FreeArewaPen original
TASWIRAR KADDARA
- 1views
- 1chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
✍️ Writer | DijahAM (Oum Amani) 📖 Author of Taswirar Kaddara & more 🌙 Islamic • Family • Romance • Drama 🖤 Stories of love, pain, secrets & second chances Welcome to my little world of stories. 🤍
Sample · Page 1
*TASWIRAR KADDARA* DijahAM(Oum Amani) Page 1 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Zaune nake a matsakai cin tsakar gidan mu ina duba littafin dake hannu na, kasancewar wannan shekarar zan rubuta Jamb gashi lokaci yana ta kurewa, ynxu haka saura sati biyu mu zama jamb din. Hankali na ya kasu kashi biyu, daya yana kan English din dana ke duba wa daya kuma yana ga tunanin inda *MIMI* ta shiga, tun da akai la'asar ta fita ban kara ganin taba, kwafa nai ina tunanin yadda zan hukunta ta tunda tasan cewa bana son tana fita da yamma haka ita kadai. Ni ban ma san wane tsautsayi bane yaja ta fita ko da yake gidan ba kowa dole ta samu ta silale ai. Wata yarinya yar kimanin shekaru 4 fara kar kamar balarabiya sbd tsabar hasken da Allah yai mata ce ta shigo gidan tana sanye da riga yar kanti har kasa duk da rigar tadan kode amma kal take a wanke sai alamun kasa kasa daka kasan rigar da alama yarinyar tayi wasa a kasa ne. Tunda ta shigo na kafe ta da ido ina tasbihi a raina, kullum na kalli Mimi sai nayi tasbihi ga Ubangiji sbd tsabar kyaun ta, fara ce tass mai dauke da zagayayyiyar fuska tana da manyan idanu sosai tubarkalla sai dogon hanci wanda ya dace da zagayayyiyar fuskar ta sai kuma karamin bakinta jajir dashi, maida kallona kan gashin ta nai dake tufke amma jelar har kusan duwawun ta take sbd tsayin gashin ta. Lumshe idona nai jin wani hawaye yana kokarin zubo min a dalilin tuna wani shudadden lokaci, muryar ta mai cike da shagwaba naji a kusa dani tana fadin “*MAA* kiyi hakuri baxan sake ba, Hidiya ce tace inzo muyi wasa a kofar gidan su." Kallon ta nake kawai ina bin kumatun ta da kallo yadda dimple dinta na gefen kumatun ta na dama yake lotsawa sosai, hakan ba karamin kyau yake karama ta ba. Hade rai nai cikin dan fada fada da saurin maganar da nake da shi nace "ban hana ki fita ba? amma saboda kin fara raina ni koh Mimi shine har zaki fita ba tare da na sani ba" Rau rau tai da idonta daya fara tara hawaye ta kama kunnuwan ta da kananun hannayen ta tace "Maa kiyi hakuri bazan sake bafa kar kiyi fushi dani kin ji?" Ta karasa tana kifkif ta idon ta sbd hawayen da suke ciki su zubo. Daga bayan mu Umma da ta fito daga daki tayi dariya tace "zo kinji kawata kema kinsan Maa dinki baxa ta iya fushi dake ba ai” Makale kafada tai tace "toh Umma ai bata ce ta hakura ba fa" Janyo ta jikina nai cikin tsananin kaunar ta nace "na hakura babyta amma kar ki sake fita ba tare da kin fada min ba kinji koh?” Daga kai tai tana kuma kwantar da kanta a jikina sai shagwaba take zuba min ina biye mata, girgiza kai Umma tai kawai tana dauke kwallar dake neman sakko mata a fuska. Tabarma na dauko a dakin mu na shinfida a tsakar gidan, daga kasan bishiya...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.