FARAR TUMFAFIYA

Page 14

by @ummuaffan

‎...FARAR TUMFAFIYA.
‎
‎
‎
‎©UMMU AFFAN
‎


Ina masu buƙatar kyawawan atamfofi da  lace, mayafai, shoes and bag. Tare da kyawawan kayan kitchen na 'yan gayu masu kwaliti, zaku iya tuntuɓar ASHNURR COLLECTION wacce ke Kano kwari market domin ƙarin bayani ku tuntuɓeta a lambar waya kamar haka *** Tana aika kayanta ko ina a cikin aminci.

Shin kuna da labarin AK ASHKAD COLLECTION to ku matso kusa ku ji, ita ce wacce take kawo muku kyawawan  abayas na gani a faɗa na shiga ko wanne guri kai tsaye, haka tana kawo muku  kitchenwares masu kyau da aminci cikin farashi mai rahusa zaku iya tuntuɓarta a 070444564938 ko *** shafinta na Instagram ashkad_collection adireshinta Daura, Katsina State tana aika kayanta ko ina cikin aminci.
‎
‎
‎Page *14*
‎
‎
‎
‎
‎Nazifi.
‎Da ya shiga ɗakinsa a hankali ya rufe ƙofar, gajiya sosai yake ji a cikin jikinsa ya ajiye duk abin da ke hannunsa saman wata drower da ya tanade ta takanas saboda ajiye fayilolin da yake zuwa da su gida gefe guda kuma Laptop ɗinsa, bathroom ya faɗa wanka ya yi tare da ɗaura alwala, yana yawan yin alwala musamman idan ya yi wanka ko da ba lokacin sallah ba ne haka idan zai kwanta bacci ma da wuya ya kwanta babu alwala, hakan yabi jikinsa sosai. Bayan ya fito sai ya saka jallabiya mai laushi fara ƙal har ɗaukar ido take duk da marece ne, ya gyara sumar kansa sannan ya fito zuwa falon.
‎
‎Shukuriyya daman tuni ta shirya masa abincinsa a saman dinning table, tafi kowa sanin ƙa'idar da ya saba da ita tsawon shekarun da suke tare ba ya son cin abinci da dare sosai musamman abu mai nauyi idan ya dawo gida da wuri, yana cin abinci tun kafin Magriba domin ya samu damar yin ibada cikin kwanciyar hankali haka kuma abincin ya samu lokacin narke masa kafin lokacin da zai  kwanta bacci don yana cikin irin mutanen da abinci baya narke masa da wuri duk ranar da ya kuskura yaci abinci yana gab da kwanciya to tabbas yana haifar masa da ɗa mara ido, ya zauna a kujerar da yaja da ke fuskantar Shukuriyya. Baby Ayrah na zaune kusa da shi tana tayi masa surutu, murmushi kawai yake yanajin kalaman nata har cikin zuciyar shi, a irin hirar nan ne har idan Murjanatu taje gurinta take faɗa masa, yau dai bai ji zancen taje ɗin ba daman kuma yasan da wuya wai gurguwa da auren nesa. Shukuriyya ta zuba masa abincin tuwon semo da miyar ɗanyar kuɓewa shi mutum ne mai son abincin gargajiya kwarai da gaske ya saba tun a wajen Amminsa, hakan yasa yaci tuwon sosai daman wunin yau ba ya ce yaci wani abu da zai riƙe masa ciki ba.
‎
‎"Na gode."
‎
‎Ya furta cikin sanyin murya idanuwansa akan Shukuriyya wacce tayi murmushi tare da mayar da idanuwanta ƙasa, shima murmushin ya tsinci kan shi da yi, har kullum yana ƙara godewa da ni'imar da Allah ya yi masa na haɗa shi aure da Shukuriyya tana da kunya, har yanzu ba ta iya haɗa idanuwa sosai da shi duk kuwa da sun haifi Ayrah ya lura kunya halittar ta ce, tana haƙuri da shi shi ya sani don yadda yake ba aikinsa lokaci nata lokacin kaɗanne a ciki, amma ba ta taɓa masa ƙorafi ba, zai iya cewa a duk zamansu lokuta ƙalilan ne zaka ga fushinta, akan Murjanatu ne da a baya duk idan taje gidan to fa ranar zai gane ba ta cikin walwala haka ta dinga fushi da shi amma kuma da an kwana komi sai ya wuce, ya sani Shukuriyya na da kishi a kan shi amma tana ƙoƙarin danne abubuwa da yawa hakan kuwa na ƙara mata kima a zuciyarsa. Amma duk da yadda yake ƙoƙarin mayar da hankalinsa kan Shukuriyya tunaninsa yana yawo ne a kwanyar kansa, lambobin da ke cikin takardun binciken, kayan da aka ce an saya da kuma aikin makarantar da bai kai yadda ya kamata ba kwata-kwata haka ma'aikacin da aka kama yana ƙoƙarin goge bayanan, sai kuma Murjanatu eh tabbas ita, kewaye yake a kwanyar kansa domin gane wane ne abin zargi a cikinsu, amma fuskar ta kawai ke haska masa, Shukuriyya ta lura kamar yana cikin damuwa, murya ta a sanyaye take tambayarsa.
‎
‎"Lafiya Yallaɓai?"
‎
‎Ya ɗan ɗago ya zuba mata idanuwansa masu sakar mata da kasala lokaci guda.
‎
‎"Lafiya ƙalau madam."
‎
‎"Ka gaji ne har haka? Ya kamata ka samu ka huta, kwana biyun nan na lura kanka ya ɗauki zafi."
‎
‎"Eh to na ɗan kaji amma kaɗan."
‎
‎Ya kashe mata ido ɗaya da yasaka dariya har sai da fararen haƙoranta suka bayyana tare da siririyar wushiryar tsakannanin haƙoranta wacce ke ƙarawa fuskarta kyau idan tana dariya, ganin yadda take dariyar sai ya tsinci kansa da farin ciki shima ya biye mata duk da shi murmushi yake ba dariya ba.
‎
‎Ayrah da ke kusa da shi ya duba cikin natsuwarsa ya ce,
‎
‎"To gimbiya Daddy zai tafi masallaci."
‎
‎"Sai ga dawo Daddy nima zamu yi sallah da Mummy"
‎
‎Ta ƙarashe tana kallon fuskar Shukuriyya wacce ta ɗaga mata kai da sauri tana murmushi.
‎
‎"In sha Allah gimbiya."
‎
‎"Ka yi mini addu'a Daddy."
‎
‎"Allah ya ƙara miki ilimi da hazaƙa, ya raya mini ke naga kin zama babbar likita gimbiyar Daddynta."
‎
‎"Amin Daddyna!"
‎
‎Daga haka ya tashi ya nufi masallaci Shukuriyya na bin shi da addu'ar sauka lafiya da dawowa lafiya.
‎
‎Bayan sallar Isha'i Nazifi suka shugo gidan tare da Abba, Alhaji Al-Hassan mahaifinsa, ɓangaren Ammin suka shiga, nan ya tayasu hira har wajen goma saura ya sha shayin Ammi mai daɗi irin wanda take haɗawa Abba kafin ya musu sallama ya koma ɓangarensa cike da addu'arsu.
‎
‎Da ya shiga ya tarar Ayrah har lokacin ba ta yi bacci ba.
‎
‎"Ba ki kwanta ba gimbiya?"
‎
‎Ta miƙe ta nufe shi da gudu tana faɗawa jikinsa.
‎
‎"Ina jiranka Daddy."
‎
‎Nazifi ya ɗauke ta tare da rungumeta ƙirjinsa ya fara buga bayanta a hankali bayan ya zauna saman kujera, lokaci guda kuwa bacci ya kwashe ta, ya lallaɓa ta a hankali ya kai ta ɗakinta ya kwantar da ita kan gadonta, ya lulluɓe ta sannan ya rage ƙarfin AC saboda sanyin da akayi yau, ya fita tare da rufe mata ƙofar a hankali. Kai tsaye ɗakinsa ya koma Shukuriyya zaune tana jiran sa.
‎
‎"Ta yi baccin?"
‎
‎"Eh."
‎
‎Ya amsa ta tare da zaunawa gefen gadon, sai shiru ya biyo bayan amsar tashi, Shukuriyya ta lura cewa hankalin mijinta yana wani gurin sakamakon yadda ya zubawa laptop ɗinsa da ya jawo ido.
‎
‎"Ba aikin ne ya fi damuna ba Shukuriyya, face abin da ban sani ba game da binciken nan."
‎
‎Shukuriyya ba ta fahimci abin da yake mata magana a kai ba, tasan dai da ita yake saboda yadda ya ɗago daga laptop ɗinsa ya zuba mata ido, ita ma namujiyar ta zuba mishi cike da son jin ƙarin bayani daga gare shi, lura da hakan ne ya saka shi kama yatsun hannunta yana matsawa a hankali.
‎
‎"Mutane da yawa suna iya yin ƙarya idan ana tambayarsu, wataƙila mutum gaskiyarsa yake faɗa ko kuma akasin hakan, kaina ya kulle matuƙa muka ina son na gano gaskiya da wuri don bana son binciken nan ya ɗauki wani lokaci."
‎
‎Murmushin ta saki, cike da son ƙara masa kwarin gwiwa ta ce,
‎"Daddyn Ayrata fa jarumi ne, kuma babban jami'in da aka shaida cewa muddin ya saka abu gaba sai ya ga abin da ya turewa buzu naɗi, wannan ma ina da tabbacin za kayi nasara."
‎
‎Tana ƙarashe maganar tare da zame hannuwanta daga nashi, ta kwanta gefensa tana faɗin.
‎"Allah ya baka nasara a wannan aikin Daddy Ayrah".
‎
‎Murya a sanyaye ya amsa da amin, kuma yana jin daɗin yadda take fahimtar sa tare da yi masa uzuri a duk irin wannan yanayin
‎Ya miƙe ya buɗe jakar aikinsa.
‎
‎Nan take kuwa ya zaro wasu fayiloli, ya shimfiɗa su a kan tebur sai ya fara nazarinsu akwai sunayen mutane da yawa shugaban kamfanin, shugaban sashen kuɗi, mai kula da kayan aiki da jami'in da ke kula da kwangilar, Murjanatu ce sai wasu sunaye da ke cikin takardun biyan kuɗi Nazifi ya fara haɗa bayanan su duka a cikin zuciyarsa.
‎
‎Fitilar gefen gadonsa ce ya ragewa haske don Shukuriyya ta samu bacci, fayilolin binciken da ya shimfiɗe su a kan tebur suna gurin amma a lokacin yana ƙoƙarin haɗa abubuwan da suka warwatse ne a cikin kansa zuwa abu guda domin kamo bakin zaren.
‎
‎Ya ɗauki takardar da ke ɗauke da jerin mutanen da suka sa hannu a kan takardun aikin ya sake kallon sunan farko sai na biyu sannan na uku, ya yi ƙoƙarin tunawa da yadda kowannensu ya kasance a lokacin da suka zauna a ɗakin taron, wanda ya fi yawan magana a cikinsu da kuma waɗanda suka yi shiru zuwa waɗanda suka yi gaggawar kare kansa a lokacin, ya san wani abu mai muhimmanci a irin wannan bincike, sau da yawa wanda ya fi ƙoƙarin nuna cewa ba shi da hannu a cikin wani abu, ba lallai ne ya zama mai laifi ba, haka nan wanda ya yi shiru ba lallai ne ya zama marar laifi ba saboda haka dole ya yi nazari sosai, bai son yanke hukunci lokaci guda haka, yana kuma son tsara abubuwan da ya kamata ya gudanar a gobe idan Allah ya kai mu, domin ɗaurawa daga inda ya tsaya har sai ya ga abin da ya turewa buzu naɗi.
‎
‎Dole ne su sake duba bayanan banki kuma a tantance dukkan sa hannun da ke kan takardun, kuma a binciki wanda ya ba da umarnin biyan kuɗaɗen a dawo da ma'aikacin da aka kama yana goge bayanai domin a sake yi masa tambayoyi haka a ware duk mutanen da suka samu damar shiga bayanan kwangilar.
‎
‎Murjanatu kuwa daman dole ne a sake tantance dukkan bayanan da suka shafe ta, ai ya sauke numfashi yana gyaɗa kai tare da ambatar sunan nata a fili amnma a hankali ta yadda ko da ace Shukuriyya idon ta biyu ba lallai taji me yake cewa ba.
‎
‎"Murjanat!"
‎
‎Ya ƙara ambata, ba ya son a ce saboda tsohuwar alaƙarsu ya yi mata sassauci, haka kuma ba ya son ya zamana kamar yana neman hanyar da zai cutar da ita ba ma zai iya ba har abada, abin da yake so shi ne gaskiya, kawai gaskiya ya yake buƙata ya rufe fayilolin sannan ya kashe fitilar gabakiɗaya tare da tofa addu'a Shukuriyya tana kusa da shi, ya manna ta da jikinta yana ƙara jin nutsuwa na shigarsa. Ita kuwa kuwa daman tuni bacci ya yi awon gaba da ita.
‎
‎
‎Da asuba kiran sallah a kunnen shi, ya tashi ya shige bathroom ya ɗauro alwala sannan ya fice zuwa masallaci bayan an idar da sallah sai ya dawo gida, bai jin motsin kowa ba a falon ya shiga ɗakinsa Shukuriyya ta koma nata ɗakin ma don ko da ya shugo bai ganta ba kuma bai ji motsinta a toilet ba sai kawai ya kwanta nan take kuwa wani bacin ya ƙara ɗaukarsa, sai ƙarfe tara saura kwata Nazifi ya farka,
‎
‎Ya miƙe ya shiga banɗaki ya yi wanka, bayan ya shirya cikin wani yadi marun colour mai taushi ya fito falon, ko ina tsaf sai ƙamshin ke tashi yasan aikin masu taya Shukuriyya kula da gidan ne, amma ita da kanta ke shiga kitchen tayi masa girki sai su gyara kitchen ɗin da su wanke-wanke, tayi wankata cikin shigar abaya baƙa da tayi mata kyau kasancewarta mai hasken fata.
‎
‎"Ka tashi Yallaɓai, barka da fitowa"
‎
‎
‎"Barka Shukuriyya sannu da ƙoƙari"
‎
‎Nan suka gaisa yana ƙarasawa gurin cin abincin, bayan sun zauna ta zuba masa arish da soyayyen kwai ne sai bread da shayin da ta haɗa masa mai kauri.
‎
‎"Ayrah tun takwas direba ya kai ta school, ta so ta ganka na ce ta bari dai sai ka dawo don kana bacci lokacin."
‎Murmushi ya sauka a fuskarsa ba tare da ya ce komi ba, ya ci gaba da breakfast ɗinsa, bayan ya gama ya tashi ya ɗauki jakar ofishinsa, sallama ya yi mata ya fice da key a hannunsa, maimakon ya nufi motarsa kai tsaye, sai ya wuce ɓangaren Ammi fuskarsa a sake  ya shiga falon.
‎
‎Ammi tana zaune tana magana da wani daga cikin yaran gidan, yayin da Alhajinsu shima zaune yake yana duba wasu takardu da fasfo a gabansa.
‎
‎Nazifi ya zauna ƙasan Ammi ya gaishe su cikin girmamawa, Alhaji ya fara amsawa yayin da Ammi ta sallami yaron da suke magana, wanda ya duƙa ya gaishe da Nazifi kafin ya fice.
‎
‎
‎"Alhajinmu ba dai tafiya zaka yi ba?"
‎
‎"Ai kuwa zanje Dubai ne zamu tattauna da wasu abokanan kasuwancina akan kwangilar da za a ba kamfanina."
‎
‎"Amma Abba ya kamata kana hutawa, Nazir duk zai iya ji da wannan fa."
‎
‎Har lokacin murmushi ne ɗauke a fuskarsa ya jinjina kai ya ce,
‎"Haka ne Nazif tabbas Nazir zai iya musamman idan da kai a gefensa, nima na san an kai wani lokaci da ya kamana na huta saboda ku, duk da kai baka ɗauki layina ba amma nasan lokaci zai zo da kai ma zaka dawo da hankalinka a kai ka ajiye wancen aikin naka, muna kan tattaunawa da shi ma akan samun sabbin ma'aikata, masu amana muke so saboda cigaban kamfaninmu Nazir ya ce ya yu magana da Mansoor ɗan'uwanku da ke Sokoto."
‎
‎Yadda Abban ya ƙarashe maganar da sauke numfashi sai duk Nazifi yaji babu daɗi, yasan tun kafin ma ya yi karatu business mahaifinsa yaso ya karanta domin ya faɗo harkar kasuwancinsa sai dai a lokacin Accounting  ya karanta sai ga shi ƙaddara ta faɗa da shi ya zamo jami'i a hukumar EFCC ba zai ce baya son kasuwanci ba domin a cikinsa ya tashi duk da ba abin da ya karanta ba ne amma yana da ilmi sosai a kai ko don shi mutum ne mai ƙwaƙwalwa oho amma ya sani haka da yawa sun sani yana da wata irin ƙwaƙwalwa mai ɗaukar abubuwa nan take, shi ya sa ma Abban yaso ace shine zai gaje shi, sai ga shi Nazir ƙaninsa shi ke ƙoƙarin kamanta aiyukan Abban.
‎
‎Ammi ce tayi gyaran murya ganin yadda duk kan su suka shiga tunani na wucin gadi.
‎
‎"Nazif zai yi aiki a kamfani in sha Allahu, ni kaina aikin nan nasa na bincike tsoro yake ba ni, kar yaje a ƙulla masa wata ƙulalliyar ko a nemi rayuwarsa kamar yadda aka taɓa a baya a saka mu a zullumi."
‎
‎Ganin idan ya ce zai tsaya maganar ce zata yi tsayi shi kuma yana son aikinsa ainun, sai ya miƙe yana ƙara rataya jakarsa.
‎
‎"Abba Allah ya tsare ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya, zan yi da magana da Nazir akan ma'aikatan da za a samu masu inganci in sha Allah."
‎
‎Ya kalli Ammin yana ɗan ranƙwafowa.
‎
‎"Ammi a sakamu addu'a wani aiki nake yi yanzu haka, ina fatan idan Allah ya ba ni nasara a aikin zan ajiye aikin na kama na Abba ka'in da na'in in sha Allahu."
‎
‎Lokaci guda Abba da Ammin suka masa addu'ar nasara cike da jin daɗin furucinsa na ƙarshe, zai fita suka haɗu da Nazir zai shugo, gaisawa suka yi Nazif na tabbatar masa yana son ganinsa idan ya dawo gida, shiga ciki ya yi yana ɗan ɓata rai yasan maganar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi magana zai masa akan aure shi kuma bai shirya hakan ba a yanzu ya rasa me yasa yayan nasa ke son takura masa akan ya yi aure, ko yasan abubuwan da yake na holewa ne, da sauri ya kama bakinsa baya fatan yayan nasa yasan komi da halayensa, sai yaji gabansa na faɗuwa idan ya zamana ya gano maganar da yake so suyi fa kenan, nan take cikinsa ya ɗuri ruwa don yana matuƙar ƙaunar yayan nasa baya son abin da zai haɗasu ko kuma ya gane abin da yake yi, ina zai saka kansa idan hakan ta kasance?
‎
‎Nazifi na ƙarasawa harabar gidan, cikin motarsa ya shiga ya yi mata key ya fita gidan a sittin..
‎
‎
‎Sadiya.
‎Duk a tunaninta Sadauki zai zo gidansu ya ganta ko kuma yazo gurin suya ko lambarta ce ya amsa sai ya kirata amma shiru babu wani labari, duk da cewa ita ce ta ba shi kwana takwas ya yanke hukunci amma ba tayi zaton zai ƙi zuwa ba, ko ba ta kai yaso ta ba ne? Haka kawai taji gabanta na faɗuwa a daren da tayu tunanin nan kuwa tasha kuka sosai, ita dai Allah ne ya ɗaura mata ƙaunar Sadauki kuma ba ta fatan ya ce bai amince ba, a kan soyayyarsa zata iya aikata koma mene ne domin cikar burinta, yadda tayi lamo a katifarsu ko wayar ta kasa dannawa ta kalli Tiktok ɗin da yake rage mata kewa balle kuma series hausa film ɗin da take kallo, wayarta ce taga fitilar bayan na haske, alamar ana kiranta kenan don a salent take barin wayarta.
‎
‎Tana dubawa kuwa taga Alhaji Bashar ne, sai da tayi mamakin da daren nan yake kiranta haka, ta juya ta kalli gadon Hauwa, baccinta take hani'an tana sakin munshari, haka ƙannanta mata da suke kwanciya tare. Ta danna wayar tare da karawa a kunnenta.
‎
‎"Alhajin Allah sai yau?"
‎
‎Ƙwarai yaji mamakin yadda ta kira shi, don a baya idan ya kirata ta ɗauka ko magana yake daga uhmm sai uhmm uhmmm, yau har da kiransa Alhajin Allah kamar wata mai buɗaɗɗen idon? Ai shi idan idon ma nata za a buɗe da sai yafi kowa farin ciki.
‎
‎"Sadey beb ashe baki yi bacci ba?"
‎
‎Shima ya tambayeta cike da duniyanci.
‎
‎"Ina zan iya bacci ina tunanin Alhajina yana wata ƙasar, ga shi ya ce sai ya samu dama zai iya kirana tsawon sati guda."
‎
‎Ai wata shegiyar dariya irin ta Alhajin duniya ya ce.
‎
‎"Kai Sadey ke ce kuwa? Ko dai tafiyar nan da nayi aka sauya mini wata?"
‎
‎Ita kanta mamakin kanta take, amma ta sani muddin tana son faranta ran Sadauki ta samar masa kuɗin da ya buƙata to fa shuru-shuru ba nata ba ne, dole sai ta saki jikinta ne zata iya cin kuɗaɗen nan.
‎
‎"Ni ce dai Alhajina, kasan fa na ƙosa ka dawo, akwai wata magana ma da zamu yi amma sai ka dawo ɗin."
‎
‎"Kar ki sami damuwa ai kamar yau ne sati gudan ba ga shi har nayi kwana uku ba yau, Allah ya sa dai za a amnshi buƙata ta na jiyarar gidan hutuna ce?"
‎
‎"Alhaji kenan ai koma me ka ke so za a yi maka, amma dai sai ka dawo ɗin tukunna!"
‎
‎Ya sauke wani numfashin da har tana jiyo shi ta cikin wayar, a ransa kuwa yana ayyana ashe damo ya kusan kaiwa ga harawa ko bai ci ba zai sha ɓarna, ya saki wata dariyar da shi yasan manufarta, ita ma tana binshi da murmushi.
‎
‎"Kin ga matsalar rashin account baki da account number da na saka miki wani abu, amma nasan kina da katin ɗan ƙasa ko? Ina dawowa sai a buɗe miki idan kuma kina son Opay ne ko sauran irin na intenat ai sai ki samu wanda ya iya anan kusa ya buɗe miki da lambarki tunda akwai waya hannunki."
‎
‎"Eh ina da katin ɗan ƙasa har ma da na zaɓe, zan tambaya gobe sai nayi."
‎
‎"Yauwa haka dai ya kamata, bari na barki haka babyna."
‎
‎Sallama suka yi tabi wayar da kallo da tuna yadda Alhaji Bashar ke kiranta da babyna tsofai-tsofai ko kunya ba yaji mai budurwar zuciya kawai, haka ta kwanta cikin farin ciki ko ba komi zata cikawa Sadaukinta buri kuma tana da yaƙinin zai zaɓi aurenta, da wannan tunanin bacci mai daɗi ya yi awon gaba da ita....
‎
Gobe ne! Daga gobe fa!!! shin kun biya ko har yanzu kuna jira??? To kuyi gaggawar tura kuɗin karatunku kar ayi babu ku!

*Littafin Farar tumfafiya na kuɗi ne, free pages zai ƙare ne a 15 pages don haka masu buƙatar saya za su tura 700 ne a yanzu, idan mun kammala free pages kuɗin littafin 1k za a tura kai tsaye ta 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC sai shaidar biya ta *** kar ku bari wannan damar ta wuce ku, farar tumfafiya har yanzu sharar fage muke.*


Kuna da labarin UmmuAffan GHT Supplement, tana sayar da Supplement na kamfanin ght masu kyau da inganci tana garin Kaduna tana aika kayanta duk inda kuke a faɗin ƙasar nan dama wajen ƙasar nan, kai tsaye kuyi mata magana ta lambar waya kamar haka *** sayen na gari mai da kuɗi gida, sai kunzo.