Chapter Nine
by @suttie0
Sun isa asibitin dake nan cikin unguwarsu Al-Hilal Orthopaedic & Trauma Specialist Clinic, aka karɓesu. Nan Rafeeq yama nurses ɗin bayanin accident ɗin wanda Ammi tasa Imaani ta faɗa musu yadda ya kasance a hanya.
Direct suka shiga da ita X-ray room bayan Rafeeq ya musu bayanin first aid ɗinda ta samu a gida.
Gaban Imaani sai faɗuwa yake dan bata so ko kaɗan a ƙara taɓa mata ƙafa. Basu wani yi manipulating ɗinshi ba sanin halinda take ciki dan fuskantarta ta ɗan kumbura saboda kuka.
Result ɗin ya nuna babu matsala da ƙashin, ligaments ɗinne kawai sukayi pulling saboda bata taka ƙafar daidai ba garin faɗuwa shiyasa wurin ya kumbura. Magani suka bata sai sukayi advising da tayi cold compress da ice bag kuma kartayi stressing ƙafar na wani lokaci har sai ciwon yankan ya warke zuwa sannan zata iya fara takawa. Sunyi laying emphasis akan keeping cuts ɗinda tasamu clean and dry to prevent infection kuma saboda yayi healing dawuri.
Sai bayan Maghrib suka koma gida zuwa sannan Abbu ya dawo, Ammi ta taimaka mata tayi sallahn Maghrib da Qada ɗin Asr datayi missing. Shukrah na maƙale da ita tunda suka dawo ashe tana can tana bacci gun Halita tunda taci abincin rana.
Baaba Salame ta kawo mata farfesun kaza data yanka tsokan sala sala yasha kayan ƙamshi. Kaɗan ta rage a bowl ɗin, Baaban ta zauna da ita har bayan Isha'i, ta taimaka mata ta gabatar kafin ta tafi da kwanukan abincin.
Saida Imaani ta jira wurin awa ɗaya a zaune dan abincin ya sauka, har Abbu yashigo ya dubata Rafeeq ma haka kafin ta kwanta gefen ƙanwarta take mata game da waya.
Duk ta zama inconvenienced saboda ciwon, daƙyar tasamu position ɗinda bazai takura mata ba. Bata jima ba wayarta ta fara ringing a hannun Shukrah. Dubawa tayi dan taga mai kiran, screen ɗin ya nuna Z. A. M.
Dukda hannunta ɗaya zata iya amfani dashi amma tasa Shukrahn data sanya mata earbuds ɗinta dan tasamu sauƙin yin wayar. Sai ta sata ta tafi ayi mata shirin bacci kafin ta ɗauka kiran.
Sallamarshi tayau har cikin kanta taji da buɗaɗɗiyar muryarshi. Amsa mishi tayi da nata muryar dake fitowa aɗan sarƙe.
Dakatawa yayi jin yanayin muryarta, sai yace, “Are you alright?”
Sai ta rasa mai zata ce mishi kawai tayi shuru.
Ya kira sunanta, “Imaani..”
Sai tace, “Na'am.”
Yace, “Bakida lafiya ne?”
“A'a naɗan samu kitchen accident ne.”
Zunnurain yace, “Subhanallah, garin yaya? Yaushe?”
Imaani tace, “Dazu ne, naje ɗauko plates a cabinet shine na faɗi akan glasswares dana buge by mistake.”
Yace, “Bakiji ciwo sosai ba ko?”
Ɗan juyawa tayi akan gadon ahankali tace, “Na yanke sai nasamu targaɗe.”
Ajiyar zuciya ya sauke wanda taji, yace, “Allah Ya ƙara sauƙi. Akwai zafi sosai ko?”
Murmushi kawai tayi bata amsashi ba, sai yace, “I wish muna tare, I would take good care of you.”
Nanma batace komai ba kawai smiling tayi wanda yaji daga ɓangarenta.
Yace, “Tun ɗazu naso na kiraki amma bansamu time ba, wani aiki yazo min which I'll have to leave for very soon.”
Shuru taɗanyi, sai tace, “How soon?” Har ga Allah batayi tunanin zai iya tafiya ba cikin ƙanƙanin lokacinda suka haɗu.
“Nan da three days time haka, zuwa Wednesday. Tanzania zani, munada wani project that's coming to an end so munaso muyi finalising komai kafin ayi handing over sai muyi settling ɗinsu.”
Tunawa tayi shi Accountant ne dake aiki as Finance Manager a IDB, sai tace, “Allah Ya kaika lafiya.”
“Ameen ameen, inason ganinki kafin in tafi. Would that be possible?”
Imaani tace, “Bazan iya takawa ba, a ƙafa nayi targaɗen.”
Shuru yayi ya rasa mai zaice, dan yadda yake jin son ganinta ba da sauƙi bane saboda in har yatafi da wuya ya dawo nan kusa saboda yanayin aikinshi that takes him away from home for a long time. Inhar yanason tarayyarsu ta ƙarƙe to aiki ne a gabanshi babba, bayaso ko da wasa Imaani ta suɓuce mishi and it seems their first obstacle is going to be his job.
Ya sauke ajiyar zuciya kafin yace, “Indai kinsamu sauƙi kafin na tafi zan iya zuwa na ganki idan babu matsala ko?”
Tace, “Zan tambaya Ammi tukunna.”
Murmushi yayi yace, “Allah Yasa Ammi ta yarda.”
“Ameen.” Imaani tace ahankali wanda yasa ya faɗaɗa murmushinshi har saida taji.
Zunnurain yace, “Ki kwanta kiyi bacci ko? Don't stress yourself, ki bari ki warke da kyau kinji?”
Ɗaga kanta tayi kaman yana gabanta tace, “Okay.”
“Good night beautiful, I'll call again gobe kinji.”
Kunya taji tace, “Okay, have a good night too.”
Sai ya amsa da, “In Sha Allah.” Kafin ya kashe wayar.
***
Haka Imaani tayita jinyar ciwonta, kullum safe da dare zai Zunnurain ya kirata sunyi hira kuma yaji lafiyarta wanda hakan yasa zuciyarta creating mishi wani gurbi acikinta. Naseemah data dawo daga tafiyarta ta ziyarceta sosai dan rage ma Imaani kaɗaici, sannan ta ɗaukar mata excuse a makaranta bayan tayi making sure notes ɗinta are updated saboda Imaani tasamu na dogara.
Zunnurain bai samu yazo ba saboda ayyuka da suka mishi shamaki kuma har ya tafi Imaani bata fara taka ƙafarta ba balantana ta sauko downstairs.
Bayan sati ɗaya ciwukan sun warke sai abunda baza'a rasa ba, Ammi tana sata takawa akai akai har tayi ƙwari wurin tafiya da ƙafar da kanta. Zuwa sannan ancire bandage ɗin daga ƙafarta da suka koma asibiti yankan ma sun warke harda na hannunta sai aka ƙara mata wani maganin na shafawa a ankle ɗinta da supplements da zai ƙara boosting immunity ɗinta.
Lokacinda Imaani ta fara joining sauran ƴan gidan wurin cin abinci a Dining, da taga Rafeeq baya ci tare dasu sai ta tambaya Ammi. Nan ta sanar mata ai a sashenshi yake ci yanzu tareda Sameer daya dawo gidan yanzu saboda ƴan bikin gidansu sun hanashi sukuni.
Ɗan taɓe baki Imaani tayi batace komai ba suka cigaba da cin abinci. Satinda za'a shigane za'a fara bikin Muhibba dana Hafsa ƙanwar Sameer wanda coincidentally yazo a lokaci ɗaya.
Ranan Sunday yaran Abiyy suka hallara, su uku; twins Abou Bakr Siddiq da Siddiqa masu shekaru 20 sai ƙanwarsu Nazeera data ɗara Shukrah da shekaru huɗu making her 11 kenan. Daga Nijer suke inda suka ziyarci ƴan uwan mahaifiyarsu dasuke cousins da Ammi ta ƙanin Tamghart Aïchatou. Yaran tubarkallah dasu duk sun ɗauko yanayin mamansu na light brown skin tunda jininsu na Tuareg yafi ƙarfi.
Nan gidan ya kacame da hayaniyar yaran, wanda inbanda ƙiriniyar Shukrah to kullum shiru kakeji kowa na harkar gabanshi.
Imaani taje school Monday zuwa Wednesday tunda ba kullum takeda suke lectures ba, ta kuma leƙa restaurant ɗinta agurguje tayi catching up da abubuwanda ya faru da bata nan.
Ranan Thursday an shirya Kamu na Muhibba da yamma sai Dinner ran Friday bayan ɗaurin aure. Maman Hafsa kuma Kamun ƴarta Friday ne washe gari zatayi Dinner itama bayan ɗaurin aure.
Abun ya haɗema Ammi sai tace tunda Siddiqa tana nan tayi accompanying Imaani, taraba events ɗin biyu idan bata samu zuwa wani ba su Imaani sa wakilceta. Amatullah tazo har gida ta kawo ma Ammi passes ɗinta dana mutanenta sanin babu wanda zai kawo mata tunda har suka fidda anko ba wanda ya sanar da ita.
Siddiqa abun nema ya samu tunda yanzu ake ganiyar ƴanmatanci. Dama Ammi na tanadar kayan sawa na ƴammata saboda irin haka tunda ba laifi tanada ƴaƴa daga yayyinta.
Ranar farko Ammi ce taje Kamun Muhibban, the next day ne su Imaani zasuje Dinner wanda za'ayi bayan Maghrib. Ammi kuma ta halarci bikin gidan maman Hafsa.
Kamar yadda aka saka a invitation card ɗin, Dinnern zai fara bayan Maghrib a Rendezvous Event Centre dake Unguwan Sarki. Bayan Isha’ suka shirya, Siddiqa tasa light brown brocade jacquard lace, threaded with gold veins and woven maroon flowers, ɗinkin maiduguri style na half gown da straight skirt. Sai tasa maroon veil to complement flowers ɗin jikin kayan.
Imaani kuma tasa farin Broderie Anglaise lace ɗinkin boubou. Mai wani ratsin baby blue daga gefen inda akwai floral prints daga kafaɗarta na dama har ƙasa. Ɗinkin yayi kyau sosai tafito kamar wata babban mace. Colourn veil ɗinda ta yana a wuyanta ya sauka a bayanta na ɗaya daga cikin colourn floral prints ɗin jikin rigarta ne. Jewelries ɗinta white pearls ne ɗankunne, sarƙa mai hawa biyu da bracelets. Sai silver bangles da zobba. Tunda har yanzu akwai ɗan ciwo a ƙafarta bazai barta ta saka heels ba sai tayi opting for silver half cover shoes da silver beaded clutch na ZA Collections.
Sunyi kyau ba ƙarya, suka fito a mutunce saboda Ammi bata ɗaukan wargi a tarbiyar suttura. Sai baza ƙamshi suke ta ko ina.
Sun samu Baaba Salame ta tafi da Shukrah can wurinta saboda ta ɗauke hankalinta kar tayi musu rigima, dama tare suke da Nazeera so abun yazo musu da sauƙi.
Kamar ko yaushe Samuel da Cynthia suka kaisu event center lokacin 8 yakusa. Wurin ya cika ba laifi ƴan mata sai kwarkwasa ake a harabar wurin tareda abokan ango ana jiran isowar couple ɗin domin a shigar dasu.
Can Imaani taga Asma'u an kile da anko, itama tayi kyau amma irin shigarta ba irin wanda Abbu zai bari ta taka tsakar gidansu dashi bane.
Girgiza kanta kawai tayi tana ma Asma'u fatar shiriya. Nan tacema su Cynthia zasu jira sai bayan amarya ta shiga tukunna zasu shiga suma.