TASWIRAR KADDARA

Page 8

by @oumamani



*TASWIRAR KADDARA*




   




DijahAM(Oum Amani)





Page 8







BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM






   Tun daga kafar sa na fara kallo yana sanye da takalmi half cover Wanda ya bayyana fatar kafar sa fara tas mai sirki da ja, a hankali na soma bin jikin sa da kallo yana sanye da three quarter light blue sai rigar sa armless dark blue, idona ne ya sauka akan tattoo din hannun sa na zaki sai kuma jelar micijin da ta biyo ta gefen wuyansa, a hankali na daga kaina zuwa fuskar sa wani irin bugawa kirjina yai dahar Saida na dafe hijab dina.




Kamar su daya da Mimina, Mimi diyata yarinyata suna kama kamar yayi kaki ya tofar idonsa bakinsa girar sa har yanayin gashin sa dukda yayi aski amma ba salsal yai ba aski yau irin na yan iskan samari, kara kure fuskar sa da kallo nake ko zanga wani abu daya banbanta shi da Mimina diyata amma babu ina Kara Kallonsa kamannin sa da Mimi suna Kara bayyana.




Yatsina fuska Azlan yai yana kallon ta ganin yadda ta zuba masa ido tana kallon sa har wani Kara bude ido take, cikin takunsa ya fara takowa har ya iso daf dani, ganin haka yasa na ja baya kadan amma still idona na cikin nasa ina ganin ikon Allah har irin kallon da yake haka Mimi take kallo.




Dan lasar lips dinsa yai cikin husky voice dinsa yace "hey baki da hankali ne zaki gefa min dutse a mota"




Wani irin kallo nai masa kafin na juya idona Wanda hakan ya zamar min jiki in har zanyi fitsara sai na juya su nace "koh, kai baka lura dacewa Ka kusa take min kafa bane ko baka gani ne?"




Ware manyan idonsa yai akanta  cikin kufula yace "kutttt***** ke ni kike zagi saboda baki da tarbiyya"




Kallon sa nai tundaga kasa har Sama kafin na tsaida idona akansa nace "sannun Baba in Ka koya min tarbiyyar ai ba lefi bane"




Matso ni ya shiga yi ina baya cikin bacin ran da ya taso masa don tunda yake ba'a taba zagin sa haka ba sai gashi wata kwaila tana zaginsa akan titi, ganin ina baya yasa shi tsayawa yace "ki tsaya na koya miki tarbiyyar mana"




Miyau na hadiya don Allah ya sani na tsorata da yadda yake biyo nin nan gashi hanyar ba mutane sosai, kallon cilla nai daya sunkuyar da kai harara na balla masa da sauri ya karaso gun da muka tsaya yace "kayi hakuri don Allah kuskure ne"




Takaici ne ya kamani hakan yasa nace "Kai cilla meye zaka dinga wani basa hakuri bayan shi ya kamata ya bamu hakuri, bige mana kafafu ya kusa yi fa, daya murje mana yatsu ya gudu shikenan ya nakas tamu dama su masu kudi wasun su shegen iya mugunta ne dasu"




Cikin neman sulhu cilla yace "uwar dakina mubi komai a sannu kinji"




Tsaki naja nace "amma ka bani kunya bansan cewa kana da tsoro ba sai yau kai ynxu wannan ne zai baka tsoro"




Rungume hannu Azlan yai yana binta da kallo cike da mamaki yarinyar da zata yi sa'a da Mufeeda autar gidan su itace Take tsaye a gabansa tana zabga masa rashin kunya haka, cikin wata murya yace "Ashe bakin ciki ne yasa kika wurga min dutse a mota sbd kinga ina da kudi"




Baki na bude ina kallon sa kamar zanyi magana sai kuma nai Shiru kawai na kalli cilla, cikin takaici na warci takadduna a hannun cilla na tsallaka titi ina tafe ina masifa gefe daya kuma zuciya ta tana wani irin bugu sbd kamannin sa da ya tsaya min a wuya.




Cilla ne ya karaso inda yake yace "kayi hakuri don Allah uwar dakina ce wani lokacin tana da zafi amma bata da damuwa kuma ita bawai bakin ciki ne yasa ta wurga maka dutse ba kawai yadda kaso take mune kuma kayi gaba abin ya bata haushi”



Tabe baki yai kafin ya juya ya shige motar sa yaja da mugun gudu ransa na baci fuskar sa har tayi ja sbd bacin rai badaban duka ba dabi'ar sa bace ba abinda zai hanasa rufe wannan fitsararriyar yarinyar da duka.




Kwafa yai kawai har ya isa gidan Baffa, yana zuwa tun daga waje yake ganin motoci karamin tsaki yai shifa wannan meeting din ba karamin takura sa yake ba.




A waje yai parking motar sa shima ya shigo gidan kansa tsaye, tun daga kofar babban palourn baffa yake jiyo hayaniya da magana na tashi ana dariya, girgiza kai yai yasan yau da ciwon kai zai kwana sabodawannan hayaniyar da zai shiga.




A hankali ya tura kofar ya shiga bakinsa dauke da sallamar da shi kadai yasan yai kayansa, gaba daya mutanen palourn dagowa sukai suna kallon sa, hakan yasa shi hade rai sosai dama ga bacin ran da ya kunsa kafin ya shigo.




Cikin takunsa na cikakken namiji kuma lafiyayye ya nufi gurin Baffa dake zaune a 1 seater, a hankali ya zauna a kasa kusa da kafar sa, dauke kansa yai kawai ya kasa bude baki ma ya gaishe sa shi sai ynxu ma yake mamakin kansa da har ya tsaya ya biye mata yau shine rana ta farko daya tsaya gaba da gaba da mace sukai musayar yawu sukai magana don shi baya tsayawa ma a kusa da mace Sam sbd gudun raini ko Mufeeda zai wa magana sama sama yake ya wuce.




Baffa ne da ya zuba masa ido saboda tun shigowar sa ya lura ransa a matukar bace yake ya dora hannun sa akan gashin sa yana shafawa a hankali, lumshe ido Azlan yai yana sakin ajiyar zuciya ba abinda yake hangowa sai fuskar ta tana juya ido da tsuke baki tana masa rashin kunya da sauri ya bude idonsa da suka juye suwa jaa sai kuma kawai ya saki wani murmushi yana shafa gemun sa.




Da mamaki Baffa ya zuro kansa ya leka fuskar Azlan ganin da gaske murmushi yake yasa shi fadin "ZAKI meye kuma nake gani haka"




Dago idonsa yai ya sauke akan Baffa kauda maganar yai ta hanyar ce masa "Ina wuni"




Gyada kai Baffa yai don ya gane ma'anar hakan da yai baya son ayi maganar knn.




Juyawa Azlan yai ya kalli Uncle Mustapha kanin Abie ne kuma tasu tazo daya sosai don baya takura masa sai dai ma duk lokacin da suka hadu zai masa wa'azi ne akan ya rage wasu halaye da yake mara sa kyau, Amma sam baya masa fada kasancewar sa mutum ne mai sanyin hali yace "Good Afternoon Uncle M"




Murmushi Uncle M yai yace "Afternoon Son ya kk ya kuma aiki"




Lumshe idonsa yai yace "Alhamdulillah Uncle M"




Maida duban sa gun Mommy yai itama kanwa ce gurin Abie kuma yayar Uncle M, ita kam mace ce mai masifa da kuma zafi don har tafi Abie zafi kuma tana da nuna isa da iko akan komai, jinin su Sam baizo daya da Azlan ba saboda yadda take son taga tana juya su Shi Sam baya yadda da haka.




Dan rage fara'ar sa yai yace "Good afternoon Mum"




Sai da ta tabe baki tace "sannu bature da baza ka iya gaishe da mutum da yaren hausa ba sai dai Ka masa yaren nasara"




Kankance ido yai yace "to Mum”




Cikin masifa tace "ni kake fadawa haka Azlan wai Kai mai yasa baka da kunya ne gaba daya dama xaman nan da mukai kai muke jira kawai kuma akan ka akai wannan zaman, halayen Ka sun ishe mu kana kallon Dan uwanka shekarar sa biyar da aure amma kai kana zaune ba abinda kake sai shashanci"




Baffa ne yace"Ke Hafsatu dakata mana ki rage tsaurin maganar ki ai ba ta haka zaki masa magana ba koh"




Hade rai tai tana juya fuska cikin Jin haushin katse ta da Baffa yai itafa badon komai take son ayi maganar auren Saba sai sbd diyarta Zainab data mace akan son sa amma in ba haka ba ita ina ruwanta bata shiga sabgar sa sbd bashi da kunya ko kadan.




Kallon yaron palourn baffa yai yace "ku shige dayan palourn zamuyi magana"




Mikewa jikokin sukai gaba dayan su banda Junaid ya rage palourn daga Abie sai Mami da Mama sai Uncle M da matar sa Aunty Sarah sai kuma Mummy da Baffa sai Oga kwata kwata AZLAN.




Kallon Azlan Baffa yai yace "Zaki tunda har ynxu baka da wata budurwa shine muka ce Mai zai hana ka nemi yar uwarka Zainab tunda kowa yasan tana sonka kuma kaga ta gama karatu sai ayi tuwo na maina kawai."




Kankance ido yai kafin ya juya ya kalli Baffa yace "tsoho Umarni kake ban ko kuwa shawara ce"




Murmushin manya Baffa yai yace "shawara ce zaki"




Kallon Abie Azlan yai yadan daga hannun sa yace "ra'ayina ake bukatar ji Abie kar kace nai rashin kunya"




Kallon Baffa yai yace "tsoho bana so, sbd tamin kankanta in na damke ta sai na karya ta kuma gaskia ni ina son mace mai abubuwan laushi manya sbd na dinga matashi da su"




Salati Mummy ta dauka ita da Mama, yayinda Mami da Aunty Sarah suka sunkuyar da kansu kawai, Abie Kam tagumi yai yana kallon Azlan cike da mamakin sa.




Dan gyaran murya Baffa yai yace "kai shine abinda kake so knn amma tarbiyyar zaka duba Zaki"




Dan tsotsar lips dinsa yai kafin yace "da wannan amma baxan iya auren taba tsoho in ba haka ba kuma kullum sai an kaita asibiti an dinke ta, wannan tanadi danai na budurci na na dinga tattalin sa dukda hare haren da ake kawo masa ai dole na samu wacce zata iya jure ni koh kar aje nayi kisan Kai daren farko Nima a kashe ni"




Mikewa Mummy tai cikin masifa tace "wannan budurcin da kake fada na banxa da wofi waye baisan cewa kana zuwa club ba duk dare, kalle Ka don Allah da irin shigar da kake in ba yan uwa ba waye zai baka auren yar sa"




Shima mike wa yai yace "kuma nace bana son auren a wajen da kike ganin baza ba bani ba nan zanje gidan mutunci aban"




Matsowa kusa da shi tai tace "ni kake wa rashin kunya? ko da yake ba laifin Ka bane duk laifin Haj Maryam ne ita ce bata kwafar Ka in kana yi gashi ynxu ai Ka zama tsagera"




Rintse ido Mami tai ita ba abin tai magana ba sbd tana gaban Baffa Amma ta rasa mai ta tsare wa Haj Hafsat da sam bata sonta duk wani abu da zata nuna cewa ta gaza gurin bawa yayanta tarbiyya Shi take fada duk da kuwa Allah ne shaidan ta tana iya kokarin ta akan tarbiyyar yaranta Maza guda biyu da ALLAH ya bata, ko Azlan duk abinda yake tana godewa Allah da baya shaye shaye baya wani abin assha club din da yake zuwa ne kawai da yanayin dressing dinsa, neman Mata ma tana masa kyakkyawan zato cewa bayayi don Azlan baya karya.....




Muryar Mummy ce ta katse Mata tunanin da take tana fadin "iskancin banxa da wofi budurcin yaci ubansa waye baisan cewa kana zuwa club ba in kaje club din salati kake yi ina mata ne a gurin kamar tsirara suna yawo"




Kankance ido Azlan yai yace "in na fahimci zancen ki Hajia Mummy kina tantama akan budurci na dana kewa Iyalina tanadi” dage kafadar sa yai yace “fyn bara na bude Miki ki duba kiga yana nan ko baya nn"




Belt din wandon sa ya cire ya shiga kiciniyar zuge zip din wandon sa, salati mutanen palourn suka dauka, cikin daga murya Baffa yace "Zaki meye hakan me kake kokarin yi"




Cikin rashin damuwa yace"zan bude ne ta duba taga ko budurcin nanan ko baya nn" ya karashe yana karasa zipping wandon sa......












***********




Ina masifa har na isa gida, da Mimi na fara cin karo tana wasa da yar tsana a gurin famfo wai wanka take Mata, zuba mata ido nai ina kallon tsantsar kamannin ta da Mutumin daya kusa bige ni dazu.




Cikin rashin kwarin jiki na isa gurin ta na ce “me kike yi ne Mimi"




Dagowa tai ta zuba min idonta da suka sani Jin cikina ya karta don hatta kallon Mimi irin na mutumin dazu ne. Cikin muryar yara tace "Maa ina yiwa babyna wanka tayi datti"




Murmushi kawai nai mata na mike na shiga palour, ajiye takaddun nai a dakin mu na fito Palour daidai fitowar Umma daga dakin su, Zama nai ina bata labarin yadda muka yi photo copy din takaddun mu.




Cikin nutsuwa Umma tace "lafia kike kuwa Batul mene yake damun ki"




Gaba nane ya yanke ya fadi cikin damuwa na shiga tunanin shin na fadawa Umma mutumin da na hadu dashi yau ko kuma kar na fada mata.......















***