Page 9
by @ummuaffan
...FARAR TUMFAFIYA.
©UMMU AFFAN
Page *9*
"Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un, Allahumma ajurni fi musibati, wakhluf li khayran minha!"
Iyah ta faɗa tantan karfinta tana girgiza Barirah wacce ko motsi ba tayi.
"Ka gani ko? Na ce Balarabe ka gani ko? Yanzu idan ta mutu ai kun huta ita ma ta huta, wannan wacce irin rayuwa ce haka, tur! Tur da wannan baƙar zuciya!"
Ta fara ƙoƙarin ɗaga Barirah amma ta kasa, Kawu Balarabe da haka kawai yaji jikinsa ya ɗauki rawa ne ya taimaka mata suka kama ta zuwa falon Iyah ɗin, haka ta ɗauko ruwa bayan sun shimfiɗeta tsakar falon ta zuba mata amma ko alamar zata motsa babu, daga Iyah har Kawun suka yi wani curko-curko a tsaye suna kallonta, kowa da tunanin da yake, don idan ban da faɗuwa babu abin da gaban Kawun yake.
'Yanzu idan mutuwa tayi ma fa tsaf su Kawu Bature za suce ko shine ya kasheta, saboda a yadda yaje musu jiyan akan batun Barirah na faɗin zai dawo musu da ita ko ya saketa tabi duniya, don Kawu Habule ne ma ya kawo shawarar aje ayi shela ko za a samu wanda zai ce yana sonta sai su aurar da ita hakan zai fi kawai, ranar Ubale yazo wajen wani abokinsa anan Kalambaina ɗin, don shi yana ƙauyen ƘUSA ne yamma da Kalambaina ɗin (Babu ƙauye mai suna Ƙusa a yankin na ƙirƙiri sunan ne kawai saboda akwai batutuwan da zanyi a ciki don haka babu Ƙusa da mutanen cikinsa duka ƙirƙira ce.) shine fa yaji ana wannan shelar, duk da a ɓoye yazo kawo mishi wani saƙo don sun hana 'yan Ƙusa shiga musu yanki sakamakon wani babban al'amarin da 'yan yankin ke da shi da ba sasu suma abin ya shafe su.
Jin yadda ake ta tallar mai auren Barirah a faranti kamar gyaɗa, kuma babu wanda ya tanka ne ya sa shi tambayar Sallau abokinsa ko me ya sa babu wanda ya amsa. Cikin ƙasa da murya yake ce masa ai yarinyar mahaifinta ɗan Ƙusa ne, kuma yasan dai yadda suka kware a tsafi da maita, shiyasa babu mai so hatta su dangin nata don mahaifiyarta anan take yazo ya tsafaceta ya aure ta, yanzu ma ana tunanin ya cinye namanta don tunda suka bar shiyar har yau ba a ƙara ganin ƙeyar kowa ba, Ubale ya jinjina lamarin yaji kuma ai tasu ce don haka shi baiga abin gudu a gurinta ba, nan take kuwa ya ɗagawa su Kawu Habule hannu cewa shi yana sonta zai aureta, nan take suka amince duk da sai da Kawu Balarabe ya tambaye shi shima anan yake? Nan take suka haɗa kai da Sallau ya ce ai shi ɗan'uwansa ne, yana zuwa cirani ne shiyasa ba a sanshi sosai ba, babu wani bincike suka amince sannan Kawun ya ce yazo suje can Sokoton ya ga Barirah idan har tayi masa to gobe zai kawota nan a ɗaura musu aure, ai kuwa Ubale ya saje da 'yan gari yabi bayan Kawu Balarabe kuma abin mamaki babu wanda ya musa cewa ba ɗan gari ba ne duk da ba su sanshi ba.
Wannan abin da ya farun ne kawai ke dawowa Kawu Balarabe yasan Barirah ta mutu a yau tabbas za a ce silarsa ne, fatansa ace ba mutuwar tayi ba, ace ta jinkirta zuwa gobe idan an kaita gidan Ubalen sai ta mutu a can ɗin zai fi.
Iyah kuwa sosai ta shiga ruɗu da kaɗuwa ta kuma furgice da halin da ta ga Barirah ta rasa tunanin da za tayi, kafin tayi furgigit ta kalli Kawu ta ce.
"Asibiti, asibiti ya kamata a kaita Balarabe."
Sai shima ya furgita don shurun da sukayi ne duk yasa ka faɗawa duniyar tunani, ai kuwa ya saka hannu ya ɗauketa, Iyah na biye da shi har mota suka wuce Asibitin Murtala, sun amsheta cikin gaggawa aka fara bata taimako, tare da addu'ar Allah ya saka ta dawo hayyacinta don suyi nasaarar dawo da numfashinta cikin hukuncin Allah, Kawu kasa tafiya ya yi sai da yaje ya biya komi sannan ya dawo gurin Iyah ya zauna yana sauke numfashi kamar wanda yaci tseran gudu, sosai ta lura da Kawun yana cikin damuwa duk da tana tunanin wacce take ciki tafi tashi, ga likitan da ya bar kanta yana ta masifa, saboda ba ayi gaggawar kawo ta asibiti ba a cewarsa ta zubda jini kuma an saka mata wani abu a goshin maimakon a kawota asibiti.
"Me yasa ku kayi wannan sakacin? Wa ya yanke hukuncin cewa a bar mutum da irin wannan mummunan rauni a goshinsa ba tare da an kawo shi asibiti ba? Kun san abin da kuka yi kuwa? Raunin da yake zubar da jini sosai ba abin wasa ba ne, goshi yana da jijiyoyi masu yawa, kuma zubar jini mai yawa na iya jawo ƙarancin jini ko ma sanya rayuwar mutum cikin haɗari, maimakon a kawo shi asibiti domin a tsaftace raunin, a duba ko ƙashin kansa ya samu matsala, ko akwai buƙatar ɗinki, sai aka manna masa maganin gargajiya kawai. Shin kun tabbatar maganin da aka manna yana da tsabta? Idan ba haka ba, zai iya jawo mummunar ƙwayar cuta ta shiga cikin raunin, Kuma yarinyar nan tana fama da zazzaɓin cizon sauro, lokacin da mutum yake da irin waɗannan cututtukan, jinkirta samun kulawar asibiti na iya ƙara tsananta yanayinsa, dole ne a tantance shi sosai, a duba yanayin rauninsa, a dakatar da zubar jini idan har yana ci gaba, sannan a ba shi maganin da ya dace gwargwadon sakamakon bincike. Ku sani, maganin gargajiya ba zai maye gurbin binciken likita ba.
Idan mutum ya sami mummunan rauni, abin da ya kamata ku fara yi shi ne ku kawo mara lafiyar asibiti cikin gaggawa, da an yi hakan tun farko, da an rage haɗarin kamuwa da ƙwayoyin cuta, ci gaba da zubar jini da sauran matsalolin da ka iya tasowa, don haka a gaba, idan irin wannan abu ya sake faruwa, kada ku ɓata lokaci da magungunan da ba a tabbatar da ingancinsu ba, rayuwar mutum ta fi komai muhimmanci, ku fara kawo shi asibiti, sannan idan akwai wani ƙarin maganin da ya dace, za a yi shi bisa ƙa'idar lafiya."
Ta sauke numfashi mai nauyin tana duban Kawu Balarabe.
"Ka ga dai wannan shine kana naka shi kuma Allah yana nashi, shin har yanzu kana kan bakanka akan Barirah ko ka sauka?"
Kafin ya yi magana wayar da ke gaban aljihunsa ta fara ƙara, ganin Andi ce ya sauke numfashi ya amsa kiran.
"Wayyo na bani na shiga uku Faruk yana jijjiga, duk inda ka ke ka dawo yanzu mu tafi asibiti, Aliyu ma baya gida na shiga uku zata kashe mana Faruk shima. Ga Usman jikinsa ya matsa yau na shiga uku Barirah zata cinye mana yara, daman Runduna ya faɗa Runduna ya faɗa mana haka zata faru amma kaƙi yarda, na shiga ukuna na lalace ni Rakiya!!"
Yadda take maganar da ƙarfi kuma ya saka ta amsa kuwa har Iyah naji komi, daman shi muddin zaiyi waya haka yake sakata acewarsa yafi jin magana sosai.
Jiki na rawa yayi hanyar fita da waya a kunne ba tare da ya ƙara bi ko takan Iyah wacce ta bishi da ido ba, tanayi masa wani kallo wanda ba zaka taɓa gane kallon mene ne ba, sai ita kaɗai, ta kauda idanuwanta a kanshi ta doshi hanyar shiga ɗakin da aka kwantar da Barirah, kwance take an saka mata abin ƙara taimakon fitar numfashinta fuskarta tayi fayau duk da tana da duhu a launin fata, sai tayi wani hasken ciwo ga ramarta da ta bayyana ƙara a fuskarta.
Gefen gadon ta ƙarasa inda kujerar da aka tanada domin majinyaci taje ta zauna har lokacin idanuwanta suna kan Barirah, wacce lokaci guda taja wani numfashi ta fara wani irin motsi, har zufa ta fara tsatstsago mata a saman goshi tana wata irin miƙa da ta saka Iyah miƙewa a sukwane ta fita kiran likitan, ko da suka dawo sai suka iske babu wannan motsin kuma babu zufar a goshinta. Iyah tana jan salati take faɗin.
"Wallahi yanzu fa take miƙa da rawar jiki, shi ya sa na fita da sauri na faɗa muku."
Likitan bai ce komi ba ya ƙarasa gaban gadon nata, sai yaga wani ciwo a gefen muyanta wanda lokacin da ya duba ta da farko babu shi, kamar yakushinta akayi kuma babban yakushi ma irin na mugunta.
"Amma wannan raunin da babu shi a jikinta."
Iyah ta ƙaraso tana tambayar wanne ciwon kuma? Nan kuwa ita ma idanuwanta ya nuna mata.
"Ya Allah! To nima dai yadda ka kagani haka na gani."
Ya gyara tsayuwarsa tare da rubutu a fayil ɗinta, sannan ya ajiye ya fara ƙoƙarin wanke mata ciwon.
Iyah kuwa tana gefe tana tunanin anya babu shafar iskokai a lamarin yarinyar nan, abin da ta ɗan fahimta kenan, kuma za ta ci gaba da duba lamarinta idan har ta tabbatar zata nemar mata taimakon na iskokai ɗin don ba za a barta haka tana ta wahala ba.
Kawu Balarabe
Bayan fitarsa daga asibitin a furgice jikinsa idan ban da rawa babu abinda yake yi, Allah ne kawai ya kaishi gida lafiya, amma sam tuƙin da ya yi ba bisa ƙa'ida ba ne sannan baya cikin natsuwarsa, mutanen da ya hango suna shiga cikin gidan ne abin ya ƙara ba shi tsoro, yana parking ya fita a gigice suka yi kiciɓis da Aliyu rungume da Faruk cikin tashin hankali ya doso ƙofar wajen.
Key da ke hannunsa na motar ya miƙa masa kawai da nufin ya kai shi asibitin, don yadda yake jin cikinsa na murɗawa ba zai iya zuwa ba. Aliyun ya fice da sauri Kawu ya ƙarasa ciki yana kallon yadda Andi ke kuka mutane na riƙeta, shima ya ƙarasa ya zauna yana dafe kansa da ke barazanar tarwatsewa. Tsaiba ta haifa musu masifa ta tafi ta bar su da ita, amma ya saka a ransa tabbas daga yau Barirah ta gama kwanan gidansa, dole daga asibiti sai Kalanbaina za ta wuce.
Andi ce ta dawo kusa da shi tana faɗi.
"Sai ta kashe mana 'ya'ya duka zata bar mu, na shiga uku Balarabe, ta kassara mini Usman ya dawo bai da wani amfani, ta kashe Saudatu ko uku ba a yi ba zata ɗauki ƙaninta Faruk, ya Allah ka kawo mini agajin gaggawa."
Ta ƙarafashewa da wani irin kuka mai gurnani, duk dauriya irin ta Kawu haka ya sakko ƙasa gabanta ya rungumeta, shima ya saki wani irin kuka don mutum ne mai matuƙar son 'ya'yansu, gabaɗaya matan gurin da maƙotansu ne ihun da Andi ke yi ya shugo da su suka dunga ba su haƙuri tabbas a lokacin duk wanda ya kalli Kawu da Andi sai ya tausaya musu.
Ihun Usman da suka ji ne ya ɗagasu daga gurin har suna rige-rigen shiga ɗakin da yake, suka tarar kamar ana murɗe masa wuya ne, kan shi suka yi suna kurma ihu musamman Andi, a cikin maƙotansu wata Malamar islamiyya ce ta ƙaraso gurin ta kama hannuwansa duka biyun ta fara tofa masa addu'a, nan yaci gaba da wannan juyin sai ta fara karatun ƙur'ani a kansa, gurnanin ya ƙaru sosai yana fitar da wani irin ihu wanda sam ba zaka taɓa cewa muryar Usman ba ce, sai ga Kawu da Andi sunyi gefe cikin tsoro, malamar nan ta ƙara ɗaga sauti tana ƙira'a, ai kuwa suka ga wani duhu mai kamar inuwa ya fita daga jikin Usman ya fice ta tagar ɗakin, nan take Usman jikinsa ya yi sanyi babu gurnanin nan sai wata zufa da ta shiga yankowa a duka jiki da fuskarsa, duka jikinsa sai ya zamo kamar ba lakka tsabar sanyi, kuma idanuwansa a rufe suke don nan take wani barci mai nauyi ya yi gaba da shi.
Lokaci guda suka saki ajiyar zuciya, malama ta kalli Andi ta ce, "Idan akwai waya ko mp wacce ke ɗauke da sururin Qur'ani ku kawo a kunna masa."
Sai duka suka yi tsurko-tsurko don babu mai karatun Qur'ani a wayarsa dama Aliyu na nan ne ƙilan da baza a rasa ba don shi ma'abocin sauraren shi ne, malamar ganin alamar babu sai ta kunna masa a watarta ta ajiye kusa da fillon da ya yi matashin kai ta ce duka su fita.
Kallonsu tayi ta ce,
"Maganar gaskiya sai kun tashi tsaye, akwai sihiri mai girma jikin ɗanku, anyi masa turen miyagun aljanu ne na ga alamar haka sosai."
Kawu ya ɗauki sakati yayin da Andi ta fashe da kuka.
"Wallahi ita ce, ka dai ji ko? Na shiga uku Tsaiba Runduna ko zo ku ɗauki masifarku don gado gaskiya ne yau na ƙara yarda, idan ba kiyi maita da tsafi ba ai ke ba jinin Rundana ba ce."
"Don Allah ki daina surutun nan yafi ma kiyi tunanin mafitar da zaku samawa ɗanku, akwai babban Shekh, shugaban makarantar da nake koyarwa, zan ba ku lambarsa ku tuntuɓe sa don yana amsar marasa lafiya masu turen iskokai idan kunbi hanyar da ta dace Usman zai sami sauƙi."
"Dole inyi kuka malama, baki san irin ciwon da ke cikin zuciyata ba, ni kaɗai nasan abin da nake ji, ƙilan sai dai kuji zuciyata ta buga kuma."
Kawu ya tallabeta tare da zaunar da ita kan kujera ya dubi malama.
"Malama ki ba ni laman Shehin, ni da Aliyu zamu je mu kai masa Usman in sha Allahu."
Babu musu ta koma ɗakin Usman ta ɗauko wayarta tazo ta ba shi lambar ya adana a rashi wayar sannan suka yi musu sallama suka fice a gidan, sosai kuma suke jin tausayin halin da maƙotan nasu suke ciki.
Bayan Kawu ya zauna kusa da Andi ne ya kira lambar Aliyu yake tambayarsa jikin Faruk ɗin, ya amsa masa da har lokacin dai likitocin suna kansa bai san komi ba sai sun fito kuma, jin abin da ya faɗa fa Andi ta ƙara rushewa da kuka tana faɗin shi ke nan Faruk ɗin shima mutuwa zai yi, haka Kawu ya dinga rarrashinta da kyar tayu shuru ta dunga ajiyar zuciya a kai a kai, kusan awa ɗaya ganin ta ɗan natsu ya dube ta.
"Bari naje nabi Aliyun asibiti kar a bar shi, shi ɗaya ke ki zauna gida ki kula da Usman."
Ta jinjina kai kurum da alamar ma maganar wahala take yi mata, tabbas ita kaɗai tasan zafi da raɗaɗin da zuciyarta ke mata, ya girgiza kai cikin damuwa.
"Don Allah Rakiya ki saka natsuwa a cikin zuciyarki, ki tashi kiyi alwala kiyi sallah ki roƙawa Faruk lafiya, nima masallaci zan fara shiga kafin na wuce."
Ta gyaɗa kai a hankali, ya taimaka mata ta miƙe, zuwa toilet shi kuma ya fice daga gidan ransa ba daɗi, bayan ya yi sallah a masallacin da ke unguwarsu, ya kira Aliyu a waya ya faɗa masa sunan asibitin da ya kai Faruk, bayan ya sauke wayar ya ƙarasa bakin titi ya samu mai mashin ya kaisa har bakin gate ɗin asibitin, daman motarsa ɗaya ce jal, kuma da ita Aliyun ya kai Faruk, bayan ya biyashi ya nufi ƙofar gate ɗin, haka kawai yake jin shi a sanyaye da haka ya ƙarasa bakin ƙofar shiga cikin, yana ƙoƙarin kiran lambar Aliyun ya hangoshi dafe da bango ya riƙe kansa da alamar kuka ma yake yi.
Da sassarfa ya ƙarasa gabansa tare da dafa bayansa, yana juyowa ganin Kawu sai ya faɗa jikinsa kukansa ya ƙara sauti yana faɗin.
"Faruk ma ya rasu Kawu, yanzu likitan yake sanar da ni mutuwarsa Faruk ma yabi bayan Saudatu."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un ya sami bakinsa da furtawa, Faruk ya mutu so shock yaji batun kwarai da gaske, ya tuna yadda ya bar Andi a gida, ya zata ji idan ta kuma jin anyi wata mutuwar, wanne hali za ta shiga matuƙar taji Faruk ma ya mutu, yadda zai sanar mata mutuwar ne ya saka shi damuwa ainun, yasan mutuwa dole ce akan kowa, amma ya sani Rakiya ba zata iya ɗauka ba, ko ta ɗauka to abin ba zai zo mata da sauƙi ba, kwana ɗaya da rasa Saudatu Faruk yabi bayanta "Hasbinallahu wa ni'imal wakil!"
Haka suka cike komi, sannan suka tafi da gawar Faruk zuwa gida cike da taraddadin halin da Andi za ta shiga muddin taji Autanta ya mutu..
Sadiya.
Wunin ranar tayi suyarta cikin daɗin rai da annashuwa, gab da magrib kamar kullum yau ma ta ƙarashe komi, almajiranta suka kwashe kayan suka nufi gida da su, ita kam ta ɗan tsaya karɓar sauran kuɗaɗenta da ke hannun jama'a kafin ta kalli ƙofar gidansu Sadauki ta saki murmushi, kamar ta shiga ta dubo shi don ta ƙara ganin fuskarsa sai kuma ta hani kanta da faɗin.
"Ki bari Sadiya, akwai lokacin da shi da kansa zai riƙa zuwa gurinki, ki bari dai tarkonki ya kama kurciya."
Da wannan tunanin ta ƙarasa gida, sai dai tana shiga ta iske sabon bala'i tsakanin Hauwa da Ramatu suna watsawa junansu maganganu masu zafi.
"Wallahi Ramatu baƙin cikina da 'yata Sadiya shi zai yi ajalinki, hassadarki ta kasa ɓoyuwa to nan gani nan bari FARAR TUMFAFIYA, Sadiya dai sai dai ki ganta ki ƙyale mun fi ƙarfinki, tun da ba mu ne muka ɗaurawa Salame baƙin jini ba, sai dai hassada ta kashe ki."
"Wa ke hassadar da ke? Allah suturibuƙi inyi hassada da ke, wallahi Hauwa baki kai matsayin da zan miki ba, ni kaja wacce ta isa a gurin miji da ita ake hassada ba ke da kika dogara da 'yarki taje yawon dandinta da sunan suya ta kawo miki kuɗi ba, da ba a san asalin mage ba ne sai ta ce mana daga masar take."
Hauwa ko nauyin tsohon cikin da ke jikinta ba taji ba ta nufi Ramatu gadan-gadan ta kai mata duka.
"Wallahi ƙarya kike masharraciya, kowa yasan Sadiya wajen suya take wuni ba Salame da ke yawo cikin gari tana raba kai ba."
Ai nan fa suka fara kaiwa juna duka, shugowar Sadiya ne ya sakata ƙarasawa da sauri tana ture Ramatu.
,"Haba wai me ke damunku ne?"
Ta fara jan hannun Hauwa tana faɗin.
"Kizo muje kar ta bige miki ciki ta bar mu da Allah ya isa ta cuce mu."
Haka ta dunga jan hannun Hauwa har suka isa bakin ƙofarsu, amma bakin Hauwa bai mutu ba, tana nishi tana aikawa da Ramatu magana ita ma tana jifarta da nata, daman matan gidan sun saba basa rabon faɗa sai dai suyi kallo suna dariya da zuga, yau ma hakan ta kasance, malama ce kawai ke raba faɗa shi ya sa ita ba shiri take da kowa a gidan ba don akwai tsage gaskiya, yau da alama ba ta cikin gidan ne ko ta ɗan fita, ilai kuwa Sadiya na jan Hauwa cikin ɗaki ta hango shugowar malama daga waje hannunta da leda da alama cefane tayo.....
***
Ina masu buƙatar kyawawan atamfofi da lace, mayafai, shoes and bag. Tare da kyawawan kayan kitchen na 'yan gayu masu kwaliti, zaku iya tuntuɓar ASHNURR COLLECTION wacce ke Kano kwari market domin ƙarin bayani ku tuntuɓeta a lambar waya kamar haka *** Tana aika kayanta ko ina a cikin aminci.
Shin kuna da labarin AK ASHKAD COLLECTION to ku matso kusa ku ji, ita ce wacce take kawo muku kyawawan abayas na gani a faɗa na shiga ko wanne guri kai tsaye, haka tana kawo muku kitchenwares masu kyau da aminci cikin farashi mai rahusa zaku iya tuntuɓarta a 070444564938 ko *** shafinta na Instagram ashkad_collection adireshinta Daura, Katsina State tana aika kayanta ko ina cikin aminci.
Kuna da labarin UmmuAffan GHT Supplement, tana sayar da Supplement na kamfanin ght masu kyau da inganci tana garin Kaduna tana aika kayanta duk inda kuke a faɗin ƙasar nan dama wajen ƙasar nan, kai tsaye kuyi mata magana ta lambar waya kamar haka *** sayen na gari mai da kuɗi gida, sai kunzo.