FARAR TUMFAFIYA

Page 15

by @ummuaffan

‎....FARAR TUMFAFIYA.
‎
‎
‎
‎
‎©UMMU AFFAN
‎
‎
‎
‎Page *15*
‎
‎
‎
‎_Anan na kawo ƙarshen littafi na ɗaya wanda ya zamo free pages, I hope you will continue to follow me as we move forward, because this is only the beginning of the story ba muyi komi ba yanzu muka fara, yanzu za mu fara cakwakiyar and there is still much more to come as we continue this struggle together._
‎
‎_Ku tura kuɗinku kai tsaye ta 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Shaidar biya ta *** 1k whatsApp 'yan'uwanmu mutanen Nijar kai tsaye zaku tura da 500f ta My Nita +227 99 53 98 24 sai ku tura shaidar biya ta ***_
‎
‎
‎
‎
‎Barirah.
‎Zazzafan marukan da taji a duka kuncinanta biyun kuma lokaci guda su ne suka ɗauke mata ji da ganinta na wucin gadi, kuma duk wata magana da akayi bayan nan na kusan sakon goma ba taji komi ba, ba ta gama dawowa hayyacinta ta sake jin wasu marukan, ai a wannan lokacin sai ta ga wasu taurari na gilmamata kafin ganinta ya ɗauke lokaci guda duhu ya mamaye ko ina.
‎
‎"Har yanzu ba ta farfaɗo ba ne?"
‎
‎Taji saukar tambayar tamkar saukar aradu a ka, da ace tasan abin da zai kuma faruwa jin cewa ta farfaɗo da ta roƙi Allah tayi ta zama a sumen da take, muryar Kawu Habulen ta sake mamaye duniyarta da sabon duhun da ya saka cikinta murɗewa lokaci guda.
‎
‎"Mutumin da muke jira Ubale da zai auri Barirah ya iso, ina Balarabe maza fito muje a ɗaura kar a kuma wani rashin."
‎
‎
‎Ba tasam Kawu Balaraben yana ɗakin da suke ciki ba sai da taji takun tafiyarsa yana fita, ta ɗago a hankali sai ta ga Iyah ce a gefenta ta zuba uban tagumi kuma babu kowa a ɗakin sai su.
‎
‎"Me ya faru Iyah? Me ya faru da ni Iyah?"
‎
‎Da sauri Iyah ta ƙarasa jikinta ta rungume ta, sai Barirah ta fashe da kuka ita ma Iyahn kukan take.
‎
‎"Tasi'u ɗan Kawunki Habule ne Allah ya yiwa rasuwa daga ya ga takalminki gurin mota ya ɗauka!"
‎
‎Ƙirjin Barirah ya buga da ƙarfi ta kuma rushewa da kuka, wai abin da ya faru kenan ita kuwa wacce mummunar ƙaddara ce ke bibiyarta? Shin da gaske kenan dai ita ɗin mayya ce mai cin mutane.
‎
‎Lokacin da su Kawu suka shugo cikin gidan, kai tsaye ɗakin Atika ya shiga da Tase ya kwantar da shi kan tabarma Atika da ke gefe zaune ta ƙaraso gurin da sauri ta fara zare ido da tambatar lafiya me ya samu Tasen ta tana tattaɓa shi.
‎
‎"Wai daga ya ɗauki takalmin Barirah a ƙofar gida ya faɗi, kuma fa faɗi ake kamar ya mutu!"
‎
‎Shima ya ƙarashe maganar jiki a sanyaye, domin suna ƙaunar Tase duk da kasancewarsa ƙarami kuma shine ɗa ɗaya tilo namiji da suka haifa sauran duk mata ne, shi ya sa suka ɗauli son duniya suka ɗaurawa Tase sai ga shi ashe ƙaddarar mutuwarsa a kusa take, ashe ba zai girma Kawu Habule ya sami magaji shima namiji ba kamar yadda yake faɗi, ai wata kururuwa da Atika tayi ita ta dawo da hankulan mutanen gidan kansu, daman Kawu Batule da Balarabe suna tsaye cirko-cirko a ƙofar ɗakin dukansu sun rasa abin yi, don shi kam Kawu Bature jira yake yaji ya za a yi domin a ransa ya gama shirya tafiyar Barirah dole fa ta fita ta bar musu gida don kar a kuma, tun da ta cinye yaran Balarabe duk ƙaunar da yake mata da tausayinta da yake ɗan uban waye ba zata ci ba.
‎
‎Atika da suka ga ta fito a fusace ne suka bi bayanta, ɗakin Hajara ta shiga inda su Barirah suke, tana shiga ba tayi wata-wata ba ta saukewa Barirah maruka har huɗun nan, duk da ta sume hakan bai hana taƙi rufe ko ina na jikinta da bugu ba.
‎
‎"Da hahuwar irinki gara ɓarinki, Tsaiba ta bar miki mugun abin da ba zai fita jikinki ba, Alɗah wadaran halinki, Tasi'u me ya miki da zaki kashe shi? Allah ya isa tsakanni na da ke shaiɗani muguwa. Kin gama da 'ya'yan Rakiya zaki dawo kan nawa wallahi yau sai kema na kashe ki."
‎
‎Duk maganar da take dukan Barirah take da ƙyar Iyah ta ɓanɓareta jikin Barirah tana faɗa mata ba ta motsi fa amma ba ta fasa abin da take ba, bayan Iyah ta mayar da ita gefe tayi kan Barirah tana kuka, haka aka zo aka fitar da Atika.
‎
‎
‎Nan suturta Tasi'u aka kai shi gidansa na gaskiya, gaɓaɗaya kuwa garin ya ɗauki cewa ɗiyar Tsaiba ce ta dawo za a aurar da ita kuma mayya ce, ita ce ma ta cinye Tase, nan fa ƙaramar magana ta zama babba, hatta su Kawu sai ake musu ɗan kallo.
‎
‎Suna zaune ƙofar gidan sai ga Ubale yazo afuzazan, da sauri suka tarbe shi babu kamar Kawu Bature ma da jininsa yake bisa farce.
‎
‎"Yauwa daman kai muke jira tashi muje a ɗaura auren!"
‎Faɗar Kawu Bature jikinsa har rawa yake yana ƙoƙarin miƙewa, har ga Allah a tsorace yake da lamarin yadda ta kashe Tase kar shima abin ya faɗa kansa, ga shi yadda ya ga jikin Kawu Habule ya yi sanyi matuƙa yasan dole yaji mutuwar, gabaɗaya burinsa akan Tasi'u ne ɗansa ɗaya namiji da Allah ya ba shi sai ga shi lokaci guda wai ya mutu, ko sun manta da Allah ne oho, wanda yake rayawa kuma yake kashewa wannan rashin tauhidi ne sosai. Shi ne fa Kawu Habule ya miƙe da sauri ya shiga ciki ya kira Kawu Balaraben cewa ya fito Ubale ya ƙaraso, bayan fitowarsu zama suka yi.
‎
‎Ubale ya gyara zamansa ya ce,
‎"Tukunna dai, kusan al'adar garinmu ce ba ka aure wani yare da ba naka ba, to an ɗan fafata sosai amma yarinyar ba ance ɗiyar Runduna ba ce?"
‎
‎Gabaɗaya sai da cikinsu ya bada wani sauti jin an ambaci sunan Runduna, cikin kwarin gwiwa da sanyin jiki Kawu Balarabe ya ce,
‎
‎" 'Yarsa ce kuma kana da ikon aurenta tunda ƙabilarku ce, duk abin da nake ina lissafi Ubale, duk lalacewar Barirah 'yar ƙanwarmu ce mace ɗaya da tazamo cikon ta huɗu gare mu, nasan me nake nasan kai ɗan ƘUSA ne kuma na amince da haɗin ne don nasan Barirah 'yar cikinku ce 'yar Runduna ce kuma shima ɗan Ƙusa ne."
‎
‎Gabaɗaya gurin ya ɗauki shuru, Ubale ya ce, "To to hakan ya yi tunda har ɗiyarsa ce na yarda za a ɗaura, amma zaku ƙara mini kwana ɗaya zuwa gobe zan dawo, zan sanar da mai garinmu zan aureta a haka saboda ɗiyar Runduna ce gobe zan dawo a ɗaura aure."
‎
‎Dukansu zubawa Ubale ido suka yi jikinsu a mugun sanyaye, Kawu Bature cikinsa yafi na kowa ɗurar ruwa, yanzu idan Barirah ta kwana gidan nan tabbas yasan ɗansa za ta ɗauka a kanshi zata dawo, sai ya yi saurin yun magana cikin rawar baki.
‎
‎"Za...mu...baka damar tafiya da Barirah 'yan uwanka su ganta sosai alabashi goben sai ku dawo tare a ɗaura muku auren."
‎
‎Guri ya ɗauki shuru, musamman Kawu Balarabe da ya yi ƙasa da kansa, ciwo yake ji sosai, sannan a yau yaso su koma gida saboda su ɗauki Usman su kai shi gurin malamin nan ya ba su magani ko addu'o'in da za a riƙa masa. Baya so ko kaɗan ya kwana a garin nan, idan har sai gobe ne, to fa dole ya kasance shima ya koma gida goben ya dawo.
‎
‎Sauran kuwa Ubale suka zubawa ido suna cike da yaƙinin Allah ya sa ya amince da batun Kawu Baturen domin ita ce kawai mafitar da zasu samu na kwanan Barirah cikin gidan nasu.
‎
‎"To idan hakan kuke ga ya yi, ba matsala sai mu tafin ai."
‎
‎Har sun fara washe haƙoran murna Kawu Balarabe ya ce,
‎"Ba zai yuwu a ba shi yarinya budurwa ba ya ace ya tafi da ita gobe ya dawo da ita, wannan ba mai yuwuwa ba ne, ya dawo dai goben idan an ɗaura auren sai su tafi."
‎
‎"Haba Balarabe! Ya ka ke abu kamar baka san komi ba? Maganar gaskiya idan bai tafi da ita ba to ya tsaya a ɗaura auren sai ya tafi da ita kawai."
‎
‎"A ɗaura aure su tafi? Yaya Bature kayi maganar hankali anan, ince ana yinin biki da wankin amarya? Ko da naa ce a ɗaura aure a yau nufina gobe sai ayi yini da sauran al'adu mu saya mata kayan ɗaki sai ayi mata rakiya aga inda take kamar sauran amare, wai ƙiyayyarmu da Tsaiba har ta kai haka?"
‎
‎Zuwa lokacin Kawu Bature ya gama harzuƙa da kalaman ƙanin nasa, don haka murya a ɗage yake daɗin.
‎
‎"Eh dole ka ce haka, ddaman masu iya magana na faɗin idan tsautsayi ya wuce ta kanka ya faɗa ko akan uban waye, tunda kaima duk ta ƙarar maka da yara muma kenan mu dawo daidai da kai, ban ce ba zamu yi wunin biki ba, za a yi goben amma fa bayan an kaita yau, Tsaiba kuwa kome muka yiwa 'yarta ai ita ta zawo komi ita ce silar komi ka sani ba sai na nanata maka ba, barewa ba za tayi gudu ɗanta ya yi rarrafe ba, wannan ba sabon abu ba ne."
‎
‎Kawu Habule kam gyaɗa kai kawai yake kamar ƙadangare babu baka sai kunne don magana ma wahala take yi masa sakamakon mutuwar Tase shima ya ji a ransa muddin suka bar Barirah a gidan wasu za ta ƙara ci, wannan dalilin ne ya saka ana kiran sallar la'asar Kawu Bature ne ya zamo wakilin Ubale yayin da Kawu Balarabe ya zama wakilin Barirah aka ɗaura auren akan sadaki dubu talatin wanda shi Kawu Balaraben ne ma ya biya masa sadakin, nan suka shaida auren sannan fa duka suka ji hankalinsu ya kwanta, suna dawowa kuwa Kawu Baturen noe ya shiga ya ce bari ya kirawo  ta suka ma hanya su tafi, Kawu Balarabe ya zauna saman tabarma jikinsa duk a mace shin ya kyauta kuwa? Daidai ne ya haɗa Barirah da wannan mutumin? Shin ya kamata ma su mayar da Barirah ƘUSA bayan sun san komi? Me ya shiga cikinsa ne har haka? 
‎
‎"Kashe maka yara da take.''
‎
‎Kawu Habule da ke gefensa ya amsa masa, sai lokacin ya gane a fili kenan yake don da farko ya son a zuci ya fara. Ya gyaɗa kai cike da gamsuwa da maganar Habulen, sunan zaune kusan minti ashirin bayan shigar Kawu Bature amma shuru bai fito ba.
‎
‎Miƙewa suka yi har Ubalen suka ce ya shugo ciki suje, suna shiga kuwa yadda suka ga Kawu Bature kwance ƙofar ɗakin Hajara yana burgima kaamar ƙaramin yaro hankalinsu ya tashi sosai, da sauri suka ƙarasa gabansu, don Atika Hajara da wasu mata da suka shugo gaisuwa duk suna gurin tsaye suna sallalami babu wanda ya iya ƙarasa kusa da shi.
‎
‎Iyah da Barirah suma suna gurin zaune, sai dai abin mamaki Iyah ta saka niƙaf a fuskarta, Kawu Balarabe yasan tana sakawa amma sai idan za taje danginta yana ganin tana sawa amma a gida haka bai taɓa gani ba, ba su damu da yadda suka gantan ba da sauri suka yi kan Kawu Bature, sai dai kafin su ƙarasa Kawu Habule da ke gaba shima ƙafarsa ta maƙale ya fara rawar disko a tsayen da yake tamkar wanda shokin ɗin nepa ya kama. Cak Kawu Balarabe ya tsaya cike da al'ajabi, mata kuwa tuni suka fara ja baya cikin tsoro, Ubale ne ya ƙarasa gurin ya yi wasu surkullensu sai ga shi duka sun daina rawar diskon Kawu Bature yana tashi ya ce ƙafa mai naci ban baki ba, da mugun gudu ko nauyin jikinsa baya ji ya ruga ɗakin yaransa ji kake ɓaram ya rufe ƙofar, ai Kawu Habule ma ture mata ya yi ya shige ɗakin Atika ya rufe, ai ganin haka nan mata suka fara gudu masu fita nayi masu shigewa wasu ɗakin nayi, aka bar Ubale Iyah Barirah da Kawu Balarabe tsaye a gurin..
‎
‎"Wai me ke faruwa ne?"
‎
‎Ya tambaya yana kallon Iyah wacce tunda suka shugo idanuwanta ke kan Ubale, yana juyowa zasu haɗa ido kuwa ta kamar da tana gefe.
‎
‎"Sabuwa ke fa nake tambaya me ya faru da su Yaya Bature."
‎
‎
‎Kafin tayi magana Ubale ya rigata tankawa.
‎
‎"Gaskiya Barirah tana da tsafi irin na mahaufinta Runduna, shiga da ita yankin Ƙusa akwai matsala domin ba za a wanye lafiya ba."
‎
‎Kawu Bature daga ƙuryar ɗaki yake faɗin.
‎
‎"Balarabe ka ce Ubale ya ɗauketa su wuce, su fita kawai wannan yarinyar zata iya kashe kowa a cikin gidan nan."
‎
‎Kawu Balarabe ya yi jugun yana bin Barirah da ido, shi kanshi a hargitse yake ji yake da za a kuma cewa kule zai antaya ne a guje, gabaɗaya jikinsa rawa yake.
‎
‎Lokacin da Kawu Bature ya shugo gidan da niyar Barirah ta fito su tafi, ba tayi musu ba ta miƙe, Iya ta ɗauko niƙab ɗinta cikin jakar da tazo da ita ta ce, ita ma za tayi mata rakiya ai ba a barta ita ɗaya su tafi da Ubale, duk rashin gatanta dai ai a rakata ɗakinta, kuma tana da yaƙinin Kawu Balarabe zai mata kayan ɗaki ba za a kaita daga ita sai halinta ba.
‎
‎Suna fitowa Barirah ta ɗaga ido ta kalli Kawun sai kawai ya fara rawa da girgiza.
‎
‎" 'Yar fires kasuwan mata, nawa ne, ashirin da biyar, sha biyar banga dama ba, to na tafi, haba baby baby zo ki hau!"
‎
‎Waƙar da Kawu Baturen ya fara kenan yana wata irin girgiza da ta saka matan da ke ciki fitowa.
‎
‎"Mage a hammatar ɓera, jaɓa tana musu fiffita, ringin-ringingin-ringin-ringingin."
‎
‎Wata irin rawa yake yana waƙar nan har da zubewa ƙasa kuma bai fasa rawar a kwance ba, nan fa mata suka hau sallallami Sule yana dariya ya ce.
‎
‎"Lah ashe Baba ya iya rawa da waƙa haka?"'
‎
‎Hajara ce ta bige masa baki tana jawo shi jikinta don tsoro taji matuƙa tasan ba haka banza ba yake wannan abin ba, musamman da taga Barirah a gurin. Atika kuwa ta ce,
‎
‎"Ke kam Barirah me dangin Tsaiba suka miki da zafi haka da ki ke musu ɗauki ɗai ɗaya? Shima Yaya Baturen ba zaki bar shi ba? Me kika saka masa haka?"
‎
‎Barirah ta fara kuka tare da zubewa gurin da take tsaye tana kukan, Iyah ta duƙa kusa da ita fuskarta cike da damuwa, daidai nan su Kawu Balarabe suka shugo suka ga abin da ke faruwa.
‎
‎"Ke Barirah tashi ki bi mijinki ga shinan Ubale an ɗaura muku aure yau."
‎
‎Ya miƙa mata dubu talatin ɗin yana cigaba da cewa.
‎
‎"Ga kuɗin sadakin ki nan ko wata sana'ar ce idan kin je can zaki fara."
‎
‎Ya kalli Ubale, gobe ka same ni  a can gidana a Sokoto kazo da wuri zamuje wajen da za a saya mata kayan ɗaki da na amfanin gida sai ku tafi da su a saka mata a ɗakin nata."
‎
‎Ubale ya jinjina kai, duk da yasan ba zai ce bai ji maganarsa ba akan da matsala muddin tana da tsafi mai ƙarfi haka amma bai musa ba, idonsa a kuɗin da yaga an bawa Barirah ga kuma kaya da yaji ance yazo ya amsar mata, yasan watan arziƙinsa ne ya kama sai ya hau washe baki.
‎
‎"Taso mu tafi Barirah."
‎
‎Babu musu ta miƙe har lokacin kuka take, Iyah tayi hanzarin bin bayanta.
‎
‎"Kar ki bi su!"
‎
‎Maganar Kawu ta doki kunnuwanta, kuma yana faɗa ya yi shigewarsa cikin gidan, Iyah ta fashe da kuka tana kallon yadda Barirah ke bin bayan Ubale simimi tamkar kazar da kwai ya dashewa a ciki.
‎
‎Da gudu Iyah ta koma ciki, Barirah ta juyo tabi bayanta da kallo kafin ta juya tabi bayan Ubale, duk inda suka ratsa sai a bisu da ido har suka fuce daga shiyar.
‎
‎Ƙaddara kamar tana wahalar furta abin da take son gaya Mata, kamar akwai wani abu da take ɓoye a bayan labulen rayuwarta, wani abu da ba ta shirya gani ba amma alƙalamin ƙaddararta yana ci gaba da zanawa yana rubutu a hankali kuma layi bayan layi, ba tare da ya tambaye ta ko ta shiryawa hakan ba.
‎
‎Suna tafiya ne amma  ba ta iya kallon gabanta, sakamakon yadda tunaninta ya yi nisa sosai tambayar kan ta take yi, me zata tarar a wannan ƙauyen da ba ta sani ba, shin zata tarar da mutanen da za su karɓe ta hannu biyu ko kuma zata tarar da waɗanda za su ƙita suma su kira ta da mayya mai cin mutane? Shin zata samu kwanciyar hankali ko kuwa tafiyar da take ganin kamar mafita ce za ta zama farkon sabuwar wata wahala aa gare ta? Sannaan Ubale fa, mutumin da ke amsa sunan mijinta a yau me zai zama a gare ni?
‎
‎Shin zai zama mijin marainiya mijin da zata samu mafaka a ƙarƙashin inuwarsa, wanda zata iya jingina da shi idan rayuwa ta yi mata nauyi? Ko kuwa shi ma zai zama wani ɓangare na jarabawar da ƙaddara ta tanadar mata?
‎
‎Bata san shi ba ba kuma ta san irin zuciyarsa ba, bata san yadda yake kallon duniyarta ba, sannan ba ta san ko zai kalle ta a matsayin matar da aka aura masa ne kawai a wulaƙance mara gata da galihu ba.
‎
‎Ta sauke wani dogon numfashi lokacin da wasu zafafan hawaye ke bin kurmin idanuwanta, abin da na sani shi ne zata bi shi za ta tafi wurinsa, kuma wataƙila a gare shi ne zata fara samun wannan sassaucin da bata zame shi ba a nata dangin. 
‎
‎'To idan yazo a akasin haka fa.'
‎
‎Wani ɓarin na zuciyarta ya tuntuɓeta da sauri tun kafin tayi nisa a lissafin rayuwarta
‎
‎Gaba kura baya sayaki kenan ta murmusa cikin jin wani abu da ya tokare mata a wuya, shi bai fito ba kuma bai shige ciki ba.
‎
‎Ƙaddara ba abu ba ce da zata iya ɗauka ta ajiye a gefe ba don idan duniya ta tsaneka ko barkono ka kasa sai ace ba shi da yaji saboda haka a shirye take da ɗaukar komi za kuma ta rungumi duk yadda ƙaddara ta bata nata kason kuma ta yarda cewa Allah Ya fi ta sanin abin da ya dace da ita. Ta tsinci bakinta na furta.
‎
‎"Ya Allah idan wannan tafiyar alkhairi ce a gare ni ka sauƙaƙa min ita, idan akwai wahala a cikinta ka ba ni ƙarfin jurewa idan akwai mutanen da za su ƙi ni ka sanyaya mini zuciyata idan akwai waɗanda zasu cutar da ni ka kare ni daga sharrinsu ya Allah ka sanya in yarda da ƙaddarar da ka zana mini, Allahumma ajurni fi musibati, wakhluf li khairan minha."
‎
‎Ubale ya juyo kanta lokaci guda suka haɗa ido, sai da gabanta ya faɗi domin bata taɓa kallonsa ba irin yanzu, to yaushe ma suka haɗu, zuwansa na farko a furgice take ranar ba ta iya ɗagowa ta kalle shi ba, haka ko da Kawu Balarabe ya ce ta tashi tabi mijinta bayan shi kawai take bi ba tare da ta kalli fuskarsa ba. Jajayen idanuwanta sun fi komi ba ta tsoro ashe ba yaro ba ne don wannan tana da yaƙinin zai iya girman Kawu Bature ma ba ƙannansa ba, sai taji hankalinta ya sake tashi, ina zata kai wannan mutumin, kuma da gaske shine mijinta? Bawai ƙato ba ne, ba shi da wani jiki ɗan tsamurmuri ne amma fatarsa duk ta wani tattamuƙe alamun tsufa, miƙa mata hannu ya yi fuskarsa a ɗaure.
‎
‎"Ba ni kuɗin da aka ba ki."
‎
‎Babu musu ta miƙa masa jikinta na rawa, yana amsa kuwa ya saka wata dariya yana jujjuya kuɗin a hannunsa, mai mashin ya tsayar guda ɗaya ya ce tahau, babu musu ta hau, sai taga shima ya hau bayanta yana faɗawa mai mashin Ƙusa zai kai su.
‎
‎Wani hamami ya doki hancin Barirah wanda ta rasa gane daga ina yake sai da suka fara tafiya, warin dauɗa hamamin rana da wani irin karni gabaɗaya shi ke fitowa a jikin Ubale, ga kuma na ɗan achaɓan gaba da bayanta dai babu sauƙi, yadda taga sun ƙara nausa jeji yasa hankakinta ƙara tashi, Kalanbaina a bakin titi take, kuma yanzu yadda ake ta gine-gine har taso ta haɗe da garin Sokoton shi ya sa kai tsaye ba za ka kira garin ƙauye ba don wayewa daidai gwargwado suna da ita, ba ta ƙara sarewa ba sai da taga yadda ƙauyen yake bayan uwar tafiyar da suka ci, yanzu a garin nan za ta zauna, anan zata ƙare rayuwarta, babu titi babu nepa babu wata makaranta da zata ce ana yin karatu a garin.
‎
‎"Kizo mu tafi uban me ki ka tsaya kallo kuma?"
‎
‎Maganar da Ubale ya yi yana fincikar hannunta bayan ya biya mai babur kuɗinsa kenan, janta yake tana tafiya da sauri ga ƙasar da ke tashi gabaɗaya ta gama ɓata fuskokinsu haka hijabin jikinta da ƙasan doguwar rigar da ke jikinta.
‎
‎"Ya Ilahi!"
‎
‎Ta furta lokacin da taji ya saki hannunta wata iska da tazo tayi sama da ita ta kayar ta kuma ɗaga ta ta ƙara nanata da ƙasa, ba tasan lokacin da ta kurma wani uban ihuw na neman ceto ba.......
‎
‎
‎_Doguwar tafiya ce, yanzu zamu fara buga wasan ya rayuwar Barirah za ta kasance a garin Ƙusa?_
‎
‎*Me kuke tunanin zai faru da Barirah? Ya rayuwarta za ta kasance a ƙauyen ƘUSA? Shin da gaske Barirah mayyar ce ko da wata a ƙasa? Me ke bibiyar rayuwarta wane ne mahaifinta Runduna da mahaifinyarta Tsaiba? Me suka yi da har yake bibiyar 'yarsu wai shin ma ina suke suna raye ko sun mutu ne? Ɓangaren SD Sadauki burinsa zai cika na zuwa China? Zai amince da auren Sadiya, idan ya amince ya rayuwar zata kasance ina makomar Alhaji Bashar? Ɓangaren Nazifi da Murjanat ya abin yake shin Murjanatu na da laifi a binciken da yake? Duka wannan amsoshin da ma waɗanda ke zuciyarku duka amsoshin na cigaban labarin daga Iyar Affan, ku biya kuɗin karatunku hakan zai saka ku biyoni domin mu kasance tare a cikin tafiyar nan gani nan bari farar tumfafiya.*
‎
‎
‎_Ku tura kuɗinku kai tsaye ta 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Shaidar biya ta *** 1k whatsApp mutanen Nijar kai tsaye zaku tura da 400f ta My Nita +227 99 53 98 24 sai ku tura shaidar biya ta ***_


Ina masu buƙatar kyawawan atamfofi da  lace, mayafai, shoes and bag. Tare da kyawawan kayan kitchen na 'yan gayu masu kwaliti, zaku iya tuntuɓar ASHNURR COLLECTION wacce ke Kano kwari market domin ƙarin bayani ku tuntuɓeta a lambar waya kamar haka *** Tana aika kayanta ko ina a cikin aminci.

Shin kuna da labarin AK ASHKAD COLLECTION to ku matso kusa ku ji, ita ce wacce take kawo muku kyawawan  abayas na gani a faɗa na shiga ko wanne guri kai tsaye, haka tana kawo muku  kitchenwares masu kyau da aminci cikin farashi mai rahusa zaku iya tuntuɓarta a 070444564938 ko *** shafinta na Instagram ashkad_collection adireshinta Daura, Katsina State tana aika kayanta ko ina cikin aminci.

Kuna da labarin UmmuAffan GHT Supplement, tana sayar da Supplement na kamfanin ght masu kyau da inganci tana garin Kaduna tana aika kayanta duk inda kuke a faɗin ƙasar nan dama wajen ƙasar nan, kai tsaye kuyi mata magana ta lambar waya kamar haka *** sayen na gari mai da kuɗi gida, sai kunzo.