhaji Sambo Dala dashi kansa, Kar Allah ya haɗata dasu a hanya, tafiya ta ke tana tunani kala-kala bata san ina za ta ba,bata san kowa a garin ba,idan da bata ji Alhaji Sambo Dala ya ce ƙarya ya yi ma Baba Zakari akan shi mutumin Katsina ne da sai ta ce tana cikin Katsina. 

Bayan ta yi nisa sosai a tafiyarta sai ta samu saman dakalin wani masallaci ta zauna don yunwa ta ke ji sosai, ciro Jakarta ta yi daga kafaɗa, ta buɗe  ta ciro ƙullen soyayyen nama da gujjiyar da Kakulle ta saka mata ciki, duk da akwai lemar ruwa a ledar amma haka da buɗe ta ɗibo naman da gujjiyar ta fara ci a hankali kamar mai cin magani,bakinta baya mata daɗi samsam! Har wata masassara ta ke niyyar doka mata sallama, jikints ya yi zafi kaɗan maƙogaranta yana mata maƙaƙi kamar ta ciro shi tayi ta susa, kunnanta ma haka a taƙaice dai mura ce ta ke son kamata.Bayan ta kammala yakutar naman da gujjiyar sai da mai da ledar cikin jakar, Direct wurin famfon masallacin ta nufa ta buɗe tasha ruwa sannan ta koma inda ta ke tana hutawa sai kai kawo mutane suke abinsu ba tare da sun kula da wanzuwanta ba.Ta gaji iya gajiya ga baccin da ya ke idanunta kasancewar bata runtsa ba a daren jiya. Sai hamma ta ke jerawa akai-akai,ɗaukar jakarta ta yi ta saɓa a kafaɗunta sai ta samu wani ɗan wuri a harabar masallacin inda babu wanda zai lura da ita ta kwanta kan ka ce me bacci ɓarawo ya sunkuceta daman a jiyan shakkarta ya ke... ✍️

         🌎🌎🌎🌎🌎🌎

Babu za to babu tsammani Eze ya ji saukan zafafan maruka hagu da dama ji kake Tass! Tass! Ai babu shiri ya dafe kuncinsa yana kallon ƙasa. Sosai jikin Alhaji Sambo Dala ya ke rawa, idanunsa sun kaɗa sun yi ja kamar jan gauta, jijiyoyin kansa da wuyansa sun tashi sun yi raɗo-raɗo,tsigar jikinta duk ta miƙe, duk wanda ya kallesa a wannan lokacin bazai yi marmarin sake kallonsa ba domin ya koma wani kala dashi sai huci ya ke kamar kumurcin maciji ko kuma mayunwacin zaki wanda ya fito farauta,hannunsa na rawa ya ke nuna Eze cike da tsawa haɗi da hargagi ya ce

"How dare you on earth let that girl to escape from this house! Howwwww!" 

Da wani irin tsawa ya faɗi kalmar ƙarshe kusan sai da Eze ya so sakin fitsari a wando tsabar firgici, ci gaba da cewa ya yi

"Did you know the hardship I got myself for many years just to get this girl,Kai!" 

Tsagaitawa ya yi da maganar yana huci saboda zuciyarshi na matuƙar yi mishi zafi,sai can ya ci gaba da cewa 

"Na kai shekara goma ina neman yarinyar a gida da wajan Nijeriya,na kashe kuɗaɗan da bansan adadinsu ba just to get her, bayan na ganta na ci gaba da kashe kuɗaɗe just to make her be in safe before the time I want her, amma sai da aski ya zo gaban goshi, na kusa cimma ƙudirina akan yarinyar sai ka zo rana tsaka ka rusamin plans ɗina wanda na kai shekaru ina tsarasu, Never! Na rantse da DODO ƘURNUSSA sai ka nemota a duk inda ta ke, na baka nan da 48 hour ka nemota sannan ka kawota cikin gidannan idan ba haka ba! "

Bai ƙarasa maganar ba ya wuce fuuuuu! ,shiru Eze ya yi Still hannayansa a bisa kuncinsa yana jin raɗaɗin marin da mai gidansa ya yi masa,uwa-uba tashin hankain da ya ke a yanzu, shi ya yi mamaki a ce yarinyar nan za ta iya barin dajin kafin ya dawo,bayan shi ya sake kiran abokan aikinsa sun duba iya dubawa amma bata a ciki, ga wani tashin hankalin mai gadi ya mutu a sanadiyar saran da maciji ya yi masa, gashi dare ne balle ya kai shi asibiti ga uwa-uba dole ya dawo neman yarinyar, koda ya dawo daga neman ta ya samu mai gadi a kwance kumfa na fita daga bakinsa ya mutu, da ya sanar ma mai gidan ɓatan Hujayrah da mutuwar mai gadi sai  kawai tada hankalinsa akan ɓatar Hujayrah amma batun mutuwar mai gadi ya daɗe da zuba ta a kwando shara ya watsa, bai ma damu ba. 

Ganin tsayuwar ba ita ce mafita a garesa ba sai kawai ya fita daga gidan da motar da suke aiki da ita, yana fita ya kira abokansa wato yaran Alhaji Sambo Dala wa'inda suke yin aiki tare,jiransu ya yi har suka iso,rarrabuya suka yi bayan Eze ya suffanta musu yarinyar, kowa hanyar sa ya bi,babu inda basu shiga ba suna nemanta har  tambayan mutane suke ko za a dace wani ya ganta amma shiru babu ita babu labarinta... ✍️

                 🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Kwanar kwara ƙwai, Kaduna state.NIjerya*

A ɓangaren Alhaji Zakari ya shirya tsaf! Sannan ya ɗauki mukullin machine ɗinsa sabo fil!  tada machine ya yi sai ya nufa Kwarin ɗan dodo, kasancewar ƙauyen bai da daɗin tafiya a mota shiyasa  ya ɗauki sabuwan machine ɗinsa, ya jima yana tafiya a cikin daji domin a ƙarshen gari Malam Tani mai allon ƙarfe ya ke,kasancewar machine ɗinsa akwai gudu hakan yasa ya isa da wuri, fakata yayi a gefe sannan ya bi Layin shiga cikin bukkar Malam Tani mai allon ƙarfe. 

Mutane ne maza da mata suna bin Layi,mafi yawa a cikinsu alhazawa ne da hajijoyi, ga manya-manyan motocinsu  a gefe masu tsada.Ɗaya bayan ɗaya suke shiga bukkar, a haka layi na tafiya har aka zo kan Alhaji Zakari, shiga bukkar ya yi tare da zama inda aka tanadar don zama.Ƴar matsakaiciyar bukka ce mai ɗauke da yalwataccen fili,allunan  ƙarfe ne kala-kala a jingine a gefan hagu, a kusa da  Allunan wata baƙar ƙwarya ce babba mai kwalliya ja,babu siminti a bukkar sai dai buzu guda biyu,ɗaya buzu na Malam Tani Sai ɗayan kuma na masu neman taimako, a ta gefan ɗakin rami ne ƙarami wanda wuta na ci sosai a cikinsa, saman ɗakin igiya ce doguwa aka ɗaura,ƙananun ƙorai ne baƙaƙe ɗaure da igiya kusan guda goma wanda ni mai ɗaukar muku rahoto na kasa dubawa naga me akasa a ciki saboda mamakin da na shiga ganin Malam Tani  kamar malamin addini ba malamin tsubbu ba, babban mutum ne mai ɗauke da saje wanda akwai furfura a mafi yawan sajen,ya sha babbar malum-malum mai kalar ja da adon baƙi sai shigen ciki fari ne tar! A kansa  baƙar hula ce mai ratsin ja da fari, hannun sa na hagu sharɓeɓan carbi ne mai ƙirga dubu sai faman ja ya ke kamar mai tasbihi, Malam Tani baƙi ne mai ɗauke da haƙoran Makka har guda biyu. 

Koda Alhaji Zakari  ya shigo cikin bukkar ya sameshi yana jan sharɓeɓan carbinsa,da sallama ya shiga cikin bukkar sai ya amsa masa yana ci gaba da jan carbinsa. Bayan ya samu wuri inda aka tanadar na masu neman taimako ya zaune sai ya dubi Malam Tani mai allon ƙarfe da cewa

"Allah gafarta malam na zo..."

Bai ƙarasa abinda yayi niyyar faɗa ba Malam Tani ya ɗaga masa hannu alamu ya tsaya, shi daman a zuciyarsa yasan ba lallai bane Malam Tani ya bar shi ya ƙarasa faɗin abinda ya kawosa  saboda  ɗabi'arsa ce idan mutum zai fara faɗin abinda ya kawosa sai ya dakatar dashi tare da sanar masa abinda shi mutumin  ya ke da niyyar faɗa masa.Hakan ta faru domin cike da babbar murya irin na cikakkun malaman tsubbu wa'inda suka daɗe a harkar ya fara magana

"Ba sai ka ƙarasa faɗin abinda ke tafe da kai ba, Ƙaninka ne kake so a kulle masa baki a hanashi sake tuntuɓarka maganar tafiya wurin yarinyar sannan kana so ya daina taimaka ba mahaifin yarinyar, ya zamana komai ka umurcesa shi zai bi ba tare da ya maka musu ko jayayya ba"

Jiki na rawa Alhaji ya amsa da cewa

"Eh Hakane Allah ya gafarta malam" 

Ci gaba da jan carbinsa ya yi kamar ba zai ce komai ba sai can ya ce

"Ka zaɓa cikin  biyunnan kodai ka amince a rufe masa baki akan maganar tafiya wurin yarinyar ko kuma ka zaɓa ya daina taimaka ma mahaifin yarinyar amma bazaka samu duka ba"

Shiru Alhaji Zakari ya yi yana tunani wanne ya da ce ya ɗauka, shin ya zaɓi wanda za a hanashi taimaka ba Audu ko kuma ya zaɓa wanda za a rufe masa baki kar ya sake tuntuɓarsa zancen ina Hujayrah. Sosai ya ke tunanin wanda zai zaɓa tabbas yana son a hana Musa taimaka ma Audu saboda a da kafin ya makance ya na ɗan na rufin asiri,duk da a lokacin Audu ya sha taimaka masa da na cefane yafi sau a ƙirga amma yanzu cikar burin sa ya ke nema wato ƙumbar susa, duk inda yasan mutuncina zai zube yana taka-tsantsan don haka maganar farko ya zaɓa na a rufe Musa baki a game da batun tafiya wurin Hujayrah in yaso daga baya ya sake dawowa a yi masa aiki akan hana Musa taimaka ma Audu saboda iyayensu sunfi sonshi a bisa da su, komai Audu komai Audu hatta laƙanin bada magani Audu aka ba mawa wanda a matsayinsa na babban ɗa shi ya dace a ba ma laƙanin haka ya yi haƙuri, da kuma Audu ya makance sai aka sake ba ɗiyarsa dalilin haka  ne ya tsani Audu da ahalinsa. Ganin lokaci na ƙurewa mutane na jira a waje shi kuma Alhaji Zakari ya ƙi zaɓan ɗaya daga cikin biyune sai faman tunani ya ke, kawai sai Malam Tani ya ce mishi  a tsawa ce

"Wai har yanzu baka zaɓi ɗaya daga cikin biyun ba, ka yi shiru bayan kasan akwai mutane a layi" 

Firgigit ya dawo cikin hayyacinsa tare da fara magana da inda-inda yana cewa

"Eeehhh ayimin rai Allah ya gafarta  malam, na ji kuma na zaɓa a rufe masa bakin a yanzu in yaso daga baya na dawo ayi mishi aiki na hanashi taimaka na mahaifin yarinyar" 

"A'a ba haka muke aikinmu ba kasani tun ba yau ba idan muka umurci mutum ya zaɓa ɗaya daga cikin biyu, duk abinda ya zaɓa shi kaɗai muke mishi aiki akai, koda ya dawo daga baya ya ce a yi masa aiki akan zaɓi na biyu bama yi" cewar Malam Tani yana cilla masa harara alamun almatsutsan suna kusa. 

"To shikenan a rufe masa bakin kawai hakan ma ya wadatar" cewar Alhaji Zakari fuska a cunkushe, bai so hakan ba, ya so ace daga baya ya hana Musa taimaka ma Audu sai yaga yadda Inna za ta kasance,amma babu damuwa gaba tafi baya yawa ko ba wurin Malam Tani ba ne zai je wurin wani malamin a yi mishi aiki akan Musa. 

Gyara babbar rigarsa Malam Tani ya yi tare da miƙewa ya ɗauko wata ƙwarya daga cikin ƙoran da suke ɗaure da igiya,ajiyeta ya yi a gabansa ya yi sannan ya sake gyara babbar rigarsa,cikin ƙanƙanin lokaci yanayinsa ya sauya, sajensa duk ya mimmiƙe ga idanunsa sun kaɗa sunyi jajur,. Wasu irin surukatai ya ke cikin wata iriyar murya mara daɗi sauraro, sai faman girgiza kai ya ke yana surkullansa wanda ban fahimci komai a cikinsa ba, bai gama surkullansa ba lokaci guda  bukkar ta turnuƙe da uban hayaƙi, baka iya ganin komai a bukkar in banda hayaƙin, sosai Alhaji Zakari ya sarƙafe da tari, tarin yake babu ƙakƙautawa saboda hayaƙin yana ɗauke da yaji-yaji a cikinsa, masu bin layi a waje suma tarin suke saboda har waje hayaƙin ke fita. (My Esteem fans a gaskiya badani ba sa lallin kaza,Ina ni ina shiga wannan  bala'in haka,dole tasa na fito daga bukkar a sittin ina tari hannuna riƙe da ƙirji,Anya zan iya komawa ciki don ɗauko muku rahoto kuwa🤔, amma bara na gwada shiga nagani🤭🤭🤭) 

Bayan ƴan wasu lokutta hayaƙin ya ɓace kamar bai taɓa wanzuwa a bukkar ba,Malam Tani ya ke ɗauke da wata ƴar ƙaramar kwalba baƙar suɗuk! A samanta wani baƙin tsinke ne sai ya yi kamar tsinken kwalli, direct ya miƙawa Alhaji Zakari yana cewa

"Wannan kwallin aikin ɗaya ne ba a saka shi sau biyu, abin nufi da ka koma gida ka daidaici zuwan shi ƙanin naka sai ka saka kwallin a idanunka ka kula ba irin saka kwallin da mata su ke yi za ka yi ba, a'a za ka fara jan ƙwallin daga ƙarshe zuwa faro na idanun naka"

Cike da girmamawa ya amsa kwallin sai "To " ya ke ce masa yana ɗaga kansa na ya fahimta.Haka dokar malam Tani ya ke dubu ashirin ce ake bashi sadaka,sai dai idan aikin mutum ya girmi hakan ko kuma akwai abinda zai kawo na aikin shi ne kuɗin yake fin haka,Godiya ya masa sosai sai ya fito daga bukkar ya hau machine ɗinsa ya bar Ina suke, direct ya nufi cikin ƙauyen inda dadironsa take daman ya sanar mata da yana nan zuwa.Cike da murya ta amsa mishi da sai ya zo daman kwana biyu tana fama da talauci. 

Machine ɗinsa ya yi parking a wani  gida babba wanda daga shi sai daji kasancewar a kusa da ƙarshen gari gidan ya ke,a gefan wata  bishiyar magwaro ya aje machine ɗinsa sannan ya ƙarasa cikin gidan da... ✍️

A ɓangarensu Hannatu bayan Alhaji Zakari yabar gidan zuwa kwarin ɗan dodo, Sai kawai wata shawarar ta zo mata akansu Mammi, aikawa ta yi a kira mata Murja babu jimawa sai gata ta shigo ɗakin da sallama a bisa labɓanta, cike da izza Hannatu ta ke amsa mata tare da yi mata nuni da kujerar da ta ke kai, sai dai Murja ta yi ƙwafa sannan ta je ta zauna a bisa kujerar a zuciyarta tana cewa 'Ki zuba mulkinki son ranki nima lokacin nawa yana gab' gyara zama Hannatu ya yi sannan ta ce

"Wai kinsan Musa ya kira Mijina da mijinki akan maganar auran Hujayrah wai mai yasa ba a sanar masa ba a matsayinsa na ƙanin mahaifinta" 

Taɓe baki Murja ta yi tana cewa

"To sai me idan an ƙi faɗa masa, naga koda an faɗa masa babu abinda zai yi illa zuba idanu" cewar Murja

"Hmmmm Nima abinda na gani kenan, abin ban haushi a matsayinsa na ƙaraminsu ya ke umurtar Alhajina ya shirya zuwa gobe ya kai shi gidan Hujayrah tunda ya ce Alhaji Sambo Dala abokinsa ne" 

Sakin baki Murja ta yi tana kallon Hannatu saboda yawancin surrukan Hannatu tana sanar ma Murja, ko dalilin auran Hujayrah ga Alhaji Sambo Dala sai da ta sanar ma Murja,cike da mamaki Murja ta ce

"Innalillahi! To yanzu ya zai yi tunda bai san inda Alhaji Sambo Dala ya ke ba sai dai garin su" 

Wani ƙasaitaccen murmushi Hannatu ta saki tana cewa

"Idan yasan wata ai bai san wata ba,mu zai nunawa ɗanyen kai ai in faɗa miki kwarin ɗan dodo ya nufa yanzu, bayan sun kammala zantawa da Musa sai ya shigo ɗaki cike da damuwa da tashin hankali wanda a ƙarshe kawai ya yanke shawarar zuwa wurin Malam Tani mai allon ƙarfe don samun mafita"

Jinjina kai Murja ta yi tana cewa 
"wannan kuwa ita ce mafitar kinga idan an rufe masa baki bazai sake tattago maganar shegiyar yarinyar nan" 

"Hakane nima kawai na ce mai zai hana mu fara aiwatar da namu ƙudirin akan su Zaytuna,ko ya kika gani"

"Amma bamuyi gaggawa ba kuwa,naga shekaran jiya aka yi bikin Hujayrah"

Taɓe baki Hannatu ta yi tana cewa

"Babu wani gaggawa wallahi ai da zafi-zafi ake bugun ƙarfe ba sai ya huce ba"

"To shikenan yanzu wa ce shawara kike da ita don ni ba shiryawa nayi ba amma tunda kince haka da alama kinada naki shirin"

Ƙasaitaccen murmushi Hannatu ta saki tana duban Murja sannan ta ce

"Matso da ƙunnanki sahibar don  ki ji dakyau"

Babu musu ta matso da ƙunnanta duk da zuciyarta ta fara gajiya da halin Hannatu amma ya za ta yi tunda ita ma tana da nata ƙuɗirin akansu da ita kanta Hannatun, raɗa ta mata a kunne da saurin Murja ta kalleta da cewa

"A'a gaskiya Innar Harira wannan kuɗirin naki ya yi tsauri da yawa,taya za ki ce a yi ma Salim asirin sata haba don Allah,yaron da shiru-shiru ne babu ruwansa da hayaniya kema karan kanki kin sani ba halinsu daya da Hujayrah ba,Yana da sanyi hali irin na Zaytuna" 

Taɓe baki Hannatu ta yi kana wani irin kallon Murja Sama da kasa tana cilla mata harara,juyawa gefe  ta yi tana murguɗa baki da huro hanci sai  jijjiga ƙafa ta ke tana jin Murja,bari ta yi sai da ta dasa aya sannan ta dubeta da kyau ta ce

"Yaushe kika fara son Zaytuna da ƴaƴanta Murja! "

Bata saurari mai za ta ce sai ta ci gaba da cewa

"Ni da nake so yaranmu su fi nata ɗaukaka ita da Fatsima amma kike faɗar haka,Ina so yaranmu su  kasance a sama da yaranta da na fatsima,bari ki ji Murja! na tsani Zaytuna da yaranta tsana mai tsanani,kin manta lokacin da mijina bai dashi,sai yanga ta ke min wai ita ga mai miji mai kuɗi,karki manta Inna tafi son mijinta da yaranta sama damu,ko Baba ma haka ya ke nuna banbanci akan mazanmu da Audu kafin ya rasu,ki ga fa laƙanin bada magani Audu Inna taba,sannan da ya makance taba yara, a matsayin mijina na ɗan farko shi yafi cancanta ta bashi amma taƙi,idan ma haka ta ke ji ai sai taba mijinki a matsayin ɗanta na biyu amma saboda bata son mazanmu shiyasa ta hana ɗaya daga cikinsu ta miƙa ma Audu,Ke Murja! Buɗe idanunki da kyau kisan me ya ke miki ciwo,Zaytuna da yaranta ba ababan tausayi bane,don ni ko sau ɗaya ban ji zan iya tausayawa halin da suke ciki balle na janye kuɗirina akansu ba,yanzu aka fara wasan "

Shiru Murja ta yi tana sauraron Hannatu wacca ta ke maganar Kamar a zafafe,tunani ta shiga yi Tabbas maganar Hannatu tana a kan gaskiya don itama bata jin daɗin yadda Inna ta ke banbanta mazansu da Audu da Musa,musamman ma Audu da yaransa.Bata ƙi ta Hannatu ba amma asirin sata fa,gaskiya ya yi tsauri da yawa,da sauran imani a cikin zuciyarta.Ɗan nisawa ta yi cikin sanyi murya mai nuni da karaya ta dubi Hannatu ta ce

"To shikenan a yi masa asirin satar duk da yayi tsauri gaskiya,yanzu dai wurinwa zamu je ya yi miki aikin"

Gyara zama Hannatu ta yi sannan ta ce

"Yawwa ƴar gari ko kefa ai babu tausayi tsakaninmu da Zaytuna sai dai sharri"

Dariya suka saki lokaci guda suna tafawa,murya Hannatu ta gyara sannan ta yi ƙasa da muryarta tsoron kar iska da ɗauki maganarta tare da ƙara matsowa inda murja ta ke,cikin ƙasa da murya ta ce

"Ƙauyen Ciri-tawa zamu je anjima"

Da mamaki Murja ta kalleta ta ce

"Ƙauyen Ciri-tawa kuma,akwai wani malami ne a can? "

Jinjina mata kai Hannatu ta yi tana ci gaba da cewa

"Mardiyya matar mai unguwa ta faɗamin,hmmm baki ji daɗin da na ji ba,ta ce aikinsa kamar yankan wuƙa ya ke,shafa-shafa in ji turawa haka aikinsa ya ke,ta yi min kwatancen gidan malamin,amma fa ɗan daudu ne malamin sannan aljanun kansa ma ƴan daudu ne"

Waro idanu murja ta yi waje tana sakin bakinta galala,sai kuma da rufe bakin tana cewa

"Ɗan daudu ne malamin? anya ya iya aiki  Innar Harira,mai zai hana mu tafi kwarin ɗan dodo wurin Malam Tani mai allon ƙarfe,ke ma ganau ce ba jiyau ba kinsan aikinsa kamar yankan wuƙa ne"

"A'a ba zamu je can ba gaskiya don banso mu hadu da Alhajina,kin manta bai daɗe da tafiya can kwarin ɗan dodo,gwara kawai mu canza malami mu gwada wannan malamin mu ga tashi baiwar" cewar Hannatu tana mikar da kafarta saboda daɗewar da ta yi a zaune

"Karfe nawa zamu je ƙauyen Ciri-tawan"

Kallon sama Hannatu ta yi tana nazari sai can ta ce

"Bayan sallar tsayawan rana,sai mu je kinga lokacin Alhajina ya dawo"

"To Allah ya kaimu"

Daga haka suka ci gaba da hirarsu suna raha wanda kusan akan su Zaytuna da Fatsima su ke yi...✍️

               🌍🌍🌍🌍🌍🌍

*Ƙungiyar Black Pytons Society*
*Karfe 1:30am na dare*

Wani irin sauti ne mai Kama da kukan mujiya ke tashi mara daɗin ji balle sauraro a wani babban wuri ko in ce babban ɗaki mai ɗan duhun  sai hasken wutar candle da bai wadaci ɗakin sosai ba,mutane ne sama da goma sanye da baƙaƙen kaya fuskokinsu da Zanen  baƙin fenti,kowannansu na ɗauke da wani kambu mai kwalliyar maciji a dantsan hannunsa,a yatsansu na manuniya  zoben gold ne mai kwalliyar maciji,kowanne a cikinsu fuskar nan babu annuri balle ɗigon imani,kowa yasha mur! Kamar jira suke ace kule su ce chas! 

Sun yi circle hannayansu riƙe da ƙoƙo shima anyi masa kwalliyar maciji, a tsakiyar ɗakin gunki ne mai suffar gabjejan maciji ya fasa kai a cikin bakinsa akwai wutar candle tana ci,an yi  gunkin ne da ruwan zinari  sai walwali ya ke.Lokaci guda suka fara surkulle suna faɗin wasu yarurruka wanda bansan daga ina suka samo yaran ba,har da muryoyin mata a cikin masu surkullan, sosai suke surkullan tun suna yi a hankula har koma yinsa da ƙarfi kuma da sauri-sauri, ga sautin nan mai kama da kukan mujiya sai ƙara ƙarfi ya ke, babu zato babu tsammani wani abu mai nauyin gaskiya ya sauka ji kake Dammmmmm! Sai da ƙasa ta girgiza babu wanda a cikinsu ya yi gezau sai ni mai ɗaukar rahoto domin na firgita matuƙa-ainun,su kuma ko a jikinsu basu tsaya da surkullansu ba. 

Juyawan da zan yi sai da ƙirjina ya yi matuƙar mugun faɗuwa ganin wani gabjejan mutum mai suffar samudawa, shima ya yi shiga kalar tasu amma akansa akwai golden ring Irin na sarakuna mai kwalliyar kan maciji, a gefansa wani ƙasurgumin maciji ne baƙi siɗik! Kana ganinsa kaga *Mesa* mai haɗiye mutane,sai huci ta ke tana fidda harce.Baƙi ne mutumin fuskarsa babu  kyawun gani kamar dodo haka ya ke,idanunsa fari ne babu baƙar tsakiya,yana da sharɓeɓan leɓe na sama,ƙasan leɓensa ƙarami ne wanda ya shige ciki sosai.Takawa ya yi zuwa wata kujerar zinari a samanta kwalliyar maciji ne,yana tafiya ƙasa na girgiza shi kuma macijin na biye dashi,direct ya nufa kujerar ya zauna shi kuma macijin ya nannaɗe a saman wata kujerar zinari wacca ta Ke kusa da na basamudan, kamar jira suke ya zauna shida macijin sai suka tsaya cak! Daga surkullan tare da russunawa don miƙa gaisuwa garesu.Shiru wurin ya yi kamar ɗaukewar ruwan sama,ga sautin kukan mujiya na tashi sosai. 

Cike da amon murya mai firgitarwa basamudan ya fara magana yana kallon wani a cikinsu

"Kai Sambo Dala Linkaku!!!" 

Da sauri Alhaji Sambo Dala wanda sai yanzu na gane shi saboda sauyawar da yayi ya ɗago yana kallon shugabansa,cike da rawar baki ya furta 

"Na'am ya mai girma Demon King" 

Cike da amon murya wacca tafi ta ɗazu ya ci gaba da cewa

"Ka saɓa dokar ƙungiya Linkaku!!! dole doka ta yi aiki a kanka!!!" 

Sosai hantar cikin Alhaji Sambo Dala ta kaɗa, yasan hukuncin ƙungiya ba mai sauƙi ne, cike da rawar murya ya ce

"A yi min afuwa shugaba kuskure..." 

"Rufemin baki Linkaku ko kuma na aiwatar da hukuncin ƙungiya akanka!!! Ka bar yarinyar ta gudu bayan kasan  mun kai tsawan shekara hamsin muna jiran zuwanta duniya!!! Ita ce mahaɗar ɗaukakarmu!!! Ita ce wacca DODO ƘURNUSSA ya jaddada kar muyi sake ko wasa wurin nemota amma bayan ka nemota sai ka yi sake har tabar gidanka!!!! Bar ganinta yarinya itama sheɗaniyar kanta ce!!! Tana da ifiriɗan aljanu masu ƙarfi da taurin zuciya, suna matuƙar taimaka mata a duk inda ta ke!!! Linkakuuuuu!!! "

Da sauri ya amsa da 

" Na'am Demon king"

"DODO ƘURNUSSA ya baka daga yau zuwa wata biyu ka binciko duk inda ta ke a faɗin duniyar nan ka kawo ƙungiya, kuma kai za ka yi aikin babu taimakon kowa a cikin ƙungiya,saura wata huɗu yarinyar ta cika shekara 23 dole mu fara aiki akanta kan ta cike shekera 23, idan baka bincikota ba to kasaniiii! DODO ƘURNUSSA zai yi fushi da kai sannan hukunci zai  sauka akan ahalinka baki ɗayaaaa!!!! 

Da wani irin ƙarfi zuciyar Alhaji Sambo Dala ta bada Dummmmmm!!! Lokaci guda ƙwaƙwalwarsa ta tafi  wucin gadi na ƴan wasu sakanni,jiri da niyyar kai shi ƙasa amma ya dake,bibbiyu ya ke kallon kowa, cike da matuƙar tsoro da firgici ya duba Demon King... ✍️




*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
 ***