Page 4
by @oumamani
*TASWIRAR KADDARA*
DijahAM(Oum Amani)
Page 4
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Kallon Junaid Azlan yai ya saki wani malalacin murmushi sannan ya juya kansa gefe yana shafa gemun sa, girgiza kai Abie yai kawai kafin yace "wallahi Azlan kar ka kara kwana a waje in ba haka ba sai na Saba maka wallahi"
Lumshe idonsa yai kafin ya bude su a kan Abie din, cikin kasa kasa da murya yace "insha Allah" daga haka Abie ya mike ya bar palourn.
Kallon sa Junaid yai bayan fitar Abie yace "me yasa baka Jin magana ne wai Azlan kai kafison kullum Ka dinga batawa Abie da Mami rai koh, ynxu sbd tsabar rashin kunya a gaban su kake cewa mace na kwanciya akan kirjina.."
Zakudowa Azlan yai daga kan kujerar da yake ya kalli Junaid yana kankance idonsa daya sha kwalli rambadadau don shi baya ware idonsa gaba daya shiyasa ake masa kallon rikakken dan iska, tsuke karamin bakin sa yai kafin yace "ai gani nai ba karya nai ba, ba abinda kuke yi kenan ba ku masu auren kullum matan ku suna kirjin ku shiyasa naga nima zan maida hankali nayi auren nan ko naji abinda kuke ji"
Girgiza kai Junaid yai yana kallon Azlan kawai don shikam dama tuni Azlan yafi karfin sa, mikewa Azlan yai yana gyara wandon sa daya sassako sannan ya kalli Junaid yace "Ka gaida Mai dakin Ka ni zan wuce gurin tsoho"
Da ido Junaid ya bisa har ya fita kafin shima ya mike ya nufi part din Mami don yana son magana da ita akan tafiyar da yake son yi India akan matsalar rashin haihuwar sa...
********
Ban koma gida ba sai bayan Isha'i don Saida na gyara wa Yakumbo bangaren ta tsaf duk da ba wani datti kasancewar Yakumbo macece mai tsafta, bayan mun koma gida ban samu Umma a Palour ba nasan maybe tana daki hakan yasa nima na kwantar da Mimi da tai bacci a daki, addua nai mata sannan na fita zuwa kitchen don dora zobo na so nake nayi shi tun da daddare nasa a fridge kafin safe yayi sanyi.
Nida Aisha ne muka shiga kitchen din muna hada zobon muna hira tana bani labarin school dinsu fadan da akai yau akan wani saurayi, girgiza kai kawai nai cikin takaici ina mamakin yadda mata suke zubar da ajinsu da kimar su ta diya mace suna fada akan namiji, tabe baki nai takaici kamar zai kashe ni don haushi cikin saurin magana ta nace "ke ni ki daina bani labarin nan haba bakomai a ciki sai kayan takaici"
Dariya tai tace "dama nasan haka zaki ce ai Ya Batul don ba a gaban ki sukai damben bane ba wallahi nasan da sai kin kusa kuka kinga yadda suka yagawa juna hijabi kuwa, kuma abin takaicin Wanda suke damben akansa yana zaune yana kallonsu amma ko uhm bai ce ba daga karshe ma mikewa yai ya tafi ya barsu agun irin su kashe junan nan nasu ma"
Cije lips dina na kasa nai cikin takaici nace "taya suke tunanin ma zai ga darajar su ita mace ai MAI DARAJA ce ynxu alal misali ko da ace a cikin su yana son wata wannan zubar da mutuncin da sukai a bainar jama'a ai dole ma yaji baya ra'ayin su"
Gyada kai Aisha tai tace "kuma a haka fah wai su basu yadda ba sun burge sbd sunyi fada akan abinda suke so sai hura hanci suke nidai banga karshen yadda aka kare ba na taho kar Umma tai min fada tace na dade Amma wallahi Ya Batul Allah Allah nake gobe tayi naje naji yadda ake kare"
Tabe baki nai nace "anan kika fi kauri ai son Jin gulma da munafurci"
Turo baki tai tace "ynxu ya batul nice nake da son gulmar"
Kallon ta nai nace "toh in bason gulma ba ina ruwan ki da son sanin yadda fadan ya kare"
Gyada kai tai tace "Hmm Ya Batul knn"
Kamal ne ya shigo hannun sa rike da leda yar madaidaiciya, kallona yai yace "Ya Batul yau tun da muka dawo daga school ban ganki ba ina ta tambayar Umma tace kina kin je babban gida"
Zobon dana kulla a a leda na ajiye nace “ina can naje duba Manniru sai kuma na tsaya gurin yakumbo daka sani ai daka shigo gurin nata tana ta min mitar baka zuwa wai khalil ne kullum sai yaje amma banda Kai"
Dariya yai yace "rikicin tsufa ne kawai yake damunta Allah amma ko ranar Monday fa sai da naje na gaishe ta nine ma na kai mata abincin da Umma ta bayar a kaimata"
Miko min ledar yai yace "gashi inji Mansur Mai shago wai cake din ya kare nan kudin cinikin ne dubu Biyu da dari uku shine yace na kawo miki in ba damuwa wai ki yi gobe da wuri sbd ana siya da safe sosai"
Karbar kudin nai na ciri dari ukun kai na mikawa Aisha naira dari, dari biyun kuma na bawa Kamal nace "gashi Kai da Khalil ku raba"
Godia suka fara min suna murna don dama haka nake musu in har nayi ciniki toh ina basu dari dari wannan ina ragewa Abba kudin kashewar sune tunda in na basu kudin basa tambayar Abba kudin makaranta har sai ya kare.
A gajiye na mike bayan mun gama jera Zobon a fridge nace "gaskia Kamal Ka fadawa Mansur ba lalle nayi cake din gobe ba, kaga gobe kamun Khadija kuma ni ta bawa In Mata cake da donut ga kunun Aya da zobo zanyi jibi na yini gaskia ba lallai wannan satin nayi cake ba kuma fa Monday zamu fara waec"
Marairaice fuska Kamal yai yace "Ya Batul zamu taya ki don Allah ko a cake din goben da zakiyi ki kara kayan hadin kawai sai kiyi duka hadda Wanda za'a Kai shagon"
Aisha ce tace "laaaa kuma haka ne basa banba sumu munzo da shawara mai kyau"
Harara ya sakar mata sannan ya juyo ya kalle ni yace "ko Ya Batul zamu taya ki Allah gobe Friday muna dawowa daga school in baki gama ba sai mu tayaki ko Aisha"
Hararar sa Aisha tai tace "wai sa'ar kace ni shekara biyu na baka amma Ka raina ni don wulakanci baxa ka dinga cemin Ya Aisha ba sai wani Aisha kana ganin yadda Khalil yake cemin duk zai kira ni sai yace Ya Aisha Amma Banda kai banza mara kunya"
Zai yi magana na janyo hannunsa na tura sa palour nace "wuce muje toh ka taya ni duba abinda Banda Shi na cake din sai Ka siyo min tunda ga kudi sun shigo"
Shiga palour mukai yana fadin "me yasa baki ce su Khadijan su baki kudi ba kafin ki musu Ya Batul"
Dariya nai nace "kawai na fison sai na gama maka abinka tsaf in kazo dauka Ka ban kudina cas kaga wannan kudin da aka ban zan ware ribata nasa a banki ragowar kuma na kara siyo kayan flour"
A Palour muka zauna muna lissafi har Abba ya shigo gidan anan aka hau hira kowa na bada labarin abinda ya faru daya basa mamaki ko wani Abu da yai Wanda Abba zai gyarawa mutun yai masa in na fada ne yayi, haka muke muna da fahimtar juna sosai mun dauki iyayen mu matsayin aminan mu da ba wani sirrin mu da muke boye musu shiyasa ko lokacin da KADDARA ta fada mana akan samuwar cikin Mimi sosai iyayen mu suka fahimci zancen kuma suka karbi KADDARAR da hannu bibbiyu duk irin bakaken maganganun da suka dinga ji suka toshe kunnen su har Mimi tazo duniya komai Abba ne yake mata sai dana fara Sana'a nema komai na samu akan ta nake karar da shi gurin siya mata sitiru masu kyau daidai talaka mai rufin Asiri.
Sai karfe 10 sannan Abba ya kashe TV yace kowa yaje ya kwanta dama haka dokar sa take tun muna kananu karfe goma kowa yake shiga daki ya kwanta sbd school sai in ranakun daba makaranta ne ma yake barin mu wataran mukai 11, dakin mu muka shiga nida Aisha su Kamal ma suka tafi dakin su dake jikin dakin mu, sai dakin su Umma dake kallon dakunan mu, koda muka shiga daki sai da muka sha hira sosai nida Aisha kafin mu kwanta bacci.
Washe gari da kaina na raka Mimi makaranta bayan tasa nai mata alkawarin zan koma na dauko ta da kaina, ina komawa gida na fara aikin cake dina tunda da wuta Allah ya taimake ni kafin 11 har na gama don da toaster biyu nake yi da toaster daya ce dani da aka fara bani order din cake na biki ko suna sai na tara kudina na siya wata toaster din sbd na rinka sauri, doughnut din na kwaba na ajiye a rana, hijab dina na zumbula har kasa dark blue nai ma Umma sallama na tafi school din su Mimi dake cikin Unguwar mu.
A compound din school din na same su itada Hidaya suna zaune suna wasa da kasa, suna gani na suka taso a guje suka taho suka rungume ni, dariya nai ina shafa kansu ina son Hidaya sbd ita kadai ce kawar Mimi mutane sun jahilci Kaddarar data same mu basa son yayansu suna kawance da Mimi duk da kuwa yadda yarinyar take da farin jini amma banda cikin layin mu don duk Wanda yasan ta yadda aka same ta kyamar ta suke banda gidan su Hidaya.
Riko hannun su nai sai murna suke nazo daukan su, sai da na tsaya na siya musu awara ta goma goma da ice cream sai murna suke suna tsalle, har gida na kai Hidaya kasancewar gidan su a jikin gidan mu yake mamarta ba wata babba bace Aunty Zainab tana da kirki sosai Hidaya ce yar ta kadai sai ynxu da take dauke da wani cikin.
Muna shiga gida wanka nai ma Mimi na sa mata atampar ta ta sallah na mata kwalliya dai dai da shekarun ta na sa mata dankwali, abincin da Umma ta dafa na Rana na zuba mata na koma gurin aikin doughnut din da nake, kafin karfe 2 na gama doughnut din na ajiye a gefe, kafin na mike daga gurin kanwar Khadija da yayar ta suka shigo, gaisawa mukai bayan sun gaishe da Umma, a tare muka kirga cake da doughnut din sai da na tabbatar ya cika iya adadin Wanda suka ban na jera su a cikin kwali, dubo talatin Yayar Khadija ta miko min tace "ga kudin nan Batul mun gode sosai sai gobe insha Allah kinsan yini da wuri ake yi don Allah kafin karfe daya muke son zobon da kunun Aya."
Karbar kudin nai na mikawa Umma sannan nace "Insha Allah zaku samu da wuri sai dai ku kawo kulolin da zan sa zobon a ciki tunda kinga sai na zuba kankara akai yadda zasuyi sanyi koh"
"Insha Allah goben da safe za'a kawo mun gode sosai"
Kati ta mika min guda biyu tace"gashi na kamun ne karfe 4 ne za'a yi don Allah kuzo keda Aisha"
Kallon Umma nai ganin bata kallona ma yasa na karba nace "zan Kira Abba na tambaye sa in ya bari mai zai hanani zuwa"
Har kofar gida na raka su sannan na shigo na gyara gurin Aisha da dawowar ta knn ta tayani muka kintsa inda na bata, cake din da nai na zuba a Bokitin fenti na ajiye a gefe ina jiran khalil ko kamal wani ya shigo na basa ya kaiwa Mansur, Zama nai gurin Umma muna lissafin yadda za'a yi da kudin sai murna muke sbd wannan ne order da aka taba bani mai tsoka ragowar duk basa wuce na 10k koh 15k Amma ynxu gashi 30k zuwait ga gobe ma Insha Allah zan musu zobo da kunun Aya na 20k
Kasancewar inada banki da nake tara kudi kodan university din da nake son shiga in na gama waec, sbd na ragewa Abba wani abun yasa Umma yanke shawarar a ajiye 30k din duka a bankin nawa,
Kallon Umma nai nace "a'a Umma keda Abba kudai dubu 20k kusa albarka ko Umma"
Girgiza kai tai tace "A'a basai mun dauka ba ke da kike Tara kudin ki"
Damun Umma nai dole sai da ta dau 5k tace "zamu raba wannan nida Abban naku Allah ya karo kasuwa mai albarka yai muku albarka gaba dayan ku"
Nida Aisha muka hada baki gurin fadin "Ameen Ummanmu"
Wayar Umma na karba don kiran Abba na gwada tambayar sa zuwa bikin Khadija ko Allah zai sa ya barmu
*********
Gyara zaman sa yai yana kallon Baffa yace "toh kai tsoho meye damuwar ka da aure na"
Kallon sa baffa yake yana gyara zaman glass din idonsa yace “so nake kaima kayi aure kamar yadda da uwan Ka yai kana kallo dai shekarar Dan uwanka biyar da aure amma kana zaune Kai baka da aiki sai zuwa gidan casu kuna juya mazaunai"
Murmushi Azlan yai har saida fararen hakoran sa suka bayyana yace "tsoho kaima fa Ka iya vawulence fah ynxu meye na cewa mazaunai"
Salati Baffa ya saki yace "ynxu Azlan nine na iya vawulence din"
Gira daya ya daga yace "yesss tsoho"
DijahAM
***