Page 11
by @ummuaffan
...FARAR TUMFAFIYA.
©UMMU AFFAN
Page *11*
DK.
A ranar ya ɗauki mashin ɗinsa ya fita daga lungunsu ya ƙarasa wata babbar Shopping plaza da ke saman babban titin layinsu ya yi sayayyar kayan abinci masu ɗan dama shinkafa ƙaramin buhu da su taliya makroni, tumaturin leda, man gyaɗa, manja da Seasoning da Spices aka haɗa masa komi cikin babban buhu, ya ɗaure su tamau a bayan mashin ɗinsa sannan ya nufi hanyar gida. Inna ta dunga saka masa albarka da ganin irin kayan da ya saya musu ya danƙa mata dubu goma a hannunta ya ce ta ɗauki jarinta a ciki sauran ta sayi Tattasai da albasa, ta riƙe haɓa ta ce,
"Sadaukin maza! DK inji su Mansoor! Anya kuɗin nan ba suyi yawa ba? Ka ga fa kayan abincin da ka sayo kai baka buƙatar ka sayi komi ne?"
Wai Dk inji su Mansoor? Maganar Innar sai da ta saka shi ya murmusa kafin ya dube ta cikin kulawa.
"Haba Inna, ai babban burina a gidan nan shine naga na wadata ku da abin da ya dace, boko ma ina so yaran nan su koma amma dai bari muga yadda Allah zai mana a gaba, naga kayan islamiyyarsu ma duk sun tsufa naso na basu kuɗi su sake amma dai a cikin satin nan in sha Allahu."
Nan fa Inna ta fara matsar hawaye.
"Umarun Faruku Allah ya maka albarka, Allah ya cika maka burinka na alkhairi ya baka aikin nan, Allah ya gafartawa mahaifinku shi kuma Mansoor Allah ya saka masa da alkhairi."
"Amin Inna!"
Ya amsa mata tare da miƙewa daidai lokacin su Maryam suka shugo daga makaranta, ta nuna musu kayan abincin da ya sayo da kuɗin da ya bayar, nan suka dunga masa godiya suna farin ciki. Murmushi ya suɓuce masa, yana ƙaunar 'yan uwansa da mahaifiyarsa, burinsa ya saka su farin ciki, ya yiwa Inna sallama bari ya wuce masallaci don har an fara kiran sallar magriba, ita ma miƙewa tayi ta ɗaura alwala yayin da su Maryam suka shiga ciki suka cire uniform sannan suka dawo suka shigar da komi ciki sai suma suka yi alwalar.
Tun da ya fito daga masallaci yarinyar nan da ko sunanta bai sani ba ta dunga dawo masa, hakan ya sa ya koma ciki ya ɗauki mashin ɗinsa, inda ya bigeta ɗazun ya koma yana dudduba ko Allah zai saka su ƙaracin karo amma shuru kamar an aika bawa garinsu. Dole ƙanwar naki ya dawo unguwarsu, sai da ya yi sallar isha'i sannan ya koma gida, jin ajiyar mashin ɗinsa Inna ta saka Ummul ta kawo mishi abinci ya amsa ya shiga da shi ciki, amma ya kasa ci sai tunanin yarinyar yake.
'Tana neman taimakona, me yasa na kasa taimaka mata har wannan mutumin ya tafi da ita?'
Ya faɗa a ransa domin tabbas sai yanzun ya ƙara gano ba ƙaramin taimakonsa take naima ba, kuma yaji a zuciyarsa kamar wanda ya amsheta cutar da ita kawai zai yi, haka kawai yaji ransa ya masa baƙi, ina zai ganta? Wace ce ita? Wanne irin taimako take naima? Tambayoyin da ya dinga jeho ma kansa kenan ganin ba shi da amsa dole ya haƙura da takurawa kansa, sai ya tsinci bakinsa na furta mata addu'ar kariya da neman tsari ga mutum ko aljan.
Kaɗan ya iya cin abincin sannan ya ɗauki wayarsa ya kunna data, saƙon Mansoor ne ya ɗauki hankalinsa musamman ganin 3 misscall ɗinsa tun da rana amma bai kira shi ba ko da ya gani, don haushinsa yake ji duk da baya da ruƙo amma bai ji daɗin abin da ya masa ba da wani dogon bayaninsa na banza da wofi.
"Sadauki na kira wayarka amma ba ka ɗauka ba, don Allah kar ka yanke hukunci a karen kanka ba tare da bincike ba."
Saƙon murya (voice note) da ya ajiye masa kenan, ko saƙon jiya bai ba shi amsa ba wannan ma bayajin zai amsa masa, kiransa ne yaga ya shugo ta whatsApp ɗin alamar yana online ɗin kuma ya ga ya buɗe saƙin amma bai bada amsa ba.
Kamar kar ya ɗaga, sai ya yi tunanin idan bai ɗaga ɗin ba bai yiwa Mansoor ɗin adalci ba, a matsayinsa wanda ke yawan taimaka masa.
"Sadauki!"
Mansoor ya kira sunansa yana ɗaga kiran.
"Ina jinka!"
Ya amsa masa.
"Nasan kana fushi da ni ne akan ban iya cika maka burinka ba duk da kana tunanin nafi ƙarfin kuɗin da ka faɗa mini, eh ba kayi ƙarya ba nasan Daddy zai iya ba ni amma dole fa sai yaji me zanyi da su, kuma ba amsar ba ne bazan iya ba kawai dai kaine nake ganin baka zaɓawa kanka hanyar da ta dace ba, zama da samun gidan zaman a birnin Beijing da naji kana burin zuwa samun gida a can ba abu ne na wasa ba a bajiya mai ƙarfi da na jiyo ɗaki mai yalwa da banɗaki a ciki da kitchen kusan 1.5m ne duk wata, na ɗari biyar zuwa bakwai kuwa ba ma a cikin birnin ake samu ba sai a gefen gari, kuma daga wurin kafin ka shiga ciki ba ƙaramar tafiya ba ce sai ka dinga kashe kuɗi, ni babban tashin hankalin ma nawa da babu aikin da ka ke da shi tsayayye da zaka tafi kanka tsaye, wannan ɗin fa ba abin wasa ba ne, kana da ilmi daidai gwargwado, wayewar nan ba za a nuna maka ba, amma na rasa me ya sa kake niyyar saka kanka a shiga uku Sadauki."
"Ka gama?"
Tambayar da ya jeho masa kenan bayan kammala wannan dogon sharhin da ya yi.
"Umar!"
Ya kira ainihin sunansa.
"Na'am Mansoor! Ina so fa kasan wani abu, bana saka abu a raina sai na cimmasa dole ne na kai kaci ga duk abin da nayi niyya, Sadaukin Inna da Baba ne yayan Maryama da Ummul salama ko ka manta ne?"
Sosai Mansoor ya murmusa duk ƙoƙarin da ya ɓoye dariyarsa kar Sadauki yaji amma ya kasa kwarai maganar ta saka sa dariya.
"To kaji ko? Mahaukaci ma ka mayar da ni ina magana, ni kuma zan nuna maka ko ba ta hanyarka zan iya cika burina."
"Sadauki kar fa ka shiga hanyar da bai dace ba domin neman kuɗin nan, zan...."
Tun kafin ya ƙarasa Sadaukin ya katse kiran yana jan tsaki, da tunanin Mansoor so yake kawai ya ƙara ɓata masa rai, amma zai shayar da shi zumar mamaki, kuma ta hannun mahaifin nasa zai sami kuɗin lokaci guda yaji cewar zai amincewa Sadiya cewa zai aure ta ɗin idan ta samo masa kuɗin amma sai ya dawo daga tafiyar da zai yi, yasan kafin ya dawo tayi aurenta don baya jin nan kusa zai dawo sai dai ya dinga yiwa su Inna aike shi ya sa ma yake so kafin ya tafi ya buɗewa Maryam account ko da Opay ne kuma ya samu waya ya saya musu, yasan dai iyayen Sadiyar idan sunga ta isa aure ba zasu zuba mata ido ba ne ace dole sai yadawo, tunda ko a yanzu Sadiyar cikakkiyar budurwa ce, don za ta girmi Maryam ɗin duk da aji ɗaya suka taɓa yi kuma jikinsu ma ba iri ɗaya ba ne.
Da wannan tunanin ya kwanta barcinsa bayan ya tofa addu'a a duka jikinsa ya shafe jikin ya tofa a duka kusurwar ɗakin kafin yaja bargo ya rufe idanuwansa a hankali.
Amma sai me? Hoton Barirah da ko sunanta bai sani ba ya shiga yi masa gizo, haka ya dinga buɗewa da ya rufe yaga tana miƙo masa hannu wai ya taimake ta.
Ganin barcin ba zai ɗauke shi ba dole ya tashi ya fita yaje ya ɗauro alwala ya dawo ciki ya fara sallar nafila yana mata addu'ar fita daga halin da take ciki, bayan ya idar ya jingina da katifarsa yana tuno baƙar fuskarta, duk da tana cikin damuwa kuma yanayinta ya nuna tana cikin tsanani amma kyawun fuskarta bai ɓuya ba, ba baƙa ce sosai ba duk da ya lura halin da take ciki ya ƙara sakata duhun, yasan da zata samu hutu aininhin fatarta choculate zata fito sosai, haka kawai yaji yana murmushi lokacin da ta miƙo masa hannu ta zuba masa kyawawan idanuwanta masu ɗan girma ga kalarsu masu kyau farare ne duk da kukan da tayi sun sauya kala kaɗan abin da ya saka tsigar jikinsa tashi bai wuce launin kwayar idanuwanta da ya tuna ba, lokacin da ta kalle shi ya ga kwayar idanuwanta ba irin ta kowa ba ce maimakon baƙa tata ash colour ce irin ta mage ba ƙaramin burgeshi kwayar idanuwan tata suka yi ba, ya lumshe ido yana murmushi a zaunen kishingiɗe a katifar tasa barcin da bai shirya zuwansa ba ya yi awan gaba da shi.
Barirah.
Ba ita ta farka ba sai kusan la'asar cikin wani mawuyacin hali, lokacin Iyah na zaune a ƙasan gadon da take saman tabarmar wata mata suna cin abinci tare, ganin tun da suka zo wajen sha biyu har lokacin babu wanda yazo a danginsu kuma Iyar ba taci komi ba, hakan yasa matar tayi mata tayi.
Bata musa ba ta saka hannu suna ci domin gaskiya tana jin yunwar, ga shi ba ta ruƙo ko sule a hannunta ba saboda yadda suka fito a kiɗime, shi kuma Kawu Balarabe ya tafi bai bata komi ba saboda yadda hankalinsa ya tashi da kiran da Andi tayi masa.
Da sauri ta miƙe tana kiran sunanta.
"Barirah! Barirah."
Amma ba baka sai kunne, sai wani irin juyi da take zufa irin ta ɗazun tana ƙara feso mata lungu da saƙo na jikinta, tana wani girgiza da jijjiga kwatankwacin irin wacce Usman ya yi ranar da lalura ta same shi. Kuka Iyah ta fashe da shi, ganin haka da sauri matar da suke cin abinci ta fita ta kira masu likitan don ita kanta a ruɗe take da irin halin da taga yarinyar ta shiga, da saurinsa yazo abin mamaki kuma yana zuwa komi ya lafa sai dai wuyanta duk yakushi ne an ƙara ji mata launi da yawa ga gurin ya yi wani ja duk da bata da hasken fata.
"Subuhanallah, yarinyar nan anya ba sihiri jikinta, kin ga wuyanta kuwa?"
Likitan ya faɗa yana taɓa gurin da hannunsa wanda yake rufe da safar hannu.
Iyah ta dubi gurin ta fara hawaye.
"To ga shinan dai, wayasani ko da sihirin ni kaina abin ta ya fara bani tsoro."
"To gaskiya yana da kyau a samu malaman addini akan lamarin ko aje Islamic Kemis a amsar mata ingantattun magunguna na musulinci wannan ciwon nata yafi ƙarfin asibiti ba ma na asibiti ba ne, amma zamu bar ku zuwa gobe saboda ta ɗan sami ƙarfin jikinta sai ku tafi."
"To likita muna godiya Allah ya saka da alkhairi."
Iyah ta faɗa jiki a sanyaye matar ɗazun na ƙara ba ta haƙuri, nan likitan ya ƙara dubata da gyara mata ruwan da aka ɗaura mata sannan ya fita.
Wajen ƙarfe shidda na yamma Iyah ta roƙi alfarmar matar nan da ta bata abinci akan ta kular mata da Barirah za taje gida ta dawo, don tana so tayi wanka sannan ta taho musu da abinci, ta ruƙi alfarmar idan tana da ɗari biyu ta bata sai ta hau besfa ko ɗan sahu ta ƙarasa gida idan zata dawo zata taho mata da kuɗin.
Matar ta miƙa mata ɗari biyar tana faɗin.
"Haka dai 'yar uwa, wallahi babu komi ai yanzu an zamo ɗaya tunda musulmi ɗan uwan musulmi ne."
Iyah na mata godiya ta ƙarasa gaban gadon ta sake duba Barirah da har lokacin bacci take yi, ta sauke numfashi kafin ta fice daga ɗakin, tana hanya tana tunani kala-kala har ɗan sahu ya ajiyeta bakin titi inda zata sauka, tsallakawa kawai tayi ta hango ƙofar gidan nasu da maza maƙota ana ta alwala da alama masallaci zasu saboda sallar magrib da aka soma kira, ga tabarmi a guda biyu shimfiɗe a gurin, tana shiga harabar gidan suka ci karo da Kawu Balarabe zai fito cak taga ya tsaya yana kallonta, kafin ya fara bin bayanta da kallo, tunaninsa ƙilan zai ga ta dawo da Barirah ne amma sai ya ga akasin hakan, nan take taga ya sauke wani dogon numfashi, ba tare da ya kuma ce mata komi ba ya doshi hanyar fita daga gidan, tabi bayansa da kallo baki sake, cike da tsantsar mamakinsa. Kafin tayi kwafa ta nufi hanyar shiga ciki, tsakar gida taga matar Kawu Habule tana alwala.
"Sannunku da zuwa Atika kune a tafe?"
"Ai kuwa mune ai ance mana kina asibiti tare da waccen bala'in."
Iyah ba taji daɗin maganar Atika ta ƙarshe ba amma sai ta danne suka gaisa a haka, taga kitchen wayam ba kowa a ciki yadda ta lura kamar ma yadda suka barshi tun safe haka yake har yanzu, tayi kwafa a karo na biyu kafin tabi bayan Atika zuwa falon Rakiya.
Sai tayi mamakin har da Inna Hajara matar babban yayansu Kawu Bature a tafiyar, tana zaune tana yiwa Rakiya firfita wacce take kwance idanuwanta ƙeƙashe kamar kurma. Ga wasu mata biyu zaune gefe Halima ƙawar Rakiya sai Malama maƙociyarsu, Iyah ta zauna suka gaisa a mutunce suka yi mata ya ƙarin haƙuri da amsa da angodewa Allah don sam ba ta kawo mutuwar Faruk ce ya kawo su ba, don ta suka ji Mutuwar Saudatu an barshi sai uku zasu zo sai ga wannan ma ba shiri suka taho domin tayasu wannan jimami na mutuwa biyu a jere.
"Rakiya ya jikin Faruk ɗin, ina can da Barirah ko wayata a gidana na barta shi ya sa ban kira ki ba."
Duka suka zuba mata ido ban da Rakiya da ta fashe da sabon wani kukan, domin a lokacin da su Kawu Balarabe suka dawo gidan tana zaune ɗakin Usman saboda jijjigar da yake ta dawo, haka ta kira malama akan tazo ta taimaka mata ta saka masa karatu kafin Kawu ya dawo asan yadda za a yi aje gurin malamin da ta basu lamba don ko natsuwar kiransa ba su samu sunyi ba.
Da aka saka mishi karatun sai ya sami barci, shine fa suka zauna suna ƙara mayar da zance akan lalurar tashi, sai jin sallama suka yi, haka suka fito tsakar gidan suka iske Kawu Balarabe ne, Andi na ganin yanayinsa ta fara kurma ihu tana faɗin.
"Kar ka faɗa mini shima yabi Saudatu? Kar ka ce mini na sake rasa Farukuna, na shiga uku ni Rakiya, Tsaiba kin barni da masifa Runduna ka cutar da ni ka silarka na rasa yara biyu ga wani kwance rai a hannun Allah. Me yasa kuke aikata hakan akan yara, me yasa ni baku kashe ni kun bar mini yarana ba?"
Jin yadda take gunjin kuka Kawu Balarabe ya rungume ta yana rarrashi, duk dauriya irin nashi sai ga shi yana hawaye.
"Rakiya muma ba laifinmu ba ne, kome ya same mu laifin Tsaiba ne, da bata aikata komi ba da komi bai faru ba, amma ga 'yarta nan ƘUSA ba ƙusa ne dai ko? To 'yarta ma za tayi rayuwa a ciki wallahi sai dai idan bana numfashi, ba ni ta zalumta ba kanta ta cuta."
"A'a Balarabe ni ce, a kaina ne Runduna ke ɗaukar fansa, don Allah ka faɗa masa ban aikata ba, ban aikata komi ba ya dawo mini da Saudatu, ban aikata ba kar ka ce mini Faruk ma ya mutu, komi saboda Tsaiba ne duk nayi don ceton Tsaiba ne ba a karen kaina ba."
Ta kuma fashewa da kuka tana danƙar Kawu, kafin lokaci guda ta sake shi ta fara ja da baya, ta fara gyaɗa kai kamar wacce ta fara zautuwa, ta zubawa Kawu idon tanaci gaba da gyaɗa kan cikin raunin jiki, rayuwa, da sarewa, daidai ta kai bangon gurin, Kawu ya ƙaraso shima cike da rauni.
"Don Allah Rakiya kiyi haƙuri, duk wani mai rai mamaci ne, Faruk ma dai ya rasu..."
Ai da ta kurma wani ihu nan take ta zubewa a sume, cikin kaɗuwa da ɗimuwa Kawu da malama suka ƙarasa kanta. Saboda tun da suka fara maganar malamar ke tsaye tana kallonsu cikin damuwa da mugun tausayi, babu abin da ba ta saƙa ba da jin kalamansu, amma duk ƙoƙarinta ta kasa kamo bakin zaren, hakan yasa ta ƙara tausaya musu sosai tare da fara yi musu addu'ar samun mafita a zuciyarta. Andi kuwa daga lokacin ba ta sake gane wanda yake kanta ba, sai da aka kira wata likita tazo har gidata duba Rakiya daga ƙarshe ƙarin ruwa ta saka mata, anan gida bayan ta farfaɗo amma ba uhmm ba uhmm Uhmmm, barci ma ta shiga yi saboda allurar barcin tayi mata, haka shima Faruk aka suturta shi har aka kai shi aka dawo Rakiya barci take, tun kafin su tafi kai shi Kawu Balarabe ya kira gida yayunsa ya sanar musu an kuma yin wani rashin a gidansa, yana jin irin tsinuwa da la'antar da Kawu Habule ke aikawa da Barirah, tare da ƙara shaida masa kar ya sake ya wuce goben bai kawo Barirah ba an haɗata da kalarta, tunda daman ance kalar zaren kalar yadin, ɗan garin Ƙusa ne ya dace da ita, saboda Kawu Bature ya yi bincike bayan tafiyar Kawu Balarabe kuma ya gado tabbas Ubale ɗan yankin Ƙusa ne, ba su tuntuɓe shi a tsakaninsu suka kuma tattauna ta waya akan a ɗaura auren daman ta inda aka hau tanan ake sauka haka kyawun ɗa ai ya gaji ubansa, da wannan tunan Kawun ya fice, shi kanshi Aliyu kamar bai da lafiya don tun da ya yi shuru bai ƙara ce da kowa komi ba, haka Kawun kallo ɗaya zaka mishi ka hango wata rama da ya yi kamar ba shi ba har wani tsawo zaka ga ya ƙara tsabar halin da yake ciki, haka maƙota sukayi ta shugowa gaisuwa kowa na tausayawa Rakiya don mutuwa irin wannan kam akwai tashin hankali ga uwa sai dai kuma dole sai haƙuri amma abin na shigar mutum sosai, wanda ya taɓa shiga halin ne kawai zai ƙarar da maganar.
Sai wajen biyar na yamma Rakiyar ta farka lokacin mutanen Kalanbaina sun iso haka aminiyarta Halima da sukayi 'yan matanci tare, ita ma a Sokoton take aure, taji a gurin ɗanta Nasir ne don abokin Aliyu ne na kusa.
Iyah ta fashe da kuka lokacin da Atika ke faɗin.
"Oh baki san wacce kike jinyar ta kuma lashe Farukun har lahira ba don ita ta tashi a jinyarta? Wannan muguwar yarinya baƙin halinta da mugun nufinta ai ita zai fi da ikon Allah sai tabi bayansa!"
"Innalillahi wa'inna ilaihi raju'una shima Faruk ya mutu?"
Iyah ta kuma tambaya tana kuka, wannan karon babu wanda ya kulata sai Rakiya da ke tayata kukan cike da tashin hankali.
Jin an idar da sallah dole mutane suka fara tashi domin zuwa suyi alwala suyi sallah Atika ma bayan yada zancen ta tada tata sallar. Malama kam sallama tayi musu ta wuce gida, Iyah ɗaki ta fara shiga tayi 'yan uzurorinta kafin ta fito kichen ta shiga nan taga yaran maƙota na ta kawo abincin sadaka kula-kula, ga maƙotansu gidan Alhaji Sammani an aiko da shi a wata babbar kula, ta ɗaura ruwan zafi abubuwa da yawa suna zo mata a rai tana tsaye har ruwan ya yi zafi ta juye a bokiti ta kashe gas ɗin, bayinta da ka falonta ta wuce, tayi wanka tare da alwala ta fito, sai da tayi har isha'i kana ta dawo falon Andi ɗauke da ɗaya daga kular abincin da aka kawo ta ajiyewa su Atika, ta zauna jum har kusan tara, a ranta tana ta tunanin Barirah da halin da take ciki, shugowar Kawu Balarabe ta sauke numfashi, tana dubansa ta ce,
"Bari na koma asibitin likita ya ce sai zuwa gobe zai yi sallama!"
"To ki sani muddin ki ka koma asibitin nan a bakin aurenki Sabuwa, kuma ina so ki sani goben ma anayin addu'ar uku zanmu karkata da su matan yaya zuwa can zanje na ɗauko ta da safen da kaina!"
Yana faɗa ya shige, tamkar saukar aradu aka haka Iyah taji kalaman Kawun hawaye taji na saukar mata yayin da Atika tana zuba abinci tana yada nata zancen, duk akan kisan da Barirah ke yi acewarsu da kuma irin mugun bakin da take mata.
Iyah ta miƙe jiki a sanyaye ta fice Halima taja dogon tsaki tana kallon Rakiya da take ta faman kuka.....
*Littafin Farar tumfafiya na kuɗi ne, free pages zai ƙare ne a 15 pages don haka masu buƙatar saya za su tura 700 ne a yanzu, idan mun kammala free pages kuɗin littafin 1k za a tura kai tsaye ta 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC sai shaidar biya ta *** kar ku bari wannan damar ta wuce ku, farar tumfafiya har yanzu sharar fage muke.*
Ina masu buƙatar kyawawan atamfofi da lace, mayafai, shoes and bag. Tare da kyawawan kayan kitchen na 'yan gayu masu kwaliti, zaku iya tuntuɓar ASHNURR COLLECTION wacce ke Kano kwari market domin ƙarin bayani ku tuntuɓeta a lambar waya kamar haka *** Tana aika kayanta ko ina a cikin aminci.
Shin kuna da labarin AK ASHKAD COLLECTION to ku matso kusa ku ji, ita ce wacce take kawo muku kyawawan abayas na gani a faɗa na shiga ko wanne guri kai tsaye, haka tana kawo muku kitchenwares masu kyau da aminci cikin farashi mai rahusa zaku iya tuntuɓarta a 070444564938 ko *** shafinta na Instagram ashkad_collection adireshinta Daura, Katsina State tana aika kayanta ko ina cikin aminci.
Kuna da labarin UmmuAffan GHT Supplement, tana sayar da Supplement na kamfanin ght masu kyau da inganci tana garin Kaduna tana aika kayanta duk inda kuke a faɗin ƙasar nan dama wajen ƙasar nan, kai tsaye kuyi mata magana ta lambar waya kamar haka *** sayen na gari mai da kuɗi gida, sai kunzo.