ƘYAURE KARIYAR GIDA

BOOK ONE CHAPTER 16

by @hindatuauwal



*ZAINAB*

Daga yanda sukaga mutane a tsatstsaye cirko cirko suka san tana wurin. Ku tsawa su keyi inda take, kwance take idanuwanta alumshe, hijjabin ta ya yaye, numfashin ta na fita dakyar, ƙeyanta na fitar da wani irin jini daya jiƙe wurin gaba daya.


"Ku ɗauko ta muje asibiti."


Alhaji Haruna yafadi ganin yanda suka durƙushe agabanta suna kallon ta.


With empty emotions Zainab tasa hannu ta ɗagota. Khalid ya tai maka mata suka shiga motan.


Tun a hanya Alhaji Haruna ya kira ƴan sanda ya gaya musu abin da ya faru, da asibitin da zasu je.



Imbanda faduwa ba abinda gaban Khalid keyi, idanunsa na kafe akan Khadijah da bata ko motsi. Tunanin wani abu mara kyau ka iya samun Khadija kadai na sanya numfashin shi barazanan ɗaukewa. Ba zai iya ba, bazai iya ɗaukan nauyin rashin wani daga cikin ahalin shi ba, yashir yama komai na rayuwa amma banda rashin wani acikin su.



Ramlat da Anis kam kuka su keyi sosai. A haka suka isa asibitin da ko sunanshi basu sani ba.



A reception suka ga police guda biyu anturo su, hakan yasa aka shigar da ita O.T su kuma aka tsayar dasu anan wurin.


Addu'a sosai su keyi acikin zukatansu suna mata fatan samun sauki.


*

Seda suka shafe kusan awanni biyu suna sannan likita da maƙarraban shi suka fito.


Dasauri suka tare babban likitan da tambayar "Ya jikin nata?!"


Likita ya gyara tsayuwa. Da wani irin yanayi mata daɗi a muryanshi ya soma musu bayani.


"Accident din da tasamu babbane, an taka tane akai hakan yasa ta samu injury akanta.

Bazan iya cewa komai akai ba se result din hoton da akai mata yanzu ya fito nanda mintina ashirin kafin lokaci yayi za kuje kuyi clearance din kuɗaɗen magun guna da na oxygen da aka sa mata."


Takarda ya karɓa awurin nurse ya miƙama Zainab yana cigaba da cewa"gayinan sai ai abinda yadace Allah ya bata lafiya."



Zainab ta ɗaga takardan, ta ɗora ƙwayannin idanuwan ta akan amount din kudin '35k'. Kallo tayi, ta kuma kallo taga da gaske naira dubu talatin da biyar ake buƙata daga gare ta.




Jitayi ƙafafuwanta suna lauyewa suna niman gaza ɗaukarta. Wani irin jiri ya ɗibeta yana niman kayadda ita, Alhaji Haruna yai saurin taro ta jikinsa da fadin"sannu."



Yanayin da take ciki ya hanata bama abinda ya faru muhimmanci, se kawai ta zame jikinta daga nasa tana jan numfashi.



Khalid ya manne agaru, ya jin gina kansa a bangon hawaye na saukar masa. 



Wayan Alhaji Haruna tai ƙara ya ɗauka da ambaton sunan Alhaji Mahbub yaɗan matsa nesa daga wurin su yaje ya amsa wayarsa, sedai be jima ba yakatse wayar yadawo ga Zainab shawarar da Alhaji Mahbub ya bashi na mai yawo.



Inda Zainab ke zaune iyanzu Anis da baccin wahala ya ɗaukesa na kwance akan jikin ta bisa doguwar kujerar ƙarfen da suke kai. Ramlat na gefenta tana sharɓan kuka har yanzu. Khalid na jikin bango acan karshen kujerar yana kuka mara sauti.



Cikin ƙaramar muryan da yasan Ramlat bazata iya jiyo suba yace mata"Zainab yanzu ya za'ayi asamu kudin da zaki biya asibiti gashi ma naga dayuwawar kila ace sai an mata aiki."




"Bansan inda zan samo waɗannan kuɗaɗen ba wallahi. Ba muda kudi I don't know how c....!"


Maganar nata ne yakatse sakamakon rishin kukan daya taho mata. wasu hawaye masu zafi suka ciko idanuwanta.



"Kinga kada ki kuka. Akwai mafitar yanda zaki sami kudi amma sai kin bautu da jikinki...." Ya ɗanyi shiru yana kallon reaction din Zainab.




Hakan yasa Zainab yin magana "Don Allah gayamin wani aiki ne, muje in samo kuɗaɗen."



"Kwantar da hankalin ki. Wasu ƴan lokuta kawai zaki bani muje mu ke ɓance da juna."




Zuciyar ta ne yatsaya cak. Duniyar ta na tsayawa kamar ansa mata pause. Hatta iskan dake yawatawa ta sashen ta ɗaukewa yayi ya maƙale asaman zan tukan da Alhaji Haruna keyi.



"Zainab na daɗe ina ƙaunar ki, tun ranar da na ɗora ido akan ki naji bana son kuwwa sai ke, Zainab!" Ya kira sunan yana kamo hannunta da take kallonsa kamar butun butumi.




Jin saukan hannun Alhaji Haruna tayi tamkar garwashin wuta. Ta fizge dasauri tana kallon sa da rinannun idanunta. Bakinta dake rawa ta buɗe"Ta.....tashi...ka tashi..."



Ta furta maganar dakyar cikin tsawan data sanya Anis dake jikinta motsawa ya tashi ya zauna.


Miƙewa Alhaji Haruna yayi. Ramlat ta matso inda suke a lokacin ne kuma doctor ya dawo.


"Result din ta na x-ray ya fito. I'm sorry to say tasamu rauni acikin kanta. Jini na bleeding sosai, akwai bukatar aimata emergency theater.


Ga takaddan se kuje ku biya kudin. Please kada adau lokaci because da duk yanda ku kai jinkiri da yanda take ƙara shiga haɗari. May be ma tarasa rayuwar ta."



"No Doctor ba za'ai haka ba. Za muje mu biya insha Allah."



Zainab ta fadi dasauri tana amsan takardan.


Ji tayi kanta na wani irin juyawa. Ta manna bayanta agaru tana furta"Inna lillahi wainna ilaihirra jiun."



Ramlat ta fashe da kuka mai sauti. Anis ya shiga rera nasa mai sauti yana riƙo Zainab da tambayar da ta sanya hawaye masu zafi saukowa saman fuskar ta.



"Mami ta mutu ne?... Aunty ta mutu ko?! Don Allah ki gaya min.?!!!"


Magana yake yana jijjiga Zainab da tambayoyin dake ƙara karya mata zuciya.



"150k"


Muryan Alhaji Haruna tai amsa kuwwa acikin kunnuwan Zainab.


Jajayen idanuwanta ta ɗago ta sauke akan Alhaji Haruna dake tsaye a gaban ta yana kuma mai maita adadin kuɗaɗen dake rubuce ajikin takarda.



Hannaye biyu ta sanya ta share hawayen ta. Ta kamo kafaɗar Anis idanuwanta cikin nasa dake jiƙe sharkaf da ruwan hawaye.



"A kodayaushe uwa itace garkuwan ƴaƴanta. Itace ƙyauren da take kare iyalinta daga dukkan wani abu arayuwa. Zanyi komai saboda farin cikin iyali na...!"



Ta ƙarke maganan tana sakin sa. Cikin ƙasa da muryan da tafi na raɗa tai amfani wa Alhaji Haruna dake kusa da ita.



"Na...amince!"


"Muje to."


"Khalid ka zauna dasu yanzu zan dawo"


Batareda ya iya amsa ta ba ya gyaɗa kai. Bayan Alhaji Haruna tabi suka hau motan shi. Tafiya kawai suke yi babu mai cewa komai har sukai tafiyar da bata da nisa wacce ta kawo su gidan hutawan Alhaji Haruna.




*JAMILA*

Kwance take laƙwas akan gadon ta. Tun adaren jiya da tai wasu mafarkai tana saduwa da Ustaz Rayyan jikinta duk ya rikice.




Duk yanda taso ta daurema yanayin ta kasa. Daƙyar tai wanka, tai sallah, ta komo ta kwanta wani wutan sha'awa me kisan rai babu jinkiri na cigaba da ci aduk jikinta.



Wayanta dake bedside drawer ce ta soma ruri. Daga ringing tone din ta gane mahaifiyar tace, yanda duk duniya babu wanda yakai Mommy matsayi azuciyar ta yasa ko a ringing tone bata haɗa ta da kowwa ba.



Hannu tasa ta jawo wayan ta amsa sallamar da Mommy tai mata. Jin muryan Jamila yasa hankalin Mommy tashi tana tambayanta lafiya?.



Ai nan take zuciyar Jamila ta karye. Kuka ya ƙwace mata. Hakan yaƙara tayadda hankalin Mommy tana tambayanta kamar zata tsago screen din wayan ta shigo.



Jamila taja hanci cikin gursheƙin kuka tace"Mommy na gaji....na gaji da wannan rayuwar alatun babu farin ciki. Ina tsoron naje na shiga wani hali ko lafiya ta ta kassara saboda abinda nake haɗiye wa."



Numfashi mai nauyi Mommy ta sauke gamida yin tsakin da yabi iska batareda sautin sa yakai cikin kunnuwan Jamila ba.



Ita bata goyama Jamila baya ta rabuda Rayyan don tai zaman wucin gadi ta dawo ba.


Ga Abban ta da tasan ko suna asiri da baƙar jaɓa ba zasu tun kareshi da wani batu akan auren Jamilar ya saurare su ba.



Kuma da take ta batu akan rashin miji ita bata ga uwar da hakan zai haifar mata ba. sha'awar ma tana samun wurine idan aka ƙallafa ma rai ana bukatar jima'i, duk daga ƙarshe ma ta gaya mata ta dingi shan ruwan tea da lemon tsami hakan zai tai maka mata sosai. ga...."




"Mommy inaso zan dawo gida na zauna kafin Samir ya dawo."



Mommy ta girgiza kai dasauri kamar tana kallon Jamila a zahiri tace:



"Kin san ma wannan ba abu bane mai yiwuwa, har yanzu mahaifin ki da Nazir ko kallon arziki basa min. Musamman ma dai Abban naku gaba daya ya tsaneni saboda abinda ya faru, gashi ya dauki soyayyar duniya ya dorama Fatima da yarin yarki.



Ni kaina bai cin na zama turmi shadaka da ba abinda ze hana Ni barin gidannan kin sani. Don haka kada ki ƙara wannan maganar, kisha lamun tsami da ruwan lipton mai dumi kamar yanda nake fadi miki.



Idan ciwon ya sauka ki ɗanyi min transfer din kudi. Na hannu na ya kare."



"To Mommy."



Tafaɗi murya a cunkushe sabbin hawaye na sauko mata.



Kashe wayar Mommy tayi. Jamila ta runtse idanunta tana miƙewa taje kicin da kanta ta hado ruwan zafi, ta dawo ɗakinta ta rufe kada Raihan ya shigo mata daki batareda izinin taba. Don ayanayin da take idan taji kusan cin wani namiji akusa da ita komai zai iya faruwa.


Ta share hawayen ta akaro na ba adadi. Asaman laɓɓanta batareda sauti ba ta furta:

Ba mace bace kaɗai keda alhakin zama kariyar gida ba.....