Zaren Rayuwar Mu

BABI NA ASHIRIN DA TAkWAS

by @zainabb

Zaren Rayuwar Mu 

BA NA GAJI da kulawa da Zaid bane ba, na dai gaji da jin mutane a kusa dani a kodayaushe. Da wuya ɗakin shi ya kasance daga ni se shi. Yanzu duk gajiyar da Yaya Hauwa zata yi, tana ƙoƙarin zama a asibiti koda na minti talatin ne. Itace bana son ji mafi akasarin lokuta saboda ina jin idanunta akaina a kodayaushe idan tana nan. Ji nake kamar ma bata son ta blinking idanun ta idan tana kallo na ina yiwa Zaid wani abu. Yanzu ko ba komai nake mishi ba, ina zaune kawai ne, idanu take sa min ina jin har bana jin daɗi akan kallon da take min. 

Fitar physiotherapist na Zaid kenan bayan ta gama nuna mishi yadda ake son ya dinga numfashi saboda komai nashi ya zama dai-dai. Dama tun kafin ta shigo ina son goge mishi jikin shi, to bayan fitar ta na tashi na zuba ruwan zafin dake cikin flask a cikin bowl na ƙara da ruwan da basu da sanyi domin na samu even temperature. Oil perfume nasa cikin ruwan na janyo towel. Zaune Zaid yake na fara goge mishi jikin shi da ruwan ya saka dark glasses a idanun shi fuskar shi neutral baya dariya.

Abba ne ya shigo bana ma tsammanin shi a wannan lokaci. Ahankali na aje towel ɗin ina jin nauyin Abba. 
   “Ki cigaba da aikin ki, Hadiza. Allah yayi miki albarka, mun gode” Abba ya faɗa min
Murmushi kawai nayi na kasa cigaba da abinda nake yiwa Zaid. “Dama biyowa kawai nayi na duba ku. Jikin da sauƙi dai ko?”
    “Eh, Abba, yaji sauƙi sosai”
   “To Allah ya bashi lafiya, mun gode. Yau kuma Zaid dark glasses ake ji?” Abba yayi magana akan glasses na Zaid. Ɗazu da na fita yace na siyo mishi dark glasses idan na gani. Murmushi Zaid yayi yace “The room is too bright Abba”
   “Da chan baka gane it's too bright ba se yanzu bayan kaji sauƙi an kusa sallamar ka?”
Wani murmushi Zaid ya ƙara yi Abba kuma ya wuce. 
   “It's high time you stop being shy of them. They know what we did under the shower before my health deteriorated”
Wani kallo na yiwa Zaid nace “But we did nothing”
    “Really?” yace tare da ɗaga glasses nashi kaɗan ana ganin idanun shi 
  “Wannan glass naka shi zan fara fashewa tukunna”
Dariya yayi ya maida glasses ɗin a idanun shi yace “Try it”
   “What will you do?”
  “If you break it, you'll see what I'm capable of doing”
 “Yen yen yen” nace and Zaid laugh and I smile back na cigaba da goge mishi jikin shi
   “Yaushe zamu tafi gida, Hadiza? Na gaji da wannan zaman”
  “Ina tare da kai kuma kake cewa ka gaji?”
Hannuna ya riƙe “Idan aka mana sallama mu biyu zamu wuce gidanmu ba ni kaɗai ba”
“Da ka ƙara jin sauƙi za'a mana. Ina so ka samu lafiya sosai kafin mu koma”
  “Yes, i understand but there's no privacy here at all. People keep on coming”
Idanuna nasa akanshi ina kallon shi duk da glasses ɗin da yake sanye dashi yana min magana. Nasan kallona yake a ciki. “Wani abu kake so ne?”
   “We are getting to three weeks here and we have never done the married people stuff. I'm starved” Zaid yace babu wasa a tattare dashi.
Hannuna na cire a nashi jin abinda yace. “Ina jin tsoro kar wani ya shigo. Kamar yadda kace babu privacy”
    “Let's lock the door”
  “You want them to call in people for us a ce wani abu ya faru da kai kuma an rufe ƙofa. Idan zaka ji shawara ta ka jira mu koma gida tukunna kuma ni yanzu ina jin tsoro kar kazo ka kasa numfashi da kyau a ce bana kulawa”
   “Wa yace baki kulawa?” ya tambaye ni tare da ƙara riƙe min hannu
“Babu kowa. Zasu ɗauka bana kulawa dai”
“Let's lock the room minti goma ma yayi yawa. I promise it's going to be fast”
Girgiza kai nayi “Wait until we get back home”
   “I said I'm starved” Zaid ya faɗa min yana kallo na
   “Okay okay I won't lock the room but if we hear someone approaching, you're leaving me alone. Is that a promise?”
   “Yes, it's a promise”
Yana kallona na fara cire zip na riga ta slightly nayi tsaye a wurin shi ban san ya zanyi ba. 
   “I have no idea what to do next” na faɗa ina kallon shi and he smiles and I smile back.
Hannuwa na biyu ya riƙo and he made me sit on the hospital bed with him closely. A bayan riga ta yasa hannuwan shi on both sides and I felt his hands on my bosoms. I didn't stop Zaid and our faces merged and we kissed each other har yanzu glasses na sanye a idanun shi. 
Kamar tafiya nake ji jikina yana bani da akwai masu zuwa. 
  “I think there are people coming, Zaid” na sanar dashi cikin tsoro.
Fuskar shi ya kai dai-dai wuyana ina ji yana going down na ja numfashi sosai yace “No, there's no one coming. Let's just do this I'll soon let you go. Stay still stop being scared”
A dai-dai lokacin da fuskar shi ke chest ɗina ya ɗaura hannun shi a lower abdomen nawa aka buɗe kofa da sauri nace “Wayyo na shiga uku. Wallahi na faɗa maka” da sauri kuma na cire jikina a nashi. Ban tsaya ganin ko su waye ba na shige cikin banɗaki zuciya ta na wani irin duka. Fuska ta na fara watsawa ruwa a sink ina numfashi sama-sama. Hular dake kaina ma Zaid ɗin ya cire gashi sumar kaina bata da kitso ko ribbon ban saka ba haka na saka hula ga sumar a watse da yake nayi retouching. Kama sumar kaina nayi na ɗaure a bayana. Fuska ta na cigaba da watsawa ruwa. Zip na riga ta kuma na ja shi. Tsaye nayi na haɗe hannuwana a wurin kirjina. Naji nuryar Yaya Hauwa. Naji muryar Shahida. Naji muryar Muhammad. 

Zaid a chan kuma shi yana da glasses nashi be cire ba. Yayi kamar basu ga abinda yake faruwa ba yana bin su da idanun shi dake cikin dark glasses. 
Muryar Yaya Hauwa naji tana cewa “Hadiza ki fito daga banɗakin Shahida na so zata yi amfani dashi”
Zuciya ta naji tayi duka. Bani da niyyar fitowa se idan sun tafi. Kyalewa nayi duk bana jin daɗin jikina. 
Jin ban fito ba yasa Yaya Hauwa ta ƙara ce “Dan Allah kiyi haƙuri ki fito ki bata wuri” rufe idanuna nayi na ƙara sanyawa fuska ta ruwa. 
Shahida tace “Yaya kunya fa take ji”
  “Ai da sun faɗa mana ba zamu shigo ba”
   “Haba Yaya. Faɗa muku me?!” Shahida ta ƙara ce da murmushi akan fuskar ta shi kuma Zaid yana yi kamar be san abinda ake faɗa ba. .

Fitowa nayi daga banɗakin ina kallon su saboda bana so na zama embarrassed. Shahida ta wuce cikin banɗakin. Muhammad shima ya fita. Daga Yaya Hauwa se ni se Zaid. 
  “You should have locked the door” Yaya Hauwa tace. Zaid nake kallo directly ina yi kamar ban ji abinda tace ba. Zaid be cire glasses nashi ba ina ganin fuskar shi kamar yayi dariya amma be yi ba. 
Shahida ce ta fito daga banɗakin fuskar ta amusingly nasan har yanzu abinda suka gani na cikin kanta tana so tayi dariya amma babu dama. 
  “Yaya, yaushe za'a muku sallama?”
Haɗa idanu nayi da Yaya Hauwa tun ɗazu take kallona ina jin idanun ta a kaina. Ban san wannan wane irin observing ne take min ba. Ban san abinda take son ganowa akai na ba. 
  “Ba zan iya ce ga rana ba, Shahida, se Zaid ya ƙara samun lafiya”
Nodding kai Shahida tayi tace “Yaya ina ganin wasu dark glasses a Amazon masu kyau nasan kina sa glass idan zaki fita aiki. Ko zaki duba ki ga wanda kike so se mu sa order” Shahida ta faɗa tare da ɗauko wayar ta tana dubawa.
Zaid yace “Duk shagunan dake Abuja babu inda za'a samo dark glasses se anyi order daga Amazon”
Murmushi nayi na sunkuye kaina ina son kallon shi amma nasan Yaya Hauwa ni take kallo ta tsare ni da idanun ta. Shahida tace “Yaya kai ma fa inason ka siye ɗaya tunda naga ka fara saka glasses kuma a chan za'a yi order harda kai”
   “A Abuja ba za'a samu glasses ba har se an kai order a Amazon? Shine tambayar da nake yi”
Duba wayar ta take tace “Yaya abinda ake kenan fa. Yaya Hauwa ma a chan nake so ta siya stethoscope”
Ahankali na ɗago kaina na kalla Yaya Hauwa naga tayi murmushi tace “Ke zaki biya kuɗin ko?”
Miƙo min wayar ta tayi na amsa tace wa Yaya Hauwa “A'a, Yaya. Ke dai zaki biya”
 “Ni na faɗa miki ina buƙatar sabon stethoscope ne?”
Girgiza kai Shahida tayi tace “Yaya wannan fa ya jima”
   “Amma yana yi ko? Yaran nan ku se kuna kashe kuɗi har lokacin da be kamata ba shi yasa baku iya saving ba”
Murmushi Shahida tayi tace “Kaii Yaya! Ai ke kin wuce saving”
Murmushi Zaid yayi nima nayi murmushi harda Yaya Hauwa. 

Muna nan tare da juna har Nurse ta shigo ta duba vitals na Zaid. Bayan ta gama ta wuce. Direction na idanun shi na kallon Yaya Hauwa a cikin glasses nashi yace “Inaso a min sallama Yaya. Na gaji da zama a asibiti”
  “Ni nace ka shiga shower Zaid? Da baka sa kanka a shower ba nasan da yanzu an mana sallama but you and your wife caused it so you bear the consequences”
   “Yaya...” Zaid ya fara se kuma yayi shiru. Wata irin ajiyar zuciya na sauke dama bana so yace komai kar a tsawaita maganar kunyar da naji ta dawo min sabuwa. Kallona suka yi a ɗakin saboda sun ji ajiyar zuciyar da na sauke. Sunkuye kaina nayi amma duk da haka ina jin idanun Yaya Hauwa a kaina. Na kasa gane wane irin dalili ne yasa take min irin wannan kallon. Or I look like an alien to her?! 

Ba su suka tashi tafiya ba se ƙarfe goma na dare. Zaid na zaune akan gado nima ina zaune a wurin ƙafafuwan shi amma na ɗan kwanta saboda gajiya ina jin hannuna da nayi stretching yana taɓa ƙafar shi. 
  “Ku kula da kanku” Yaya Hauwa ta faɗa instead of saying “Ka kula da kanka, Zaid” kamar yadda take cewa a kodayaushe. Murmushi nayi jin abinda tace har cikin zuciya ta se da naji sanyi. 

Washegari da safe Khalifa ne ya kawo mana abinci daga gida. Yace min Mummy tace tana nan zuwa idan ta gama lecture da zata yi a makaranta. 
Muna yin magana dashi kamar case na Rahama be taɓa haɗa mu ba. Na dai gane shi bayi da riƙo a cikin ranshi ko kuma kawai ya aje wannan zancen ne saboda baya so yayi wani iri a wurina. 
Ya jima a inda muke domin har ƙarfe sha biyu yana wurin mu. Se bayan sha biyu tayi ya tashi yace makaranta ze tafi yana da lecture sha biyu da rabi. Magana yayi da ɗan uwan shi wacce ban ji ba tukun ya fita.