Page 6
by @ummuaffan
...FARAR TUMFAFIYA.
©UMMU AFFAN
Ina masu buƙatar kyawawan atamfofi da lace, mayafai, shoes and bag. Tare da kyawawan kayan kitchen na 'yan gayu masu kwaliti, zaku iya tuntuɓar ASHNURR COLLECTION wacce ke Kano kwari market domin ƙarin bayani ku tuntuɓeta a lambar waya kamar haka *** Tana aika kayanta ko ina a cikin aminci.
Shin kuna da labarin AK ASHKAD COLLECTION to ku matso kusa ku ji, ita ce wacce take kawo muku kyawawan abayas na gani a faɗa na shiga ko wanne guri kai tsaye, haka tana kawo muku kitchenwares masu kyau da aminci cikin farashi mai rahusa zaku iya tuntuɓarta a 070444564938 ko *** shafinta na Instagram ashkad_collection adireshinta Daura, Katsina State tana aika kayanta ko ina cikin aminci.
Page *6*
Malamin da ya yi magana a farko ne ya matsa kusa da Andi yana girgiza kai da faɗin.
"Hajiya! Allah Ya ba ki haƙurin jure wannan babban rashin, mun san zuciyarki na ciwo kuma kuka abu ne na dabi'a, amma ki tuna cewa dukkanmu amana ce a wajen Allah, kuma idan lokacin amsa ya cika, mai ita yana karɓarta, muna roƙon Allah Ya gafarta wa 'yarki, ya sanya Aljanna ta zama makomarta, ya kuma ba ki haƙurin da zai sa ki samu lada mai yawa, ki ci gaba da yi mata addu'a, domin addu'ar uwa tana da daraja. Allah ba Ya ɗora wa rai abin da ba zai iya ɗauka ba."
"Ai ita ce ta kashe Saudatu, ita ce ta kashe ta don haka tare za a binne su. Saudatu ba za ta taɓa tafiya ta bar Barirah anan ba, ita ce ta kashe mini 'ya!!"
Ta faɗa da sauti na kuka da hayagaga, da sauri Kawu Balarabe yayo kanta yana riƙeta.
"Rakiya ki natsu nan ba a gida muke ba, don Allah ki bar ruhin Saudatu ya kwanta cikin salama."
"Bazan yarda ba, Balarabe bazan bari ran Saudatu ya tafi a banza ba, kai ka sani ni na sani Barirah ce mai wannan alhakin, shin me ya sa ba za a ɗauki mataki a kai ba? Wayyo jama'a wannan ita ce ta kashe mini yarinya, kuma yanzu haka ta lashe kurwar Usman shima yana kwance bai gane kowa!"
Ta ƙarashe maganar tana nuna Barirah wacce gabaɗaya ji tayi kamar ba a duniyar take ba, musamman yadda ta ga mutane sun fara ja da baya jin furucin Andi a kanta, nan fa ƙusƙus ya fara tashi. Iyah ce ta taho ta fincike hannun Barirah daga ruƙon da Andi tayi mata.
"Rakiya nasan baƙin cikin da kike ciki ba ƙarami ba ne, kuma rasa ɗa ko ɗiya babbar jarrabawa ce. Amma muna roƙon ki da ki yi haƙuri, ki guji yanke hukunci kan wani ba tare da hujja tabbatacciya ba, idan akwai gaskiyar cewa Barirah ta yi laifi, Allah shi ne mafifici mai adalci, kuma akwai hanyoyin shari'a da za su bincika lamarin. Amma idan babu hujja, zargi na iya cutar da wanda ake zargi kuma ya ƙara miki nauyin zunubi, Rakiya ki bar al'amarin nan a hannun Allah, ki ci gaba da yi wa Saudatu addu'a, domin abin da ya fi amfanarta ke nan. Allah ya ba ki haƙuri, ya nuna miki gaskiya, ya kuma ba ki natsuwa."
Ai Andi ganin maganar da Iyah tayi ya saka mutane fara nuna maganarta haka yake, ai sai ta kurma uban ihu tabi su a guje bayan ta kwace hannunta daga riƙon da Kawu Balarabe ya yi mata.
"Wallahi ƙarya ne, ba za a binne Saudatu ita kaɗai ba sai an haɗasu da Barirah!"
Ganin yadda ta doso su da gudu Barirah ta kwace hannunta daga Iyah ta ce ƙafa mai naci ban baki ba, don ba ta manta dukan jiya ba, da sauri Yaya Aliyu yabi bayanta, Kawu Balarabe kuma ya shigar da Andi gida har ɗakinta ya kulleta sannan ya fito suka wuce binne Saudatu a maƙabarta.
Barirah kuwa gudu take har ta hau babban titin ba tare da tasan inda ƙafafuwanta ke takawa ba, sai dai taji abu ya bigeta haka ta faɗa gefen titi ta bugu da ƙaton dutse, duk da taji a azaba amma ƙoƙarin gudu take don kar Yaya Aliyu ya kamata.
DK.
Ta ƙara ƙanƙame DK ganin yaƙi ba ta damar guduwa ta ce,
"Ka taimaka mini, don Allah kar ka bari ya kamani."
Kallon fuskarta yake ga jini yana zuba daga goshinta har ya ɓata gefen fuskarta, amma ya lura tafi buƙatar ta gudu fiye da ciwon da ke jikinta. Ƙarasowar Yaya Aliyu ne ya saka shi kallon shi, kama hannunta ya yi ya fuzga da ƙarfi ya fara tafiya da ita, ta juyo inda Sadauki ke tsaye kamar an dasa shi tana miƙa masa ɗayan hannunta.
"Ka taimake ni, ka taimake ni!"
Kalmar da ta maimaita kenan sau biyu ta sulale idanuwanta na rufewa, da sauri Yaya Aliyu ya tare ta, ta faɗa jikinsa. Sadauki ya ƙarasa wurin da sauri yana kallon Aliyu.
"Amma asibiti ya kamata ka kai ta, ta zubda jini sosai wani abu zai iya samunta."
"Ok!"
Ita ce kalmar da Aliyu ya faɗa ya fara tsaida abin hawa, ya ɗauke ta suka shiga mashin mai ƙafa uku, suka bar Sadauki tsaye yana bin napep ɗin da kallo, har sai da ya daina hangosu ya sauke kanshi ƙasa, haka kawai yake jin kamar bai kyauta ba, kalmar 'Ka taimake ni' tana ta dawowa masarrafar sautinsa. 'Anya kuwa banyi ganganci ba da nabar mutumin nan ya tafi da yarinyar nan? Ko ma cutar da ita zai yi shi ya sa take cewa ya taimake ta?' Haka ya dinga saƙawa a ransa kafin cikin sauri ya tada babur ɗinsa, bai sami wata matsala mai yawa ba sai gefen robar hagu da ta fita, duk ta ɓalle ma, hakan yasa ya fara ƙoƙarin tayar da shi, inda suka nufa yabi da sauri sai dai ko da ya ƙaraso bai gansu ba, duk napep ɗin da ya leƙa baya ganinsu dole ya haƙura da nemansu ya nufi hanyar gida, daidai inda za a sha kwanar gidansu Sadiya ya hango wata ƙatuwar mota, abin da ya yi mugun ba shi mamaki ganin Sadiya ta fito daga kwanarsu ta nufi motar.
Nesa da su kaɗan ya sami guri ya tsaya yadda ba zasu hangoshi ba, ilai kuwa motar ta nufa ta shige ciki kuma, sosai mamakinsa ya ƙaru mene ne gaminta da mai motar? Duk da motar glass ɗin ya maka shamaki da ganin mamallakinta saboda Tinted glass ne sai dai na ciki ya kalleka amma yasan wanda zai mallaki mota mai tsada kamar waccen Toyota (LC300) dole babban mutum ne, kuma idan bai manta ba kamar motar tana ɗaya daga cikin irin motocin Daddyn Mansoor lallai mamallakin ta babban mutum ne, don Mansoor ya taɓa faɗa masa kuɗin motar ba ƙarama ba ce.
Yana nan tsaye kusan minti talatin ya ga Sadiya ta fito motar hannunta kamar da kuɗi, kuma mamallakin motar ma ya fito ya buɗe mata bayan motar, ya ga ta saka kai ciki sai ga hannunta da wata babbar farar leda mai rubutu a tsakiya, da alama shoping ne ya yi mata, sosai ya sandare ganin waye yazo gurin Sadiya.
"Kai a haka dai kamar na ƙwarai ashe mutum ne da rigar dabba!"
Sai kuma wani ɓaein na zuciyarsa ya ba shi 'Ko dai sonta da aure yake yi kar ya yi saurin yanke masa hukunci' Yayin da wani ɓarin ya ce 'Masu kuɗi ne ke yarda su auri 'ya'yan talakawa! Musamman ma irin Sadiya 'yar talla babu karatu sai wuni a titi ko a talakawan ma ba kowa ba, Amma duk da haka kar kayi saurin yanke masa hukunci, Alhaji Bashar ne fa mahaifin amininka Mansoor!' Ya sauke numfashi yana girgiza kai, yana ɗagowa ya ga har ya koma mota yaja ya tafi. Sadiya na niyyar gangarawa lungunsu da sauri ya fito daga maɓoyarsa yana kwala mata kira.
"Sadiya! Sadiya!"
Ta juyo da sauri ta zubawa mai kiran nata ido har ya ƙaraso gabanta.
Sadiya.
Tana fita daga ɗakin ta doshi ɗakin maƙociyarsu Mama Baraka, tana da kyirki kuma suna shiri sosai da ita, yaranta huɗu amma ƙananu ne don babban shekarunsa takwas yanzu, zaunawa tayi saman kujerarta da yara sun gama lalata ta duk ta ɓurma tana sauke numfashi.
"Sadiya an dawo suya kenan?"
"Na dawo Mama Baraka ina wayata take?"
Da yake tana da waya da ta saya da kuɗin da Alhaji Bashar ke ba ta, don shima yana kiranta lokaci-zuwa-lokaci ba ta fita da wayar ne sai take ba ta ajiya idan ta dawo ta amsa.
"Kin yi sallah kuwa? In ce baki daɗe da shugowa gidan ba, ga Magrib har an idar."
Ta ɗan sosa kai, matar nan ita ce kawai ke mata tuni kan sallah, Hauwa kullum ta kuɗinta take, ta miƙe jiki a sanyaye ta ɗauki butar mama Balaka ta fita zuwa banɗakin gidan tana ta saƙe-saƙe, sallar asuba kawai take yi ita ma sai wajen takwas ko tara idan ta tashi barci, azahar da la'asar daman tana gurin suya ba tashi yinsu take ba,, sai idan ta dawo tayi magriba idan mama Baraka ta tuna mata. Bayin ma kaca-kaca sai ɗoyi yake ga ruwan fitsari nan kwance don kowa ya daina gyaran bayin, ada kullum da wacce za tayi amma kyashi da baƙin cikin nayi da kyau wacce ba tayi da kyau ba yasa suka bar bayin ya lalace ya fita hayyacinsa, kowa idan yaje buƙatarsa ne zai gyara inda zai yi ya yi ya fice, wannan ɗabi'a ba ta da kyau sam don kansu suke jawowa cuta da 'ya'yansu.
Ta samu gefe ta kama ruwa ta fito tana watsar da miyau, bayan ta ɗaura alwala ɗakin mama Baraka ta koma tayi sallah sannan ta amshi wayarta, babu wanda ya kirata, daman lambar ƙawayenta ne da Alhaji Bashar sai wasu daga masu sayen dankalinta. Data ta kunna ta hau Tiktok tana kallo don daman kallon kawai take da wayar, idan ta gaji da Tiktok ta koma ta kalli finafinan hausa ta take zuwa a tura mata, nan ta ɓungure ta yaran Mama Baraka suna kallo har sai da Babansu ya dawo ta fice babu batun sallar isha'i haka ta koma ɗakinsu suka dasa kallon da ƙannanta har ma da Hauwa. Bagiyo daman ba kullum ma yake kwana gidan ba yanzu, sai ranar da ba shi da gurin zuwa.
Da safe Alhaji Bashar ya kira ta a waya cewa yana nan zuwa anjima, ta amsa ma shi da to, sannan ta sanar da Hauwa, nan fa ta fara murna.
"Gaskiya Sadiya ke ɗin mai goshin arziƙi ce, ai nasan ki ka dunga tatsar mana Alhajin nan kayan ɗakinki ma kaf ta hannunsa zasu fito tunda yana da sakin hannu, don Allah ki ba shi sau da ƙafa kina biyayya kar ya gudu ba mu tara uban komi ba."
Kallon Hauwa kawai take, wai uwar da ta haife ka ke sanar da kai kabi wani sau da ƙafa shi ba mijinka ba, don kawai ana tatsar abin arziƙi a jikinsa.
Ba ta amsa mata ba ta amshi kuɗin Dankalin da zata sayo kasuwa sai mai ta fice a gidan, Napep guda taho da kayan dankali sai Mai galan guda babba da ta sayo, sai 'yan kayan miya don tana so kafin ta fita su dafa taliya, don har kifi ɗanye ta sayo, ai kuwa tana dawowa Hauwa ta fara firar dankali ita kuma ta kunna gawayi ta dafa taliyar leda biyu duka 'yan ɗakinsu suka ci har ta zubawa yaran Mama Baraka ta miƙa musu, shaf-shaf tayi wanka saboda Alhaji Bashar ya kirata yana bakin titin saman layinsu, tana shiryawa ta fito gyalenta a hannu.
"Hauwa ya ƙaraso ina zuwa."
"Sai kin dawo kashe kala, farar mace alkyabbar mata, fara mai farar aniya, 'Yar gudaliyar Hauwa."
"Ke dai Hauwa baki da kara, wai 'yar farin ce ake wasa wa haka ko ta ido babu! To ayi dai mugani idan tusa zata hura wuta."
Da sauri ta fice tana jin Hauwa tana ba Ramatu amsar baƙar maganar da ta yaɓa mata kan ta wasa Sadiya, ita dai ta fice don tasan faɗan matan gidan baya ƙarewa ƙiris suke jira su fara yaɓa maganganu.
Gefen titi ta hangi motarsa don yanzu ta fara gane motocinsa don yafi zuwa ma da wannan ɗin, tana ƙarasawa ya buɗe mata mota ta shiga.
"Ina wuni Alhaji!"
"Haba Sadiya tasha faɗa miki ba na son Alhajin nan da ki ke ce mini, ina ma laifin a sama mini suna irin na masoya."
Tayi ƙasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta da yasha jan kalle iyakar yatsun, kafin ta kwanta jiya bayan sun gama kallo ta ɗaura jan lallen a hannunta kuma ya yi ja sosai ya ƙarawa farar fatarta kyau.
"Ah ƙunshi aka yi shine ba a faɗa mini ba in kawo kuɗin lallen?"
Ya ƙarashe maganar tare da kamo hannunta yana shafa saitin inda tayi lallen.
"Da yake lallen babu yawa iyakar yatsu ne shi ya sa!"
"Ai ko da a yatsu ne yaci a baki kuɗin kunshi, kin ga yadda ya yi kyau kuwa?"
"Na gode!"
Ta faɗa tana niyyar jan hannun nata sai ya ƙara kamowa ya ce,
"Sadiya ina sonki da gaske ne babu wasa a cikin lamarina, ki ba ni dama kaɗan za ki ga yadda zan mayar da ke sarauniya, hatta tallar nan da kin ba ni dama da tuni an wuce gurin."
"Alhaji ni fa ba wai ba na sonka ba ne, dole in soka tunda iyayena suna ƙaunarka."
Ya gyaɗa kai yana murmushi a ransa yana faɗin 'Dole ai su soni tunda ina musu ɓarin kuɗi. A fili kuma ya nuna mata ledar da ke kujerar baya.
"Kin ga har tsayawa nayi nayo miki sayayya ga abubuwa nan masu sanyi da su kayan fulawa nasan wajen suyar nan kina shan wuta gara kina yi kina ɗan sha ko?"
Ya ƙarashe maganar yana mata wani kallon yaudara, "Na gode Alhaji!"
"Babu komi ai idan mutum na ƙaunarka babu abin da ba zai iya maka ba, abin da ya sa nazo ina so na sanar da ke ne zanyi wata tafiya ta sati ɗaya ce kachal, saboda haka ba zaki ganni ba sai na dawo, kuma ba lallai na kira ki a waya ba saboda tare da madam zamu je amma idan na samu sarari zaki jini kafin na dawo a wayar, tsarabar me ki ke so na dawo miki da ita?"
"Allah ya kaiku lafiya ya kuma dawo da ku lafiya, sannan duk abin da ka kawo mini a matsayin tsaraba ina so kar kaji komi."
Hannunta ya yiwa kiss saitin lallenta sannan ya ba ta kuɗi masu yawa ya ce wanda zata kashe ne da kuma na lallen da tayi. Godiya tayi masa ya fito ya buɗe mata ta ɗauki ledar kayan da ya kawo mata suka yi sallama ya koma mota ya tafi, sannan ta nufi hanyar lungunsu zata gangara taji ana kwara kiran sunanta.
DK.
Ya ƙaraso kusa da Sadiya yana kallonta sosai, ita kuwa ba ƙaramin shock ta shiga ba, Sadauki ne ke kiranta haka? Mutumin da duk idan ta gan shi zata gaishe shi ba taɓa amsawa ba wai yau shine yake kiranta haka da sauti, farin ciki ya mamaye zuciyarta, sai dai taji faɗuwar gaba da tsoron ko wani abin zai ce mata akan kar ta ƙara aikawa su Inna da dankali, ko wani laifin tayi masa, hakan ya sa tsoro ya shigeta nan take jikinta kuma ya fara rawa.
"Na..na...am!"
Ta amsa cikin rawar murya, ya kalli kuɗin da ke hannunta da sauri ta sake su, suka faɗi ƙasa, shi da kansa ya duƙa ya ɗauki kuɗin ya fara juya su a hannunsa bandir ne har biyu da yake zaton dubu ɗari biyu ne.
"Mene ne haɗinki da Alhaji Bashar da har ya ɗauki kuɗi masu yawa haka ya baki? Ke har kin iya riƙe kuɗi kamar waɗannan?"
Jin tambayar da ya yi mata sai ta natsu ta gyara tsayuwarta tare da kallon kuɗin har lokacin suna hannunsa. Ta ɗanyi murmushi zuciyarta na raya mata Sadauki na sonta, girman kai ne yasa bai kulata, tun da ga shi don ya ganta da Alhaji Bashar yana nuna kishinsa, sai taji farin cikin da ta fara ji na kiranta da ya yi tun farko ya dawo sabo.
"Goman waɗannan idan na buƙata zai iya ba ni, kasan shi ne?"
Kallonta yake sosai ita ma ba ta daina kallonsa ba tana sakar masa wani murmushi.
"Amma akan wanne dalili kenan? Ko kanki ki ka sayar masa ne? Don ni nasan ko ɗan cikinsa da dabara yake amsar manyan kuɗaɗe a wurinsa ballantana wata ke!"
Yadda ya ƙarashe furucinsa na ƙarshe ya ɗan taɓa ta, amma sai ta wayince.
"Ka sani ko yafi sona ne akan ɗan nasa? Kasan an ce idan mutum na ƙaunar babu abin da bai iya mallaka maka, shi kuwa ɗa ai ɗansa ne, ba lallai ya yi masa abin da ni zai iya yi mini ba."
"Sadiya!"
Ya kira sunanta da sauti.
"Suna na kenan faɗi ka ƙara, Sadauki ina ƙaunarka sosai nasan ka sani, idan kuɗin da ka riƙe kana so ne ka ɗauka na bar maka, kai ni idan zaka ƙaunace ni ka aure ni wallahi zan iya saka Alhaji Bashar a tarkona, na dunga amsar kuɗinsa ina baka, ka samu jari ka fara sana'a sai ka aure ni!"
Kallonta yake sosai, sannan ya kalli kuɗin hannunsa, nan take abin da yake nema ya faɗo masa, bai san lokacin da ya ƙarasa gabanta sosai ba har numfashinsa na sauka fuskarta, saboda ya fita tsayi sosai, Sadiya irin dirarrun matan nan ce masu diri a cure, ba ta da tsayi kam kuma tana da ƙiba sosai, sai dai fa tana da kyawun fuska sosai haka fara ce.
Kalaman Sadiya tuni suka tuna masa da fafutukar da yake, cikin sauri ya ce,
"Kina ganin zaki iya amsar mini milliyan biyar a hannunsa?"
Yadda take jin hucin numfashinsa yasa ta matsa kaɗan, ta nuna masa kwalbatin da ke gurin hanyar da za a gangara gidansu ta ce,
"Ka ga Sadauki zo mu zauna a kwalbatin can."
Abin mamaki sai ga Sadauki da kama hannun Sadiya suka ƙarasa gurin, zaunawa tayi ta nuna masa gefenta.
"Ka zauna!"
Ya zauna har lokacin kuɗin na hannunsa.
"Maganar gaskiya ban taɓa tambayar Alhaji kuɗi ba, duk wannan shi ke ba ni ba tare da na tambaye shi, sannan kuɗin da kayi magana masu yawa ne, taya zan ce ya bani, idan ya ce me zanyi da su fa?"
Sadauki ya ɗanyi shuru na wani lokaci, kafin yaja iska a baki ya fesar da hucin.
"Ki ce masa yayanki ne zai yi karatu, kuma ba shi da kuɗin da zai nemi komi, idan ki ka mini haka kin biyani Sadiya!"
"Idan na maka haka zaka aure ni?"
Kallonta ya yi, Sadiya ba ta da munin da za a ce za a ƙi ta, daga rashin tsawo sai jiki shima kuma mai kyau ne, sai dai Sadauki bai taɓa jin sonta ko kaɗan a zuciyarsa ba, amma fa dole yana buƙatar kuɗin nan.
"Kayi shuru?"
Zai yi magana ta ɗaga masa hannu.
"Alhaji ya ce mini zai yi tafiya gobe da zata ɗauke shi sati guda, daga yau har zuwa kwana takwas Alhaji ya dawo na baka dama kaje kayi tunani akan aure na domin amincewar ka kaɗaice za ta saka na samar maka abin da ka ke buƙata a gurin shi, sannan kuɗin hannunka kaje da shi kawai na baka!"
Tana ƙarashe maganarta ta miƙe tare da buɗe ledar ta ɗauki kwalin lemun Exotic babba ta ajiye masa ta gangara, ya dunga bin bayanta da kallo har ta ɓacewa ganinsa, kafin jiki a sanyaye ya adana kuɗin a duka aljihun wandonsa ya ɗauki Exotic ɗin ya koma gurin babur ɗinsa ya hau zuwa gida.........
***
Kuna da labarin UmmuAffan GHT Supplement, tana sayar da Supplement na kamfanin ght masu kyau da inganci tana garin Kaduna tana aika kayanta duk inda kuke a faɗin ƙasar nan dama wajen ƙasar nan, kai tsaye kuyi mata magana ta lambar waya kamar haka *** sayen na gari mai da kuɗi gida, sai kunzo.