TASWIRAR KADDARA

Page 10

by @oumamani



*TASWIRAR KADDARA*




DijahAM(Oum Amani)



Page 10



BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM






  Washe gari karfe 7 a BUK tai min kasancewar muna da class karfe 8, hall din da zamuyi lecture din na shiga na samu front sit na zauna, ajiyar zuciya na sauke ina gyara zaman sabon hijab dina.




Ban dade da zama ba hall din ya fara cika, kusan kowa a gaba yake zama karfe 8 dai dai lecturern da zai mana maths ya shigo, sai da ya fara da introduction kafin ya fara mana revision akan maths din da muka bari a secondary school, sosai na maida hankali kansa ina saurara wasu abubuwan kuma ina jotting a book dina dana ware don haka.




Sai karfe 10 ya fita amma lecturern da zai mana physics bai shigo ba hakan yasa kowa ya fara sha'anin gaban sa tunda dama physics din muke da 10-12 daka nan kuma muna da interval har sai 1:30.




Maths din da aka mana na maida hankali sosai ina dubawa har lokaci yaja sosai, sai da na gaji na ciro wayata na shiga WhatsApp ina duba status, ina zaune wata tazo ta miko min wayarta tace in sa mata number na za'a bude group ne na yan course din ta yadda za'a na fadan duk abinda ya shafi course din, ban musa Mata ba na sama ta number din.




Sai karfe 1 na mike na fita don zuwa masallaci nai sallah, ban wani sha wahalar neman masallacin ba sbd lokacin da muka zo bude file anan nake sallah, ban dade ba na koma sbd class din da muke da shi tym din, a sit din dana zauna anan na zauna ina Zama lecturern na shigowa, sai karfe 3 muka fito.




A gajiye na fito cikina in banda karar yunwa ba abinda yake yi, cikin gajiya na daga wayata na Kira cilla don shi ma kusan tare muka fito, ina tsaye ya karaso shima dai kallo daya zaka masa kaga gajiya tattare da shi.




Kallona yai cikin kulawa yace "uwar dakina wallahi na gaji ga yunwa dake ta kwakwula ta"




Ajiyar zuciya na sauke nace "Cilla nima nan a gajiyen nake ai bazan sake wannan kuskuren na kin cin abinci ba Allah, kuma sai na dinga tahowa da cake da doughnut da zobo muna ci muna rage zafi in bamu koshi ba muje cafeteria muci abinci ko mu siya waina ko gurasa"




Murmushi yai yace "toh hakan dabara ce sosai don bazan iya wannan horon yunwar ba nifa saboda yunwa wannan lectures ta karshe da mukai ba abinda na fuskanta"




Dan dariya nai nace "Allah ya shirye ka cilla yanzu kace ba abinda Ka kwashe kawai Zama kai kana kallon malamin"




Gyada kai yai yace "ki bari kawai Uwar dakina ai kinsan irin wannan yunwar daina gani ma take sa mutun yi"




Haka muka cigaba da hira har muka fita school din Shi ya tarar mana adaidaita muka hau, ni aka fara sauke wa shi kuma za'a karasa dashi kofar gidan su.




Cikin gajiya nai sallama na shiga gida, da Umma na fara cin karo tana tankade garin dan wake tana gani na ta saki dariya tace "kaga Yan jami'a ya naganki haka kamar wacce aka koro"




Turo baki nai nace "Umma ina wuni"




Dariya tai tace "lafia qalau ya makarantar"




Zama nai akan tabarma nace "Hmmn Alhamdulillah, Umma duk abinda aka mana yau na gane sai dai yunwar dake cinye min yan Hanji"




Da mamaki tace "ba Abba ya baki kudi ki sayi abinci ba in kinji yunwa"




Mike wa nai nace "Hmm Umma tsautsayi yasa nai tunanin bazan ji yunwa ba ai kuwa na azabtu ai daga yau da cake zan na zuwa Allah"




Kitchen na shiga na zubo abinci na zauna ina bawa Umma labarin yadda yau ta kasance a school, sai da na koshi naji dai dai sannan naje nai wanka, ina fitowa sallar la'asar nai na mike kafafuna na kalli Umma dake kan sallaya tana jan carbi nace "Umma kuma wai a haka fa don karfe 3 na dawo yau gashi gobe har 6 zan Kai tab ashe haka ake Shan wahal




Tabe baki Umma tai tace "tukunna ma yarinya"




Daren ranar gaba daya nayi Shi ne ina bawa su Abba dasu Aisha labarin makarantar da yadda take.




Cikin satin sosai na maida hankali na akan karatu duk da bawai an shiga cikin karatun bane introduction kawai ake mana amma na nutsu kullum in ina school in har bamu da class zama nake nayi karatu na, in kuma cilla shima bashi da class muje mu zauna a cafeteria muci cake dinmu kowa ya duba littafi ko kuma muyi hira, sosai Amincin mu da cillah ya Kara daduwa saboda tare muke zuwa mu dawo sai dai in zan rigasa shiga lecture ne shine kawai nake rigasa tafiya.




Ban Kula kowa a course mate dina tsakanina dasu gaisuwa  ce shikenan sai dai kuma ina maida hankali ina karantar su wasu tunda ga satin farkon zaka gane sun shigo show off ne kawai duba da yanayin shigar su.




A cikin satin farko lecturer da zai dinga mana physics shi kadai ne bai shigo mana ba, muna da physics har biyu a sati amma bai shigo ba sai dai an fada a group din da aka bude cewa uzuri ne ya hanasa zuwa amma sai shigo wani satin insha Allah.




Ranar Monday kamar yadda muke da lecture tun karfe 8 da wuri na shigo school kuma na samu front sit bakin window na zauna, har malamin da zai mana maths ya shigo ya fita, yana fita Wanda zai mana physics ya shigo.




Jin class din yai shiru kamar anyi ruwa an dauke yasa ni dagowa don ganin dalilin dayasa class din Shiru haka, tun daga kafar sa na soma kalla gabana yana bugawa da karfi yana sanye da takalmi boots black colour sai wandon jeans fari kar sai Riga daya sa black wacce ta dan kamasa kansa sanye yake da p-cap, a hankali idona ya fada cikin nasa daya sha kwalli sosai sai sheki yake, kallo daya yamin kusan a tare muka janye idanun mu.




Cikin faduwar gaba nake tunanin badai shine malamin namu ba tab, jinai cikina yayi kugi da yasani saurin dafe cikin ina tuna rashin kunyar danai masa.




Azlan kuwa kallo daya yai mata ya janye kansa a ransa yace lallai wato shiyasa tai masa fitsara ashe tashen balaga take yi ita zata shiga jami'a, kankance idonsa yai bayan yadan lashi jajayen lips dinsa ya fara bayani cikin harshen turanci.




Yadda ya hade rai yana bayanin yasa ni maida hankali sosai ina jotting duk wani Abu mai muhimmanci don jikina naban yadda nai masa rashin kunyar nan tsaf zai iya bani carry over.




Hour biyu ya dauka ya fita bayan ya dauki attendance kuma bai fita ba Saida ya bamu assignment yace ayi submitting gobe karfe 8 in ya wuce 8 bazai karba ba, yana fita aka fara magana akansa matan ajin sai zuzuta kyan sa suke suna fadin shine sabon lecturer da ake maganar sa Ashe.




Nidai tagumi nai na zubawa assignment din ido, ganin hakan bazai fishshe niba yasa na fara solving assignment dina tunda yace gobe karfe 8 yake so ayi submitting nasan class rep za'a bawa, saukin tama goben muna da class karfe 8.




Sai da na gama assignment din na kara dubawa na tabbatar nayi daidai sannan na mike na fita don zuwa cin abinci, a inda muka Saba haduwa da cilla na gansa yana zaune yana cin meat pie da lemo, yana gani na yace "uwar dakina tun dazu nake zuba ido ai naga baki fito ba ina shirin in na gama ci naje na duba ko lafia sai gaki lafia kuwa?"




Zama nai na sauke ajiyar zuciya nace "Hmm cilla ina ruwa kusa da Kada wallahi"




Da mamaki yace "lafia wani abun ya faru ne?"




Sosa gira ta nai nace "ai komai ma ya faru Cilla, ina wannan mutumin mai kama da Mimi Wanda ya kusa kade min kafa na masa rashin kunya"




Gyada kai cilla yai yace "ai bazan manta Saba uwar dakina kodan yadda yake kama da shashalelen ki"




Sai da nayi murmushi kafin na girgiza kai nace "shine lecturer dinmu na physics wallahi ni nasan da kyar in bazai ban carry over ba ya rama abinda nai masa"




Zaro ido cilla yai yace "kice min wannan maganar ba haka bane uwar dakina"




Dan cizar lip dina na kasa nai nace "Hmm cilla ina ruwa gashi daga gani bashi da kirki har ya bada assignment fah kuma wai ayi submitting gobe in ya wuce 8 bazai karba ba ai assignment din na tsaya nai shiyasa ban fito da wuri ba".




Tagumi cilla yai yana ajiye meat pie dinsa a gefe yace "da damuwa uwar dakina Allah yasa dai bai gane kiba"




Girgiza kai nai nace "ya gane ni don Saida muka hada ido da shi sannan ya janye idon sa ni bansan ya zanba har wani zazzabi ma nake ji"




Nan mukai zugun zugun nida Cilla har lokacin sallah yai duk sona da abinci kasa cin komai nai, sallah naje nai na koma hall din da xamuyi next lecturen mu, ana tashi mun fito nida cilla muna tafiya kamar ance na daga idona suka sauka akan sa Yana tsaye tare da wani suna magana shima dago idonsa yai ya zuba a fuska ta kuma yaki dauke wa ganin haka yasa ni balla masa harara na murguda masa baki, sai kuma na zare idona ina dafe bakin, ganin ya ware min manyan idon sa irin ni dinnan, da sauri na juya na kalli cilla Naga hankalin sa Yana gurin nema mana abin hawa, sai nai Shiru kawai gabana yana faduwa 




Shi kuwa Azlan da mamaki yabi bayanta da kallo, gyada kai yai yace "uhm lallai"






Ranar haka na wuni a gida suku suku, Umma ta tambaye ni har ta gaji daga karshe sai ce Mata nai malamin physics din da nace mata bai shigo bane ya shigo kuma har ya bamu assignment yace muyi submitting gobe ai ko Karen hauka ne ya cije ni baxan ce Mata wanda ya kusa bige ni bane sabon lecturer dinmu karshe sai dai tace Allah ya kara maganin mai tsiwa.



Washe gari da wuri na fita sai dai na kasa samun abin hawa da wuri sai wajen 7:45 na samu adaidaita kamar zanyi fitsari a wando haka nake ji, ban shiga school ba sai 8:15 cikin sanyin jiki na nufi hall din da muke da lecture tuni lecturer ya shiga amma ganin baya hana wadanda suka zo a makare yasa na shiga cikin sanyin jiki, yau a baya na zauna don ba waje a gaba.




Sai 10 ya fita yana fita na mike na nufi gurin class rep din mu, cikin damuwa nace "Hamza har anyi submitting assignment din jiya koh"




Daga mun kai yai yace "nima nayi mamaki dana ga baki zo da wuri ba ya akai haka"




Kamar zanyi kuka nace "wallahi abin hawa na rasa shiyasa, yanzu don Allah ba yadda za'a yi Ka kaimin nawa tun jiya na gama wallahi"




Zare ido yai yace "wa? ai saidai kije ki Kai masa ko zai karba don nikam ba ruwana, da na kai masa saida yace na Kara fada in 8 ya wuce duk Wanda yakai masa bazai karba ba"




Shiru nai cikin damuwa nidai banason nayi missing wannan assignment din don yace zai iya Zama first test dinmu, ajiyar zuciya na sauke nace "toh don Allah ina ne office din nasa"




Kwatance yai min na fita don bamu da lecture sai 11, sai da na fara biyawa na taho da cilla Wanda bai shigo ba sai 9 tunda 11 yake da lecture, tare muka nufi office din nasa gaba na Yana faduwa.




A kofar office din muka tsaya na daga kai na kalli inda aka rubuta sunansa *AZLAN MUHAMMAD ABDULLAH* knocking nai sau daya Jin shiru yasa na Kara wani, ciki ciki naji ance “come in”.




A hankali na tura kofar muka shigo nida Cilla, sai da na sauke ajiyar zuciya jin office din yana wani sassanyan kamshi ga sanyin AC dake tashi, dago kaina da zan suka fada cikin nasa yana zaune akan doguwar kujera ya mike kafafun sa yana sanye da kananun kaya kafarsa ba takalmi sai sheki take.




Zuba min ido yai shima tun daga Sama ya kalle ta tana sanye da hijab brown colour dogo har kasa, sai jakarta data rataya shidai kullum da hijab yake ganin ta, maida dubansa kan cilla yai dake bayanta kansa a kasa yana mamakin meye alakar ta da wannan namijin da kullum zaka gansu tare suna tafiya kuma da dukkan alamu ba gida daya suke ba.




Maida duban sa kanta yai hakan yasa ni bude baki a hankali nace “GOOD MORNING SIR.............”




















***