FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
🖋️ Welcome to my world of stories! ❤️📚 Ina rubuta labaran soyayya, ƙaddara, cin amana da sirrukan rayuwa waɗanda za su sa ki dariya, ki yi kuka, kuma ki yi tunani. ✨ Kowanne labari yana ɗauke da nasa saƙon. 📖 Ku kasance tare da ni a wannan tafiya!
Sample · Unexpected encounter
Chapter One unexpected encounter by Rabi'ah Muhammad Shariff Aka Ramsha Tales.Latif Abdurrahman!Sunan da idan ya shiga kunnen mutane da yawa a duniyar kasuwanci, ba abin da zai fara zuwa musu a rai face kuɗi, iko da nasara.Shi ne mamallakin L.A Imperial Group of Companies, wani katafaren kamfani da ya shahara wajen gina manyan gine-gine, karɓar manyan kwangiloli da kuma hulɗa da manyan kamfanoni na cikin gida da ƙasashen waje.Daga cikin kwangilolin da kamfaninsa ya samu akwai manyan ayyukan gine-gine a ƙasar Amurka. Duk da cewa yana da wasu manyan 'yan kasuwa da yake hulɗa da su, Latif ya kasance mutum ne da yake son komai ya tafi yadda ya tsara.A wajen kuɗi kuwa, ba ƙaramin attajiri ba ne. Yana da manyan motoci na alfarma, gidaje masu kayatarwa da kuma kadarori da suka sa sunansa ya zama abin girmamawa a duniyar kasuwanci.Amma duk da wannan nasarar da ya samu, akwai wani abu da Latif ya kasa fahimta.Soyayya!A ganinsa, kuɗi su ne ginshiƙin rayuwa. Da su ake samun iko, mutunci da jin daɗi. Don haka, bai ganin dalilin da zai sa ya ɓata lokacinsa wajen neman abin da yake ganin ba shi da amfani.Girman kansa kuwa, sai wanda ya san shi.Latif ba ya son a yi masa gardama, ba ya yarda da uzurin da bai gamsu da shi ba, kuma ba ya yawan nuna tausayinsa ga kowa. Idan mutum ya yi kuskure a wajen aikinsa, ko da kuwa ƙaramin kuskure ne, zai iya rasa aikinsa ba tare da Latif ya damu da abin da hakan zai haifar masa ba.Fuskarsa kuwa, da wuya ka ga murmushi a kanta. Kullum cikin ɗaure fuska yake, kamar wanda duniya ta yi masa laifi.Amma duk da wannan halin nasa, akwai wani abu da ya sa mata da dama suke sha'awar sa.Kyawunsa!Latif dogo ne, mai faɗin ƙirji da kyakkyawan sura. Gashinsa baƙi ne, mai yawa, kuma kullum ana gyara shi yadda zai zauna cikin tsari. Idan ya sa kayan alfarma, musamman baƙar kwat ɗinsa, yana ƙara bayyana irin kyawun da Allah ya yi masa.Kuɗinsa kuwa, ba ƙaramin ƙarin jan hankali suke yi ba.Matan da suke aiki a kamfaninsa da dama suna mafarkin samun kulawarsa. Wasu suna neman hanyar da za su kusance shi, yayin da wasu suke jiran ranar da zai nuna wa ɗayansu wata alamar soyayya.Amma abin takaici, Latif bai taɓa nuna cewa akwai macen da ta isa ta ɗauke masa hankali ba.Ko da yake mata da dama suna sha'awar sa, su kansu suna tsoronsa. Idan ya shigo ofis, kowa sai ya gyara zamansa. Wasu ma sai dai su saci kallonsa daga nesa, domin babu wanda yake son ya kama idonsa ba tare da wani dalili ba.Latif ba ya wasa da aikinsa.Kuma ba ya wasa da kuskure.Wannan shi ne mutumin da ya kasance yana ganin kuɗi a matsayin komai a rayuwa.Amma bai san cewa wata rana za a kawo shi gaban wata jarabawa da kuɗinsa ba za su iya warware masa komai ba.Wata safiya da sassafe, a cikin wani katafaren gida mai kayatarwa, Latif ya farka da niyyar shirya kansa domin wat...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.