Soyayya Ta

The Unexpected Job

by @ramsha002

CHAPTER THREE

THE UNEXPECTED JOB

by Rabi Muhammad Shariff 
Ramsha Tales 

Hibba ta ɗago kai, amma abin da idanuwanta suka sauka a kansa ya sa gabanta ya faɗi.

Latif!

Shi ne mutumin da ya buge Aunty ɗinta, wanda ya bar ta cikin damuwa da fargaba game da halin da take ciki. Amma a yau, ga shi a gabanta, a cikin ofishin da ta zo neman aiki.

Da sauri zuciyarta ta fara bugawa. Ta ji kamar ƙafafunta sun daina ɗaukarta. A tunaninta, babu yadda za a yi mutumin da ta taɓa samun matsala da shi ya amince ya ɗauke ta aiki.

Ta fara tunanin ta bar wurin saboda tasan ba zai bata aikin ba.

Amma kafin ta ɗauki matakin fita, Latif ya haɗe rai, ya nemi wurin zama. Bayan ya zauna, ya ɗago idanunsa ya kalle ta.

"Zauna."

Hibba ta yi mamaki. Ta tsaya cak tana kallonsa, kamar ba ta tabbatar da abin da kunnuwanta suka ji ba.

A hankali ta nemi kujera ta zauna, amma saboda yadda ta rikice, har ta kusa faɗuwa.

A wannan lokacin, tunaninta ya rikice gaba ɗaya. Ita dai tana matuƙar buƙatar wannan aikin, amma ganin Latif a wannan matsayi ya sa ta shiga wani irin yanayi da ba ta taɓa tsammani ba.

Me yake shirin yi da ni? Ko kuwa akwai wani shiri da yake yi a kaina?

Latif ya miƙa hannunsa gare ta, yana jiran ta ba shi takardunta.

Hibba ta miƙa masa takardun, hannunta yana rawa.

Ya karɓa, ya fara dubawa ɗaya bayan ɗaya. Ya duba bayananta, takardun karatunta da sauran bayanan da ta gabatar.

Hibba ta zauna tana jiran tambayoyi, domin ta shirya amsa duk abin da za a tambaye ta.

Amma abin da ya faru ya ba ta mamaki.

Latif ya mayar mata da takardunta ba tare da ya yi mata ko tambaya ɗaya ba.

"Congratulations, you got the job."

Hibba ta zaro idanu.

Na samu aikin? Haka kawai? Ba tare da an yi min interview ba?

Ba ta san abin da za ta ce ba. Farin ciki da mamaki suka haɗu a cikin zuciyarta, amma duk da haka, tambayoyi sun ƙara yawaita a ranta.

Latif ya miƙe tsaye, ya kalle ta.

"Ki mata bayanin abin da ya dace."

Yana gama faɗin haka, sai ya fita daga wurin ba tare da ya jira Hibba ta ce komai ba.

Hibba ta bi shi da kallo har ya ɓace daga idanunta.

Alisa, wadda ta lura da yadda Hibba ta rikice, ta matso kusa da ita.

"Ke kam kina da sa'a, amma ban taɓa ganin Latif ya yi interview haka ba. Na ga bai tambaye ki komai ba, sannan samun wannan aikin fa ba ƙaramin sa'a ba ne. Gaskiya na taya ki murna."

Hibba ta yi murmushi kawai.

Amma a zuciyarta, tambayar da take yi wa kanta ita ce: me ya sa Latif ya ba ta aikin nan cikin sauƙi haka?

Shin saboda ya ga cancantarta ne, ko kuwa akwai wani dalili na daban?

Alisa ta ci gaba da yi mata bayanin yadda kamfanin yake aiki, inda za ta zauna da kuma abubuwan da ake buƙatar ta sani kafin fara aikinta.

Ta kuma gaya mata cewa za ta iya fara zuwa aiki daga gobe, domin akwai wasu ayyukan da suke kammalawa a yanzu.

Bayan sun gama tattaunawa, Hibba ta yi wa Alisa godiya, sannan ta tattara kayanta ta fice daga ofishin.

Amma duk da farin cikin da take ji na samun aiki, zuciyarta ba ta samu cikakkiyar nutsuwa ba.

Latif ya ba ta aikin, amma har yanzu ba ta fahimci dalilinsa ba.

Bayan Hibba ta koma gida, ta zauna cikin tunani. Ta kasa cire Latif daga ranta, domin duk lokacin da ta tuna yadda ya ba ta aikin ba tare da wata tambaya ba, sai ta ji wani irin fargaba.

A wannan lokacin ne Aunty ɗinta ta shigo ɗakin.

Ta lura da yadda Hibba ta nutsu cikin tunani, don haka ta matso kusa da ita.

"Me ya faru, Hibba?"

Hibba ta ɗago kai ta kalle ta.

"Aunty, wannan mutumin da ya kaɗe ki shi ne mai company ɗin da na je neman aiki. Na ɗauka ba zai ba ni aikin ba, amma kuma sai na ga ya ba ni."

Aunty ta kalle ta cikin mamaki.

"To, me abin damuwar anan, Hibba? Ai kamata ya yi ki yi farin ciki da samun aikin."

Hibba ta sauke ajiyar zuciya.

"Aunty, ni fa a yadda na ga mutumin nan, bana tunanin yana da kirkin da zai ba ni aiki bayan abin da ya faru. Ba ki tunanin wannan wani shirinsa ne?"

Aunty ta yi murmushi a hankali, tana ƙoƙarin kwantar mata da hankali.

"Ki yi masa kyakkyawan zato mana. Sannan wataƙila ya ga cancantarki ne, shi ya sa."

Hibba ta ɗan yi murmushi, amma ba wai don ta gamsu da bayanin Aunty ɗin ba.

A zuciyarta, tana fatan abin da Aunty ta faɗa ne gaskiya, domin ba ta son samun wata matsala da za ta jefa ta cikin damuwa fiye da wadda take ciki a yanzu.

Tana matuƙar buƙatar wannan aikin, musamman saboda halin da take ciki da kuma nauyin da take ɗauke da shi na taimaka wa Aunty ɗinta.

Saboda haka, ta yanke shawarar cewa duk abin da zai faru, za ta je ta yi aikinta yadda ya kamata.

Ba za ta bari tsoron Latif ya hana ta cimma burinta ba.

Washegari da sassafe, Hibba ta shirya cikin jajayen abayar ta. Ta yi kyau sosai, duk da cewa ba ta yi wani kwalliya mai yawa ba, domin zuwa wurin aiki take yi.

Ta gyara mayafinta, ta ɗauki jakarta, sannan ta fito daga ɗakinta.

Tana tuna kalaman Alisa game da halin Latif na rashin son makara, don haka ta yanke shawarar fita da wuri domin ta isa kamfanin kafin lokacin fara aiki.

Amma duk ƙoƙarinta, sai da ta ɗan daɗe a bakin titi tana jiran abin hawa.

Ta yi ta duban hanya, tana fatan wani abin hawa zai zo da wuri, amma shiru.

Lokaci yana tafiya, damuwa kuma tana ƙaruwa a zuciyarta.

A ƙarshe, bayan ta samu abin hawa, ta nufi kamfanin cikin gaggawa.

Da ta isa, kusan ƙarfe goma na safe ne.

Ta shiga cikin ginin da sauri, tana fatan wataƙila ba a lura da makarar tata ba.

Amma abin da ta tarar a cikin lobby ya sa ta tsaya cak.

Latif ne a wurin, yana ta faɗa a cikin fushinsa. Ya bayyana a fili cewa akwai wani abu da ya ɓata masa rai, kuma babu wanda ya kuskura ya katse shi.

Hibba ta matso a hankali, ta tsaya a gefe tana jiran ya gama.

Amma da Latif ya lura da shigowarta, sai ya ɗaga hannunsa ya kalli agogonsa.

Ya sake kallonta.

"Is this the right time to come to work?"

Hibba ta yi shiru, domin a tunaninta wataƙila ba ita yake magana da ita ba.

Amma sai ya sake magana.

"I'm talking to you. Ko a karatun da kika yi ba ki jin Turanci ne?"

Hibba ta kalle shi, ta haɗiye yawu, sannan ta amsa masa cikin Turanci. Ta bayyana masa cewa rashin samun abin hawa da wuri ne ya sa ta makara.

Latif ya ƙara haɗe rai.

"This is not an enough reason to come by 10. Ke, kin ga, I don't care ko ƙarfe nawa za ki taho, but idan kin san ba ki samun abin hawa, to ko da asuba ne ma ki fito saboda bana tolerating makara."

Hibba ta buɗe baki za ta yi magana, amma Latif ya juya ya wuce ba tare da ya ba ta damar cewa komai ba.

Ta tsaya tana kallonsa, zuciyarta cike da takaici.

Ashe ma wannan mutumin ba ya sauraron mutum?

Amma ba ta ce komai ba. Ta san cewa fara aikinta take yi, kuma ba ta son fara shiga matsala tun ranar farko.

Alisa ta matso kusa da ita, ta nuna mata wurin da za ta zauna domin fara aikinta.

Hibba ta zauna, ta kunna system ɗinta, sannan ta fara shirya abubuwan da take buƙatar yi.

Ta yi ƙoƙarin manta abin da ya faru a baya, ta mai da hankali kan aikinta.

Amma ba ta da masaniyar cewa a wannan kamfanin, fara aiki ne kawai ta yi, kuma ainihin ƙalubalen da ke gabanta bai fara ba tukuna.

Bayan wani lokaci, sakataren Latif ya zo wurin Hibba.

"Yallabai na kiran ki."

Hibba ta miƙe ba tare da ta yi wata magana ba, ta nufi ofishin Latif.

Da ta shiga, ta tarar da shi zaune a kan kujerarsa, gabansa cike da wasu fayiloli.

Ta nemi wuri ta zauna.

Amma kafin ta gama zama, Latif ya ɗago kai ya kalle ta.

"Wa ya ba ki izinin zama?"

Hibba ta miƙe tsaye nan take.

Latif ya ɗauko wasu fayiloli ya miƙa mata.

"Wannan wasu kwangilo ne da aka ba mu na wasu gidaje. Je ki duba duk yadda suke bukatar designs ɗin, sannan ki tsara project ɗin. Ina bukatar su nan da ƙarfe huɗu."

Hibba ta karɓi fayilolin, ta fara dubawa.

Da ta ga yawansu, ta yi mamaki. Akwai aiki mai yawa da za a yi, kuma lokacin da aka ba ta ya yi kaɗan sosai.

Ta ɗago kai ta kalle shi.

"Amma waɗannan fa suna da yawa, ba zan iya gama su zuwa ƙarfe huɗu ba. Amma bari na raba su, sai na yi wasu yau, sai gobe na yi sauran."

Hibba ta matsa za ta ajiye fayilolin, amma Latif ya katse ta.

"Anan ni nake ba da umarni, ba ra'ayinki nake tambaya ba. If you know you can't do it, just quit."

Hibba ta yi shiru.

Ta ji kalamansa sun sosa mata rai, amma ba ta son ta ba shi damar ganin raunin da take ji.

Ta tattara fayilolin, ta juya ta fita daga ofishin.

Da ta koma wurin aikinta, sai ta zauna ta buɗe fayilolin ɗaya bayan ɗaya.

Ta fara duba abubuwan da ake buƙata, sannan ta fara zana designs ɗin a kan system ɗinta.

Aiki ne mai yawa, amma Hibba ta ƙuduri aniyar cewa za ta yi iya ƙoƙarinta.

Lokaci yana tafiya, ma'aikata kuma suka fara shirin tafiya gida.

Wasu sun tashi, wasu kuma suna tattara kayansu, amma Hibba tana nan tana aiki.

Alisa da ta fito domin tafiya gida ta lura da ita.

Ta matso kusa da teburinta.

"Hibba, yanzu ai lokacin tashi ne. Ba yanzu za ki tafi ba?"

Hibba ta ɗago kai.

"Zan tafi, amma ban gama wannan aikin ba. Fayilolin guda goma ne, ni kuma guda huɗu na yi."

Alisa ta zaro idanu cikin mamaki.

"Amma Latif baya ba da aiki da yawa haka. Me ya sa ya ba ki su, alhali ya san ba za ki gama su a yau ba? Anyway, ni gaskiya tafiya zan yi. Ki je ki same shi ki yi masa magana."

Bayan ta faɗi haka, Alisa ta tafi.

Hibba ta kalli sauran fayilolin da suka rage, ta yi ajiyar zuciya, sannan ta ɗauke su ta nufi ofishin Latif.

Da ta shiga, ta tarar da shi ya shirya tafiya. Yana sanye da kayansa na fita, kunnuwansa kuma suna ɗauke da AirPods.

Hibba ta matso ta tsaya a gabansa.

"Sir, ban samu na gama wannan aikin ba gaba ɗaya. Guda huɗu na yi, ga shi kuma lokacin tashi. Sir, in ba damuwa, zan tafi da su sai na ƙarasa aikin a gida."

Ta yi ta magana har ta gama, amma Latif bai nuna wata alamar ya saurare ta ba.

Sai da ta yi shiru sannan ya cire AirPod ɗin da ke kunnensa.

"Naga kin shigo min office kina ta surutu. Me kike cewa? Me ya faru ne? Hope kin ƙarasa?"

Kalaman nasa sun ɓata wa Hibba rai sosai.

Ta ajiye fayilolin a kan teburin, sannan ta ɗago kai ta kalle shi kai tsaye cikin ido.

"Me ya sa ka ba ni aiki a wannan company ɗin, sannan ka tashi ka ɗauki aikin da kafin na gama su za su ɗauki lokaci, sannan ka ce kana da bukata a ƙanƙanin lokaci? Me intention ɗinka a kaina, eh?"

Ta faɗi hakan ba tare da tsoro a fuskarta ba.

Latif ya saurare ta har ta gama magana.

Sai ya ce cikin sanyin murya mai ɗauke da fushi:

"Kin fiye magana. Idan kina tare da ni, ki saita yadda za ki na magana."

Bayan ya faɗi haka, ya ɗauki gilashinsa ya saka, sannan ya fice daga ofishin ba tare da ya ƙara cewa komai ba.

Hibba ta tsaya tana kallonsa, zuciyarta cike da takaici.

Wannan wane irin mutum ne?

Ta ɗauki fayilolinta, ta fice daga ofishin cikin fushi.

Da ta isa waje, ta fara magana ita kaɗai.

"Shi ne ya ba ni aikin nan don ya nuna min irin isar da yake da ita ko me?"

Ta girgiza kai cikin takaici, sannan ta nufi hanya domin samun adaidaita, ta koma gida.

Amma duk da fushin da take ji, ta san cewa ba za ta iya barin aikin ba a yanzu.

Ba don tana son yin aiki da Latif ba, sai don tana da dalilin da ya fi komai muhimmanci a gare ta.

Kuma wannan dalilin shi ne Aunty ɗinta.