NURI

SCARS BENEATH HER STRENGTH 3

by @saddiqahhh

Ita da bata so yanzu taga tana kuka gaban mutane yau ta kasa riqe kanta, she needs to cry. She's down with everything happening in her life. Kamar yadda ta fada ne bata da kowa arayuwar nan duk kuwa da cewa bata rasa kowa ba. Abba kawai ta rasa Maminta da Afif suna raye amman kowa a duniya daban.

Wani daya zo wucewa ne ya dakata ganin yadda qafarta take zubar da jini. Kallon yadda take kuka yayi kamin ya durqusa gabanta yana kiran sunanta don ya santa. Few people in their neighbourhood didn't know her. She never meddled in anyone's affairs, but if anyone wronged her, they'd better be ready to face the consequences.

"Nuri kiyi haquri ki tashi daga nn muje na kaiki chemist you're seriously injured" bata kalleshi ba kuma bata da niyyar kallon nasa kawai dai tayi realizing kukan da take ta dena.

"Taso muje..."

"Kuje Ina?" Yaji wata qatuwar murya daga bayansa tana tambayar sa. Nuri hade rai ta sake yi jin muryarsa.

Juyawa Usman yayi yana kallon mai maganar da duk tsukun unguwar an sanshi riqaqqen dan daba ne da baya ragawa kowa sai kan Nuri ya fara dan saituwa. Shine mai gidan hayan nasu sannan shine ya jawo kowa yake tsoron batawa Nuri rai. Shi wai bai yadda ba sonta yake duk kuwa da bata taba bashi fuska ba amman ya gama yadawa unguwar ita yake so kowa ya guji shiga harkarta shisa kowa yake takatsantsan da kulata.

"Ciwo ne aqafarta kana gani Jibson.." wata harara ya masa da wannnan muryar da kana ji kasan a make yake ya furta "Kai eh ka shiga hankalinka.. kasan wace fa.. yanzu sai insa yarana su qaddamar maka wallahi.. sarauniyar zuciyar tawa zaka kai chemist... Da izinin uban wa?..."

Tsaki Usman yayi kamin ya juya wajen Nuri dake shirin tashi ya miqe tsaye yana kallonta ya sake cewa "sannu Nuri muje na kaiki chemist din kinsan sai anyi miki TT ko.."

"Usman wallahi sai na bar maka tabo yanzun nan.. ya ina cewa baka da hurumin kulata kana sake shige mata ehhh.. bana son yawa faaa..."

Bai kulashi ba, still looking at Nuri, who had started taking a few difficult steps towards their house yace "muje chemist din sammani dake kusa da gidan naku.." duk wannan abinda yake bata kulashi ba daga shi har jibson da tayi kamar ma bata san da wanzuwarsa anan wajen ba.

Take musu baya jibson yayi yana rangajin maye yake cewa "baaa...na son nayi maka illa Usman... Ka rabu da sarauniyar zuciyata haka nan.. zan kirasu coge su qaddamar maka ai ka sanni eh.."

Shi kadai yake surutansa babu wanda ya kulashi cikin Usman da Nuri da ba taji har Usman din zata kula ba bare shi dan mayen. Opposite din gidansu chemist din sammanin yake ba tayiwa Usman musu ba ta bishi akayi mata allurar don tasan tana buqatar ta. Awaje jibson ya tsaya banda zagi babu abinda yake durawa, yadda yake daga murya ne ya jawo hankalin kowa ciki har da 'yan gidansu tuni masu son gulma har sun fara leqowa.

Kallon Usman tayi tana bude baki da kyar ta furta "nagode.." kai ya girgiza mata yana cewa "babu godiya ki rinqa kula kinji Allah ya kiyaye gaba..."

Kai kawai ta gyada masa tana yin gaba zata fita ya take mata baya har zuwa qofar gidansu da jibson yake tsaye yana aikin zagin Usman din. "Wato Kai jan wuya baka ji ko.. ka jira kaga abinda zai faru da kai wallahi.."

"Wai meye naka aciki ne jibson yarinyar nan tana buqatar taimako don na taimaka mata wani abin ne??"

"Ina sane da kai fa sonta kake jibi yadda kake mata wani kallo kowa anan yasan Nuri tawa ce tun daga ranar da suka zo unguwar nan nayi tsundum cikin tafkin qaunarta..."

Kamar Usman ya shareshi sai yaga ba zai iya ba hakan yasa ya bude bakinsa yana cewa "and so what idan ina sonta, mace allurar cikin ruwa ce mai rabo ka dauka.. ka gwada naka sa'ar na gwada nawa sa'ar..."

Yunqurawa jibson yayi yana son miqewa sai dai babu qwari hakan yasa ya koma ya sake zama yana cewa "kaci sa'a yanzu nayi nauyi da wallahi saina barar da kai... Kuma ka guji haduwa ta da kai don bana jin zai maka kyau...."

Juyawa Usman yayi yana ja masa tsaki ya bar wajen, shi ba son Nuri yake ba kawai yana tausayinta ne irin sosai dinnan don duk wanda ya kalleta sai yaji ta bashi tausayi she's not mentally stable.

Bata tsaya bata lokaci ba wajen 'yan gidan nasu da suke binta da kallo kamar basu taba ganinta ba. Dakinsu ta shiga ta tarar da Inna kwance tana bacci, hankalinta taji bai kwanta ba tayi saurin qarasawa wajenta ta saka hannunta wajen hancinta ta tabbatar she's breathing sai dai kamr akwai zazzabi tare da ita.

Ajiyar zuciya ta dauke ta samu waje nan kusa da Inna ta zame ta kwanta da nufin hutawa. Tana iya jiyo qusqus din 'yan gidan wai Usman yana son Nuri.

Hutawa tayi kadan tana son kanta yadan lafa mata sannan ta miqe ta fita taje ta dauro alwala tazo ta tayar da sallar Azahar da la'asar da ba tayi ba. Hankalinta duka yana kan Inna don haka bayan ta idar sai ta sake komawa gefe da ita ta zauna tana kallon yadda numfashinta yake sauka da sauri sauri. Inna was in serious pain, hakan yasa Nuri miqewa tsaye ta qarasa wajen kayanta ta zaro kudin da Afif ya turo mata ta sake kirgasu 38 thousand ta gani. Ita kanta bata da strength sosai amman tana buqatar ta kaita asibiti a dubata sannan tayi ma kanta alqawari wannan karan duk taurin kan da Inna za tayi mata sai an dubata anga abinda yake damunta.

Hijab dinta ta mayar ta fita waje da niyyar samo abin hawa yazo har qofar gida akai Inna asibiti. Tana zuwa soron gidansu sai ga Nusaiba ta shigo agigice tana kuka amman ganin Nuri yasa tayi kanta da sauri tana cewa "Allah ya isa tsakanina dake Allah ya tsine miki munafika algunguma kawai wallahi bazan yafe miki ba..." Ta qarashe tana qoqarin kai hannunta zata cakumi Nuri da tayi saurin dakatar da ita tana hankadata baya. Bata kulata ba tasa kai zata wuce Nusaiba ta bi bayanta ta juyo da ita da qarfi wanda Nuri tana juyowa ta sauke mata lafiyayyen marin da qararsa ya isa har cikin gidan tana furta "kinsan bana hulda da marasa hankali ko?"

Da sauri Nusaiba ta dafe inda Nuri ta mareta tana jin radadin yana zaga mata ko'ina "wallahi sai na rama nagaji da abinda kike ba'a tsawatar miki... Idan duk da ina shiru yau bazan iya ba.. wato Usman kike so shine sai da kika san yadda kikayi ya fara sonki ko.. bayan sarai kinsan shine wanda nake so ko??"

Wani tsaki Nuri taja tana danasanin tsayawa kula Nusaiban da tayi. Wato akan namiji take wannan haukar, wani tsakin ta sake ja zata juya ta fita sai ta fasa ta dawo wurinta tana balla mata harara mai cike da warning ta furta "yau ya zama rana na qarshe da zaki sake shiga gonata Nusaiba ki kama kanki.." tana gama fadin haka ta juya ta fita tana mita aranta.

Tana jin haushin matan da suke hauka kalar na Nusaiba akan maza and the way she's acting ta tabbatar ita ke son Usman ba shine yake sonta ba.

Watsar da zancen tayi ganin kamar bai shafeta ba kawai dai ta tabbatar duk ranar da ta sake kuskuren shiga harkarta ta dauki alwashin nada mata na jaki ne kawai dama tun ba yau ba ta lura da take-taken Nusaiban.

Tunda ta fito 'yan unguwar suke kallonta hakan ya sake sawa ta daure fuskarta fiye da da aranta tana furta bata taba haduwa da 'yan sa ido kamarsu ba. Kamin taje bakin titi ta samu napep ta tsarar suka yi ciniki sannan ta hau ya dawo da ita bakin kofar gidan nasu ta sauka ta shiga da sallama ciki-ciki. Tarar da 'yan gidan tayi sunyi curko-curko an saka Nusaiba agaba ana bata haquri shigowarta yasa kowa yayi tsit yana binta da kallo. She wished she had a way to leave that house.

Dakinsu ta shiga ta tarar da Inna a yadda ta barta sai dai yanzu ta farka tana hada uban gumi. Wajenta ta karasa da sauri tana cewa "Inna lafiya?"

"Kai ta girgiza mata tana cewa "ina tunanin mutuwa zanyi Nuratu..." Wani wawan nishi ta sauke da wanda yake waje ma zai iya jiyowa.

Da sauri Nuri ta riqe hannunta tana girgiza mata kai "ba zaki mutu ba Inna ki dena wannan maganar don Allah..."

Idon Inna kawai ka kalla kasan she's suffering sosai don gaba daya kammaninta sun sauya "Nuratu kiyi haquri ki yafemin nasan na zalinceki keda mahaifiyarki don Allah ku gafarta min..."

Nuri bata bari ta qarasa ba ta furta "ki dena wannan maganar Inna asibiti za muje yanzu a dubaki..."

Kai ta girgiza mata da sauri tana dafe cikinta ta furta "ba sai munje ba Nuratu karki kashe kudinki inaji ajikina mutuwa zanyi...."

Da wani kalar ihu daya jawo hankalin mutane kansu Nuri ta furta "ki dena zancen mutuwa... Ba zaki mutu ba.. ki mutu ki barni da wa? Da wa zan zauna? Ya kike so nayi? Wa nake dashi?"

Hawaye ne ya fara biyo fuskar Inna cike da tausayin kanta da Nuri "Allah yana tare dake Nuratu.. amman inaji ajikina kamar tafiya zanyi.. kamar ciwon nan bana warkewa bane..."

Hannunta Nuri ta saki tana share hawayenta da sauri ta miqe taje ta daukowa Inna hijabi ta saka mata tana cewa "karki sake magana don Allah idan kinsan zancen mutuwa zakiyi.." da kyar ta iya taimaka mata suka miqe suka fita waje da duk da cewa kana ganin halinsu kasan suna buqatar taimako amman haka mutanen gidan nan suka yi kamar basu gansu ba suka kyale su suka fita su kadai.

Da kyar ta iya qarasar da Inna wajen mai napep ta shigar da ita ta zauna tana rungumota jikinta tana qoqari sosai wajen hana kanta kuka. Ka kalleta alokacin hardai kana da saurin kuka sai ka mata kuka. Tana state din da take jin kamar zata rasa Inna sannan ita kadai ta rage mata, kamar dai Inna kadai ce hope dinta haka.

Itama Innan rungume Nuri tayi tana jin wata nadama da danasanin abinda ta aikata musu ita da mahaifiyarta. Bata taba tunanin ranar da za tayi nadama kalar wannan zata zo ba. Duk da dama tun farkon shekara biyun da suka wuce ta tuba ta gane abinda take duk ba daidai bane. But she never imagined that she would regret what she had done to Bintu and her children. Musamman NURI! She fell victim to Inna's schemes more than anyone else... Komai kamar akanta ya fada.

Yau jinin wadda ta tsana ce take kula da ita, ci sha har dama sutura wani lokacin! Yarinyar Bintu yau itace kadai gatanta a duniya! Bintu dai matar data tsana saboda bata da dangi ba kuma asan asalinta ba... Jininta data tsana dai itace ta zama gatanta duk kuwa da cewa tana da yara guda biyu a raye Zakiya da Sallama.. Zakiya ta zabi duniya kanta.. while Salama ta zabi mijinta!!!!

To be continued..

#nur

NURI
By Saddiqa
65.

like, comment and share