BA NI DA MADOGARA

Chapter 5

by @narrnarhhbukar00

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*









*Bani da Madogara*
  (Sai Allah...)





005


Da wani irin ƙarfi zuciyar Alhaji Sambo Dala ta bada Dummmmmm!!! Lokaci guda ƙwaƙwalwarsa ta tafi  wucin gadi na ƴan wasu sakanni,jiri na niyyar kai shi ƙasa amma ya dake,bibbiyu ya ke kallon kowa, cike da matuƙar tsoro da firgici ya duba Demon King da DODO ƘURNUSSA wanda ya ke a suffar maciji ya ce

"Zzzann nnemota! Na kawoo nnann amma karku taɓa ahalina"

"Da yafi maka kwanciyar hankali idan ka yi hakan ko kuma ka fuskanci mummunan hukunci akan ahalinka dama kai karan kanka Linkakuuu! "cewar Demon king cikin amon muryarsa mai firgitarwa

Jinjina kai Alhaji Sambo Dala ya yi ba tare da ya sake cewa komai ba,Miƙewa Demon king ya yi Zuwa tsakiyar ɗakin inda babban gunkin maciji yake macijin na biye dashi har tsakiyar ɗakin, ba a fi minti ɗaya da zuwansa tsakiyar ɗakin ba sai jerin mutane har su biyar da jajayan kaya fuskarsu a rufe suka shigo ɗakin a ta wani ƙofa, hannan kowanne riƙe da  ɓaƙar ƙwarya,a natse suke tahowa cikin ɗakin,sautin kukan mujiya na sake tashi da ƙarfi,har inda Demon king da macijin yake suka je, suna zuwa wurin suka sunkuyar da kansu suna miƙa gaisuwa,jinjina masu kai Demon king ya yi Sai suka nufi wani wuri a cikin ɗakin suka tsaya kasancewar ɗakin babba ne sosai, basu daɗe da zuwa ba sai ga wasu mutane da shigar ɓaƙaƙen kaya, ba a ganin fuskokinsu hannayansu ɗauke da plate, Sai a wannan karo naga abinda ke saman plate ɗin domin mutanen farko masu ƙwarya mutum baya iya ganin abinda suka ɗauko a cikin ƙwaryar saboda  zurfin ƙwaryar, da yake wannan plate ne sai idanuna suka yi arba da abinda yaso rikirkitamin ƙwaƙwalwa da lissafina sosai hankalina ya tashi ganin sassan jikin mutane musamman ma yara a saman plate din sai turiri suke da alamu anyi pepper soup ɗinsu ne,kamar yadda mutanen baya suka miƙa gaisuwa ga demon king haka suma suka yi tare da samun wuri suka tsaya. 

Ɗaya bayan ɗaya, layi na bin layi su Alhaji Sambo Dala suke zuwa suna miƙa ƙoƙonsu ga wa'innan mutannan na farko suna zuba musu wani kalar ruwa ja sosai, duk wanda aka zuba ma ruwan sai ya amshi wani sashe na daga cikin jikin mutum wanda yake saman plate ya koma wurin tsayuwansa, haka kowa ya amsa Demon King aka kawo mishi nashi cikin babban ƙoƙo wanda yafi nasu girma da kyau, sai a sannan ne mutanen nan suka koma ciki ta inda suka fito. Demon king ya miƙa ƙoƙonsa sama suma suka miƙa nasu ƙoƙon sama suna wani surkullen daban ba wanda suka yi a farko ba, sannan kowanne a cikinsu ya kafa kai ya shanye wannan jan ruwan tas!, sai faman lashe baki suke, inda hankalina ya yi matuƙar tashi sosai shi ne ganin sassan jikin mutane suna ci suna santi kamar sun samu naman kaza. (My Esteem fans a gaskiya na kusa gudu da kayan ɗaukar rahotona, don bazan iya ganin ana cin naman mutum a gabana ba, Allah kasa mu dace😞😞😞) 

Haka suka ci gaba da cin naman suna santi, bayan sun kammala cin naman lokaci guda suka kwashe da dariya mazan da matan,basu yi minti uku da kammala ciye-ciyansu ba sai majicin nan ya rikiɗa ya koma wani gabjejan basaƙarƙaran dodo mai mummunan suffa,nan take kowa ya zube ƙasa har da Demon king suna miƙa gaisuwansu ga dodonsu,babu wanda a cikinsu ya iya ɗago kansa ya dubi dodon,da wani irin ƙarfi ƙirjina ya bada Dammm! Dammm ! Dadammmm! Lokacin da na ɗago kaina na dubi dodon, tabbas! Wannan dodon ya ci sunansa DODO ƘURNUSSA suffarsa ba abin kallo bane ga mutum, don idan mace mai ciki da kalli Dodon nan to da wuya bata yi ɓari ba tsabar firgici, ,yanada matuƙar tsawo sosai don duk girman Demon King sai naganshi ɗan ƙarami a gabansa,balle a je gunsu Alhaji Sambo Dala, kamar ƙananun ƙwari suke a gabansa, suffa biyu ne dashi,suffar maciji da suffar mutum, gangan jikinsa na mutum ne,kan mabanbanta macizai bakwai ne akansa,a tsakiyar kan akwai ido ɗaya mai girman gaske, babu alamar baki balle hanci,kan macizan sai juyi suke suna fidda harshensu, Sannan harshen kowannansu tsaga biyu ne,yatsun hannayansa da na ƙafarsa ba irin na mutane ba ne, don bindin macizai ne a madadin yatsun.A tsakiyar randameman cikinsa zanan baki ne mai faɗi da girma,sai a sannan ne naga bakin har da haƙora.Haka ya tsaya ƙiƙam! Da wata iriyar murya ya fara magana cikin wani irin yare na daban wanda Demon king yake fassara ma su Alhaji Sambo Dala, su kuma cikinsu sai tsuma yake suna jinjina kai kamar wasu ƙadangaru, suna kammala zantawa lokaci guda a tare suka ɓace ɓet! Sai a hankali ginin shima ya baje, babu abinda kake iya gani illa ruwa wanda bai da iyaka,gabas,kudu, arewa da yamma baka iya ganin ƙarshen ruwan don babban ruwa ne mai girman gaske... ✍️


*Tarihin Ƙungiyar Black Pytons Society*

Ƙungiyar Black Pyton Society Ƙungiya ce ta tsagerun ƴan mafiya wanda a turance ake kiransu da ƴan secret cult.An kafa ƙungiyar ne shekaru 60 da suka wuce, tana da members a ciki da wajen Nijeriya sannan akwai rassanta a ƙasashe goma a Africa irinsu Niger,Mali, Burkina Faso, Congo, Kenya, Zimbabwe, Chad, Cote d'Ivoire,Ghana da Benin Republic,sai gudu huɗu a wasu ƙasashen fararan fata irinsu India, London, Australia,America.Main branch na ƙungiyar a Nijeriya take. 

Demon King ne ya kafa ƙungiyar da taimakon wani Ifriɗin aljani mai suffar maciji,a cikin jinsin aljanu suna kiransa da ƘURNUSSA,kuma koda Demon king ya kafa ƙungiyar sai ba a canja mishi suna ba ake kiransa da DODO ƘURNUSSA.Demon king wanda a zahiri shaihin malami ne mai da'awar addinin musulunci ana kiransa da *Sheikh Munnir Haladu Al-Misriyy* ,a zahiri shi malamin addini ne amma a baɗini shi cikakkyen malamin tsubbu ne mai aiki da ifriɗan aljanu,a aikinsa na tsubbu ne ya haɗu da wannan sheɗanin aljani mai suffar maciji wanda ya mishi alƙawarin ɗaukaka da samun alatun duniya idan ya haɗakai dashi ya bashi abinda yake buƙata,kasancewar Sheikh Munnir akwai shi da son abin duniya da son ɗaukaka kawai ya yarda da majar suka haɗe kai bayan DODO ƘURNUSSA ya sanar masa da sharaɗin zamantowarsu tare ba komai bane illa zubda jinin ɗan Adam musamman yara ƙananu,sosai ya aminta da sharaɗinsa saboda zai haɗa kai da manyan mutanen da suke zuwa wurinsa neman taimako don ɗaukaka,siyasa,kuɗi da kasuwanci, hakan kuwa aka yi don duk wanda Sheikh Munnir ya yi masa maganar shiga ƙungiyar da sauri yake amincewa har da sharudɗan da DODO ƘURNUSSA daya gindaya, a haka manyan mutane maza da mata su kai ta shiga ƙungiyar, daga cikinsu akwai Alhaji Sambo Dala wanda ya zo neman taimako na ɗaukaka, dukiya da siyasa saboda ɗan uwansa wanda suke uba ɗaya ya fishi kuɗi da ɗaukaka shi yasa ya bazama neman dukiya da ɗaukaka kota halin ƙaƙa ne burin sa kawai yaga yafi ɗan uwansa komai,tunda Sheikh Munnir ya sanar masa da wannan ƙungiyar bai yi wata-wata ba ya amince. Tun ƙungiyar na guda ɗaya har ta koma biyu daga biyu ta koma mai rassa da yawa a Africa da kuma India.Da taimakon DODO ƘURNUSSA da wasu ifriɗan aljanu suka gida tanƙameman gida a ƙasan wani baban ruwa, komai ya suke buƙata akwai shi a gidan.Duk ƙarshen shekara members ɗin ƙungiyar ciki da wanjan Nijeriya suke haɗuwa don yi meeting a gidan da yake a ƙasan ruwa

DODO ƘURNUSSA ya sanar ma Sheikh Munnir wato Demon king za a haifi yarinyar da mahaɗar ɗaukakarsu ta ƙarshe take a tattare da ita, Idanunta su za su kasance masu yajo hankalin mutanan duniya baki ɗaya akansu, sai zuciyar kuma za ta kasance kowa zai so su ya ƙaunacesu,za su ɗaukaka matuƙa ainun,za su yi kuɗi sosai wanda babu kamarsu a faɗin duniya,dole su nemota sannan karsu bari ta wuce shekara 22  ba tare da sun nemota ba, don aikin da zai yi akanta dole a farashi tun tana shekara 22 don da ta cika shekara 23 zai cire Idanunta da zuciyarta da kansa. Dalilin haka yasa kowa a cikin ƙungiyar na ciki da wajen Nijeriya bazama neman birni da ƙyau wanda kowa ya yi ƙoƙarinsa matuƙa amma Alhaji Sambo Dala ya takasu sannan ya damesu a wurin neman son ɗuniya da ɗaukaka, shi yasa ya baza yaransa ciki da wajen Nijeriya, birni da ƙauye wanda a ƙarshe ya yi sanar ganinta a wani ƙauye mai suna Kwanar kwara ƙwai lokacin tana da shekara 12 a duniya, koda ya sanar ma Demon King ya yi farin ciki sosai, sai ya ce ya ci gaba da kula da ita har lokacin da za ta shekara 22 a duniya sai ya kawo ta ƙungiyar don DODO ƘURNUSSA ya fara aiki akanta.Wannan kenan. 

         🌎🌎🌎🌎🌎🌎

A ɓangarensu Eze bincike iya bincike sun yi, lungu da saƙon garin Bauchi babu inda basu shiga ba,har da ƙauyakun dake garin Bauchi sun zagaya kasancewar suna da yawa masu nemanta sannan sun rarrabu zuwa ɓangarori, wasu ɓangaren suka shiga cikin gari, wasu dazuzzukan musamman dajin da a can ne Hujayrah ta ɓace musu, wasu  kuma suka nosa ƙauyaku.Sosai hankalin Eze ya ƙara tashi saboda kowa ya kira a cikin masu nemanta magana ɗaya ce basu ganta ba,shi tsoransa ɗaya kar mai gidansa ya hallaka rayuwarsa da na iyalansa don hatsabibi ne na ƙin ƙarawa,bai da mutunci sannan bai da imani inda akan cikar burinsa ne, bai ƙi ran kowa ya salwanta ba in har burinsa zai cika, akwai matsala tabbas in dai bai gano yarinyar ba.Tun safe suke nemanta har dare basu ganta ba,mai makon su huta amma ina kamar an ƙara musu ƙwazo da karsashi wurin nemota, har wayewan gari suna nemanta,sosai hankalin Eze sake tashi tsoransa idan har yau basu ganta ba, to kashinsa ya gama bushewa,haka suka ci gaba da nemanta, wanda har daran ranar basu ganta ba. 

Cikin dare bayan Eze da wasu masu taya shi nemanta sun dawo gida,suna zaune suna hutawa kamar walkiya babu zato babu tsammani suka ji maganar Alhaji Sambo Dala a bayansu,cike da tsawa ya ce

"Ina take Ezeeee!" 

Ai wata iriyar ƙundumbala Eze ya yi har sau biyu ya yi saurin dawowa cikin hankalinsa,hantar cikinsa ta yi matuƙar kaɗawa,cikinsa ya bata wani sauti ji kake Ƙulululuuuu!!! Nan take ya fara jin kashi,ƙirjinsa na ba da nashi sautin na musamman, cike da tsoro da firgici haɗi da inda-inda ya ce

"Sssirr har yanzu muna kkann nnemmanta..." 

"Are you stupidddd! You are telling me Har Yanzu Kuna kan nemanta, ka manta wane ne ni,kwana biyu sun cika amma baka ganta ba" 

A zafafe yake maganar yana kallon Eze duk ilahirin jikinsa rawa yake tsabar fushi,idanuna kamar bana mutane ba saboda sauyawar da suka yi zuwa ja,jijiyoyin kansa da na wuyansa duk sun tashi.Ba ƙaramin shiga ruɗu Eze ya yi ba don yadda halittar mai gidan nasa ta koma abar tsoro ce musamman ma shi da ya yi sanadiyyar ɓacewar cikar burinsa.Shiru ya yi yana kallon ƙasa don bazai iya haɗa raunannun idanunsa da nashi ba.Da wani irin ƙarfi ƙirjinsa ya ba da Dummmmm! Jin Mai gidansa na faɗin a yau ba sai gobe ba zai hallaka ɗiyarshi,lokaci guda  ƙwaƙwalwarsa ta tafi wucin gadi na ɗan wasu sakanni.Zubewa a ƙasa Eze ya yi tare da sakin kuka mai ratsa jini da ɓargo har da zukatan masu sauraronsa ,cikin muryarsa wacca bata fita sosai  saboda kukan da yake ya fara roƙon Alhaji Sambo Dala akan ya yi haƙuri kar ya kashe mishi kudan jininsa tilo a duniya,amma ko ɗar! Na tausayi bai wanzu a zuciyar Alhaji Sambo Dala,sai ma ƙara zafafa da zuciyarshi ta yi.Wayarsa ya ɗauko daga aljihu ya bude tare da nuna masa Video na yarinyarsa an saka mata wuƙa a wuya, mahaifiyarta sai ihu take an ɗaureta,tana ta faɗin 

"Yeeee! my daughter ooooo! Don't kill her please! I beg u in the mighty name of Jesus, please don't take Her life, yyeeeee!!!! Chineke ooooo ahhhhh!!" 

Sosai take kuka duk wanda ya ga matar a lokacin dole ya tausaya mata amma babu tausayi da imani Alhaji Sambo Dala ya faɗi kalmar *Done* kawai mutumin ya ja kaifaffar wuƙar a wuyan yarinyar, nan take ta faɗi jini ya ɓalle, ita kuma mahaifiyarta ta sume. Da ƙarfi Eze ya saki ƙara ganin ƴarshi a ƙasa ta mutu ga matarshi ta suma,hannu yasa a kansa yana ihu kamar wani zautacce mai sabon hauka,sauran masu aiki dake a wurin sai da suka sha jinin jikinsu tare da alƙwarin taka-tsantsan a duk aikin da ya sakasu kar a samu matsala hukunci ya shafi iyalansu.

Da alama ƙwaƙwalwar Eze ta taɓu don sai sumbatu yake yana kiran sunan ɗiyarshi tare da girgiza kansa yana cewa

"Chioma my pikin don go ooooo! She Don gooooo! Yeeeeeh! My daughter my Chioma, my Angel ahhhhhh! Chineke ooooo! yeeeeee!!" 

Ko a jikin Alhaji Sambo Dala ya tambayi daya naga cikinsu ya ce

"Habib Ina Black Scorpion Sqaud suke" 

Cike da girmamawa Habib ya ce

"Yallaɓai sun je ɗauko yaran da ka umurcesu a  Kwara State,cikin daran nan zasu iso" 

"Fine Inaso kuyi aikin tare dasu don nasan basu da wasa kamar shashashan nan" 

Nuna Eze ya yi wanda sumbatunsa yake yana kiran ɗiyarshi, ya ci gaba da cewa

"Inda Black Scorpion Sqaud ne suke tsare da yarinyar da bazata gudu ba, amma shegan ya sha giya ya yi mankas! Yabar ta da gudu daga gidan mtwsss! Ehen! Kamar yadda Eze ya suffanta muku yarinyar Inaso su nemota a duk faɗi Nijeriya da wajanta, nasan I won't have any problem with Black Scorpion Squad Sai dai ku,kunga dai yadda na hukunta Eze, so believe me Idan kuka yi kuskure irin nasa to hukuncina akanku ba zai yi muku daɗi ba,daga yau zuwa kwana 60 wato wata biyu ku nemo yarinyar, har da wasu State ɗin ma ku dubata,zan kira yarana na Kaduna su duba ƙauyan da na ɗauko yarinyar ko ta koma can, nima zan ci gaba da nemanta"

Jinjina masa kai suka yi sai ya ɓace daga idanunsu, dole su yi taka-tsantsan da mai gidan nan nasu don sheɗani ne na gasken-gaske.(My Esteem da alama basu san Demon King ba shi yasa suke tsoran Alhaji Sambo Dala Linkakuuuu ko shi Linkakuu tsoran Demon King yake😂😂😂😂)... ✍️

                    🌎🌎🌎🌎🌎🌎

A ɓangaren Hujayrah baiwar Allah baccinta take sha kashirɓin wanda ba ita ta farka ba sai wurin sallar Zuhr, kiran sallar ne ma ya sakata   farkawa, a hankali ta tashi daga kwancen ta zauna,idanunta sun ƙara manya saboda baccin da tasha,sai kallon kai kawon mutane take a zaunan,ganin kar lokaci ya ƙure mata bata yi sallah ba yasa ta miƙe a hankali tana yamutsa fuska,jira tayi sai da aka kabbara sallah lokacin wajan inda ake alwala babu kowa sannan ta taka a hankali zuwa wurin da ake alwalar, zama ta yi ta ajiye Jakarta a gefe sannan ta fara alwala bakinta ɗauke da niyya, a natse take alwalar har ta kammala ta ɗau jakarta ta saɓa a hammata sannan ta koma inda ta taso,kabbara sallah ta yi, a natse ta yi sallah bayan ta kammala ta sake kabbara sallar na nafila raka'ah biyu daban-daban,duk sujjadar da za ta yi sai ta roƙi Allah ya tsare ta daga sharrin Alhaji Sambo Dala da maƙarrabansa, har da Baba Zakari sai da ta haɗa dashi a cikin sujjadarta. Bayan ta kammala nafila sai ta miƙa ƙafarta tana hamma,tabbas yunwa take ji bara ta miƙe ta kaga gari in ji Hausawa suka ce na zaune bazai ga gari ba. Miƙewa ta yi tabar masallacin ta ci gaba da tafiya ga yunwa na ƙwaƙular cikinta,haka ta yi ta wuce layuka ba tare da zauna don hutawa ba.Sai can ta ga wani gidan cin abinci mai kyau, wasu mata na wanke-wanke a wani ɓangare na gidan abincin,sosai gidan abincin ya haɗu, ga ƙamshin abinci sai tashi yake hakan ya saka Hujayrah jin wata mahaukaciyar yunwa,ganin tsayuwanta ba komai zai daɗa mata ba illar ƙarin yunwa sai kawai ta yanke shawarar zuwa wurin matan nan da suke wanke-wanke a wurin gidan abincin. 

"Assalamualaikum" cewar Hujayrah tana sakar musu murmushi har fararan haƙoranta na bayyana

Amsa mata sallar suka yi suna ci gaba da aikinsu, gyara tsayuwanta ta yi sannan ta ce 

"Don Allah tambaya nake ni baƙuwa ce a garin nan" 

Babu wanda yabi takan zancenta illar wata budurwa sa'arta wacca tunda Hujayrah ta yi sallama ta amsa mata ita ma da murmushi a fuskarta.Wanke hannunta ta yi sannan ta miƙewa zuwa inda Hujayrah take tana cewa

"Sannu da zuwa, mece ce tambayar taki" 

Tsayuwa Hujayrah ta gyara tare da saɓa jakarta da kyau sannan ta ce

"Ƴar uwa gidan abincin nan suna bama baƙi abinci kyauta" 

Da sauri budurwar ta kalli Hujayrah ƙasa da sama sannan ta ce

"Kyauta! Tab! Da alama daga ƙauye kika fito, a ina kika taɓa jin an ba baƙi abinci kyauta in ba kuɗi za su ciro daga aljihunsu su siya ba" 

"Tooooo! Au abun haka yake" 

"Sosai ma Kuwa, halan baki da kuɗi ne" 

Ɗaga mata kai Hujayrah ta yi, murmushi budurwar ta yi sannan ta ce

"Idan babu matsala mai zai hana na haɗaki da Hajiyarmu sai ta baki aikin koda wanke-wanke ne sai a baki abinci har da kuɗi" 

Riƙe baki Hujayrah ta yi tana cewa

"Laah da gaske za a bani abinci har da kuɗi, wallahi zanyi zanyi" 

Sosai Hujayrah take murna sauƙi yazo mata, garaɓasa biyu ga abinci ga kuɗi.Shikenan sai ta tara kuɗin ta yi na mota zuwa garinsu. Budurwar ce ta ce

"Amma ya sunanki to" 

Cike da farin ciki wanda fuskarta ta kasa ɓoyewa ta ce

"Sunana Hujayrah" 

"Kai sunanki akwai daɗi wallahi, ni kuma Sunana Rabi'ah amma ana kirana Rabi" 

"ke ma sunanki da daɗi" 

Katse musu hirar wata daga cikin matan da suke wanke-wanke ta yi da  cewa

"Rabi wai me ya tsayar dake ne da ba zaki zo mu ci gaba da aikinmu ba, ke ga me shegen wayo wato muyi miki aiki a raba mana abinci da kuɗi iri ɗaya, mtwsss! Dallah malama kizo mu ci gaba da aiki" 

Jikin Rabi na rawa ta ce 

"To" 

har zata wuce Hujayrah ta ce

"Amma ke matsoraciya ce wallahi, wannan matar ce kike tsoro har jikinki ya fara ɗaukar ɗan mazari, Tab! Zo muje wurin Hajiyarmu in yaso daga baya na tayaki aikin, idan kuma ta ce za ta dukeki ni Hujayrah ɗiyar Audu jikar Kamalu Angon Hindatu mai tsoran mutuwa zan shigar miƙe koda ba ita kaɗai bace "

Sosai ta yi mamakin Hujayrah ganin idanunta babu tsoro balle firgici,jan hannunta Hujayrah ta yi matan wurin sai kiran Rabi suke amma Hujayrah taƙi sakinta sai janta take suka bar wurin.

Direct Rabi ta nufi cikin gidan cin abincin da Hujayrah,sakin baki Hujayrah ta yi tana kallon kyau da tsaruwan gidan,sai kalle-kalle take tana murmushi. (My Esteem fans don Allah kuyiwa Hujayrah nasiha ta daina nunawa daga ƙauye ta fito don za ta kwafsa mana dayawa 😂😂😂) 

Gidan abincin yana da ɓangarori ya yawa, akwai babban falo inda kujeru ta taburan cin abinci suke,har da tanƙameman plasma TV a falon, mutane na cin abinci hankalinsu kwance,haka suka wuce falon zuwa wani ɗakin 

"Wayyo Uwata ni jikar Hindatu mai tsoran mutuwa! Kanbatasi Aljannar duniya" cewar Hujayrah ganin ashe falon ba kallo ta yi ba nan ne kallon yake,murmushi Rabi ta yi suka ci gaba da tafiya har suka wuce sashe masu girki, da sauri Hujayrah ta cema Rabi 

"Ni wallahi Hajiya kawai ta ajiyeni a wurin girka abinci" 

Dariya Rabi ta yi bata ce komai ba don taga alamar Hujayrah Ƴar daru ce akwai sukuru, wani hadɗan ɗakin ne har da gado Rabi ta shiga da sallama, Hujayrah ma tabi ta ciki da sallama. Wata mata ce mai ɗan ƙiba a zaune bisa cushion tana kallon tv hankalinta kwance ta amsa musu sallamar ba tare da ta ɗago ta dubesu ba. 

Zama a ƙasa Rabi ta yi ita ma Hujayrah ta zauna yadda taga Rabi ta yi. Cike da girmamawa Rabi ta ce

"Hajiyarmu mun zo wurinki ne" 

Ta kai minti goma ba ce dasu komai tana kallonta, har Hujayrah ta fara cilla mata hararar ƙasan ido don a rayuwar ta tsani masu wulaƙanci. Sai da Hajiyar ta mulla ta mulle sannan ta juyo ta dubesu ta cewa

"OK ina saurara ki Rabi" 

Gyara zama Rabi ta yi, cike da ƙanƙan da kai ta ce

"Hajiyarmu ga baƙuwa nan ta ce tana so ta yi aiki damu in da halin da kuma yiyuwar hakan" 

Hajiya bata ce komai sai kafe Hujayrah da ido ta yi, tana kallonta babu ko ƙiftawa,sai can ta ce

"Ya sunanki ƴan mata" 

Cike da ladabi kamar yadda taga Rabi ta yi mata har ƙarawa da iyayi Hujayrah ta ce

"Hajiyarmu mai share kukan mu sunana Hujayrah" 

Sosai Hujayrah ta birge Hajiya don a rayuwarta tana so a girmamata, sai lokaci guda Hujayrah ta shiga ran Hajiya,fuskarta a sake ta ce

"A wani gari kike" 

Tashin hankali nan da nan Hujayrah ta rasa makama, sai can dubara ta zo mata, sai ta yi fuskar tausayi ta ce

"Hajiyarmu mai share kukanmu ni kawai na tsinci kai na ne a garin nan, bansan Kowa ba bansan sunan garin nan ba, ni Ƴar Kaduna ce a kwanar Faru ƙwai mahaifana suke, dalilin son fara aiki a nan shi ne  don na tara kuɗin mota na koma gida koda sati biyu ne nayi a nan"

"Allah sarki Hujayrah ki ce sace ki aka yi, mutane! Mutane! Basu da imani, babu damuwa Hujayrah za ki zauna a gidan nan ki yi aiki har ki samu kuɗin zuwa garin in shaa Allah, idan ma na samu kuɗi sai na baki kawai ki wuce gida kar hankalin iyayenki su tashi"cewar Hajiya tana ƙara tausayawa Hujayrah 

Sosai Hujayrah ta shigo gode ma Hajiya tana jero mata addu'o'in nasara da ci gaba a rayuwa,Hakan kuwa yama Hajiya daɗi a rai, nan take ta ce a je da Hujayrah masaukin ƴan aiki sannan a kawo mata abinci tashi kafin a sanar mata da aikinta.fita suka yi daga ɗakin amma bakin Hujayrah bai daina godema Hajiya ba har suka bar ɗakin, direct Rabi ta kai ta masaukinsu inda suke kwana, babu laifi ɗakin babba ne sosai, akwai gadajen  kwana irin da ƴan bodin skul da yawa a ɗakin ga wata ƙofa wanda nake kyauta zaton bayi ne, wurin wani gado Rabi ta je da Hujayrah tana cewa

"Ga gadonmu nan sai ki zaɓa sama kike so ko ƙasa za ki dinga kwana, a gaskiya ke Ƴar baiwa ce Hujayrah nayi mamakin lokaci guda Hajiyarmu ta amince ba tare da ta yi halinta na kafiya ba, murmushi Hujayrah ta yi ba tare da ta ce komai ba sai ma zama da ta yi a bisa gadon tana shafa katifar tana murmushi, Rabi na fita daga ɗakin zuwa ɗauko mata abinci, Hujayrah ta yi wata ƙundumbala tana cewa

"Honi Honi jikar Hindatu mai tsoran mutuwa, wannan gado haka, ga abinci, ga kuɗi kai anya zan koma gida kuwa wannan daɗi bisa daɗi haka hhhhhhhh!!!" 

Surutunta take ita kaɗai tana dariya har Rabi da dawo da plate ɗin abinci da sachet water mai sanyi, sauka ƙasa Hujayrah ta yi tare da cire hijab ɗinta ta linke sannan ta yi bismillah ta fara saɓa loma hannu baka hannu ƙwarya, tas! Ta cinye abincin tare da yin gyatsa sai ta yi hamdala ta godewa Allah sai sannan ne ta lura da Rabi bata ɗakin.Miƙewa ta yi ta shiga bayin ta wanko hannunta sai ta ji kamar ana hayaniya a bayan ɗakin inda ake wanke-wanke da sauri ta sako hijab ɗinta ta fito zuwa wurin. 

Rabi ce a tsakiyar matan nan na ɗazu tana kuka su kuma nuna mata masifa a kai, ai da sauri Hujayrah ta je gun tana cewa

"Rabi mai ya sameki kike kuka" 

Wata a cikinsu ne ta ce 

"Marinta nayi ko za ki..."

Bata ƙarasa maganar ba ta ji saukan zafafan maruka hagu da damanta ji kake tas! Tas! Ai da sauri matar ta  riƙe kumatunta hannu biyu don ba ƙarya ta ji marin sosai,Hujayrah na huci ta ce... ✍️

                🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Kwanar faru ƙwai, Kaduna state. Nijeriya *

A ɓangaren Alhaji Zakari bayan ya faka machine ɗinsa a wajan bishiyar mangwaro sai ya shiga gidan dadironsa da sallama, wata a cikin gidan ne ta amsa masa tana kashe murye ko za ta yi kasuwa,idanunsa ƙyar! Akanta yana lashe baki kamar wani maye ya ce

"Bintoto na ciki ko" 

Juyi ta yi tana wata girgiza ko'ina na jikinta ta rawa ta bashi amsa a yangan ce ta ce

"Ehhhh Tana ciki Alhajin muuuu!" 

Sosai salon karuwar ya rikita Alhaji Zakari ya ce 

"To to to, amma ɗan bani numbanki nama Hajiya ta" 

Yana kashe mata ido da nashi salon na barikanci, babu musu ta bashi numbanta sai ya wuce inda ɗakin Bintoto yake wacca ta kasance dadironsa, a duk lokacin da ya zo garin sai ya je gurin ya rage gajiya kuma sun daɗe a tare,matar da ta amsa mishi sallama bai santa ba, don duk zuwan da zai yi bai ganinta da alama sabuwa ce,ai kuwa zai zuba harka da ita, sai zancen zuci yake har ya iso inda ɗakin Bintoto yake, da sallama a bisa labɓansa ya shiga ciki.Amsa masa ta yi tana miƙewa zuwa inda yake babu ta zo babu tsammani ta rungume Alhaji Zakari, ai nan take ya ɗauke wuta. (O'oo'oo su Alhaji Zakari wannan ɗauke wuta haka,😂😂😂, kar a manta dai akwai yara har da jikoki, a ji tsoran Allah tammm ni babu ruwana koya kuka ce My Esteem fans 🤭🤭🤭) 

Lokaci guda Alhaji Zakari jikinsa ya fara tsuma, bai yi wata-wata ba ya tsunduma da ita cikin masha'a basu ji basu gani illa abinda suka sa gaba,sun daɗe suna masha'a sai daga bisani kowa ya dawo cikin hankalinsa, ba wata sitirar kirki a jikinsu, shiru ɗakin ya yi sai daga bisa Bintoto da dubeshi ta ce

"Alhaji yau bada wuri za ka gida ba ko" 

Murmushin yaudara ya yi yana dubanta ya ce

"Karki damu sahibar zuciyata, ai zan zo garin nan bada jimawa ba" 

"To Allah ya yarda" 

Ciro kuɗi masu yawa ya yi daga aljihinsu ya bata sannan ya tashi ya sanya kaya,koda ya fito bai ga  karuwar nan a tsakar gida ba ya ficewarsa,garinsu ya nufa lokacin ana kiran sallah Zuhr, har sashensa ya shiga da machine ɗinsa ya faka a inda yake ajiyeta, cikin ɗakin ya shiga da Sallama, Hannatu ta amsa masa tana shafa hoda a fuskarta,lallausan murmushi ya sakar mata sannan ya ce

"A'ahhh uwar gidan ran gida sai ina haka" 

"Unguwa za mu nida Innar Balki" cewar ta tana shafa kwalli a idonta,ƙanƙance muryarsa ya yi yana cewa

"Ko na yi rakiya ne" 

"A'a ai ka fita muma fitar za mu zuwa suna" 

Zama ya yi bisa cushion yana cewa

"A dawo lafiya" 

"Ameen"

Tana yafa gyalanta ta fice abin ta, shi kuma zama ya yi yana tuna garar daya kwaso ɗazun wurin Bintoto da badan-badan ba da aure Bintoto zai yi kawai, don tana da ni'ima sosai shiyasa baya gajiya da ita amma Hannatu ta yi baka-baka ta hana kowacce shigowa,daga ita sai ita. Yana zaune sai can ya ji kamar muryan Musa, ai nan da nan ya ciro kwallin da Malam Tani mai allon ƙarfe ya bashi,kamar yadda ya umurcesa ya saka haka ya saka don a duk abinda zai yi yana taka-tsantsan, miƙewa ya yi ya fita ba tare da ya yi wankan janaba balle sallar Zuhr ya fice abinsa. 

Ya koyi sa a Baba Musa na tsakar gida suna gaisawa da Attine ƙanwarsa,bai ce dasu komai ba sai kawai ya kira sunan baba Musa, shima sai ya amsa yana kallonsa, nan take idanunsu suka  sarƙafe dana juna, sai Alhaji Zakari ya ce

"To ya batun zuwan namu gobe" Yayi maganar ne don ya gwada yaga ko maganin ya yi aiki, ɗan shiru Baba Musa  ya yi sai can ya ce

"Ban gane zuwa ina ba daman munyi magana da kai  zamu fita gobe ne" 

Jinjina masa kai Alhaji Zakari ya yi, buɗar bakin Baba Musa ya ce

"A'a ni ban ce zamu je wani wuri ba, to yaushe na dawo gidan" 

Attine ce ta saka musu baki tana cewa

"Yaya Zakari tunda ya ce baku yi maganar fita ba ai shikenan" 

Wani daɗi ya ji a ranta yana ƙara godema aikin Malam Tani, wucewar ya yi yana nishaɗi ba tare da sake ce musu komai ba.

Koda Baba Musa ya shiga sashensa, Fatsima ta yi masa maganar Hujayrah sai kawai ya kama mata faɗa yana tada jijiyoyin wuya har da cewa idan ta sake tado masa da maganar Hujayrah sai ranta ya yi mugun ɓaci, shiru Fatsima ta yi tana sauraron bambaminsa, mutumin da ya yi faɗa akan rashin sanar masa da bata yi ba amma yanzu kuma faɗa yake akan mai yasa ta tado masa da maganar Hujayrah, sosai abun ya bata mamaki anya Alhaji Zakari bai yi wani abu ba akan mijinta lokaci guda ya canja ra'ayi kai ina, miƙewa ta yi tabar ɗakin zuwa ɗakin Kakulle.Sosai Kakulle ta yi mamaki bayan Fatsima ta sanar mata yadda suka kwashe da mijinta akan  batun Hujayrah,cike da damuwa da ɓacin rai Kakulle ta ce

"Wallahi Ɗan Inna zai Iya sawa a rufe masa baki kar ya sake tado da maganar Hujayrah ko kaffara bazan yi ba,bansan meke damun Ɗan Inna ba a ce yana babba yana zaluntar ƴan uwansa sai ka ce ba ciki ɗaya kuka fito ba, Haba! Wannan wace iriyar musiba ce haka, ya je ai duniya ce ta ishe kowa riga da wando, wanda ma bai zo cikinta ba a shirye take da zuwansa, kayi na kirkin ya ka ƙare balle ka yi mara kyau, Mtwsss Babban Banza! "

Sosai ran Kakulle ya yi matuƙar tashi, haka ta ƙaraci faɗanta ta haƙura, Fatsima dai ta yi shiru tana sauraronta,sai can ta miƙe ta ce bara ta je sashensu Zaytuna. Fita ta yi daga ɗakin zuwa sashensu Mammin Hujayrah... ✍️

               🌎🌎🌎🌎🌎🌎

A ɓangarwnsu Hannatu da Murja sun shirya tsaf! Musamman Hannatu kamar za ta gidan wani ƙasaitaccan biki, kaya sababbi ta saka, haka suka nufi gidan mai unguwan garin. Babu laifi gidan ya haɗu kamar gidan su Alhaji Zakari, da sallama suka shiga cikin gidan, Direct suka nufi ɗakin uwar gidan da Sallama, amsa musu ta yi sai suka shiga ciki, a gaggauce suka gaisa sai ta yi musu kwatancan gidan bokan sannan suka fito, mai machine suka samu guda biyu suka hau,har Layin da zai sadasu da gidan bokan masu mashinan suka ajiyesu, bayan sun sauka Hannatu ta sallami masu mashina ita Murja daman ƴar rakiya ce, haka suka taka har gidan, akwai layi amma ba mai tsayi ba haka suka bi layi har ya iso kansu sai suka shiga ɗakin, ai da wani irin sauri Hannatu da Murja suka ja daya, zuciyar kowa ta tsinke... ✍️





*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
 ***