KADDARAR ZUCIYA

A HIDDEN SECRET UNVEILED

by @jiddaahbarkum

*KADDARAR ZUCIYA*

*CHAPTER FOURTEEN: 14*

*A HIDDEN SECRET UNVEILED*

*JIDDAAH BARKUM*

————

Daddy ya rungume Inteesar tsam a ƙirjinsa, yana jin yadda jikinta ke karkarwa kamar tsuntsun da aka jefa a ruwa, kukan nata ya yi tsanani har numfashinta ke neman sarƙewa, yayin da jikinta ke rawa a cikin hannunsa, ganin halin da take ciki ya sa hankalin Daddy ya tashi gaba ɗaya, ya fara ƙwala kira cikin wata murya mai ɗauke da tashin hankali, “Haleema! Haleema!! Fito maza!” Mommy Haleema ta turo ƙofar falon ta shigo a birkice, amma da zarar idanuwanta suka sauka kan Inteesar, wacce ke kuka a gaban mahaifinta kamar ƙaramin yaro da aka yi wa wani mugun abu, sai ta tsaya cak, “Ya Allah! Inteesar!” Ta ƙarasa da sauri, ta karɓe ta daga hannun Daddy, sannan ta zaunar da ita a jikinta, ta ɗago habarta a hankali tana share mata hawaye da hannunta, fuskarta cike da damuwa, “Daughter, what happened to you?” Ta tambaya cikin muryar tausayi, “Don Allah ki yi magana, wani abu ne ya faru a Abuja? Me aka yi miki? Someone hurt you?” Amma Inteesar ta kasa cewa uffan, sai shessheƙa take yi, tana ƙara lafewa a jikin Mommy kamar tana neman mafaka daga wani babban haɗari, ta matse jikinta da ƙarfi, hawaye na sake zubo mata duk da yadda Mommy ke ƙoƙarin kwantar mata da hankali.

Ganin yadda Inteesar ta kasa magana ya ƙara tayar wa Mommy hankali, a hankali ta ɗago kai ta kalli Daddy, idanuwanta cike da fargaba, “Alhaji, kiran Umar za ka yi a waya yanzu-yanzu! Shi kaɗai zai iya gaya mana abin da ya faru da yarinyar nan a can,” Daddy bai yi wata-wata ba, kamar an tsikari shi, ya lalubi aljihunsa, ya ɗauko wayarsa sannan ya danna lambar Umar kai tsaye, a zuciyarsa kuwa, tambayoyi ne kawai ke ta yawo, ya kasa fahimtar abin da zai iya sa Inteesar ta bar Abuja ta dawo Katsina cikin wannan yanayin, amma a lokacin, ba shi kaɗai ke cikin ruɗani ba.

ABUJA, gidan ya shiga tashin hankali, Nana ce ta fito daga ɗakin Inteesar da sauri, fuskarta cike da damuwa, ta sake duba wasu wurare a cikin gidan tana kiran sunanta, amma shiru, “Inteesar! Inteesar!” Babu amsa, ta nufi inda Umar yake tsaye a tsakar falon, kusa da takardunsa, ya kasance cikin wani irin yanayi na rashin natsuwa, yana ƙoƙarin fahimtar abin da ke faruwa, “Babe!” Nana ta kira shi cikin fargaba, “Inteesar ba ta cikin gidan nan! Har toilet na duba, ban ganta ba,” Umar ya ɗago kansa da sauri, “What do you mean she’s not in the house?” Bai jira Nana ta sake magana ba, ya fice daga falon da sauri, kai tsaye ya nufi compound ɗin gidan, da ya isa wajen parking lot, idanuwansa suka sauka kan wurin da ake ajiye motar Inteesar, motar ba ta nan, ya tsaya cak, wani irin zafi da firgici suka ratsa zuciyarsa, ya zaga parking lot ɗin da idanuwansa kamar yana fatan motar za ta bayyana kwatsam a wani ɓangare na gidan, amma babu ita, “Ina Musa?” Ya juyo da sauri, sannan ya ƙwala kira cikin wata murya mai firgitarwa, “Musa! Musaa!!” Maigadin gidan ya jiyo da gudu, jikinsa na rawa, ya tsaya a gaban Umar, ya sunkuyar da kansa, “Na’am, Yallabai!” Umar ya matso kusa da shi, fuskarsa a murtuke, idanuwansa sun kaɗa sun yi jawur tsabar fushi da ruɗani, “Ina Inteesar? Yaushe ta fita daga gidan nan? Kuma me ya sa ka buɗe mata gate ta fita ita kaɗai, bayan na ba ka umarnin kada ka taɓa buɗe mata ƙofa sai idan za ta makaranta, kuma sai lokacin da ba na nan?” Musa ya haɗiye miyau, jikinsa na ƙara rawa, “Wallahi, Yallabai, yadda ta kunna motar nan cikin zafin nama da gudu, da ban buɗe mata gate ba, bi ta kaina za ta yi ta wuce! Shi ya sa na tsorata na buɗe mata, a gafarce ni, Yallabai!” Umar ya matse haƙoransa, yana ƙoƙarin danne fushin da ya mamaye shi, “Get out of my sight!” Musa ya ja da baya da sauri, amma kafin Umar ya sake cewa uffan, wayarsa da ke cikin aljihunsa ta fara ruri da wani irin sauti mai nauyi, ya zura hannu ya ɗauko ta, da ya kalli screen ɗin, sai ya ga sunan DADDY yana bayyana, zuciyarsa ta buga da ƙarfi, a take, wani irin nauyi ya tsaya masa a maƙogwaro, ya san Daddy ba zai kira shi a wannan lokacin ba tare da wani dalili ba, musamman bayan Inteesar ta ɓace daga gidan.

Ya kalli wayar na wasu daƙiƙu, yana ƙoƙarin tattara nutsuwarsa, amma ta yaya zai yi bayani idan Daddy ya tambaye shi inda Inteesar take? Da yake ba shi da wata mafita, sai ya ɗaga kiran, hannunsa na rawa, “Hello… Daddy,” amma Daddy ya katse shi cikin wata murya mai tauri da cike da iko, “Umar, ka bar dukkan abin da kake yi ka taho Katsina yanzu-yanzu, Inteesar tana gabana a yanzu haka,” Umar ya lumshe idanunsa, she’s in Katsina? Ya kasa magana na wasu daƙiƙu, kamar kalaman Daddy sun ɗauke masa dukkan ƙarfin da ke jikinsa, muryar Daddy ba ta nuna fushi mai zafi ba, amma sanyin da ke cikinta ya fi kowace tsawa firgitar da Umar, “Ka ji abin da na faɗa maka?” Daddy ya tambaya bayan ya lura da shirunsa, “Na… na ji, Daddy,” “Good, ina jiran ka,” Daddy ya katse kiran, Umar ya sauke wayar a hankali, yana kallon screen ɗin kamar yana fatan za ta sake yin ƙara, ta ba shi damar jin wani abu dabam, amma babu komai, ya ɗago kai ya kalli Nana, wacce ke tsaye tana jiran jin abin da ya faru, “Tana Katsina…” Ya yi maganar a hankali, muryarsa na rawa, “Tana gaban Daddy yanzu haka,” Nana ta dafe ƙirji, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Allah ya sa lafiya, amma me ya kai ta can haka? Why would she leave without telling anyone?” Umar bai ba ta amsa ba, ya juya ya shiga cikin gidan da sauri, ya tattara abubuwan buƙatarsa, sannan ya nufi airport domin neman jirgi mafi kusa da zai kai shi Katsina a wannan ranar, a zuciyarsa kuwa, tunani ɗaya ne kawai yake yi, meye ya faru?

KATSINA — BAYAN KUSAN SA’O’I BIYU, bayan kusan sa’o’i biyu, Umar ya ƙaraso gidan Daddy da ke Katsina, da ya shiga gidan, bai tsaya yin dogon gaisuwa da kowa ba, kai tsaye ya nufi private parlour ɗin Daddy, inda ya san zai same su, ya tura ƙofar a hankali ya shiga, a cikin falon, Daddy yana zaune a kan kujerarsa, yayin da Mommy ke zaune kusa da Inteesar, wacce har yanzu ta lafe a jikinta, idanuwanta sun kumbura saboda kuka, fuskarta ta yi ja, ga wani irin gajiya da ya bayyana a jikinta, da Umar ya shigo, sai idanuwansu suka haɗu, Inteesar ta ɗauke nata da sauri, wannan ƙaramin motsi bai kuɓuce wa Umar ba, ya ji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarsa, amma ya danne abin da yake ji, ya ƙarasa ya gurfana a gaban Daddy, zuciyarsa na bugawa da ƙarfi, har yake jin sautin bugun a kunnensa, Daddy ya zuba masa idanu na ɗan lokaci ba tare da ya ce komai ba, sannan ya yi magana cikin nutsuwa, “Umar, ka gaya mini abin da ya faru,” Umar ya ɗago kai, ya haɗiye miyau, “Wallahi, Daddy… ban sani ba, kawai na fito ne, Nana ta gaya mini cewa Inteesar ba ta cikin gidan, na tambayi gateman, ya ce mini ta fita da gudu a mota,” ya ɗan dakata, sannan ya ƙara da sauri, “Ban san inda ta nufa ba, Daddy, da na gano ta tafi, sai ka kira ni,” Daddy bai amsa nan take ba, ya ci gaba da kallon Umar, kamar yana son karanta abin da ke ɓoye a zuciyarsa, daga nan sai ya juya ya kalli Inteesar, “Ɗiyata Inteesar, ki faɗa mini abin da ya faru, kar ki ji tsoron kowa, ina saurarenki,” Inteesar ta ɗago fuskarta a hankali, hawayen da ta yi ƙoƙarin gogewa sun sake taruwa a idanunta, ta share su da bayan hannunta, sannan ta miƙa wayarta ga Daddy, ta buɗe saƙonnin da suka daɗe suna tsoratar da ita, ta nuna masa ɗaya bayan ɗaya, a ƙarshe, ta ɗago kai ta kalli Umar, wannan karon, ba ta kawar da idanuwanta ba, “Yaya Umar…” Muryarta ta fara rawa, “Yayana na uwa ɗaya, uba ɗaya…” Ta haɗiye wani irin kuka da ya taso mata, sannan ta nuna wayar, “Shi ne Unknown Number ɗin da yake tsoratar da ni tsawon lokacin nan!”

Ta juya ta kalli Daddy, hawaye na zubo mata, “Daddy, na ga saƙonnin a wayarsa! Duk saƙonnin nan da ya yi ta turo mini… duk waɗannan abubuwan da ya sani game da ni… na same su a wayarsa!” Ta yi shiru na ɗan lokaci, tana ƙoƙarin daidaita numfashinta, “Na amince da shi, na ɗauke shi a matsayin yayana, I trusted him with everything… amma shi ne yake yi mini waɗannan abubuwan?” Muryarta ta karye a ƙarshen maganar, “Me na yi masa, Daddy? Me na yi masa har zai riƙa tsoratar da ni haka?” Falon ya ɗauki shiru, shiru mai nauyi, na tsawon mintoci aƙalla biyar, babu wanda ya yi magana, kowa yana jin numfashin ɗan uwansa, amma babu wanda ya kuskura ya katse shirun, abin da ya fi ba Inteesar mamaki shi ne, ba ta ga wata alama ta tashin hankali ko girgiza a fuskar Daddy ko Mommy ba, ko kaɗan, su biyun sun kasance cikin wani irin natsuwa mai ban mamaki, kamar abin da ta faɗa ba sabon abu ba ne a gare su, ita kuwa Inteesar, wannan natsuwar ta ƙara ruɗar da ita, why aren’t they surprised? Ta juya ta kalli Umar, shi ma yana gurfane, kansa a ɗan sunkuye, babu wata alama ta mamaki a fuskarsa, sai sanyin gwiwa da wani irin damuwa da take kasa fahimta, wannan ya ƙara karya mata zuciya, domin a tunaninta, idan har mutum ya gano cewa wanda ya ɗauka a matsayin amintaccen ɗan uwa shi ne ya aikata abu irin wannan to ko da kuwa komai ya faru, dole ne a ga alamar mamaki a fuskar waɗanda ke kusa da shi, amma me ya sa nasu ya bambanta?

Daddy ya sauke wani babban numfashi, sannan ya kalli Inteesar da kyau, “Fateema…” Zuciyar Inteesar ta buga da ƙarfi, ta ɗago kai a hankali, tana kallon mahaifinta da idanun da suka cika da tambayoyi, domin ta san abu ɗaya, idan har Daddy ya kira ta da ainihin sunanta na gaskiya, to tabbas maganar da ke tafe ba ƙarama ba ce, wannan sunan ba ya fitowa daga bakin Daddy haka kawai, yana da wani irin nauyi, wata ma’ana da ta saba ji tun tana ƙarama, ta gyara zamanta, tana jiran abin da zai biyo baya, Daddy ya ɗan yi shiru, kamar yana neman kalmomin da suka dace da abin da zai faɗa, sai ya fara magana cikin sanyin murya, “Yau ne ranar da ya kamata ki san gaskiya,” Inteesar ta haɗiye miyau, Daddy ya kalli Umar na ɗan lokaci kafin ya mayar da dubansa gare ta, “Umar ba yayanki ba ne na uwa ɗaya, uba ɗaya,” Inteesar ta lumshe idanunta, kamar tana ƙoƙarin fahimtar kalaman da suka fito daga bakin mahaifinta, “What?” Ta sake buɗe idanunta, tana kallonsa da mamaki, Daddy ya ci gaba, “Umar ɗan ɗan uwana ne da ya rasu tun yana ƙarami, bayan rasuwarsa, na ɗauko Umar na riƙe shi a matsayin ɗana, na raina shi tare da ke, kuma tun daga lokacin, ban taɓa nuna miki wani bambanci a tsakaninku ba,” Inteesar ta buɗe baki, amma ta kasa magana, idanuwanta suka zaro waje tsabar mamaki, ta juya ta kalli Umar, sannan ta sake kallon Daddy, “Amma… Daddy…” Ta kasa ƙarasa maganar, duk rayuwarta, ta san Umar a matsayin yayanta na uwa ɗaya, uba ɗaya, mutumin da suka girma tare, wanda ta saba kira da sunan Yaya, wanda ta amince da shi ba tare da tunanin cewa akwai wani ɓoyayyen abu a tsakaninsu ba, amma yanzu… all this time?

Daddy ya ɗan gyara zamansa, sannan ya ci gaba da magana, “Dama na yi wa kaina alkawari tun Umar yana yaro cewa zan ba shi aurenki idan kun girma,” kalaman sun sauka kan Inteesar kamar wani sabon abu da aka jefa mata a lokaci guda, ta juya ta kalli Umar da sauri, shi kuwa yana zaune ne kansa a sunkuye, ba tare da ya ce uffan ba, Daddy ya ci gaba, “Amma saboda wasu dalilai na dangi, Umar ya auri Nana, ita ma ɗiyar ɗan uwana ce, cousin ce a gare ku, ni kuma a matsayina na uba, ba zan taɓa yarda Umar ya haɗa Nana da ke, Inteesar, a gidan aure guda ba, shi ya sa na janye wannan maganar,” Inteesar ta kasa cewa komai, kamar an buɗe mata wata ƙofa ce da ta daɗe a rufe, aka jefa ta cikin wani sabon yanayi da ba ta taɓa tsammani ba, auren ta da Umar? Wannan shi ne abin da Daddy ya shirya tun suna ƙanana? Ta ji kanta ya fara sarawa, Umar kuwa ya ɗago kai ya kalli Daddy, idanuwansa cike suke da wani irin roƙo, da kuma wata soyayya da ya daɗe yana ɓoyewa a cikin zuciyarsa, amma bai ce komai ba, Daddy ya lura da kallon da Umar yake masa, amma bai bari hakan ya sauya maganarsa ba, ya gyara zamansa, muryarsa ta ƙara yin nauyi, “Saboda haka, Umar, ina son ka fahimta sosai, tun ranar da ka auri Nana Aseeyah, maganar aurenka da Fateema ta tashi har abada,” ya ɗan dakata, yana tabbatar da cewa Umar yana sauraron kowace kalma, “Ba zan taɓa yarda ka haɗa yara biyu nawa da na ɗan uwana a gidan aurenka ba, wannan hukunci ne da na riga na yanke, kuma babu canji a cikinsa,” falon ya sake yin shiru, Umar ya sunkuyar da kansa ƙasa, yana ƙoƙarin danne rauni da fargabar da suka mamaye ƙirjinsa, ya san halin Daddy, idan ya yanke hukunci, ba ya sauya shi saboda roƙo ko wani irin matsin lamba, cikin wata murya mai ɗan rawa, ya amsa, “Na gane, Daddy, na amince da hukuncinka, kuma zan kiyaye,” ya ɗan yi shiru, sannan ya ɗago kai a hankali, “Amma Daddy… don Allah, ina neman alfarma guda ɗaya,” Daddy ya kalle shi ba tare da ya ce komai ba, Umar ya ci gaba, “Karatun Inteesar a Nile University ya riga ya yi nisa, tana da babban aiki a gabanta, kuma ba na so ta rasa damar da take da ita saboda abin da ya faru,” ya sauke numfashi a hankali, sannan ya ƙara da wata murya mai ɗauke da roƙo, “Ina roƙonka ka bar ta ta koma Abuja ta ƙarasa karatunta, I promise you, Daddy… ba zan ƙara shiga sha’aninta ba, zan kiyaye iyakata, kuma ba zan sake damunta da komai ba,” ya ɗan sunkuyar da kansa, “Don Allah, Daddy,” Inteesar, wacce ke zaune kusa da Mommy, ta tsinci kanta da saurin ɗago kai tana kallon Umar, ba ta yi tsammanin zai roƙi hakan ba bayan duk abin da ya faru, bayan saƙonnin da suka tsoratar da ita, bayan yadda ta yi kuka har ta kasa numfashi, bayan yadda ta bar Abuja cikin ruɗani da baƙin ciki, why is he asking Daddy to let me return? Ta kasa fahimtar abin da ke zuciyar Umar, kuma a wannan lokacin, ba ta da ƙarfin tambayarsa, Daddy kuwa ya yi shiru na ɗan lokaci, yana nazarin maganar Umar, ya juya ya kalli Inteesar, wacce har yanzu idanuwanta ke kansa, tana jiran jin hukuncinsa.