SAWU BIYU

Page 21

by @khadijahsulaiman406

SAWU BIYU 

BY 

Khadijah Sulaiman 

Young Talented Writers Association (YOTA)

Book 1

Page 21

Bayan tafiya mai nisa ya sake duba mirror ganin har lokacin motar na biye dasu,ya gangara gefen titi idon shi kafe a kan motar,Bilal yayi saurin riƙo hannun shi ganin yana ƙoƙarin buɗe ƙofa.
"Ina ka ke son zuwa Sadauki,are you okay?"
"Sake ni Bilal,i wanna teach that idiot a lesson".
Bilal ya ce "Please calm down Falcon,ba zai yiwu ka fita ba,babu makami tare damu,idan ka fita a haka akwai matsala wallahi".
Yana ƙokarin bashi amsa motar ta wuce su da mugun speed.
Bilal ya sake mishi hannu yace"to sun ma tafi,dan Allah kunna motar nan mu bar wannan dajin kafin a ji story that touches the heart,sai dai ka ji sanarwa a gidan jaridu an sace sojoji guda biyu a hanyar su ta zuwa Bauchi".
Sai kuma ya dafe kai yace"kai wannan abin kunyar da me tayi kama,dan Allah kunna motar nan mu bar nan".
Zarah gabaɗaya hankalinta ya gama tashi, Sadauki ya sake duba mirror ya kalleta,ganin yadda ta frigice lokaci ɗaya yasa ya ɗauke kai ya kalli Bilal ya ce"anya kai namiji ne kuwa,ko dai mu sake bincike?"
"In dai ta wannan fannin ne ku kira ni Zainab".
Sadauki ya girgiza kai ya ce "Allah ya shirye ka".
Hankalin Zarah bai kwanta ba sai da ta gansu a ƙofar gida,ta sauke numfashi ta buɗe ƙofar ta fito riƙe da jakarta.
Da sallama ta shiga ciki,Inna Yalwati dake zaune kusa da ƙofar ɗakinta ta bita da kallon rashin sani,ta ɗan durƙusa ta ce"ina wuni".
"Lafiya ƙalau".
Ta ƙarasa kofar ɗakin Umma tayi sallama,daga ciki aka amsa mata,ta cire takalmanta ta shiga ta shiga,Umma dake zaune kan darduma tayi murmushi tare da buɗe mata hannu alamar ta rungumeta.
Cike da kunya ta shiga jikin Umma kamar wata jaririya,Umma ta shafa kanta ta ce"ya hanya?"
A hankali ta ce"hanya Alhamdulilah Umma,mun same ku lafiya?"
Umma ta ce"lafiya ƙalau,ina Mamin ta ku?"
"Tana gida,ta ce a gaida ki".
Dai dai nan Sadauki da Bilal suka yi sallama a bakin ƙofa Umma ta amsa.
Sadauki ya fara shigowa Bilal biye dashi,ya bita da kallo ganin yadda ta shige jikin Umma.
Bayan sun zauna kan tabarma Bilal ya fara gaishe ta,tana murmushi ta ce"sannu da zuwa Bilal,kun zo lafiya ya aiki?"
Aiki Alhamdulilah Umma".
Ta ce"Masha Allah".
Ta ɗan kalli Zarah ta ce"bari in kawo ruwa ko takwara?"
Ta tashi daga jikinta ta koma bakin gado ta zauna,Umma ta ɗauko pure water da ta aika a siyo mata saboda su ta ajiye a tsakiyar dakin ta ce"ga ruwa sai dai babu sanyi".
Bilal ya ce"babu damuwa Umma".
Zarah sai wasa take da yatsun hannunta feeling uncomfortable kusa dasu.
Bayan sun sha ruwan Sadauki ya ce"bari muyi sallah mu dawo Umma".
"To sai kun dawo".
Bayan fitar su Zarah ta cire mayafin jikinta ta ɗauki buta ta fita,a waje tayi alwala ta dawo ciki ta tarar Umma ta shinfiɗa mata darduma.
Dambun Shinkafa da ya ji zogale da gyaɗa Umma ta ajiye wa Zarah,sai nasu Sadauki ta ɗora shi kan tabarma.
Bayan ta idar ta ninke darduman ta koma ta zauna, Umma ta jawo abincin kusa da ita ta ce"ga abinci Zarah".
Zarah ta ce"sannu da aiki Umma".
Sosai dambun ya yiwa Zarah daɗi,ta kalli Umma ta ce"Umma dambun nan yayi ɗadi sosai,yana cikin abincin da nake so,sai dai aikin shi ke bani wahala".
Umma tayi murmushi ta ce"na gode Zarah,ai ku yaran yanzu ba ku son abinda zai wahalar daku amma babu wahala a aikin dambu,shima Sadauki na so sosai,shi yasa nake yawan yi saboda shi".
Tana rufe baki suka shigo da sallama,ya buɗe kulan,ganin dambu yasa yayi murmushi ya ce"Umma sannu da ƙoƙari,kamar kin san na kwana biyu rabona da dambu".
"Shi yasa da ka sanar dani kana nan tafe na hau aiki".
Zarah ta koma can ƙarshen gado ta kwanta,a haka ta dinga jin hirar su sama sama har bacci ya ɗauketa.
Ba ta tashi farkawa ba sai la'asar,ta ɗauro alwala ta dawo tayi Sallah.
Bayan ta idar Umma ta ce"bari in samo yaro a waje ya kai ki gidan Inna Mairamu".
Zarah ta ce"to Umma".
Umma ta miƙe ta ɗauki hijab ta sa ta fita,bata wani jima ba ta dawo tare da yaro.
Ta ɗaga labulen ɗakin ta ce"fito Zarah,zai kai ki ya jira ku dawo tare".
Ta dauko hijab ta fito suka fita da yaron,cike da birgewa ta dinga kallon ƙauyen har suka isa.
Inna Mairamu tayi farin ciki sosai da ganinta,ta haɗa mata kwaɗon zogale da ya ji tumatur da albasa,bayan ta gama ta sha ruwan randa mai sanyi.
Tana nan har dab da magrib sannan ta koma gida.
Tana isa ta tarar Umma ta dafa musu shinkafa da miya.
Bayan sallar Isha Sadauki da Bilal suka shigo,ya zauna a kan tabarma ya gaida Umma,ta kalle shi cike da kulawa ta ce"kun haɗu da Mallam kuwa?"
"Eh,yana masallaci har yanzu".
"Amma ka tafi gidan Inna?"
A nutse ya ce"daga can muke Umma".
Ta ce"lafiya kuwa,naga kamar yanayin ku ya canza daga kai har Bilal?"
Ya sauke numfashi ya ce"an kira mu daga wurin aiki ne Umma,an sace wasu ƴan makaranta a ƙauyen Rafi dake jihar Kaduna,ana son ganinmu a office gobe idan Allah ya kaimu".
Umma ta ce"innalillahi wainna ilaihi raju'un,Allah ka mana tsari,ka shiga tsakanin na gari da mugu, wannan fitinan tayi yawa wallahi,Allah Ubangiji ya cigaba da tsare ku ya kare ku a duk inda kuke".
"Amin Umma".
Washegari da sassafe suka bar ƙauyen, sau ɗaya tayi amai a hanya saboda maganin da ta sha.
Sha biyu da rabi suka ajiyeta a gida,sai da ya shiga ya yiwa Mami bayanin komai sannan ya fito.

**********

MILITARY HEADQUARTERS 

Sojoji arba'in da biyar ke tsaye,sai General dake tsaye a gabansu,bayan ya gama ƙare musu kallo ya ce"duk kun san dalilin tara ku anan,shekaran jiya da ɗaddare aka shiga har cikin makarantar kwana dake ƙauyen Rafi aka tafi da yara goma sha takwas maza da mata,ku tafi kuyi bincike a kan yadda al'amarin ya faru,and most importantly,muna bukatar yaran a raye".
"Lieutenant Sadauki".
"Yes, Sir".
"you will lead the investigation. You will report directly to me. Take the officers you need and begin immediately."
Yayi saluting General ya ce"Yes, Sir".
Yana gama magana ya bar wurin,Sadauki ya sauke ajiyar zuciya ya juya ya kalle su ɗaya bayan ɗaya .
A nutse ya ce"zan zaɓi officers ashirin da huɗu da zasu tafi tare dani,aiki ne mai matuƙar mahimmanci,don haka ina buƙatar cikakken haɗin kai da kiyaye sirrin aiki".
"Yes, Sir".
Cike da zafin nama yayi selecting sojoji ashirin da huɗu sai shi cikon na ashirin da biyar.
Bayan ya gama ya dube su ya ce"ku ɗauki kayan aikin da zamu iya buƙata kawai,zamu kafa sansanin wucin gadi,kare makarantar da sansanin dake kewaye da ita tare da yin iya ƙoƙarin mu don dawo da yaran da aka sace,until then, nobody discusses this case outside this team. Is that clear?"
"Yes,Sir".
Ya gyaɗa kai ya ce"Good. Prepare yourselves. We leave immediately."
Ƙarfe shida na yamma suka isa ƙauyen Rafi,nan da nan aka haɗa tent guda biyu.
Yayi selecting sojoji guda goma da za suyi patrol a gaban makarantar,ya cire Adebayo, Emmanuel,Bilal da Idayat akan za suyi aiki tare dashi.
Sauran goman yace su tsaya suyi gadin wurin da kewaye.
A wannan lokacin suka nufi makarantar,babu sauran yara don iyaye sun kwashe yaran su tsaf sai principal da sauran teachers da mai gadi.
Tuni masu patrol suka fara aikinsu,a hararbar makarantar ya tarar da principal tare da polisawa yana musu bayanin abinda ya faru.
Yana hango sojoji ya daburce daga bayanin da yake, Sadauki na lure dashi har ya isa kusa dashi.
Ya miƙawa polisawan hannu suka gaisa sannan ya miƙawa Principal,yana riƙe da hannun shi ya ce"Sunana Lieutenant Umar Sadauki,mun zo nan ne don bincike akan ɗalibai da aka sace a wannan makarantar".
Principal ya ce"to ..to..to sannun ku da zuwa,bismillah,nine Principal sunana Malam Yusufu Gobir".
Sadauki ya ce"Masha Allah,ina sauran ɗalibai da malaman makarantar?"
Principal ya ce"eh to,saboda abinda ya faru yawancin iyaye sun zo har nan sun tafi da yaran su yau,malamai kaɗai suka rage,suma saboda gwabnati ta dakatar da tafiyar mu ne har zuwa lokacin da za'a kammala bincike".
Sadauki ya gyaɗa kai ya ce"good,ko zan iya ganin sauran malaman?"
"Eh,bari a kira su,ina zuwa".
Ya bar wurin da sauri Sadauki ya bishi da kallo.
Ya koma can gefe tare dasu Bilal,a nutse ya ce"Bilal".
Bilal ya ce"Yes,Sir".
"Kusa ido sosai akan kowa,ku kula da motsin mutum duk ƙanƙantarsa,the last but not the least,kar kuyi wasa da duk maganar da zai fito daga bakin kowannen su".
"Yes,Sir".
Hango Principal tare da sauran teachers ɗin sai share zufa yake yasa ya gyara tsayuwa,polisawan su kayi sallama da su Sadauki suka bar makarantar.
Sadauki ya matso ganin yadda duk suka rikice ganin sojoji.
A nutse ya ce"ku kwantar da hankalin ku,you're all safe In Sha Allah".
Duk suka gyaɗa kai da sauri.
"Zan muku tambayoyi,abinda nake so daku shine mutum ya faɗi iya gaskiyarsa".
Suka sake gyada kai a tare,ya juya ya kalli Adebayo ya ce"kira mai gadi".
"Yes, Sir".
Suna tsaye suka iso tare,Sadauki ya dube shi ya ce"ko zan iya sanin sunan ka?"
Mai gadi ya gyara tsayuwa ya ce"sunana Malam Namadi".
Idayat ta fito da paper da biro ta fara rubutu,Sadauki ya ce"Mallam Namadi, mun sami labarin sace ɗalibai goma sha takwas da aka yi a wannan makarantar,ko za ka iya sanar damu lokacin da abin ya faru sannan kai kana ina a dai dai wannan lokacin?"
Mallam Namadi ya buɗe baki da kyar saboda kukan dake son kufce mishi,ya share fuskar shi da ƙasar rigar shi ya ce"tunda nake a rayuwata ban taɓa shiga tashin hankalin da na shiga jiya ba wallahi,Allah kar ya sake nuna min irin wannan bala'in".
"Da misalin ƙarfe biyu na dare don ban wani daɗe da kwanciya ba naji kamar motsi,na fito da sauri na fara ƙoƙarin kunna tocilata,ko ƙwaƙƙwaran motsi ban yi ba naji an bige min kai da wani abu da ba zan iya tantance ko menene ba,ban sake sanin inda kaina yake ba sai da safen nan ranka shi daɗe".
Sadauki ya ce"nagode".
Ya juya wurin Principal ya ce"Sir,a dai dai wannan lokacin kana ina?"
"Eh ina ɗaki ranka shi daɗe,ina ɗaki gaskiya,cikin bacci naji ihu da muryoyi a waje,ina fitowa na tarar da mugun labari."
Sadauki ya ce"masu gadi nawa ne a makarantar?"
Principal ya ce"ɗaya ranka shi daɗe".
Sadaki ya ce"yaran da aka kwashe,ɗaki daya suke?"
Principal ya ce"eh matan duk ɗaki ɗaya suke,suma mazan ɗaki ɗaya suke ranka shi daɗe".
"Ya kamata makarantar kwana ya kasance akwai masu duty cikin dare,a nan babu ne?"
Da sauri ya ce"akwai ranka shi daɗe".
"Wa yayi duty jiya da daddare?"
Ya juya wurin teachers dake tsaye a gefe ya ce"Labaran,kai ke duty jiya ko?"
Labaran ya matso da sauri ya ce"eh Sir, amma ban sami yin duty ba saboda nayi fama da gudawa jiyan shi yasa nayi magana da Mallam Shuaibu na ce dan Allah ya taimaka min".
Sadauki ya ce"ina Mallam Shuaibu?"
"Gani nan Sir".
"A dai dai wannan lokacin kana ina?"
"Ina kusa da male dormitory Sir".
Sadauki ya ce"ok,Ina jin ka".
"Kamar yadda na sanar da kai ina kusa da male dormitory,motsin da naji ta water point yasa nayi gaggawar zuwa wurin,gashi babu isasshen haske,ganin babu kowa ya sa na juyo da nufin barin wurin,ji nayi kawai an shaƙa min wani abu a hanci,ban sake sanin abinda ke faruwa ba sai da safen nan".
Sadauki ya gyaɗa kai ya juya wurin sauran malaman ya ce"ta yaya aka fahimci abinda ke faruwa?"
Wani daga cikin malaman ya ce"Ihun yaran muka ji, Sir. Kusan lokaci guda muka fito, sai muka tarar da su riƙe da yaran, sanye da baƙaƙen kaya, fuskokinsu a rufe, kowannensu riƙe da bindiga."
"Ba ku yi ƙoƙarin taimaka wa yaran ba?"
"Mun yi ƙoƙari Sir,wani daga ciki ya ɗaga bindigarsa yayi mana barazana akan duk wanda ya matso za su harbe shi,ba mu da makamin da za mu iya tunkarar su da shi, shi ya sa muka ja da baya. A gabanmu suka tafi da yaran."
Sadauki ya sauke numfashi cike da nazari.
Ya juya wurin Principal ya ce"take me round the School, Sir".
Female dormitory suka fara shiga,cike da nazari yake bin ko'ina da kallo,ya tsaya dai dai ƙofar shiga wurin.
Ya sa hannu ya shafa wurin ya ce"ana kulle ƙofar nan kuwa?"
Principal ya ce"eh,ana kulle shi ranka shi daɗe".
Ya gyaɗa kai suka cigaba da tafiya, ɗakin a hargitse kamar filin sukuwa,huluna kusan guda biyar ne a ƙasa,ga takalma barbaje a ɗakin.
"Mata nawa aka sace?"
Principal"mata goma ne ranka shi daɗe sai maza takwas".
Daga nan suka nufi Male dormitory,ya gama nazarin wurin tsaf sannan ya kalli Principal ya bashi hannu ya ce"mun gode Sir,zamu dawo zuwa gobe In Sha Allah".
"Mu ke da godiya ranka shi daɗe,Allah ya bada sa'a".
Ƙarfe bakwai da rabi suka isa tent,shi da Bilal da Idayat su kayi alwala su kayi sallar magrib.
Bayan sun idar ya jingina bayan shi ya lumshe ido,Bilal ya sake kallon wayar shi for the third time ganin sai blinking yake.
Ya ɗan saci kallon Sadauki,ganin kamar bacci yake ya sa ya miƙe ya fita riƙe da wayar.
Ya buɗe ido a hankali ya bishi da kallo.






***