Page 20
SAWU BIYU
BY
Khadijah Sulaiman
Young Talented Writers Association (YOTA)
Book 1
Page 17
Bilal ya kasa yin shiru yace"dama ka nada ƴar uwa haka Sadauki ka barni ina gallafiri a gari?"
Sadauki ya mishi banza tamkar bai san abinda yake cewa ba.
Emmanuel yace"this is exactly what we call beauty at its peak".
Ademola ya kalli Sadauki yace"Please i want this your sister Falcon".
Dai dai nan ta iso riƙe da dogon tray mai ɗauke da plates ɗin abinci guda uku ta ajiye, Sadauki ya ɗan mata kallon fisha ya ɗauke kai.
Bilal ya miƙe ya karɓi plate ɗin yana kallon fuskarta yace"thank you".
Dai dai nan Idayat ta ƙaraso wurin, ta ɗan kalli Zarah ganinta tare dasu tace"is she your sister Bilal?"
Bilal ya ajiye tray ɗin hannun shi yace"no,Falcon".
Tayi murmushi tace"how are you?"
Zarah ta ɗan kalleta tace"ina wuni".
"Lafiya ƙalau beauty,ya sunan ki?"
Kafin ta buɗe baki ya ɗago ya watsa mata wani kallo yace"tafi ki bar nan".
Ta ɗaga manyan idanuwanta ta kalle shi,ganin irin kallon da yake mata yasa ta juya ta bar wurin.
Bilal ya watsa mishi harara yace"wani irin wulaƙanci ne haka Cadet,so kake ka nuna mana ƙanwar ka ce ita?"
Emmanuel yace"don't forget he is not more a Cadet,this is Lieutenant,you want his sister and you're shouting at him".
Bilal ya shafa kai ya koma ya zauna yace"kuma haka ne,I'm sorry Sir".
Sadauki dai bai ce komai ba ya cigaba da cin abincin da yake.
Idayat ta ƙarasa kusa da Sadauki ta ajiye wani babban leda,ganin ko kallonta bai yi ba yasa ta ɗanyi murmushi tace"ko da ba za ka yi min magana ba,ka karɓi wannan kyauta ce daga gare ni,sannan dan Allah ina neman wata alfarma guda ɗaya a wurinka,duk abinda nayi maka kayi haƙuri ka yafe min,Allah ya baka nasara a karatunka,ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya".
Ta juya wurin su Bilal tace"zan tafi, nagode sosai da irin kulawar da ku ka bani,you're indeed the brothers I need,na san maybe mu haɗu anytime soon,thank you so much".
Tana gama magana ta bar wurin duk su ka bita da kallo.
Ko da Sadauki ya tashi barin wurin bai ɗauki abinda ta ajiye ba ya tafi wurin su Mami.
Mami ta kalle shi tace"tunda ka gama yanzu zamu tafi kar muyi dare a hanya,naga kamar weather na son canzawa".
Ya shafa kai yace"to Mami".
Motoci guda uku su Mami su ka taho dashi,Mami da Umma da Zeenah suka shiga mota ɗaya,sai Hajja,Naima da Firdausi suka shiga ɗaya.
Zarah na ƙoƙarin shiga kusa da Firdausi Hajja tace"a'a kar ki shigo ki takura min a nan gaskiya".
Zarah ta turo baki tace"amma ku biyu ne kawai a nan Hajja".
Hajja ta watsa mata harara tace"na fi ki sanin mu biyu ne ai,takura ce bana so,tunda dai babu kowa a ɗaya motar sai ki tafi can ko ki tafi wurin Hafsah".
Bata jira cewar ta ba ta rufe kofa driver ya kunna suka bar wurin.
Ko da ta juya sai hango motar su Mami tayi na ƙoƙarin fita gate,cike da baƙin ciki ta nufi ɗaya motar, Sadauki ya rufe booth ya juyo suka haɗa ido,da sauri ta ɗauke kai har tana tuntube ta buɗe back seat ta shiga,ya zaga ta ɗaya side ɗin ya shiga ya kulle kofa.
Rufe ido tayi kamar mai bacci har suka fita a makarantar.
Ko minti talatin ba su yi ba ta fara yunƙurin amai,driver ya gangara gefen titi da sauri don shi ya ɗauko ta da safe,ta buɗe kofar da sauri ta tsuguna a wurin.
Driver ya ɗauko bottle water dake kusa dashi ya fita ya miƙa mata,ta sa hannu ta karɓa ta wanke bakinta da hannayenta.
Duk wannan abinda ke faruwa Sadauki na jinsu,kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai.
Ta miƙa mishi goran bayan ta wanke fuskarta ta buɗe kofa ta shiga.
Numfashi kawai take saukewa a wahale,dalilin da yasa tace ba zata zo ba kenan Mami tace bata isa ba.
Bayan kusan fourty minutes ta bubbuga seat ɗin driver da sauri jin yadda zuciyarta ke tashi,driver ya samu gefen titi ya tsaya,ta fita a guje ta hau kakari don babu komai a cikinta,driver ya ɗauko goran ruwa ya zaga kusa da ita.
Sadauki ya buɗe ido a gajiye ya juya yana kallonta,a hankali ya gyara zama yana kallon yadda driver ke zuba mata ruwa a hannu.
Bayan ta wanke baki ya sake zuba mata wani ta ture ɗanƙwalin kanta lallausan sumarta ya bayyana ta wanke fuskar ta miƙe tsaye.
Driver sai sannu yake mata ya buɗe mata ƙofa ta shiga.
Kafin su isa Kano sai da Zarah tayi amai kusan sau uku hakan ya sa basu shiga gida ba sai kusan magrib.
A galabaice ta buɗe ƙofa ta fita ko kallon shi ba tayi ba saboda ba ƙaramin haushi ya bata ba.
Shima bai kalli inda take ba ya buɗe booth ya kwashi kayan shi ya bar wurin.
Bayan sallar Isha ya shiga part ɗin Mami,a parlour ya tarar dasu ita da Umma,ya zauna kan Carpet ya gaishe su cike da girmamawa,Mami tace"yaushe ne tafiyar Faruq?"
Yace"next week ne Mami".
"To Allah ya kaimu".
Ta dubi Naima dake zaune tace"wuce ki kawo masa abinci".
Ta amsa da toh ta wuce kitchen ta kawo mishi cous cous da vegetables sauce.
Bayan ya gama ya wuce part ɗinsu ya fara arranging kayan shi cikin wardrobe,ledan da ya faɗo ƙasa yasa ya ɗan dakata tare da zubawa ledar ido.
Da mamaki ya ɗauki ledar ganin kaman wadda Idayat ta bashi a Academy,ya zauna a bakin gado ya kwance ledar sai ga jallabiya,wrist watch da agogo.
Rai ɓace ya ɗauki waya yayi dailing number Bilal, tunda ya san babu mai mishi katsalandan a rayuwa kamar shi.
Yana ɗauka yace"what have you done Bilal?"
Bilal ya taɓe baki don ya san dole dama zai kira,a nutse yace"sai yanzu ka gani kenan?"
"Bana son abinda kake min Bilal,I hate it,how on earth za ka samin abin nan cikin kaya,na ce maka ina buƙata ne?"
"Me ya sa kake haka ne Falcon,saboda Allah menene laifin Idayat,saboda ta nuna tana sonka ko me,yarinyar na da kyau,ga ilimi uwa uba hankali,banga dalilin da zai sa ka dinga wulakantata ba".
Rai ɓace yace"hankali my foot,a Ina hankalin yake,idan kai ka gani please go ahead and date her ku yi aure ka daina damuna da wannan shirmen Bilal,I'm not interested,zan ajiye maka don babu abinda zanyi dashi".
Daga haka ya kashe wayarsa ya cigaba da abinda yake.
Washegari bayan sallar la'asar ya fito zai fita motsa jiki ya hango Zarah tare da Sudais a garden ɗin gidan,babu wanda ya lura dashi a cikinsu ya fita ya bar gidan.
Bayan ya dawo dab da magrib ya jiyo muryar Hajiya Mama sai bala'i take,daga maganganun da take ya fahimci maganar akan Zarah ne da Sudais,ita kaɗai tayi haukarta ta koma ciki.
Washegari Umma ta koma Bauchi,a ɗan zaman da tayi ya fahimci jininsu ya haɗu sosai da Zarah.
Sati na zagayowa suka wuce Uk shi da sauran mates ɗinshi.
A wannan lokacin Zarah ta rubuta WAEC,zuwa sannan soyayya ce mai ƙarfi tsakaninta da Sudais,duk da ya san mahaifiyarsa bata so amma ya kasa rabuwa da ita.
Bayan ya gama karatun shi na Engineering a BUK ya fara aiki da wani Company.
Bayan shekara ɗaya duk suka dawo as Masters of Strategic Intelligence and Counter Terrorism from Royal Institute of Strategic and Security Studies,Oxford.
Kwana ɗaya suka ƙara suka wuce Headquarter don bada report.
A nan ya tarar da Bilal da sauran roommates ɗin shi har da Idayat,Bilal ya sanar dashi transfer ta nema ta dawo Kano saboda su.
A satin wani military convoy mai ɗauke da military supply yayi ɓatan dabo,lamarin daya ɗaga hankalin Headquarter baki ɗaya,babu ɓata lokaci aka haɗa unit da za su yi investigating case ɗin ciki har da Sadauki.
Case ne mai rikitarwa da aka kasa samin mafita aka hakura aka rufe case ɗin.
Sadauki ya sadaukar da komai nasa a wannan lokacin,yayi amfani da baiwa da hikimar da Allah ya basa ya fara bincike a kan issue ɗin secretly.
Allah ya taimake shi ya bashi sa'a ya gano kan case ɗin,da farko da ya tunkari General akan ga sakamakon binciken da yayi cewa yayi ya tafi kawai tunda case ɗin is already closed.
Bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya tari Brigadier General kai tsaye,shi kanshi ya sha mamaki,amma sai bai ce komai ba ya bashi go ahead ya haɗa shi da sojoji da za su taimaka mishi akan case ɗin.
Cikin sati ɗaya Sadauki ya dawo da disappeared military supplies ɗin har Headquarter,da mamaki Brigadier ya dinga kallonsa,harga Allah bai taɓa tsammanin hakan daga gare sa ba.
Wannan ne ya ƙara masa ƙima da daraja, har aka fara ɗora masa wasu ayyuka da a matsayinsa na Lieutenant, bai kamata ko kaɗan a ba shi ba.
Abin da Sadauki bai sani ba shi ne, wannan abin da ya yi ya sanya ya zama barazana, ko kuma mu ce, ya shiga tarkon da babu mai fitar da shi sai Allah.
Cigaban Labari
Hajja ta gwalalo ido ta ce"ba ka cin tuwo?"
Ya gyaɗa kai da sauri, Hajja tayi salati cike da mamaki,ita tun da ta ke bata taɓa jin wani ya ce baya cin tuwo ba.
Addu'a kawai yake Allah ya kubutar dashi a hannunta.
"To ba dani za'a yi wannan rainin wayon ba,ko Abdullahi dake zama a kasashen turawa ya kan ci tuwo balle kai karan kaɗa miya".
A hankali yace"ki yi haƙuri Hajja, idan na dawo watarana zan ci".
Da sauri tace"babu abinda zai sa ka fita a ɗakin nan ba tare da ka ci tuwo ba,yau ina ganin sabon salo kiran Sallah da usur".
Ganin ta sake turo mishi kular gabansa ya sa hankalin shi ƙara tashi,idan ka ganshi a wannan lokacin dole ya ba ka tausayi.
Dai dai nan Daddy ya shigo,yana ganin Sadauki ya ce"Umar".
Sadauki ya sunkuyar da kai yace "ina wuni Daddy".
"Lafiya Alhamdulilah,ya aiki?"
Yace"Alhamdulilah".
Daddy yace"Masha Allah".
Ganin Hajja ta haɗe rai yasa shi cewa"Hajiya lafiya kuwa?"
Da sauri tace"ina kuwa lafiya,yanzu dama a wannan duniyar akwai marasa cin tuwo?"
Da mamaki ya ce"me kika gani Hajja?"
"To dai tunda nake ban taɓa ji ba gaskiya sai yau,daga abin arziki,ya shigo na ɗauko kulan tuwo na ajiye kusa dashi buɗar bakinsa wai ba ya cin tuwo".
Daddy ya girgiza kai yace“Haka ne,baya cin tuwo, Hajja.”
Da mamaki Hajja ta ce"ikon Allah,ai shikenan".
Sadauki ya miƙe kanshi a ƙasa yace"sai da safe".
Daddy ya ce"Allah ya bamu alkhairi Umar".
Hajja dai kasa bashi amsa tayi don gabaɗaya ya gama goge mata hadda.
Washegari ƙarfe goma na safe ya iso gidan tare da Bilal,ya shiga har parlourn Mami inda suke zaune gabaɗaya,bayan sun gaisa da Mami su Zeenah suka gaishe shi.
Mami ta ce"kayi breakfast kafin ku tafi Faruq".
"Mami nayi breakfast".
Mami ta ce"to shikenan, Allah ya tsare ya kiyaye hanya,ina Bilal ɗin?"
Sadauki ya ce"yana waje Mami?"
Mami ta ce"shine bai shigo ba?"
Sadauki ya ciro wayar shi yayi dailing number Bilal,yana ɗauka ya ce"Mami tace ka shigo".
Ya juya ya kalli inda Zarah ke zaune ganin sai juya spoon ɗin hannunta take, Mami ta ce"ki ajiye cup ɗin tunda kin ƙasa shanye abinda ke ciki,ki wuce ki kawo ruwa ki sha magani,kar ki hanasu sukuni a hanya".
Ta miƙe riƙe da cup ɗin ta wuce kitchen,bata wani jima ba ta dawo riƙe da goran ruwa.
Mami ta miƙa mata maganin ta sha ta koma ta zauna.
Bilal yayi sallama a bakin ƙofa,bayan an amsa ya shigo yana shafa kai.
Mami ta ce"me ya sa ba ka shigo ba Bilal, kamar wani baƙo?"
Cike da kunya ya ce"ina kwana Mami".
"An tashi lafiya ya aiki?"
Ya ce"Alhamdulilah Mami".
Mami ta ce"Masha Allah,Allah yayi jagora,akwai breakfast ko za ka ci kafin ku tafi?"
"Mami mun yi breakfast kafin mu fito".
"To ai shikenan, Allah ya kai ku lafiya ya dawo daku lafiya".
Duk suka amsa da Amin suka fita,Zarah ta miƙe ta ɗauki wani mini bag dake kusa da ita dai dai tafiyar kwana biyu tayi sallama da ƴan uwanta tabi bayansu.
Bilal ya buɗe ɗaya side ɗin ya zauna, Sadauki ya ce"who is your driver?"
"Kai ne mana,you're our driver,ko ba haka ba Zarah?"
Yayi maganar tare da kallon Zarah dake ƙoƙarin buɗe kofa ta shiga,ta ɗan kalle shi ta gefen ido,bai sake cewa komai ba ya buɗe ya shiga itama ta shiga,sai da yayi addu'a sannan ya tada motar.
A nutse yake driving suna ɗan hira sama sama da Bilal,bayan sun fita a Kano ya sake duba side mirror ɗin shi for the countless time.
A nutse ya dubi Bilal ya ce"I think someone is after us".
Bilal ya duba side ɗin shi da sauri,ya juyo ya kalli Sadauki ya ce"tun yaushe?"
A hankali ya ce "Tun daga Kano".
Zarah ta ƙanƙame jikinta a tsorace,Sadauki ya ɗan kalleta ta madubi,ya ɗauke kai yana mamakin yau bata tsayar dasu ba.
Oum Rijalain
***