Page 5
by @oumamani
*TASWIRAR KADDARA*
DijahAM(Oum Amani)
Page 5
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Girgiza kai Baffa kawai yai yana bin Azlan dake danna waya da kallo, ganin shirun bana karewa bane yasa Baffa cewa "kana zuwa gurin aikin kama kuwa Hussaini"
Dagowa yai daga danna wayar sa da yake ya zubawa Baffa lumsassun idonsa yace "me Ka gani tsoho"
Dan daure fuska Baffa yai kan yace"gani nai kamar baka zuwa don shashanci sun dauke ma hankali"
Hade rai shima yai sosai ya koma asalin Azlan din da Yan mata suke matukar tsoron tunkara, zakin da Maza suke tsoron shiga gonar sa, kallon baffa kawai yake yana kara kankance idonsa, tsaki baffa yai yace "ynxu dai ya maganar koyar war Ka yadda zaka fara"
Dan tsuke bakin sa yai ya juya fuskar sa gefe yace "Tsoho bana son wannan lecturing din da wanne zanji ga company ina zuwa ga kuma wani lecturing ni nasan Abie yana son na fara ne kawai sbd na zama busy sosai"
Ruwa Baffa ya dauka ya kora kafin yace "aikin companyn fa ba ko yaushe kake zuwa ba da akwai ranakun daka diba kake zuwa mai zai hana Ka karbi tayin koyarwar in yaso ranakun da baka zuwa aiki sai Kana shiga makarantar kana koyarwa"
Dan tsirawa Baffa ido yai kafin yace "mai yasa kuke son dole wai sai na fara lecturing bayan kunfi kowa sanin bana son hayaniya kuma baxan iya jurar magana mai tsayi ba ga students"
Murmushin manya Baffa yai yace "zaka iya *ZAKI* Insha Allah kawai dai ynxu kana ganin abin kamar da wuya amma daka fara zaka saba"
Hade rai yai ya kwantar da bayansa a jikin kujera kafin ya mike hannun sa na dama yana kallon zanen tattoo din zakin dake kwance a damtsen hannun sa, dan lasar lips dinsa yai kafin yace "shikenan zan yi amma sai wata shekarar baxan yi joining ynxu ba gaskia"
Murmushi Baffa yai yace "Alhamdulillah dama ai yardar taka kawai muke Jira tunda dai baza ama dole ba Allah yai muku jagora"
A kasan lebensa ya amsa da Ameen, daga haka ya kwantar da kansa a jikin kujerar yana tunanin yadda zai fara lecturing a university sufa su Abie gani suke kamar shiririta yake yi baya maida hankali a companyn da yake aiki, wani malalacin murmushi yai yana tuna zanen gidan da yai mai matukar daukar hankali kasancewar sa kwararren Architecture...
Baffa ganin yadda yai yasa shima yaja bakinsa yai shiru ya maida Kallonsa kan TV yana kallon Sunna TV...
*******
Cikin nasara muka fara waec don Alhamdulillah ina da basira sosai, satin mu biyu da fara waec mukayi yi jamb kamar dai yadda yake duk Wanda yai jamb hankalin sa ba'a kwance yake ba har sai yaga result to nima haka yake a gurin na, duk da Alhamdulillah ina saran na yi abin kirki tunda nasan fiye da rabin questions din kuma na amsa su sbd nacin karatun da nai akan jamb din, ga kuma Abba yana tayani kullum da daddare sai ya mun lesson kasancewar sa principal ne a wata makarantar gwamnati.
Jiran result nake yau sbd tun jiya an fara saki muma yau muke saran za'a saki namu, a hankali na janyo sabuwar wayata Infinix wacce Abba ya siya min satin dana fara waec ya bude min email da WhatsApp a ciki sbd wasu abubuwan ana turowa ta WhatsApp bama masu yin waec, kafin ya ban wayar sai da ya min nasiha sosai akan yadda zanyi amfani da wayar kuma ya ja mun kunne, ranar daya ban wayar su Aisha sunfi ni murna ma, Mimi kuwa sbd murna ranar ko kofar gida bata je ba tana tare dani motsi kadan zata ce nai mata hoto.
A hankali na janyo wayar na Kara tura message ga numbern da za'a turo mana jamb result dinmu ta ciki, ai kuwa ko 3 minutes ba'a dauka ba message ya shigo ta numbern, a zabure na mike ina yarfe hannuna ciki na na juyawa sbd tsoron abinda zan gani.
Da gudu na fada palourn mu ina haki, dagowa Umma tai ta kalle ni kafin tai tsaki ta juya tace "ke kuwa wani lokacin kamar baki da kai ynxu meye na fado min a guje kamar yarinya"
Yarfe hannu nake kamar zan fashe da kuka na mika mata wayar nace "Umma duba min an turo min result dina na Jamb wallahi tsoron budewa nake Umma"
Hannu tasa ta karbi wayar ta shiga message dn ta duba, da Dan karfi tace "Alhamdulillah ya Allah"
Tsugunnawa nai na dafa hannun ta nace "Umma nawa naci nayi kokari ko"
Wayar ta miko min fuskar ta dauke da murmushi mai nuni da tsantsar farin ciki, cikin rawar hannu na karbi wayar na duba, ihu nasa cikin murna kafin na kalle ta nace "Umma 228 na samu Alhamdulillah"
Itama dariya tai tace "Maza Kira Abbanku ki fada masa don shima naga alama komai yake cikin sanyin jiki yake yau yana jiran yaji nawa kika samu"
Da sauri na danna numbern Abba sai da ta kusa katsewa sannan ya dauka, yana dauka ko magana ban bari yai ba nace "Abba Albishirin Ka"
Murmushi yai yana sauke ajiyar zuciya daga Jin muryar ta yasan ta samu point din da take so cikin zakuwa dason sanin nawa ta samu yace "Goro fari kar"
Dariya nai nace "Abba 228 na samu Insha Allah in naci waec dita nima next year zan shiga university"
Dariya shima Abba yai yace "Alhamdulillah har an fara maganar university kenan toh Allah ya bada sa'a ya tabbatar da alkhairin sa"
Murmushi nai nace "Ameen Abba sai Ka dawo" kashe wayar nai na zauna ina kallon Umma da take kallona, dariya nai nace "wallahi Umma tunda aka fara cewa an saki result nake gudawa ynxu ma fa wata nake ji bara naje nayi kafin su Mimi su dawo daga islamiyya yau wainar fulawa zan mana"
Tabe baki Umma tai tace "ku kuka sani nidai bazan ci wannan wainar taki ba wacce kuke cikawa yaji duk ta batawa Mutum ciki"
Mikewa nai ina dariya nace "Ummanmu kenan ai Abba yana ci nasan in nayi zai ci Shi"
Kitchen na shiga na dora abincin dare ina yi ina duba Physics dina, bayan na gama daki na koma na kwanta akan gado.
Janyo wayata nai na bude WhatsApp anan naga kowa yana tura nawa ya samu a jamb, Wanda yaci na tayasu murna wadanda suka fadi kuma nai musu jaje, wata Halima Umar ceh ta tambaye ni kona duba nawa kuma nawa na samu, screenshot din danai na tura musu, nan suka hau taya ni murna don kusan dukan su nafi su samu.
Safiya idi ce tace “dama Batul Auwal kokarine dake shiyasa bakya shiga cikin mutane ana hira” emoji din murmushi kawai na tura musu don bana magana sosai a group din haka kuma ko a school ban cika magana ba don bana son tashin hankali mutane da yawa sunsha samu na su fada min irin gulma ta da ake akan wai bana shiga cikin jama'a ana hira dani sbd ina da kyau kuma ina da kokari sai dai kawai nace Allah ya kyauta don ni tun da Mimi tazo duniya naja jikina da mutane sbd wulakanci da nuna kyama da wasu suke min, wai a haka don Abba ya chanja min makaranta knn ma.
Ina kwance ina game Mimi ta fado jikina tana fadin "Washhh Maa dita bayana lugude yake"
Ajiye wayar nai ina dariya nace "Mimin MAA dinta bayan ne yake lugude"
Lumshe idonta tai tace "uhm Maa na gaji sosai kawai ki barni na kwanta bacci abuna"
Mikewa nai nace "tashi magriba ta matso ki bari in anyi isha sai ki kwanta ko baki so ki samu ladan sallah ne"
Turo baki tai tace "inaso mana Maa"
Kaya na chanja Mata muka fito Palour anan nake fadawa su kamal nawa na samu a jamb, sai sabuwar murna ta barke mana Umma na zaune tana kallon mu fuskar ta dauke da murmushi, a kullum ta kalli yaran nata taga yadda suke hada kansu komai tare suke farin ciki ke lullube ta tana addu'ar Allah ya cigaba da hada mata kan yaran ta.
Sai bayan Magrib da Abba ya dawo hadda tsire ya siyo mana ai kuwa mun ji dadi sosai, wainar fulawar na soya mana nida Aisha sannan na bawa Aisha ta kai palour, sai da na wanke abinda muka bata Wanda Aisha bata wanke ba sannan na shigo palourn, fridge na nufa na dakko mana Zobo Mai sanyi na ajiye a tsakiyar palourn.
Mimi da tun da aka ajiye tsiren take zaune tana kallon ledar ce ta kalle ni tace "Maa party muke yi yau"
Dariya muka sa Mata mu dukan mu, Abba ne ya janyo ta jikin sa yace "zo na sa miki tsiren nan a baki dai ki dandana ko hankalin ki zai kwanta"
Washe yan kananun hakoran ta tai ta zauna akan cinyar sa, cikin nutsuwa muke ci muna hira rabin hirar duk nida Abba ne ina tambayar sa yadda university take yana bani amsa dai dai da tambaya ta, ji nake kamar na janyo lokaci na ganni a university a matsayin student, bayan mun gama physics na dakko Abba yana kara koya min inda yake ban wahala kasancewar Shi zan rubuta gobe sai wajen 11 na tafi daki lokacin Mimi da Aisha sun dade da bacci Nima fita nai toilet na kama ruwa nai alwala, kwanciya nai a gefen Mimi ina fuskantar ta lumshe idona nai da hawaye ke son zubo min a hankali na dora hannuna akan fuskar ta nace "INA KAUNAR KI MIMI duk ta yadda aka same ki mu muna sonki sosai kuma zan kasance mai kaunar ki har karshen rayuwa ta."
Kallon fuskar ta nake da bana gajiya da kalla ina tunanin duk yadda akai Mimi da Mahaifin ta take kama nidai kowa ya ganni yasan bana kama da Mimi don Mimi fara ce tass har wani jaja take ni kuma baza a kirani da baka ba kuma bana cikin jerin farare, kuma bankai Mimi manyan ido ba don idona madaidaita ne, hanci ne kawai za'a dan iya kamanta mu shima don dukkan mu muna da dogayen hanci ne amma ni nawa hancin yafi na Mimi siriri, sai lips inda na Mimi suke sirara kuma kananu nawa kuma madaidaita ne kuma suna da dan tudu kadan sannan a zagaye suke, ko gashin kai nawa da nata ya banbanta ni nawa kana gani zaka ga gashin mune na hausawa dai dai misali, nata kuwa yawansa da tsantsin sa yafi kama dana larabawa.
Maganar kyau kam nasan Mimi ta fini kyau nesa ba kusa ba kuma ba inda ta dakko ni, Murmushi nai kawai ina ja mata hular ta data zame sai kuma na hade rai ina jawa kowa ye mahaifin Mimi Allah ya isa don haka ya zamar min jiki in har zan kalli Mimi sai na tsinewa Babanta, ina wadannan tunanin har bacci ya dauke ni....
Asuba ta gari Batul🥱
***