IMAANI

Chapter Eight

by @suttie0

Da safe Ammi da missed calls ɗin Abiyy wato yayanta Nasirudeen ta tashi. Bayan Abbu yayi musu private breakfast nasu su biyu a Kitchen ɗin sama, ta nufi ɗakinta inda Imaani da Shukrah suke kwance tun bayan sun kammala karatun asuba. 

Kasancewan malaminda ke musu karatu har su Imaani duk weekends da yamma ya koma makaranta can Saudiya ƙaro karatu, to basu samu wani ba har yanzu da zaiyi fitting schedule ɗinsu. Amma ma'aikatan maza suna halartar na asuba a masallaci, da yamma kuma Baban Nana wanda ke kulada fannin ma'aikata maza yana haɗa matan su Baaba Salame da sauran yayi musu nasu da daddare. 

Tashinsu Ammi tayi dan 10 ya kusa Imaani tasa ƙanwarta a gaba suka fita dan suyi breakfast. Bayan Ammi tayi wanka da kimtsa ɗakinta ta maida ma Abiyy call ɗinshi da tayi missing.

Dugu biyu ya ɗauka, da muryarshi na dattijai tunda an manyanta yanzu, ya amsa sallamar Ammi. 

Bayan sun gaisa yace mata, “Tamghart ta kawo ƙarar mamanta, tace ta kwana biyu bata ganta ba. Shukrah kawai taje tayi mata hutu.”

Ammi tayi dariya tace, “Ai ba'a shiga tsakanin uwa da ƴa zata je ta ganta In Sha Allah. Su Sajida zasu zo hutun dai ko Abiyy?”

Yace, “Basu dawo daga Nijer ba sai next weekend amma zasu sauka anan Kaduna kawai idan sun gama hutun sai sudawo Abuja. Ankusa resuming school ai.”

“Ankusa komawa kam, the long holiday will soon be over.” Tunda ana last week of August ne.

Abiyy yace, “Nafi'u ya kirani kwanaki biyu da suka wuce akan Imaani da yaronnan na Shafa’atu Hudhaifa, akwai wani abu a tsakaninsu ne dama?” 

Ammi tayi wondering saurin me Baba Nafi'u yakeyi haka a ranta kafin tace, “Nima ya kirani kwanaki yace yanaso ya haɗa auren Baby da Hudhaifan, amma from what I know gaskiya babu wani abu a tsakaninsu.”

Yace, “To ai it's not too late for them to know each other indai zai yiwu why not muji ta bakinta tukunna?”

Gaban Ammi ya faɗi, ai bama ta son abun yakai wannan tsawon. Ina ita ina haɗa ƴarta da ɗan hatsabibiyar matarnan Yaya Shafa'atu? To kodai Abiyy ya manta wacece ita ne? Matarda ke mulke mijinta da kishiyoyinta zata haɗa da Imaani?

Jin shuru yasa Abiyy yace, “Nasan tunaninda kikeyi Maijidda, idan yaron yanada hankali uwarshi bazata bamu matsala ba. Kiji mai Imaani zatace tukunna kafin mu yanke shawara.”

A sanyaye tace, “To Abiyy.”

Ya ƙara kwantar mata da hankali kafin suyi sallama.

Ammi tasan saboda rashin zafin Abiyy yasa suka tunkareshi kai tsaye tunda basu isa su nuna ikonsu akan Imaani ba yanzu. Da dai ace Zahradeen ne da ba ma wannan maganan akeyi ba. 

Bayan Zuhr ta sauka ƙasa ta tarar da Imaani a Kitchen ta kammala pepper soup ɗin kai da ƙafa na sa da miyar taushe, Baaba Saude tana suyan waina a murhu dake Kitchen ɗin waje.

Imaani ta gama jerama Rafeeq abincinshi dayayi requesting, zaiyi hosting abokanshi for Lunch a Chalet ɗinshi. Dama yakanyi hakan from time to time idan ya samu lokaci tunda bai cika yawo da abokai ba saboda yanayin aikinshi.

Da yawa akayi abincin kamar yadda aka saba, su Ƙarama suka miƙa na ma’aikatan gidan Imaani kuma aka barta da serving ɗin Rafeeq da baƙinshi. Already Ammi harta tafi dana Abbu sama.

Imaani ta ɗauka basket ɗaya a hannu Shukrah tayi karanbanin binta a baya da tray ɗin cutleries suka nufi Chalet ɗin. Sanye take da wani dark brown Moroccan Abaya yasha embroidery daga wuyanta har ƙasa sai ta yane kanta zuwa kafaɗunta da cream colored veil ɗinshi. A ƙofa Rafeeq ya amshesu yana sanye da loose fitted T-shirt da black trousers na Calvin Klein.

Zuwanta uku kafin ta kammala kawo musu duka abincin. A na ƙarshen ne ta shiga ciki da jug ɗin fruit pulp, a parlour ta samesu wurin su bakwai sun cika wurin da hayaniya. Palourn babba ne so ya ɗaukesu duka ba takura.

Majeed dake nan ƙasan layinsu yace ma Imaani, “Nasan santin yau nadaban ne tunda Top Chef ne a Kitchen.”

Murmushi tayi ta gaidasu suka amsata, duk ta tsargu da kallon da suke binta dashi. 

Muryar Rafeeq taji yace, “Boɗɗo kiyi serving ɗinmu, will you?” Kafin ya nufi fridge dake kitchen ya fara ɗauko ruwan sha.

Tunda umarnin Hammanta ne ba yadda zatayi da jin idanunsu, haka ta buɗe food warmers ɗin ta fara serving ɗin nasu. Biyar biyar tasa ma kowa tasa miya mai son ƙari yayi daga baya, Majeed kuma ya fara miƙa musu.

Rafeeq ma bayan ya bama kowa ruwa ya fara dishing out pepper soup a ƙananan bowls. 

Ganin plates ɗin bazai isa ba yasa Imaani tace ma Rafeeq, “Hamma bari na ƙaro plates waɗannan bazasu isa ba.”

Yace, “Akwai tumblers by the sink na ɗaurayesu ki haɗa dasu.”

Amsa mishi tayi ta nufi Kitchen ɗin, sleek grey and white tones akai amfani a interior ɗin dan ya bada masculine atmosphere kaman a bachelor's pad.

Cabinet ɗin kusada kitchen sink ta buɗe dan ta ciro plates ɗin, taga tsawonta bazai kai ba. Akwai stool dake lungun fridge shi ta ɗauko ta kara kafin ta hau ta fata ciro plates ɗin tana ajiye su akan countern. 

Motsin mutum dataji daga bayanta unexpectedly yasa ta juyo da sauri hannunta ya tura tumblers ɗinda ke gefen sink garin ajiye plate ɗin.

Karan fashewa da glasswares ɗin sukayi yasa ta razana tayi taga taga akan stool ɗin, kafin ya ƙaraso dan tare ta har ta faɗo ƙasa kan sharp pieces of glasses ɗin.

Zafin yankan data ji tare da gulɗewar ƙafarta na hagu yasa ta ƙwala kiran Abbu kaman shi ya aiketa.

***
Sameer da azama ya isa wurin da Imaani ke yashe a ƙasa tana rera kuka baiyi wata wata ba ya ɗagata cak. Akwai takalmi a ƙafafunshi saboda daga waje ya shigo ta ƙofar Kitchen ɗin na baya bayan yagama ansa wayar da ya fita yi.

Kukanta tsayawa yayi cak jinta a jikin mutum wanda hakan bai taɓa faruwa da ita ba. Kiciniyar ƙwace kanta ta fara dukda azaban da take ji, “Meye haka kuma-”

Rafeeq dayaji ƙaran fashewan glasses ya shigo Kitchen ɗin sai yayi arba da Sameer da yasa kai zai fito, “Subhanallah, Boɗɗo ya haka kuma.”

Kamar ƴar tsana Sameer ya miƙama Rafeeq ita baice komai ba yayi wucewarshi yana ɗan tsaki.

Imaani kuwa baƙin cikin zafin ciwo da sanin Sameer ne silar faɗuwanta kuka ta cigaba dayi takaici duk yabi ya isheta. A zuciyarta take faɗin ya cuceta daya taɓa mata jiki ba gaira ba dalili, ba gwara ya barta ta taka kwalabenba da ace ya taɓa mata jiki.

Kasa cema Rafeeq komai tayi ta kwanta a ƙirjinshi tana hawaye abokansa na mata sannu daya fito da ita. Da sauri ya ƙarasa da ita sashensu nan cikin main parlour ya kwantar da ita a babban Sofa.

Baaba Salame ne tafara salati da sallallami ganin state ɗinda aka shigo da Imaani, “Ya haka kuma mai gidan garin yaya taji ciwo.”

Ammi ce ta sauko ƙasa jin hayaniyan kukanda Imaani takeyi, da sauri ta nufesu tana tambayan Rafeeq meya faru.

Rafeeq ya amsa su a tare da cewa, “Ta shiga ɗauko plates nefa tana serving ɗinmu kawai naji ƙaran fashewan glasses da ihunta data faɗi.”

Zuwa sannan Ammi ta fara hasala saboda kukanda Imaani takeyi tama kasa barinta taji bayanin Rafeeq ɗin dakyau ga tausayi irinna uwa, cikin ɗaga murya tace mata, “Zaki yimun shuru ko saina buge miki baki, shiririta kawai. Taya daga ɗauko plate sai faɗuwa how does that make sense?”

Rage muryarta Imaani tayi tana sheshsheƙa zuwa sannan ƙafarta ya fara mata tsami gashi har yanzu akwai glass pieces embedded on her skin.

Rafeeq yace ma Ammi, “Inaga hospital za'a kaita saboda a cire glasses ɗinnan carefully.”

Baaba Salame tace, “Ai abu mai sauƙi ne yanzu sai na cire mata gilashin a wanke a naɗe kar ta cigaba da zubda jinin.”

Abbu daya sauko cikin shirin fita da sauri ya zo wurinda suke jin me Baaba Salame ke faɗi, “A'a kar a taɓata, kai Rafeeq ba wannan yaron Sameer physician bane, yazo ya bata first aid kafin aje asibitin.” Sai ya zauna kusada Imaani ya ɗan tallabota yana mata sannu.

Rafeeq da sai yanzu abun yazo kanshi yace, “Yeah that's right bari na kirashi yazo to.”

Ammi ta kira Ƙarama tasa taje ta ɗauko first aid box dake kitchen kafin Sameer ɗin yazo. Baaba Salame tabi bayanta ganin iyayen Imaanin na kanta yanzu.

Har sannan bata dena shashsheƙan ba amma tayi shuru dan batason Ammi ta ƙara mata faɗa kuma, Abbu kuma sai sannu yake mata yama manta da batun wani fitarshi.

Kiranda ya shigo wayarshi yasa ya tuna dan urgently ake nemanshi a office ya ciro wayar yaga secretary ɗinshi ne mai kiran. Miƙewa yayi yace ma Ammi, “Jidda ki tabbatar an kula da ita, zan tafi yanzu.” Sai ya duƙa yayi kissing forehead ɗin Imaani dana Ammi bayan ta amsa mishi kafin ya fice.

A porch ya haɗu dasu Rafeeq ya tsaya yayi musu magana kafin ya shiga motar da Chaffuer ɗinsa Horace ya buɗe masa sukayi gaba.

Ammi kuma sama tayi ganin shigowar mazan dan ta kira drivernta Xx yayi shirin kaisu asibitin bayan Ƙarama ta ajiye musu first aid box ɗin.

Haɗa rai Imaani tayi ganinshi tare da Rafeeq yana wani taku ɗaiɗai kaman bazai ƙaraso ba.

Sameer kuma daya ƙaraso duƙawa yayi a gabanta ya buɗe first aid box ɗin yasa sterile hand gloves. 

Imaani da taga dagasken dai shi zai bata first aid, da fillanci tacema Rafeeq, “Hamma ni banaso ya taɓani, shine fa yajamin na faɗi.”

Ɗaga kai Sameer yayi yana kallonta bayan ya ɗauka tweezers daga box ɗin. Fuskarta duk ya caɓe da hawaye harɗa dan zufan wahala da ta tara a goshinta ɗan kwalinta ma yana neman yayi nashi hanyan sai gashinta daya kwanta a skin ɗinta ya bayyana.

Rafeeq dake zaune a gefenta ya haɗa rai jin abunda tace, “Common stay put my friend, a ina kika ganshi da zaisa ki faɗi.”

Sameer bai biye mata ba ya kama hannun hagunta ya duba, just scrapes ne sai yasa normal saline ya wanke a cikin rubber da ya buƙaci a kawo mishi. Hannunta na dama ne akwai yanka a tafin inda ta samu garin rage impact ɗin faɗuwarta.

Nan yasa tweezers ya cire glasses ɗin yana sawa akan paper towels ya wanke hannun shima sai yashafa healing ointment yayi wrapping da gauze yana jin tana sauke ajiyan zuciya kafin ma azo mai gaba ɗayan.

Ƙafarta na dama babu wani matsala na hagun ne yaga alamun tayi spraining ankle ɗin dan har ya fara zama inflamed bayan yankan data samu.

Taɓa ƙafar yayi dan yaji yanayin ƙashin in reflex ta janye tana sakin ƙara. Ya ɗan kalli Rafeeq wanda yagane mai yake nufi shi kuwa ya dafa kafaɗun Imaani tareda matse hannayenta dan yayi locking movement ɗinta asamu agama treatment ɗin. 

Aikuwa tana jin haka tafara jan ƙafarta dan yanzu dagaske ƙafar tayi tsami sosai, Sameer bai ɓata lokaci ba ya kamo ƙafar yafara dubawa. 

Gam ya riƙe calf ɗinta dake da splatter ɗin white patches na Vitiligo yana cire pieces na glass ɗin dan baison ya ƙara ji mata ciwo dukda fisgewan data keta faman yi. Kukanta ƙaruwa yayi bata ma san yadda take fisge ƙafar ne yasa yake ƙara mata zafi ba.

Bayan ya wanke tafin ƙafar shima da normal saline sai ya fara juwa ankle ɗin dan yayi determining in akwai gocewan ƙashi ko babu.

Ai batasan sanda ta fasa wani ihu ba wanda har cikin kunnenshi Sameer ɗin yaji bai kulata ba yacigaba. Zuwa sannan Ammi ta sauko ƙasa tana jira ya gama su tafi asibitin.

Saida ya tabbatar babu ƙashinda ya fita amma kuma bashi zai hana ayi scanning ɗinba dan a sake tabbatarwa sannan ya shafa ointment ya naɗe da gauze.

A jejjere Imaani ke sauke ajiyar zuciyan wahala Hamman nata na lallaɓa ta, idan akwai abunda yafi gabada haushi to shi take ji gameda bawan Allahn daya gama taimaka mata. Da bai razanata ba da bata faɗi ba har ta samu kanta a predicament ɗinnan ba. 

Shi kuwa bayan ya gama ya cire gloves ɗin yayi disposing sai ya matsa baya dan ya basu wuri.

Mamaki yake yanda take wannan kukan tana wani shagwaɓewa sai kace wata ƙaramar yarinya.

***

Hala baka taɓa karyewa ba malam Sameeru 😭