Furen Zuciya

Chapter 2

by @nasreelml

🌸🌹🌺FUREN ZUCIYA.
 Flower of the heart.

   By Nasreel R.L.
      🤍A hausa love story…….

Chapter 2;

Bugun kofar dakinta da akeyi a haukace ya tasar da ita doga bacci mai nauyi da takeyi. Ahargitse tamike duk jikinta yay tsami tanajin yanda ribs dinta yadauka azaba saidai bata bita kanshi ba ta nufi Kofa-ta janyeta gefe tana
mutsike ido. daga daga cikin masu aikin gıdan ne tsaye ta kura mata ido tana taunar chewing gum kas-kas tana sanye da white tshirt da black knee-lenght skirt. 

Tabe baki tayi ta juya tahau tafiya sannan ta furta “ kizo Ummi na kiranki a part dinta”. Da ok Miral ta ansa dukda tasan bajinta zatayi ba dan tayi nisa sannan ta koma cikin dakin taje dan lungu da kayanta suke. Kayan duka duka basufı guda 5 ba, kuma duk sıeeping dresses ne sai abaya guda daya black data tsufa itama. 

Wata pink sleeping dress ta dauka sannan ta dau zani dake a kansu ta zura jilbab dibta ta fita daga part din. Straight part na masu aikin ta nufa dan yin wanka coz part dinda dake stores ne dan haka babu toilet a ciki saitazo nan. babu kowa a ciki kamar yadda tayi tsanmani dan kowa yatafi aikinshi. Karamin part ne dake dauke da dan madaidaicin palour dayasha furniture masu kyau da dakuna uku a ciki sai toilet na palour dayake kana shiga part din. toilet din ta nufa ta shiga tayi wanka a gurguge ta wanke jinin dake goshinta da fuskarta dayake tun jiya bata wanke ba. Dakyar ta iya wanke kan ciwon dake goshinta dukda ciwon bashida girma saidai ya suntuma sai azaba yakeyi musamman data samishi ruwa. 

Saida ta saka kayanta takuma wanke rigar data cire ta fito ta maida jilbab din sannan ta koma part din datake ta shanya rigar a jikin kofar dakinta tanajin yanda jilbab din jikinta duk warin abinci da jini da suka zubo mata jiya amma batasamu wankewaba dan jiya tana gyara palour ta dawo daki ta baje wani nannauyar bacci ya dauketa. 

A hanzarce take komai sannan cikin hanzarin ta nufi part na Ummi tana addua aranta Allah yasa kada tayi mata mummunan hukunci akan dadewar datayi dan tasan dole zata hukuntata. 

A palour ta sameta ta zauna a usual sofa datake two seater dake kallon tv dan bata iya zam a one sitter tayi mata kadan. tana sanye da wani red turkish evening gown dayasha adon embroidery kana ganinshi kasan designer ne. Wata matace a gefenta sanye da wata mahaukaciyar luxury black abaya da koda Miral batasan luxury brands ba tasan wannan kosu Ummi basasaka irinta.  

Daure kanta yake da scarf dashima kana gani kasan bana kananan mutane bane, gaban gashinta a bude face dinta kusan half arab half japanese dan kamannin japanese din sunfi karfi a face dinta.  Bazaka kira ta da kyakyawa ba saidai batada muni sam, fuskar ta a daure babu alaman dariya, kana ganinta kasan ba karamar mata bace kadaga irin zaman datayi. 

Ummi ko sai smiling takeyi ear to ear kamar wanda take watching comedy show, dajin sallamar Miral tayi saurin daga idanunta ta sauke ma Miral wani mugun kallo kafin a kule tace “ dalla malama jiranki akeyi ubanwa kika ajiye kike wani sallalabewa agurin nan”. Da sauri Miral ta karasa gaban ummi dan nesa da ita ta tsugunna cikin sassanyar muryanta so soft kamar ana shafa maka feathers tace “ Kiyi hakuri Ummi, wanka na tsaya yi. ina kwana”. Sannan ta juya ta kalli matar dake opposite din Ummi kamar zata gaisheta, kamar wanda ta tuna wani abu saita fasa ta dago idanunta daidai yanda zataga Ummi. 

Yarfa hannu Ummi tayi alaman ta gaidata sannan ta juya idanunta a kasa ta gaisheta. Bata ansa taba kawai binta da ido tayi dama Batayi tsanmanin zata ansa ba dan kusan duk kawayen Ummi banda kallon kaskanci babu abunda yake hadasu. 

Sunkai wajen 5 minutes amma ji Miral tayi kamar ta shekara goma a gurin har gwiwoyin ta sun fara sagewa tarasa meya kawota nan tunani takeyi ta tashi ta tafi ne? dan tanada aiki saidai ganin Ummi bata ce ta tashi ba yasa ta hadiye confusion dinta ta zauna. Chan kuma saiga muryar matan “ tashi tsaye”. Ta fada a harshen turanci. Mikewa Miral tayi still idonta a kasa. 

Ummi tace ta cire hijab na jikinta a sanyaye ta cire tanajin kirjinta na dukan uku uku jin yauma ansata cire hijab. Me hakan yake nufi? Dan tabe baki matar tayi tanabin jikinta da kallo sama da kasa kamar wani product dazata siya. Alama tayi mata da ta matso kusa dayake idanunta na kasa batagani ba. Tsawa Ummi tayi mata akan ta dago idanunta ta matsa da sauri jikinta na kyarma ta dago sannan ta matsa inda matar take ganin ta kara hade rai yasa ta kara matsawa dab da ita. 

Kare mata kallo tayi tas sannan tayi mata alaman ta matsa. Ummi ne ta tambayeta koh zata iya tafiya ta gyada kai dan haka ummi tace ta wuce ta jeta fara aikinta. Da sauri ta dauki jilbab din ta fita cikin hanzari zuciyarta na bugawa tana sauke ajiyar zuciya dan Allah Allah dama takeyi tabar palourn. 

A bangaren Ummi kuwa bayan Miral tafita ta juyo ta kalli matar gefenta cikin tausasa murya tace “ Miss kamila zatayi kuwa? Naga kamar batayi miki bah idan abunda zamu iya chanzawa ne sai musan yanda zamuyi tunda wuri”. 

Dan kyabe baki matar takarayi tana wani mutsika face a gadarance tace “ Kin tabbata bata san namiji bah? Karki bani wahala kinsan inda hakan zai kaiki”. Da sauri Ummi tace “ A’a na tabbatar, dukda yarinyar tayi abubuwa a baya da bazasu furtu ba amma banda bin maza intabbatar miki ma ko saurayi bata taba yi ba yarinya ce sosai”. 

Dan jim Miss ayra tayi sannan tace “ shekaranta 18 kikace? Kin kuma dauketa na shekara biyu yanzu bayan barin gidan iyayenta, kin tabbatar bata taba sanin namiji ba, sannan kuma kince tayi munanan abubuwa kafin su koreta? Yarinya yar shekara 16 kenan a lokacin? Metayi ne haka?”. 

Dan jan nunfashi ummi tayi sannan tace “ Ina tabbatar miki Miss kamila yarinyar nan 18 take, sannan a shekara sha hudu na dauketa, abunda tayi duk babu wanda bai dagama hankali ba dan babu mai zaton yarinya kamarta zatayi, a tana sheru 13 tana shirin shiga 16 tadawo makaranta ranar…..”. 

Katse ta Miss arya tayi tace “ banason ji, munada bayanan ta already babu abunda yake a boye a gurinmu, sannan duk abunda tayi matsalar tace. gobe zansa azo a duba mun ita idan abunda kika fada gaskiya ne. Idan har akaga cewa she is pure toh zamu aiwatar da plan din. Zaki kawo mun ita ghair muaddal, daga nan zan dauketa, daga ranar dana dauketa ban sanki ba, baki sanni ba Halima, bamuyi maganar yarinyar nan dake ba, bakuma wani zaiji zancen nan ba. Bakuma zaki saka a ranki cewa zata dawo ba dan ta tafi kenan”. Gyada kai Ummi tayi sannan ta cigaba. 

“ sannan naga ciwo a goshinta, face dinta a kumbure yakuma faffashe, banason sake ganin wani tabo ko ciwo a jikin yarinyarnan bama anfani da masu ciwo, sannan a bata abinci mai gina jiki zansa a kawo supplement dan she’s too skinny for my liking”. Tana gama fadin hakan kuma ta tashi ta dauki channel bag dinta. Ansawa da ok Ummi tayi tabude baki kamar zatayi magana saikuma ta fasa tadan sunkuyar dakai tana wani dan smile kamar wanda ke son yin wani abu yakasa. 

Dan juyowa Miss Kamila tayi ta kalleta cikin wani annoyed voice tace “ kyautar ki sai bayan komai ya tafi daidai, idan an tabbatar mun gobe gaskiya kike fada toh ranar da kika danka mun yarinyar nan a ghair muaddal ranar abunda kike buri zai cika, sannan koda kuwa kin chanza ra’ayinki mun riga mun ansheta, bama chanza magana, sannan idan kikayi yunkurin tona maganar dake tsakaninmu toh lallai kinsan waye mu, bama fadan hukunci, saidai hukuncin mu nada tsanani, wanda sukayi yunkurin yaudaran mu basu shaba”. 

Tana fadin hakan tayi wucewarta ta fita ta exit. Har waje Ummi ta rakata zuwa garage inda wata Arniyar bentley take a parke ga wasu bodyguards su biyu a gefen motar. Bata ko kalli Ummi dake mata sallama ba daya dage cikin bodyguards din ya bude mata kofar baya ta shiga sannan ya shiga mazaunin driver dayen bodyguard din ya shiga gaba suka ja motar da gudun gaske suka fice. 

Sauke wata nannauyar ajiyar zuciya Ummi tayi sannan ta juya ta shige gida ranta fes dan tasan yau burinta ya cika. 

A bangaren Miral kuwa aikinta ta fara yi dukda takasa cire tunanin abunda yafaru tun daga daren jiya zuwa yau. Har yanzu maganar Ummi nacewa zasu taimaki juna take tunani. A iya saninta babu abunda zataiya taimakon Ummi dashi, kudi Allah ya bata, yaya bataso tun bayan data samu hanat tace bazata kara ba, kuma ta ishe ta dabakinta ta fada batason kari, tanada miji mai sonta, ga kawaye da yan uwa masu sonta. Babu wani abu datake da bukata da zata iya batashi. Dan haka sosai abun ya girgiza kuma ya razana kwajwalwar ta. 

Gakuma wasu sabbin questions din dabata da ansar su. shin waye wannan mata datazo yau? Meyasa Ummi zata bukaci ganinta takuma sanyata cire hijab matar ta kare mata kallo? Kodai siyar da ita Ummi zatayi ne?. Dan dariya ne ya kubce mata a tunanin datayi saurin denashi sakamakon zafi daya ziyarce ta a fuska dan marikan jiya har yau kamar sabo take jinsu. Babu yanda za’ayi Ummi ta siyar da ita. Bayan Ita Ummin da kanta ta dauketa dukda batada niyya da farko? Kuma itadin dukda ba sonta takeyi sosai ba ai yayar mamanta ce, aunty dintace bazata taba yin hakan ba. Barta dai da yi mata azaba amma baza ta taba siyar da itaba. 

Wanke hannunta tayi tareda karasa jera plates din data wanke a cikin dishwasher, dan haka Ummi tasata duk wanke wanke da akeyi a gidan ita takeyi idan tagama wankewa saitasa a dishwasher yakara wankewa. Tasan salon kawai wahalar da itane dan babu wasu ayyuka a gidan masu aiki keyin yawancin su.

Wucewa tayi tafara gyaran kitchen din a hankali dan duk wani motsi datayi saitaji ribs dinta na ansawa, addua kawai takeyi Allah yasa ya warke da kanshi dan tasan ba kaita hospital za’ayi ba indai ba gani sukayi ciwon na neman kasheta ba. Saida ta gyara shi tsaf sannan ta nufi wani mini fridge da ake ajiye leftover abinci da ba’a sawa a main fridge, cikin sa’a taga wani plate na scrambled eggs dadan yawa da sausages wajen 5 cikin sauri kamar wanda za’a kwace mata ta dauko shi ta juyeshi a cikin wani rubber container dan ba’a barinta taci a plates na yan gida. 

Straight dakinta ta nufa ga yau da alaman ana rana dukda bata leka waje ba a yanda dakinta yawani dau huci kamar oven ga babu window bare tasamu wani ventilation wani dum ta shiga kawai ta zauna kan yagalgalallen bedsheet dake shinfide akan simintin dakin. 

A hankali tasa hannu tafara cin eggs din saida ta gama ci sannan ta dauki sausages din suma taci. Alhamdulillah tayi tana godema Allah atleast yau tasamu abunda zata kai bakinta kafin ta fita sharan waje. Tunawa da bata dauko ruwa ba yasata sauke ajiyan zuciya tun batayi wani komai ba harta gaji. Dan kwanciya tayi tana maida nunfashi tunane tunane na dibanta saidai jin yanda hucin zafin dakin ya rufeta yasata mikewa tareda daukar container ta fice daga dakin dan yau bazata iya zaman dakin ba a cikin zafin nan gwara ko kitchen ne taje ta zauna tasha iska.

Koda ta koma kitchen saitaga har chefs sun fara preparations na lunch dan haka bata yi kokarin zama ba kafin Headservant ta shigo tayi mata bala’i akan kitchen ba gurin zama bane. Abun shara ta dauko kawai ta nufi waje, fili ne babba sosai ga wani open garage a karshe mike idan ka shigo gate din gidan da motoci guda 4 a parke Mercedes biyu sai lambo biyu daya pink daya black. Body guards ne guda hudu biyu a gurin gate biyu kuma suna zagaye babu wanda ya nuna ya ganta cikinsu sai guda daya dake bakin gate daya kureta da ido tunda ta fito. Yi tayi kamar bata ganshi ba yanda tasaba dan idan da sabo ta saba.  

Daga gurin motocin tafara sharowa irin dogon tsintsiyan nan da ake using dinsu a tsaye. Ko rabi batayi ba tafara nishi tana gumi dan wata irin rana ake kwallawa kamar ana dafata. ji tayi kamar ta cire hijab dinta saidai sanin wannan mutumin nanan yasa mata ido bazai barta ta iya cirewa ba dan a hakan ma idanunshi kamar ya chinyeta. 

Da kyar tanayi tana zama ta huta tasamu ta karasa saidai batakai har gurin gate dinba ta kwashe adan nesa ta shige cikin gida. Nishi takeyi da karfi da karfi duk nunfashi daya sai kirjinta ya ansa. Ta jike sharkaf da gumi sai diga takeyi. Straight dakinta ta wuce a kofar data shanya rigan data cire ta tsaya tadan huta sannan ta ja rigar data kusa gama bushewa ta fita tayi part na masu aiki. Dayake kusan sun gama aiyyukan su banda masu girki dan haka a palour ta gansu wajen su 3. 

Gaishesu tayi a hankali basu ansa ba babu ma wanda ya juyo ya kalleta kawai ta shige toilet din. Daya daga cikinsu ne wata yar budurwa cikin daga murya tace “ kada ki taba mana ruwan heater dama, ba tsoho ya siya ba”. Tana fadan hakan kuma Suka wani kwashe da dariya harda tafawa. 

Tajisu sarai saidai tayi kaman bata jisu ba, dukda sosai abun ke damunta saidai tasan yes da gaskiyar su tsohonta bai siya ba, dan a cewarshi mutuwarta shine babbar kyautar da zata mishi. Haka ta kunna ruwan sanyi dan da tayi niyyan tayi wanka sosai saidai ganin bazata samu ruwan zafi ba kuma tana tsoron mura kawai ta dauraye gumin jikinta ta sanya rigarta ta wanke wandata cire tareda jilbab din sannan tafito. 

A kofar fita part din sukayi karo da wata yarinya da bazata wuce 17 years bahaka. Yar head servant ce dukda ita ba aikin takeyi ba kawai dai takanzo ta yini a gidan ta tafi da dare. Sauke kanta Miral tayi tana dan rabeta ta wuce. Saurin riko hannunta khalisa tayi tana dauke da murmushi akan cute arab face dinta tadan jawota baya tabude baki zatayi mata magana kawai Miral ta fincike hannunta idanunta suka wani yi ja sukayi ciki ciki tareda cikowa da hawaye tafara girgiza kai tareda yin baya baya daga khalisa kamar taga aljana. 

Danne kunnuwanta tayi hawaye na gangarowa daga idanunta bakinta na rawa tana furta “ no no, ban aikata ba wlh, Layla ki fada musu gaskiya Layla , Layla”. Tarinka maimaita hakan a dimauce khalisa ta matsa baya tana zazzaro ido batasan metayi ba, waye kuma Layla? Saurin shigewa ciki tayi sauran maids din dake zazzaune a cikin palourn suka juyo suna kallonta dayan cikinsu kawai ta fashe da dariya harda rike ciki tana fadin “ Jama’a akwai  mahaukata fa a gidan nan, Layla dake ake fah”. 

Ta fadi hakan tana nuna ta gefenta da alamun itace Layla. Dan zazzaro idanu tayi tana nuna kanta kafin ta kwashe da wata shegiyar dariya tana fadin “ Ni Layla menayi? Yaushe nazo gidan nan ko wata daya banyi ba shegiyar yarinya ko magana bata taba hadamu ba.  zata fada uban me nayi mata kuwa yau”. Da fadin haka ta mike a zabure sauran biyun na dariya kamar zata kashesu suka mike suka bita suka nufi Miral datake zaune a kasa ta janye gwiwoyinta zuwa kirjinta ta kifa kanta akan gwiwoyinta sai surutai takeyi tana girgiza kai. 

For more information, contact me via WhatsApp ***.