Fate Brings Them Together
by @ramsha002
Chapter Two
fate Brings Them Together
by Rabi'a Muhammad Shariff
Ramsha Tales
Latif ya juya zai shiga motarsa. Da ya buɗe ƙofar motar zai shiga, sai Hibba ta miƙa hannu ta rufe ƙofar.
Latif ya tsaya cak, cikin matuƙar mamaki. Bai taɓa tunanin wata yarinya za ta yi masa irin wannan halin ba. Ya yi mamakin ƙarfin halin da take da shi na tare shi, alhali kuwa shi Latif Abdurrahman ne.
A hankali ya juyo ya kalle ta, fuskarsa cike da mamaki da fushi.
“Kin san da wa kike magana?” ya tambaye ta cikin izza.
Hibba ta kalle shi ba tare da ko alamar tsoro a fuskarta ba.
“Na sani mana. Da mutumin da zuciyarsa babu tausayi ko jin ƙai, da wanda babu imani a zuciyarsa.”
Ta ɗan dakata, sannan ta ci gaba cikin tsananin baƙin ciki.
“Wannan ɗin da mahaifiyarka ce a kwance haka, za ka ɗauki kuɗi ka wulaƙanta ni, ka ce in kai ta asibiti?”
Da jin ta ambaci mahaifiyarsa, ran Latif ya yi matuƙar ɓaci. Yana matuƙar son mahaifiyarsa, don haka bai ji daɗin jin ta yi magana a kanta ba.
Cikin fushi ya ce, “Karki kuskura ki sake faɗin wani abu game da mahaifiyata!”
Hibba ta yi wani murmushin takaici, sannan ta kalle shi cikin baƙin ciki da ɓacin rai.
“Ashe kana son mahaifiyarka? To, wannan ma mutum ce ita ma. Tana da iyalinta, kuma suna sonta.”
Latif ya yi shiru. Duk da cewa ransa a ɓace yake saboda yadda yarinyar ta tsaya masa, maganganunta sun taɓa wani wuri a zuciyarsa. Bai yi tsammanin za ta iya magana da shi haka ba.
Bai sake cewa komai ba. Sai ya nufi inda Aunty take kwance a ƙasa, ya sunkuya ya ɗauke ta, sannan ya saka ta a motarsa.
Bayan ya gama, ya kalli Hibba da wani irin kallo da yake nufin ta shiga motar.
Hibba ta fahimci abin da yake nufi, sai ta buɗe ƙofar baya domin shiga. Amma kafin ta shiga, Latif ya sa hannu ya rufe ƙofar.
Ya kalle ta cikin izza sannan ya ce, “I'm not your driver, so sit in the front.”
Hibba ta kalle shi, ta yamutse fuska saboda ba ta ji daɗin yadda ya yi mata magana ba. Amma ba tare da ta ce komai ba, ta buɗe ƙofar gaba ta shiga.
Latif ya shiga motarsa, ya tada injin, sannan suka bar wurin.
A cikin motar, fuskar Latif babu murmushi. Ya yi shiru, yana kallon hanya, har yanzu yana cikin ɓacin rai saboda abin da ya faru tsakaninsa da Hibba.
Hibba kuwa hankalinta yana kan Aunty, wadda take kwance a kujerar baya. Tana yawan juyawa tana dubanta, cikin fargabar kada wani abu ya same ta.
Kafin su isa asibiti, Latif ya ɗauki wayarsa ya kira wani. Daga yadda yake magana, Hibba ta fahimci cewa likita yake kira.
“Muna zuwa yanzu. A shirya komai, don Allah. Matar ta yi accident,” ta ji shi yana faɗa a waya.
Bayan ɗan lokaci, suka isa wani babban asibiti mai zaman kansa da ke garin Abuja.
Da isarsu, wasu nurses suka fito da gadon ɗaukar marasa lafiya. Suka ɗora Aunty a kai, sannan suka tura ta cikin asibitin domin a duba lafiyarta.
Hibba ta bi su da sauri, zuciyarta cike da fargaba.
Yayin da take kallon yadda ma'aikatan asibitin suke yi wa Latif magana cikin girmamawa, sai ta fahimci cewa shi babban mutum ne.
Latif ya yi duk wani abu da ya dace a yi a asibitin. Ya tabbatar da cewa an karɓi Aunty kuma an fara kula da ita.
Bayan ya kammala komai, sai ya ga Hibba zaune a corridor na asibitin.
Ya ƙarasa inda take, ya ɗauko kuɗi ya ajiye a gefenta.
“Na gama duk wani abu da za a buƙata a asibitin. Wannan kuma sai ki yi amfani da shi,” ya faɗa cikin sanyin murya, amma har yanzu fuskarsa ba ta nuna tausayi sosai ba.
Hibba ta ɗauki kuɗin, ta miƙe tsaye, sannan ta miƙa masa su.
“Na lura kana ba kuɗi muhimmanci. To, ka riƙe su, za su fi maka amfani,” ta ce.
Ta miƙa masa kuɗin, amma Latif bai karɓa ba. Sai ya tsaya yana kallonta cikin mamaki.
Hibba ta matso kusa da shi, ta kamo hannunsa, sannan ta saka masa kuɗin a tafin hannunsa.
Ba tare da ta ƙara cewa komai ba, ta juya ta bar wurin. Ta nufi ƙofar ɗakin da aka kwantar da Aunty, ta tsaya a bakin ƙofar tana jiran samun labarin halin da take ciki.
Latif ya ji ransa ya sake ɓaci, amma bai ƙara bi ta kanta ba. Ya juya ya fita daga asibitin.
Hibba ta dawo ta zauna a kan kujerar corridor ɗin. Ta girgiza kai cikin takaici, sannan ta furta a hankali:
“Wannan wani irin mutum ne? Gaba ɗaya ba shi da tausayi.”
A ɗaya ɓangaren kuma, Latif ya shiga motarsa cikin fushi.
“Wannan wace irin yarinya ce? Gaba ɗaya ta ɓata min lokaci!” ya faɗa shi kaɗai.
Ya ja motar cikin fushi, ya nufi kamfaninsa.
Wato L.A. Imperial Group of Companies
Bayan Latif ya isa kamfaninsa, ya fito daga motarsa cikin sauri, duk da cewa yana tafiya da irin kasaitarsa da aka saba gani.
A saman ginin kamfanin, an rubuta babban suna mai ɗaukar ido:
L.A. IMPERIAL GROUP OF COMPANIES
Latif ya shiga cikin ginin. Da ma'aikatansa suka gan shi, sai suka miƙe tsaye cikin girmamawa. Amma saboda ɓacin ran da yake ciki, bai kula da ko ɗaya daga cikinsu ba. Kai tsaye ya nufi ɗakin taro, inda aka shirya gudanar da muhimmin taron da yake da shi da wasu Amurkawa game da aikin gina banki.
Amma da ya shiga ɗakin taron, sai ya ga babu kowa a ciki sai wata daga cikin manajojinsa, Alisa.
Ya kalle ta cikin mamaki.
“Alisa, me ya faru? Ina mutanen suke?”
Alisa ta miƙe tsaye cikin girmamawa.
“I'm sorry, sir. Sun tafi saboda sun daɗe suna jiran ka. Na ba su wani uzuri, amma yanzu sun ce za su sake tsara ranar taron, sannan su turo mana da email.”
Latif ya buɗe baki cikin takaici.
“Oh, shit! Yanzu duk komai ya ɓaci!”
Ya shafa fuskarsa cikin fushi, sannan ya girgiza kai.
“Wannan yarinyar ta zama kamar wata bad luck a gare ni!”
Ya juya cikin fushi zai nufi ofishinsa, amma Alisa ta dakatar da shi da tambaya.
“But, sir, wace yarinya ce wannan?”
Latif ya tsaya, ya juyo ya kalle ta cikin fushi.
“Yaushe kika fara shiga abin da bai shafe ki ba?”
Alisa ta sunkuyar da kanta ba tare da ta ƙara cewa komai ba.
Latif kuwa ya juya ya wuce ofishinsa.
Da ya shiga, sai ya ajiye files da ke hannunsa kan tebur cikin fushi. Ya cire suit ɗin da ke jikinsa, ya zare necktie ɗinsa, sannan ya jefa su gefe.
Ya zauna a kujerarsa, yana girgiza kai cikin takaici.
“Gaba ɗaya wannan yarinyar ta ɓata min shirina. I hope I will not see her again!”
Ya faɗi hakan cikin fushi, bai san cewa ƙaddara za ta sake haɗa su ba.
Kwana biyu bayan an kwantar da Aunty a asibiti, likita ya sallame ta.
A cikin kwanakin nan, Latif bai je asibitin ko sau ɗaya domin ya duba ta ba. Sai dai ya tura wa likitan kuɗi domin a ci gaba da kula da ita yadda ya kamata.
Hibba kuwa ta kasance tare da Aunty, tana kula da ita har zuwa lokacin da aka sallame ta.
Bayan sun koma gida, Hibba tana zaune a ɗakinta sanye da wata coffee abaya, sai ga ƙawarta Aysha ta zo.
Aysha ta shiga ɗakin cikin farin ciki, ta tarar da Hibba zaune.
Hibba ta kalle ta, sannan ta ce:
“Me ya faru ne? Domin daga ganin wannan fara'ar da ke fuskarki, na san akwai wani babban abu.”
Aysha ta ƙara murmushi cikin farin ciki tace
“Ƙwarai kuwa! Babban abu ne, kuma abin farin ciki ne.”
Hibba ta gyara zamanta, tana jiran jin abin da za ta faɗa.
Aysha ta ci gaba:
“Akwai wani babban kamfani da yake aikin gine-gine. Suna neman ma'aikata, kuma kamfanin yana biyan kuɗi masu tsoka. Gaskiya, idan kika samu wannan aikin, za ki samu damar biyan bashin kawunki, sannan ki taimaka wa Aunty da halin da take ciki.”
Hibba ta yi shiru, tana tunanin halin da kawunta ya jefa su a ciki.
Kawunta, wanda shi ne mijin Aunty Talatu, ya kasance ɗan caca. Yana yawan zuwa caca, yana cin bashi, kuma yakan jawo musu matsaloli daban-daban. Duk lokacin da ya ci bashin mutane saboda cacarsa, Hibba ce take ƙoƙarin neman hanyar biyan bashin.
Matsalolin da yake jawo musu ba su da iyaka. Kullum akwai wata sabuwar matsala da za ta taso, kuma Hibba ce take fama da ita.
Ta yi ajiyar zuciya, sannan ta kalli Aysha.
“Nagode, Aysha. Amma a ina wannan kamfanin yake? Kuma ya tsarin abin yake?”
Aysha ta buɗe jakarta, ta ciro wata takarda ta miƙa mata.
“Ga takarda kamfanin. Da wannan za ki je gobe, domin za a yi interview. Amma ki tabbata kin je da wuri, saboda mai kamfanin yana da tsauri.”
Ta ɗan dakata, sannan ta ƙara da cewa:
“Ba kasafai yake yin interview da kansa ba, amma na ji cewa na gobe zai yi saboda suna da wani babban aiki da za su gudanar, kuma yana son samun ƙwararrun ma'aikata. Ki kula da wannan takardar sosai. Da ƙyar Yaya Musa ya samo mana ita.”
Hibba ta karɓi takardar, sannan ta rungume ƙawarta. Hawaye ya zubo mata a kumatu.
“Nagode sosai, Aysha.”
Aysha ta shafa bayanta tana murmushi.
“Me ya sa za ki yi kuka? Ki dai fara shiri tun yanzu. Ni kuma yanzu tafiya zan yi, akwai inda zan je. Sai mun yi waya.”
Hibba ta miƙe ta raka ta zuwa waje.
Bayan Aysha ta tafi, Hibba ta dawo ta zauna a kan kujera. Ta ɗauki takardar da Aysha ta ba ta, ta buɗe ta fara karantawa.
A saman takardar, sai ta hangi sunan kamfanin:
L.A. IMPERIAL GROUP OF COMPANIES
Ta maimaita sunan a hankali, ba tare da sanin cewa wannan kamfanin na mutumin da ta yi arangama da shi a a wannan titin bane.
Washegari da sassafe, Hibba ta shirya domin zuwa neman aikin.
Tana shirin fita daga gidan, sai ga kawunta ya dawo. Gaba ɗaya yana cikin maye, amma bai ji kunyar komai ba.
Da ya gan ta, sai ya nemi ta ba shi kuɗi.
Hibba ta kalle shi cikin takaici. Ta san halinsa, kuma ta san cewa idan ba ta ba shi kuɗin ba, zai iya tayar da wani sabon rikici.
Ta fito da wasu kuɗi ta ba shi, sannan ta bar gidan.
Ta ƙarasa bakin titi ta hau adaidaita sahu, ta nufi kamfanin da Aysha ta ba ta takardunsa.
Da ta isa, ta yi mamakin girman ginin kamfanin. Daga yadda ginin yake da tsari da kyau, ta fahimci cewa babban kamfani ne sosai.
Ta ɗaga kanta sama, ta kalli babban sunan da aka rubuta a saman ginin:
L.A. IMPERIAL GROUP OF COMPANIES
Ta yi ajiyar zuciya, sannan ta nufi ƙofar shiga.
Amma mai gadin da ke bakin ƙofar ya dakatar da ita.
“Ina form ɗinki da zai nuna cewa kin zo neman aikin nan?” ya tambaye ta.
Hibba ta tuna da takardar da Aysha ta ba ta. Da sauri ta ciro ta nuna masa.
Mai gadin ya duba takardar, sannan ya ba ta damar shiga.
Hibba ta shiga cikin ginin, ta nufi inda aka ware domin masu neman aikin su zauna. Ta tarar da wasu mata da suka zo neman aikin, suna zaune a bakin ƙofar ofishin.
Ɗaya bayan ɗaya, ana kiran su suna shiga domin yin interview.
Hibba ta zauna tana jiran lokacinta, zuciyarta cike da fargaba. Tana fatan wannan aikin zai zama hanyar da za ta taimaka mata wajen fitar da iyalinta daga cikin matsalolin da suke ciki.
A ƙarshe, sai aka kira sunanta.
Ta miƙe tsaye, ta yi ajiyar zuciya, sannan ta shiga ofishin.
Da ta shiga, sai ta ga manajar kamfanin, Alisa, a zaune. Latif kuwa yana tsaye a kusa da tagar ofishin, yana waya.
Alisa ta yi mata nuni da hannu, alamar ta zauna.
Hibba ta zauna a hankali, tana ƙoƙarin kwantar da hankalinta.
Bayan ɗan lokaci, Latif ya gama wayarsa. Ya juya daga wajen tagar, ya kalli inda Hibba take zaune.
A lokacin da idanunsa suka sauka a kanta, sai ya tsaya cak.
Hibba ma ta ɗaga kai ta gan shi.
Nan take ta miƙe tsaye cikin matuƙar mamaki.
Latif Abdurrahman!
Mutumin da ta yi arangama da shi a wancan ranar shi ne mamallakin kamfanin da ta zo neman aiki a cikinsa.
Latif ya kalle ta cikin mamaki, kamar wanda bai yarda da abin da idanunsa suke gani ba.
Ƙaddara ta sake haɗa su.