THE BROKEN TRUST
*KADDARAR ZUCIYA*
*CHAPTER THIRTEEN: 13*
*THE BROKEN TRUST*
*JIDDAAH BARKUM*
—————
Washegari, kasancewar weekend ne babu makaranta, Inteesar ta tashi daga barci da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe, a hankali ta buɗe idanunta, tana kallon ceiling ɗin ɗakinta cikin gajiya, duk da ta kwanta ta yi barci, zuciyarta ba ta samu cikakkiyar natsuwa ba, abubuwan da suka faru a kwanakin baya sun hana ta samun kwanciyar hankali, har ta fara jin kamar rayuwarta ba ta kasance tata kaɗai ba, wani mutum yana lura da ita, wani mutum yana sanin duk abin da take yi, kuma har yanzu ba ta san ko waye shi ba.
Ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta juyar da kanta gefe inda wayarta take, ba tare da ɓata lokaci ba, ta jawo wayar ta buɗe WhatsApp, idanunta suka sauka kan chat ɗin lambar sirrin, ta ɗan yi shiru tana kallon saƙonnin da suka gabata, kafin ta fara rubuta wani saƙo, “I think we should make another plan to meet… I really want to know who you are.” Ta karanta saƙon sau ɗaya, sannan ta danna send, a wannan karon, ta yanke shawarar cewa ba za ta sake zama cikin duhu ba, idan har mutumin yana son ta san shi, to lokaci ya yi da zai fito fili.
Ta ajiye wayar a kan gado, ta tashi ta shirya jikinta, sannan ta ɗauki hular da take sakawa a gida ta ɗora a kanta kafin ta fito daga ɗakin, da ta ƙarasa falon, sai ta tsaya tana kallon wurin, babu kowa, shiru ne ya mamaye gidan, sai ƙarar agogon bango da ke tafiya a hankali, Inteesar ta kalli kujerun falon, sannan ta juya kai tana duba ko Nana tana kitchen, babu kowa a falon, a saman centre table kuwa, akwai tarin takardun office na Yaya Umar, laptop ɗinsa, da kuma wayarsa, da alama ya manta ya ɗauke ta lokacin da ya tashi, Inteesar ta wuce tana shirin zuwa kitchen domin ta nemo abin da za ta ci, amma kafin ta ƙarasa, sai wayar Umar ta yi ƙarar shigowar saƙo, Ding! Ta tsaya cak, a hankali ta juyo ta kalli teburin, wayar ce, ta ɗan yi shiru, tana sauraron ko za ta ji wani motsi daga ɗakunan gidan, babu komai, ta sake waigawa, har yanzu babu kowa, wani irin tunani ya fara ratsawa a zuciyarta, amma ta yi ƙoƙarin kawar da shi, it’s just a phone, Inteesar, me ya sa za ki damu? Ta juya za ta ci gaba da tafiyarta, amma sai wayar ta sake yin sauti, a wannan karon, ta tsaya na tsawon daƙiƙu tana kallonta, wani abu a zuciyarta ya sa ta matsa kusa da teburin, ta san bai kamata ta taɓa wayar Yaya Umar ba tare da izininsa ba, amma wani irin sha’awa da rashin fahimta ya ja hankalinta gare ta, a hankali ta ɗauki wayar.
Daidai lokacin da ta duba screen ɗin… JININ JIKINTA YA TSAYA, numfashinta ya ɗauke na daƙiƙa kaɗan, idanuwanta suka zaro waje, hannunta ya fara rawa, a saman screen ɗin… saƙon da ita kanta ta tura wa Unknown Number mintuna kaɗan da suka wuce ne ya bayyana, “I think we should make another plan to meet… I really want to know who you are.” Wayar ta fara rawa a hannunta, gabanta ya fara bugawa da ƙarfi, har ta ji kamar sautin bugun zuciyarta zai cika falon, ta sake kallon screen ɗin, tana ƙoƙarin fahimtar abin da take gani, a hankali leɓɓunta suka motsa, “Yaya Umar…?” Ta furta sunan cikin raunin murya, a’a, ba zai yiwu ba, ba zai taɓa yiwuwa ba, Yaya Umar? Yayan ta na uwa ɗaya, uba ɗaya? Mutumin da yake cikin mutanen da ta fi yarda da su a duniya? Mutumin da ya taimaka wajen rainonta tun tana ƙarama? Mutumin da take kira da Yaya cikin cikakkiyar amana?
Ta girgiza kai da sauri, kamar tana ƙoƙarin korar wani mummunan tunani daga zuciyarta, “No… no, this can’t be true,” amma wayar tana hannunta, saƙon nata yana kan screen, kuma a yanzu, tambayoyin da ta daɗe tana yi sun fara haɗuwa da wani irin amsa da take tsoron yarda da ita, da hannaye masu rawa, ta danna screen ɗin, luckily, babu lock a wayar, zuciyarta ta ƙara bugawa, ta shiga WhatsApp kai tsaye, tana jin wani irin sanyi yana ratsa bayanta, ta fara duba chats ɗin da ke cikin wayar, saƙonni da dama suka bayyana, amma idanunta sun tsaya a kan conversation ɗaya, number wayarta da akayi saving da jewel, ta danna shi, sai duniya ta fara juyawa a kanta.
Saƙonnin sun yi daidai, dukansu, daga na farko har zuwa na ƙarshe, “Beautiful…” “I missed you.” “I am always watching over you.” “Dry those tears, beautiful…” “Next time… don’t leave your room at midnight.” “Abuja is not safe… 😉” Inteesar ta ja baya a hankali, ta kasa numfashi yadda ya kamata, kowane saƙo yana dawo mata da wani tunani, yadda ta firgita a cikin ɗakinta, yadda ta kasa barci, yadda ta fito cikin dare tana tunanin za ta gano mutumin da yake tsoratar da ita, da yadda Umar ya same ta a falon gidan, ya yi mata magana cikin fushi, ya tambaye ta dalilin fitowarta, ya kuma ce ta koma ɗakinta, a lokacin, ta ɗauka cewa shi kawai ɗan’uwa ne da ya damu da lafiyarta, amma yanzu… yanzu saƙonnin da ke kan screen ɗin sun sa ta fara kallon duk abubuwan da suka faru da wata ma’ana dabam, ashe mutumin da take gudun saƙonninsa yana iya kasancewa mutum ɗaya da take kira da Yaya?
Ta kasa yarda, ta sake duba screen ɗin, tana neman wani abu da zai tabbatar mata cewa ta yi kuskure, amma duk abin da take gani yana ƙara jefa ta cikin ruɗani, wayar ta sulale daga hannunta ta faɗa kan carpet, ta dafe bakinta da hannu, “Ya Allah…” Hawaye suka fara zubo mata ba tare da ta sani ba, “Wai me ya sa?” Ta yi tambayar cikin raunin murya, “Yaya Umar… me na yi maka?” Muryarta ta karye a kan sunan, ta sunkuya ta ɗauki wayar, tana kallon screen ɗin da idanun da suka riga suka cika da hawaye, ta sake buɗe conversation ɗin, kamar tana fatan za ta farka daga wani mummunan mafarki, amma ba mafarki ba ne, kuma abin da take gani ya isa ya sa zuciyarta ta fara karyewa.
Ta fashe da kuka mai karya zuciya, kukan da ko ita kanta ba ta taɓa yin irinsa ba, ba wai kawai saboda wani ya ɓoye mata gaskiya ba ne, ba wai kawai saboda an yi mata wasa da hankali ba ne, sai saboda wanda ta fara zargin da wannan cin amana shi ne ɗan’uwanta, jininta, mutumin da take tunanin zai tsaya a gefenta idan duniya ta juya mata baya, mutumin da take kira da Yaya, ta zauna a ƙasa, ta matse hannayenta a ƙirjinta, tana kuka kamar ƙaramar yarinya da ta rasa hanyar komawa gida, “Why would you do this to me?” Ta ɗaga kai tana kallon sararin falon, hawaye suna gangaro mata a kumatunta, “What did I ever do to you?” Amma babu wanda ya amsa mata, shiru ne kawai, shiru mai nauyi, ta yi ƙoƙarin share hawayenta, sannan ta ɗauki wayar Umar ta mayar da ita a kan tebur yadda take, kamar ba a taɓa ta ba, ta san bai kamata ya gane cewa ta taɓa wayarsa ba, ta san idan ya dawo ya same ta a falon, zai iya tambayar abin da ya faru, don haka ta miƙe da sauri, tana share fuskarta da bayan hannunta, amma hawayen sun ƙi tsayawa.
Ta juya ta nufi ɗakinta da gudu, da ta shiga ɗakinta, ta tura ƙofar ta rufe, sannan ta jingina da ita tana kuka, ta kasa yarda da abin da ta gani, a cikin zuciyarta, akwai wani ɓangare da yake ƙoƙarin kare Umar, maybe there’s an explanation, maybe this is all a misunderstanding, maybe there’s something I’m not seeing, amma wani ɓangaren kuma ya kasa mantawa da saƙonnin, kalaman, lokutan da ya san abin da take yi, da yadda yake gaya mata cewa yana kusa da ita, ta girgiza kai da sauri, “I can’t stay here…” Ta furta kalmomin cikin kuka, “I can’t stay in this house,” ta san tana buƙatar ganin Daddy, tana buƙatar kasancewa a wurin mutumin da take ganin zai saurare ta, ya ba ta damar yin magana ba tare da ta ji tsoron abin da zai biyo baya ba, da sauri ta ɗauko handbag ɗinta, ta saka wayarta a ciki, sannan ta ɗauki key ɗin motar, ta saka hijabinta ba tare da ta kula da yadda ta shirya shi ba, ta duba kanta a madubi na ɗan lokaci, idanunta sun yi ja, fuskarta ta kumbura saboda kuka, ta buɗe ƙofar ɗakinta ta fito cikin sanda, a wannan lokacin, abin da take so kawai shi ne ta fita daga gidan kafin ta sake ganin wani abu da zai ƙara mata ciwo, ta wuce falon ba tare da ta sake kallon teburin da wayar Umar take a kai ba, da ta fita compound, mai gadi ya lura da yanayinta haka nan ya bude gate dan ya san bai isa ma ya tsaya tambaya ba, ta fice daga gidan, da wani mugun speed, bayan ta daidaita a hanya, hawayen da take ƙoƙarin riƙewa suka sake gangaro mata, ta goge su da bayan hannunta, tana ƙoƙarin mayar da hankalinta kan tuƙi, amma duk lokacin da ta tuna da saƙonnin, sai ƙirjinta ya matse, Yaya Umar? How could this be possible? Ta kasa fahimtar yadda mutumin da take ganin ya kamata ta amince da shi ya zama wanda take zargi da tayar mata da hankali.
Ba ta san tsawon lokacin da ta ɗauka tana tuƙi ba kafin ta ƙarasa airport, abin da ta sani kawai shi ne, ba za ta iya ci gaba da zama a Abuja ba, ta nemi available flight zuwa Katsina, kuma da ƙyar ta sami wanda zai tashi a lokacin, a lokacin da take jiran shiga jirgi, ta zauna ita kaɗai a wani gefe, ta jingina da kujerar tana share hawayenta, mutane suna wucewa suna harkokinsu, wasu suna magana a waya, wasu suna dariya, wasu suna jiran nasu jiragen, amma a cikin zuciyar Inteesar, komai ya tsaya, ta ji kamar an cire wani abu mai muhimmanci daga rayuwarta, wani abu da ba ta san yadda za ta mayar da shi ba, da aka kira fasinjojin jirginta, ta miƙe ta shiga cikin mutane, tana bin umarnin ma’aikatan airport ba tare da ta mai da hankali sosai ga abin da ake faɗa ba.
A cikin jirgin ma, ta kasa samun natsuwa, tun daga lokacin da jirgin ya tashi har zuwa lokacin da suka fara sauka, hawaye kawai take yi, ta yi ƙoƙarin dannewa, amma abin ya gagare ta, wani mutum da ke zaune kusa da ita ya dinga kallonta cikin damuwa, da farko ya yi shiru, yana ba ta sarari, amma da ya lura cewa hawayen ba sa tsayawa, sai ya ɗan karkata jikinsa gare ta, “Excuse me… are you okay?” Inteesar ba ta amsa ba, ta juya kanta ta kalli window, tana ƙoƙarin ɓoye fuskarta, mutumin ya ɗan yi shiru, sannan ya sake magana cikin tausasawa, “Please, if something is wrong, you can talk to someone, you don’t have to go through it alone,” Inteesar ta runtse idanunta, kalaman nasa sun ƙara tayar mata da wani irin ciwo, domin abin da ke damunta ba abu ne da za ta iya faɗa wa wani ba tare da ta fara fahimtar shi da kanta ba, ta girgiza kai kaɗan, “I’m fine,” ta faɗa cikin raunin murya, amma sautinta ya nuna cewa ba ta da lafiya a zuciya ko kaɗan, mutumin bai matsa mata da tambayoyi ba, sai dai lokaci zuwa lokaci yana kallonta cikin tausayi, har suka sauka.
KATSINA, da suka fito daga jirgi, Inteesar ta yi saurin ɗaukar handbag ɗinta ta nufi hanyar fita, tana son ta isa gidan Daddy da wuri, ba ta son ta sake zama ita kaɗai da tunaninta, amma kafin ta yi nisa, sai ta ji muryar mutumin da ya zauna kusa da ita a jirgi, “Excuse me, please!” Ta tsaya ba tare da ta juyo gaba ɗaya ba, sai ya ƙaraso gare ta, yana riƙe da wayarsa, “I know you probably don’t feel like talking to anyone right now, but you’ve been crying since we took off, I was worried about you,” Inteesar ta sauke idanunta ƙasa, “Thank you, I’m okay,” mutumin ya yi shiru na ɗan lokaci, yana nazarin fuskarta, “Are you sure? Do you have someone coming to pick you up?” Ta girgiza kai, “No, I’ll get a Bolt,” ya ɗan dakata, sannan ya yi ƙoƙarin magana cikin ladabi, “If you don’t mind, I can help you get a ride, or at least… can I have your number? Just in case you need someone to talk to,” Inteesar ba ta son magana da kowa, a wannan lokacin, amincewa da wani sabon mutum abu ne da ya yi mata wahala sosai, ta girgiza kai, “I’m sorry, I don’t think that’s necessary,” sai ya yi shiru, amma bai yi fushi ba, “Okay, I understand,” sai ya ɗan dakata, kafin ya sake cewa, “Please, take care of yourself,” Inteesar ta gyaɗa kai kaɗan, ta juya za ta tafi, amma sai ya sake kiranta cikin ladabi, “Please, at least let me know you got home safely, I won’t disturb you,” ta tsaya, a ƙarshe, saboda ya nuna damuwarsa ba tare da ya tilasta mata komai ba, ta ba shi numberta, ya yi murmushi kaɗan, “Thank you, and I’m sorry if I made you uncomfortable,” “It’s okay,” ta amsa a taƙaice, sannan ta juya ta nufi inda za ta samu Bolt, bayan ta shiga motar, ta ba direban address ɗin gidan mahaifinta, a wannan lokacin, tunaninta ya koma kan Daddy, Daddy will understand, he has to understand, ta jingina da kujerar, ta lumshe idanunta, tana ƙoƙarin tara ƙarfin da za ta yi amfani da shi wajen bayyana abin da ya faru, amma gaskiya ita ma ba ta san yadda za ta fara ba, ta san kawai cewa zuciyarta ta na ciwo, kuma tana buƙatar mahaifinta.
Tun daga gate ɗin gidan, ma’aikatan gidan suka gane cewa akwai matsala, domin Inteesar da suka sani ita ce wadda take fara gaishe su cikin fara’a da mutunci, tana tambayar lafiyarsu kafin ta wuce, amma yau… ba ta tsaya ba, ko kallonsu ba ta yi ba, ta wuce kai tsaye, tana riƙe da handbag ɗinta, idanunta sun kumbura saboda kuka, Shema’u mai aikin mommy ta bi ta da kallo cikin mamaki, “Anty Inteesar…?” Amma Inteesar ta riga ta wuce, ta haura saman bene cikin sauri, tana nufar private parlour ɗin da Daddy yake zama idan yana son yin shiru ko karanta takardunsa, da ta ƙarasa ƙofar, ta tsaya na ɗan lokaci, ta share hawayenta da sauri, ta yi ƙoƙarin jan numfashi mai zurfi, amma kafin ta samu natsuwa, sai ta ji muryar Daddy daga cikin ɗakin, “Come in, princess,” ta buɗe ƙofar a hankali ta shiga, Daddy yana zaune a kan kujerarsa, yana duba wasu takardu, da ya ɗago kai ya gan ta, murmushi ya bayyana a fuskarsa, “Princessss…” Ya miƙe kaɗan a kujerarsa, yana shirin tambayarta yadda take, “Look who’s here! Me ya kawo min ke ba tare da kin sanar da ni ba?” Amma kafin ya ƙarasa maganar… Inteesar ta durƙusa a gabansa, ta kasa riƙe hawayenta, sai ta fashe da wani irin kuka mai karya zuciya, “Daddy…” Ta kira cikin shessheƙar kuka, Daddy ya daina murmushin nan take, “Princess?” Inteesar ta riƙe hannunsa da ƙarfi, tana kuka kamar ƙaramar yarinya, “Daddy…” Ta sake kiran sunansa, amma ta kasa ƙarasa magana, kukan ya hana ta, Daddy ya miƙe tsaye a firgice, “Inteesar!” Ya durƙusa a gabanta, ya ɗora hannayensa a kafaɗunta, “What’s wrong, my daughter? Me ya faru?” Ta girgiza kai cikin kuka, Daddy ya kalli fuskarta da kyau, ya ga yadda idanunta suka kumbura da kuma yadda jikinta ke rawa, nan take damuwa ta mamaye fuskarsa, “Princess, look at me,” ya ɗan ɗaga fuskarta a hankali domin ta kalle shi, “Who hurt you?” Inteesar ta kasa amsawa, ta sake rungume ƙafafunsa, tana kuka kamar wadda ta rasa duk abin da take da shi, Daddy ya ji zuciyarsa ta buga, “Inteesar, please… talk to me, what happened? Wa ya taɓa mini ke?” Ya shafa kanta a hankali, yana ƙoƙarin kwantar mata da hankali, “I’m here, princess, Daddy yana nan,” amma jin waɗannan kalmomin ya ƙara karya zuciyarta, domin abin da ya fi mata ciwo shi ne cewa mutumin da ta yi tunanin zai iya zama mafita ga tsoronta shi ne wanda ta fara zargi da karya amanarta, ta ɗago kanta kaɗan, tana ƙoƙarin yin magana, “Daddy… I…” Muryarta ta karye, ta sake fashewa da kuka, Daddy ya matse ta a jikinsa, yana shafa bayanta a hankali, “Shhh… it’s okay, take your time, princess, ba sai kin yi magana yanzu ba,” ya ɗan ja numfashi, sannan ya ƙara da murya mai taushi, “Whatever it is, we’ll face it together, kin ji ni?” Inteesar ta rufe idanunta, tana kuka a ƙirjinsa, a karo na farko tun bayan abubuwan da suka faru a Abuja, ta ji tana iya sakin kanta ta yi kuka ba tare da ta ɓoye raunin da take ji ba, amma duk da haka, ba ta san yadda za ta gaya wa Daddy abin da ta gani ba, ta yaya za ta faɗa masa cewa tana zargin Yaya Umar? Ta yaya za ta bayyana cewa mutumin da take kira da ɗan’uwanta shi ne wanda saƙonnin sirrin suka nuna? Kuma idan ta yi kuskure fa? Idan akwai wani bayani da ba ta sani ba fa? Ta ƙara matse hannunta a jikin Daddy, “Daddy… please…” “I’m listening, princess,” ta yi ƙoƙarin magana, amma kalmomin suka makale a maƙogwaronta, sai dai kuka, Daddy ya ci gaba da riƙe ta, yana jin yadda take rawa a hannunsa, bai san abin da ya faru ba tukuna, amma ya san abu ɗaya, wannan ba kuka ne na ƙaramar matsala ba, akwai wani abu da ya karya zuciyar ’yarsa, wani abu da ya sa ta bar Abuja ta dawo Katsina cikin wannan hali, kuma duk abin da yake, Daddy ya shirya ya saurare ta, ya shafa kanta a hankali, ya sumbaci goshinta, “Don’t be afraid, princess, whatever happened, you can tell me,” Inteesar ta lumshe idanunta, hawaye suna gangaro mata a hankali, ta ji kamar duniyar da ta gina bisa amana ta rushe a lokaci guda, amma a hannun mahaifinta, ta samu damar yin kuka ba tare da ta yi kamar tana da ƙarfi ba, domin wani lokaci, mutumin da ya fi karya mana zuciya shi ne wanda ba mu taɓa tunanin zai iya cutar da mu ba, and sometimes… the deepest pain comes from the person we trusted the most.