Page 12
by @ummuaffan
...FARAR TUMFAFIYA.
©UMMU AFFAN
Page *12*
"Gaskiya matar nan tsoro take ba ni, nifa jikina na faɗa mini ba ta da gaskiya."
Halima ta faɗa bayan ficewar Iyah daga falon, matar Kawu Bature taja numfashi da cewa.
"Anya kuwa, ni kuma ban taɓa mata irin wannan kallon ba."
"Mugu ai ba shi da kama yaya, nifa duk biye matan da zaki ga inayi iyakar na fatar baki ne, amma wa ya aike ni bare ya ga na daɗe? Nifa matar nan ba tun yau ba na fara jefa ayar tambaya a kanta, tun lokacin da Balarabe ya aurota naga yadda take zuba mana idanuwan nan nata manya ga su jajaye jikina ya ba ni da wata a ƙasa."
Atika matar Kawu Habule ce ke sakin wannan ɓarin zancen, domin daman ita irin matan nan ce da ke sakin baki suna zance ba tauna harshe babu ɗango balle ƙafiya, ita dai ta kwaso zance kawai a gamsu shine burinta, kuma abin takaicin ga kowa ko Iyah da zasu keɓe da ita haka za tayi ta sakin bakin. Hajara matar Kawu Bature sanin hali sai ta ce,
"Ke dai Atika ki iya bakinki, gidan mutuwa muke ba gidan biki ba, sannan ko duniya ce ita mai ido a tsakar ka nan gani nan bari farar tumfafiya muke ahlin Kaka Kulu ne fa."
"Uhmmm a hakan kuma Runduna ya yi wuf da Tsaiba ba ku iya aikata komi ba."
Ƙasa-ƙasa tayi maganar tana tura baki kamar ƙaramar yarinya, don ta tsani ta kawo magana amma a ƙi yarda ko a kusheta, to ita fa akan hakan sai ku iya kwasar 'yan kallo. Andi taja numfashi har lokacin hawaye take ta ce,
"Kar ku ɗauki alhakin Sabuwa ba ta da laifi kuma babu ruwanta a wannan lamarin, samun kishiya kamar ta ba duk mata ba, don haka kar ku ɗauki alhakinta."
Halima taja tsaki tana jawo kular abincin gabanta ganin Atika ta gama zubawa, ita fa ta daɗe tana cewa Rakiya kishiyar nan tata muguwa ce, don ansha zuwa ana faɗa mata magungunan da take bayarwa har da na tsafi ba wai na gargajiya take sayarwa kaɗai ba, mijinta da kishiyarta da matan unguwa ne take yiwa basaja, don har gari-gari ana zuwa neman taimako gurinta, amma Rakiya ta musa, saboda ruwan da ya dake ka shi ne ruwa, Sabuwa bata taɓa aikata mata ba ba zata bayar da shaidar zur ba, ba ƙarya ba ne mata har maza manyan masu kuɗi suna sallama gurin Iyah amsar taimako amma ita dai tasan magungunan gargajiya ne take ba su a matsayin taimakon tunda tasan kan sauyoyi 'yar na gada ce don ta taɓa faɗawa Rakiya danginsu sana'arsu kenan, kuma ta ƙarar tunda gashi tana daka wasu magungunan kuma babu abin da zaka naima indai maganin gargajiya ne ba ka same shi gurinta ta ba, tana da su sauyoyi, sassaƙe, huntaye da ganyayyaki, haka irin su ararraɓi huntu, tazargade, sabara, rawaya da makamantansu, shi ya sa Rakiya ba ta taɓa zarginta da komi ba kuma tana ƙaunar yaranta duka kamar me, kar ma ka ce Usman da ya zamo tamkar ita ce tayi naƙudarsa a ɗakinta ya taso a ɗakinta yake kwana sai da ya girma sannan ya koma ɗakinsu amma duk da haka komi nashi na gurin Iyah, sai ta ɗinka masa kaya na musamman, tayi masa abu goma kafin tayiwa sauran ɗaya, mutane da yawa ma suna ɗauka cewa ita ce ta haifi Usman ɗin. To akan me za ta ce Sabuwa tayi mata ko tana da wani sirri da ba ta sani ba bayan komi a gabanta ake yi.
Baƙinta da suka zo amsar taimako ne kawai suke keɓewa ciki musamman idan mata ne, maza kuwa a harabar gidan suke zama. Ita dai Halima an kawo mata tsegumi kuma matar ta bata tabbacin maƙociyarsu ce ta sanar mata wai ta amso taimako gurin Iyah saboda matsa mata da miji ya yi tunda ya ƙaro aure ya tare a gidan amarya ya mantata wata da watanni aiko tana amso taimakon yanzu ya dawo da amaryar ma gidan kuma sai abin da ta ce daga mijin har amaryar suke mata, kuma wacce ta faɗa mata har gidan taje ta gani kuma ta bata tabbacin ita ma taje ta amsa don ta ɗauka sunzo suga yadda aikin yaci ne kafin suje amsar nasu taimakon, Halima ta sanar da Rakiya komi amma ta buga tsalle ta ce ba ta yarda ba.
Halima kam har yau ba ta yarda da Sabuwa ba kuma tayi alƙawarin ba zata daina bibiyarta ba har sai ta iya gamsar da Rakiya kishiryata fa ba mutiniyar kirki ba ce kamar yadda ta rufe su da wata fuskar da ba ainihin tata ba.
Iyah.
Tana shiga falonta kasa zama tayi, tunanin Barirah da halin da take ciki a yanzu shi yafi komi ɗaga mata hankali, shim me matar da ta bawa ajiyar Barirah zata ɗauka? Har ta ɗauki hijabi zata fita maganganun Kawu Balarabe suka fara dawo mata tamkar yanzun yake sake biya mata su.
"To ki sani muddin ki ka koma asibitin man a bakin auren ki Sabuwa!!"
Ta sake jin maganganun tamkar saukar aradu aka, ta rumtse idanuwanta da ƙarfi wasu hawaye masu zafi nabin kuncinta, ta koma ta zauna tana mai cire hijabin jikin nata, yunwar da take ji ma gabaɗaya sai taji tamkar an yaye mata ita, ta koma kitchen ta saka ruwa bayan ya yi zafi ta juye a kofi ta jefa lipton ta zuba suger da madara haka ta dawo falonta tasha shi a hakan shi ko kayan ƙamshi ba ta zuba ba, bayan ta sha rabin kofin ta mayar da sauran ta wuce ɗakinta, da ƙyar kuwa bacci ya ɗauketa kusan sha biyun dare.
Washe gari da wuri ta tashi ta fito ita ta haɗawa baki abin karyawa, tare da nuna tamkar komi bai faru ba, suka gaisa cikin mutumci ta ajiye musu abin kari tana ƙara yiwa Rakiya ban haƙuri ta faɗin ta samu ko ruwan shayin ne tasha hanjin cikinta su warware, ɗakinsu Usman ta shiga ta iske shi yana barci Aliyu na kusa da shi ya saka masa karatun Qur'ani saitin fillown da yake kwance.
Aliyu ya gaisheta ta aamsa tare da tambayar Usman da jiki kafin ta koma kitchen domin ƙarashe aikinta.
Misalin goma na safiya duk su Atika sunyi wanka, duk Sabuwa ce ta haɗa musu ruwan zafi ta kaiwa ko waccensu toilet har Halima, wacce ta dubi ruwan, haka kawai take tunanin ko tayi wasu haɗa-haɗe ne a ruwan, sai ta zubar da shi a toilet ɗin ta fito bohol ta kunna kan fanfan ta zuwa ruwa da shi tayi nata wankan, ba ta san komi ya haɗata da Sabuwa har sai ta gama bincikenta a kanta.
Iyah kuwa tazo gurin taga Halima na zuba wani ruwan ba ta kawo komi a ranta ba tayi wucewarta, daman tasan tun asali ba sa shiri da Haliman, tana taya ƙawarta kishi ne wanda ko ita ƙawar ba ta ɗauka da zafi ba kamar ta.
Misalin sha biyu na rana kuwa har abinci ta kammala, sai da kowa yaci ya ƙoshi sannan Kawu Balarabe ya shugo, shima wanka ya yi yaci abincin ya ce su fito su wace, tunda addu'a tin safe aka yita kuma a masallaci ma akayi, Aliyu aka ce ya zauna ya kula da Usman Rakiya kuma aminiyarta Halima tana nan, Kawu ya ce Sabuwa tazo su tafi tare, ba musu ta ɗauko jakarta da mayafi ta kulle ƙofarta suka fita.
Ita ce a gaban motar sai Hajara da Atika a baya suka nufi asibitin, lokacin da suka ƙarasa Kawu cewa ya yi Iyah taje ta taho da Barirah ɗin su ba sai sun shiga ba, haka kuwa akayi ta fita zuwa ciki zuciyarta cike da zullumi.
Ba kowa ɗakin sai Barirah zaune akan gadonta tana kallon gefe, gabaɗaya fuskarta wasu irin yakushi ne yanzu haka wuyanta, Iyah ta ƙarasa da sauri har tana tuntuɓe ta taɓa Barirah wacce tayi furgigit ta kalle ta da alamar ba taji shugowarta ba sai taɓa tan da tayi.
"Iyah!"
Ta furta tare da ƙanƙameta tana sake fashewa da wani kuka.
Tun bayan jiyan da Iyah ta tafi Barirah ta farko wajen takwas na dare, matar nan ce ta taimaka mata da sannu har ta zaunar da ita kuma ta zuba mata abinci ta bata, duk da ba ta iyaci da yawa ba sai kaɗan, ta ce ta ƙoshi nan take tambayarta waye ya kawota asibitin, matar ta shaida mata mahaifiyarta ce Sabuwa don ta faɗa mata sunanta kuma ta ce ita ce mahaifiyarta, nan take ta gane Iyah ce daman tasan duk gidan ita ce kaɗai zata iya taimakonta.
Nan matar ke faɗa mata ta ɗanje ta dawo taje gida tayi wanka tazo musu da abinci amma ita kanta tayi mamakin da har lokacin ba ta dawo ba, haka har goman dare babu Iyah, lokacin ne kuma wani babban al'amari ya faru wanda dole ya saka kowa da ke ɗakin guduwa, domin gadon da Barirah take ne ya dinga motsi ta dunga wasu abubuwa tana ihwace-ihwace, kuma yadda sautin ke fita tamkar dambe ake ta bala'i, nan take kammanin Barirah suka sauya, sakamakon duka fuskarta ta dawo da yakushi haka wuyanta, hatta likitoci sun kasa don ɗaya da ya yi gigin zuwa sai gani aka yi anyi sama da shi an nanashi da ƙasa, ai ba likitoci ba hatta nurses da masu jinya 'yan zuwa gaishe da marasa lafiya, hatta waɗanda ke gadon asibiti wato marasa lafiya haka kowa ke gudun ceton rai a asibitin.
Aka bar Barirah ita ɗaya, don wannan likitan da aka nana da ƙasa da rarrafe yana kuka da kar a kama shi ya bar ɗakin, yadda suka dinga jin wata mahaukaciyar dariya na tashi a ɗakin yasa da yawan mutanen da abin ya faru a gabansu suka fara gudu daga asibitin, matar da Iyah ta ba ajiyar Barirah na ɗaya daga cikin waɗanda suka gudu ta tattara har da mai jinyar don ta ce gara su sauya wani asibitin kawai.
Haka Barirah ta kwana ita ɗaya kamar dai mayyar da aka daɗe ana ce mata, kuma har cikin ranta da zuciyarta yau ɗaya dai ta shiga kokonton anya ba mayyar ba ce? Anya kuwa maitar ba ta bibiyarta? Duk abin da ya faru da ita a daren jiyan taji komi a jikinta, haka duk ciwukan da ke wuyanta da fuskarta suna mata zafi ainun yau ta jita a gaba kura baya sayaki don idan taƙ tuna kalaman Kawunta kafin ta suma tana jin zafi aɗ zuciyarta haka idan ta tuna rayuwar da take a gidan Kawun ma sai ta ƙara tsinkewa da al'amarin duniyar, ita ji take ina ma ta mutu ne kowa ya huta ita ma ta huta.
Tana cikin wannan tunanin taji an taɓata, a furgice ta kalli wanda ya taɓatan ganin Iyah ce kuwa ta ƙanƙame ta tana kuka.
"Iyah tabbas ni Mayya ce, maganar Andi da Kawu gaskiya ce, ni ce wacce ta cinye Saudatu haka ma Yaya Usman ko? Iyah ni ce ko? Na yarda ni ce na cinye su domin abin da ya faru da ni daren jiya ya ƙara sakawa na aminta da ba ni da wani amfani a duniyar ma, me zai saka na cinye Saudatu? Wacce asara ce za ta saka na mayar da Yaya Usman haka? Wanda shi ɗaya nake kallo nasan akwai sassauci bayan Kaka Kulu da ke Iyah, yaya Usman shi ne mutum na uku a duniyata da zan bigi ƙirji na nuna yana kula da ni yana yadda da lamurana duk da yana mini hukunci amma hakan ba zai hana gobe ya kuma aikena da damƙa duka wata yarda a kaina na cewa zan daina ba, me ya sa shi? Me ya sa sai shi zan halakawa rayuwa har haka Iyah? Ba ni da amfani ba ni da wani amfani tunda na zamo butulu mai mayar da sharri ga alkhairi."
Ta ƙara ƙanƙame Iyah tana wani irin kuka da yake fitowa daga zuciyarta gabaɗaya, jikin Iyah ya yi mugun sanyi ta fara ƙoƙarin sakko da Barirah daga gadon.
"Zo mu tafi!"
Ta faɗa da wata iriyar murya wacce da ace Barirah na cikin hayyacin zata ƙaryata ba muryar Iyah ba ce, haka ta dunga janta suna ratsa cikin asibitin har suka fito suka ƙarasa harabar inda Kawu Balarabe ya yi parking, ba ta ce komi ba ta buɗe gidan baya ta saka Barirah, ta rufe ƙofar sannan ta koma gaba ta shiga, ba ɓata lokaci Kaeun ya tada mota ya nufi hanyar Kalanbaina ba tare da ya furta ko uffan ba.
Ba ta iya ɗaga ido ta kalli komi ba sakamakon tunda suka fito hasken rana ya dake ta sai taji wannan ciwukan na wuya da fuskarta suna mata wasu irin zafi, shi ya sa ko da Iyah ta saka motar ba ta ɗago ba har motar hawan saman babban titi sannan ta ɗago, saboda tana lura tunda ta shugo matar dake kusa da ita ta matsa da sauri har tana jin saukar tsakinta, lokacin da ta ɗago ta dubi Atika wacce ita ce a kusa da itan sai taka ta dafe ƙirji tana surutu.
"Na shiga ukku ni Atika, mi nika shirin gani haka ga huska da jikinki? Anyah ko mutum kike Barirah?"
Ta faɗa da tsantsar hausarsu cike da tsoro da kuma tashin hankalin da ya saka Hajara leƙowa ta kalli fuskar Barirah, sai kawai ta matse Atika a jikinta tana addu'o'in da duk suka zo bakinta, waɗanda kawai faɗarsu take da sunan addu'a ba tare da tasan me take faɗa ba, ita tsabar tsoro ma lokaci guda taji cikinta ya katsa mata wani kuwww! Da wuya kuwa idan zawo bai ɓata mata zane ba.
Gabaɗaya jikinsu ya hau rawar mazari, sun liƙe sosai da bangon motar, ganin haka Barirah ita ma ba ta ƙara cewa komi ba ganin matan Kawun nan tane da tun asali ba sa ƙaunarta, ƙiyayyar ta faro ne daga yadda Kaka Kulu ke ƙaunarta haka komi ta samu na Barirah ne kuma duk wanda ya taɓa ta sai inda ƙarfinta ya ƙare sakamakon yaransu da gaisuwa ce ke haɗasu, sai idan sunyi wani rashin jin ne tazo tana ta faɗa da cewa yara duk sun lalace da rashin tarbiyya ba sa hanasu rashin ji, kuma ina Barirah kome za tayi sai ta ce ai ƙaramar yarinya ce, kuma bata da kowa iyayenta basa nan don haka ita ce uwarta da ubanta a barta tayi abin da take so, to hakan fa yasa suka ɗauki tsanar duniya suka watsata ga Barirah.
Kawu da Iyah duk suna jin abin da ke faruwa amma babu wanda ya ce komi a cikinsu, sunyi tafiya sosai kafin suka ƙaraso, don ma garin a bakin titi yake, ga shi ana ta gine-gine har yana son haɗewa da Sokoton ma, sai da yaje ƙofar gidan ya tsaya.
Kamar su Atika na jira yana parking suka buɗe har da rige-rigen fita. Hajara da gudu ta shige don tabbas idan ba ta shiga banɗaki ba akwai matsala, Atika kuwa amai ta dunga yi bayan ta shiga ciki. Iyah ce ta kama hannun Barirah suka shiga ciki, idan banda bugawa babu abin da ƙirjinta ke mata ga wata faɗuwar gaba da ke ta zo mata, ɗakin Hajara suka shiga tunda daman idan sunzo nan suke sauka, ita ce babba kuma matar babban yaya dole ɗakinta zasu sauka.
Ko da ta fito banɗaki kasa shiga ɗakin nata tayi duk da, da son samu ne ta kwanta tayi barci amma haka ta haƙura dole sai ɗakin yaransu mata ta shige ta kwanta, ko fuskar Barirah ta tuna sai taji cikinta ya karta.
Babu ƙarya fuskar Barirahn ta dawo abar tsoro, duk wanda ya kalleta duk dauriyarshi sai ta ba shi tsoro, wasu irin ciwuka ne wanda da farko an ɗauka yakushi ne kamar yadda ya fara nunawa a farko, sai kuma yanzu ya dinga juyewa yana zama kamar wani ciwo kuma yayi jajja baƙi-baƙi a fuska da wuyanta, ko yaran gidan kasa shiga ɗakin suka yi don tsoro take ba su, Atika kuwa daman yaranta taja ɗaki ta ce duk wanda ya yarda yaje ko kusa da ɗakin Hajara ne to Barirah zata lashe shi ne kuma nan take zai mutu ya bar duniya a kai shi kabari, maganar ta basu tsoro don suna ganin duk wanda aka kai kabari bai dawowa sai suka ƙi zuwa.
Kawu bai shugo ba ya wuce masallaci sallar azahar, bayan sun fito ne suka haɗu da su Kawu Bature yake tambayarsu ya yaga an tashi masallaci ba a ɗaura auren ba?
"Balarabe tun safe muke zuba idon ganin mutumin nan kamar yadda muka yi da shi, amma ka ga har an fito masallaci shuru kamar malam yaci shirwa."
Kawu Habule ne ya faɗa ransa a ɓace, cikin takaici kuwa Kawu Bature ya ɗaura da.
"Wallahi ko shi bai zo ba dole fa mu aurar da yarinyar nan a yau, ni dai baza ta kwanan mana a gida ba wani mugun abin yazo ya faru mu shiga uku ba, daman munyi da shi ana ɗaurawa zai ɗauketa su tafi, wunin biki ma don ya zama al'ada ne zamuyi shi gobe ko ba tare da ita ba, wankin amarya ma a yau muka tsara ayi komi su tafi, amma reshe na niyyar juyewa da mujiya abin da bazan bari ya faru ba kenan, wallahi kuɗin da ka bayar Balarabe na saka anyi mata kayan ɗaki suna gurin kafintan daman munyi da shi ya taho da motar kwasar kaya duka su tattara su tafi."
Wani gauron numfashi Kawu Balarabe ya sauke, tabbas suna cikin tsaka mai wuya, amma shi kansa zai fi son ayi auren a yau yasan sun rabu da Barirah kafin idonta ya kuma kaiwa kan wani a dangi a rasa shi, ko mugun halinta ya fara ɓata wasu abubuwan kamar yadda shima duk kayan gidansa suke ta lalacewa.
Sai dai abin da suka gani suna isa ƙofar gidan shi ya ƙara tayar da hankalinsu, ba shiri suka kutsa ciki Kawu Habule ya kama ƙaramin ɗansa Tasi'u da suke cewa Tase yana girgizawa, jin sa yake fa kamar baya numfashi ya dubi mutanen da ke gurin cikin tashin hankali yana tambayar me ya sami Tase?
Sule ɗan wajen Kawu Bature ne ya ce,
"Wancen takalmin ne ya gani a kusa da motar Kawu, shine ya ɗauka yana cewa na baƙin da suka zo ne, na ce yaje ya kai musu, ko kafin ya shiga gida naga ya faɗi a ƙasa yana birgima."
Kawu Balarabe ya kalli takalmin, tabbas na Barirah ne, domin bazai mance lokacin da Iyah ta ɗauki takalman ba da zasuje asibiti, kuma lokacin da ya hango su sun fito da zasu taho tabbas ya lura su ne a ƙafafuwanta, to me ya sa tabar wari ɗaya a gurin ta shiga da ɗaya?
'Saboda ta shirya kashe wani.'
Nan take zuciyarsa ta ba shi wannan amsar, ya dubi Kawu Habule da ya kinkimi yaron da yake da tabbacin ya zama gawa ya nufi cikin gidan, nan take kuwa suka take masa baya.....
*Littafin Farar tumfafiya na kuɗi ne, free pages zai ƙare ne a 15 pages don haka masu buƙatar saya za su tura 700 ne a yanzu, idan mun kammala free pages kuɗin littafin 1k za a tura kai tsaye ta 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC sai shaidar biya ta *** kar ku bari wannan damar ta wuce ku, farar tumfafiya har yanzu sharar fage muke.*
Ina masu buƙatar kyawawan atamfofi da lace, mayafai, shoes and bag. Tare da kyawawan kayan kitchen na 'yan gayu masu kwaliti, zaku iya tuntuɓar ASHNURR COLLECTION wacce ke Kano kwari market domin ƙarin bayani ku tuntuɓeta a lambar waya kamar haka *** Tana aika kayanta ko ina a cikin aminci.
Shin kuna da labarin AK ASHKAD COLLECTION to ku matso kusa ku ji, ita ce wacce take kawo muku kyawawan abayas na gani a faɗa na shiga ko wanne guri kai tsaye, haka tana kawo muku kitchenwares masu kyau da aminci cikin farashi mai rahusa zaku iya tuntuɓarta a 070444564938 ko *** shafinta na Instagram ashkad_collection adireshinta Daura, Katsina State tana aika kayanta ko ina cikin aminci.
Kuna da labarin UmmuAffan GHT Supplement, tana sayar da Supplement na kamfanin ght masu kyau da inganci tana garin Kaduna tana aika kayanta duk inda kuke a faɗin ƙasar nan dama wajen ƙasar nan, kai tsaye kuyi mata magana ta lambar waya kamar haka *** sayen na gari mai da kuɗi gida, sai kunzo.