THE MAN FROM THE FLIGHT AND THE NEW HORIZON
*KADDARAR ZUCIYA*
*CHAPTER EIGHTEEN: 18*
*THE MAN FROM THE FLIGHT AND THE NEW HORIZON*
*JIDDAAH BARKUM*
—————
Washegari da safe, gidan Alhaji Kabeeru ya shiga hayaniyar shirin tafiya, kowa yana cikin wani irin motsi, yayin da ake tabbatar da cewa komai ya kammala kafin lokacin barin gidan ya yi, Humaira kuwa, tana ta zagaye gidan tana neman inda ta ajiye wayarta, tana duba kan sofa, gefen tebur, har ta fara leƙa cikin handbag ɗinta, Inteesar, wadda take tsaye a bakin ƙofar ɗakinta tana ƙoƙarin kammala shirya kayanta, ta kalleta ta fashe da dariya, “Wallahi Humaira, idan kika sake manta wani abu yau, zan barki a gida!” ta faɗa tana nuna ta da yatsa, Humaira ta tsaya cak, ta ɗago kai tana kallonta da wani irin kallo, “Excuse me, Madam Organized! Ni fa ba kamar ke ba ce da kike son komai ya kasance in perfect order,” Inteesar ta ɗaga gira, “At least, I know where my things are!” “Really? To ina key ɗinki na jiya yake?” Murmushin Inteesar ya ɗan tsaya, ta sauke kanta tana duba bag dinta, sannan ta kalli Humaira, “Humaira!” Humaira ta fashe da dariya, “Exactly! Don’t come for me when your own case is not clear,” dariya suka sa gaba ɗaya, har Mommy Haleema da ke fitowa daga ɗakin cin abinci ta tsaya tana kallonsu cikin murmushi, “Allah Ya kiyaye hanya, ‘ya’yana, ku isa lafiya, ku ji daɗinku, kuma kar ku manta da kiranmu idan kun isa,” “In Shaa Allah, Mommy,” Inteesar ta amsa cikin annashuwa, Humaira kuwa ta ƙarasa gare ta ta rungume ta, “Don’t worry, Mommy, za mu kula da juna,” Mommy ta shafa kanta, “Allah Ya Kai ku lafiya,” ba da daɗewa ba, Daddy ma ya fito, yana sanye da farar shadda, fuskarsa cike da annashuwa, da ya ga Inteesar, sai ya buɗe hannayensa, “Princess ɗina, zo nan,” Inteesar ta ƙarasa gare shi da sauri ta rungume shi, “Daddy!” Ya rungume ta sosai, sannan ya ɗan ja ta baya yana kallon fuskarta, “Ki huta sosai a Lagos, ki ji daɗinki, ki more lokacinki, you’ve worked hard enough,” ta yi murmushi, tana gyada kai, “In Shaa Allah, Daddy,” “Ki kuma saurari Anty Zainab, kada ki yi ta wahalar da kanki da komai, wannan tafiyar hutawa ce, ba wani sabon assignment ba,” Inteesar ta fashe da dariya, “Okay, Daddy, I promise,” “Good girl,” bayan sun yi sallama da iyayensu, Inteesar da Humaira suka shiga mota, aka nufi filin jirgi.
A lokacin da suka isa airport, aka kammala dukkan shirye-shiryen tafiya, sannan suka zauna a wurin jiran boarding, Humaira tana ta duba wayarta, yayin da Inteesar take zaune cikin natsuwa, tana kallon mutanen da ke ta zirga-zirga a filin jirgin, bayan ɗan lokaci, wayarta ta fara vibrating, ta ɗauko wayar, sai ta ga number da ya bayyana a screen ɗin, ta yi shiru na seconds kaɗan, “He’s here already?” ta tambayi kanta a hankali, ta ja numfashi, sannan ta ɗaga kiran, “Assalamu Alaikum,” “Wa alaikumus salam, Intee,” muryar Aliyu ta fito cike da farin ciki, “Na iso,” Inteesar ta ɗaga gira, “Already?” “Eh, ina parking area yanzu,” “Okay, we’re at the waiting area,” “Alright, zan shigo yanzu,” bayan sun katse kiran, Inteesar ta ajiye wayarta, ta gyara zamanta, Humaira, wadda ta lura da yadda ta canza yanayi, ta matsa kusa da ita sosai tana kallonta amma batace komai ba, bayan mintuna kaɗan, wani dogon mutum ya bayyana yana takowa cikin natsuwa, sanye yake cikin farar shadda mai sauƙi wadda ta yi masa kyau sosai, agogo mai kyau yana ƙawata hannunsa, yayin da takalminsa ya ƙara nuna tsaftar shigarsa, fuskarsa tana ɗauke da annuri, amma abin da ya fi jan hankali shi ne murmushinsa mai natsuwa, yana tafiya ba tare da gaggawa ba, idanunsa suna bin mutanen da ke wurin har suka sauka a kan Inteesar, da idanuwansu suka haɗu, murmushin da ke fuskarsa ya ƙara faɗaɗa, ya ƙaraso gare su, “Assalamu Alaikum,” “Wa alaikumus salam,” Inteesar ta amsa cikin sanyin murya, Humaira kuwa ta dinga kallonsu a hankali, tana ƙoƙarin ɓoye murmushin da ya fara bayyana a fuskarta, Aliyu ya gaishe su cikin mutunci, sannan ya juya gare ta, “Nice to meet you, ni sunana Aliyu,” “Nice to meet you too,” humaira ta amsa, tana kallonsa daga sama har ƙasa cikin wani irin bincike na boye, Aliyu ya lura da yadda take kallonsa, amma bai ce komai ba, sai ya juya ya kalli Inteesar, wadda take ƙoƙarin nuna kamar komai normal ne, “Finally,” ya faɗa cikin murmushi, Inteesar ta ɗan haɗe gira, “Finally me?” Ya yi dariya a hankali, “Finally na ga fuskar da ta hana ni barci tun ranar da muka haɗu,” Humaira ta danyi murmushi, a hankali ta matso kusa da ita, ta raɗa ƙasa-ƙasa yadda Inteesar kaɗai za ta ji, “Intee, wannan fa ya gama shiga!” Inteesar ta harare ta, Humaira ta rufe bakinta da tafin hannunta, tana ƙoƙarin danne dariya, Aliyu kuwa ya yi murmushi kawai, yana kallonsu cikin nishaɗi, “Don’t worry,” ya faɗa yana kallon Inteesar, “Ban zo nan don na takura miki ba,” sai ya dago wani ƙaramin gift bag, ya miƙa mata, “Ina taya ki murnar gama exams,” Inteesar ta zaro ido, ta kalli jakar sannan ta kalle shi, “Aliyu, wannan kuma meye?” “Nothing much,” ta ɗan girgiza kai, “Ban ce ka kawo min komai ba,” “Na sani,” “Toh me ya sa?” Aliyu ya ɗan karkatar da kansa, murmushi yana ƙara bayyana a fuskarsa, “Because I wanted to,” Inteesar ta yi shiru, ba ta san abin da za ta ce ba, a da, irin wannan abu zai iya sa ta ji kamar ana ƙoƙarin tilasta mata wani abu, amma Aliyu ya miƙa mata kyautar ne cikin sauƙi, ba tare da ya yi wani dogon bayani ko ya sa ta ji dole ne ta karɓa ba, ta karɓi jakar a hankali, “Thank you,” “You’re welcome,” Humaira ta kalli gift bag ɗin, sannan ta kalli Aliyu, “Wai kai ma kana da wannan halin ne? You came prepared!” Aliyu ya yi dariya, “Just a little something to congratulate her,” Humaira ta gyada kai cikin gamsuwa, “Okay, I see,” “Ina jin kamar kuna yi min interview,” Aliyu ya faɗa yana kallonsu, Humaira ta fashe da dariya, “Of course! We have to know the kind of person we’re dealing with,” “Humaira!” Inteesar ta faɗa, tana jin kunya, Aliyu ya ɗan ɗaga hannayensa sama cikin wasa, “Fair enough, I’ll answer your questions whenever you’re ready,” dariya suka sa, kuma a wannan lokacin Inteesar ta tsinci kanta tana murmushi ba tare da ta damu da ɓoye shi ba, a karon farko tun bayan abubuwan da suka faru da ita, ta kasance tare da wani namiji ba tare da zuciyarta ta cika da fargaba ko jin ana matsa mata ba, akwai wani abu game da Aliyu da yake ba ta natsuwa, ba ya gaggawar neman amsa, ba ya tilasta mata ta yi magana idan ba ta son magana, kuma duk da shiru da rashin kulawar da ta yi masa tsawon watanni, har yanzu yana iya zuwa gare ta da murmushi, ba da daɗewa ba, sanarwar boarding ta katse tunaninta, Aliyu ya kalli inda ake shiga filin da jirgi ke di a passengers, sannan ya koma ya kalleta, “Looks like it’s time, ku je kar ku yi missing flight,” Humaira ta matsa da sauri tana gyara handbag ɗinta, “Mun gode sosai,” Aliyu ya gyada kai, “You’re welcome,” sai ya juya ya kalli Inteesar, “Ki kula da kanki,” Inteesar ta ɗan yi murmushi, “Nagode,” ta yi kamar za ta juya ta tafi, amma muryarsa ta sake kiranta, “Inteesar?” Ta tsaya, ta juyo, Aliyu ya ɗan lumshe idanunsa, sannan ya buɗe su yana kallonta cikin natsuwa, “I’ll wait,” Inteesar ta yi shiru, ya ɗan yi murmushi, sannan ya ƙara da cewa cikin murya mai taushi, “Zan jira,” kalmomi biyu ne kawai, amma saboda wani dalili, zuciyarta ta yi wani irin bugawa da ba ta yi tsammani ba, ta kasa cewa komai, Aliyu bai matsa mata da ƙarin bayani ba, ya tsaya yana kallonta cikin murmushi, sannan ya ɗan gyada kai kamar yana mata sallama, Inteesar ta juya ta nufi wajen boarding tare da Humaira, amma har suka isa ƙofar shiga, tana iya jin kalaman nasa suna maimaituwa a ranta, I’ll wait, Humaira ta juyo da sauri tana murmushi, “Intee…” “Hmmm?” “Wannan mutumin yana sonki sosai,” Inteesar ta kau da kai tana gyara mayafinta, “Humaira, bana tunanin soyayya yanzu,” Humaira ta yi murmushi, amma a wannan karon ba ta yi mata tsokana da yawa ba, “Na sani, kuma ba sai kin fara tunanin soyayya yanzu ba, amma dai ki yarda da abu ɗaya,” “Wane abu kuma?” “Not every man is the same,” Inteesar ta yi shiru, Humaira ta ɗan taɓa hannunta, “Ki ba kanki lokaci, Intee, ba sai kin yanke wani hukunci yanzu ba, just take your time,” Inteesar ta kalleta, sannan ta yi ɗan murmushi, “Thank you,” Humaira ta gyada kai, “Always,” su biyun suka shiga jirgi, amma kalaman Aliyu suka ci gaba da yawo a zuciyar Inteesar, a karon farko cikin watanni masu yawa, ta fara tunanin cewa watakila ba kowane namiji ne yake shigowa rayuwar mace domin ya karya mata zuciya ba, watakila akwai mutanen da suke zuwa ne domin su koya mata cewa har yanzu akwai alheri a cikin mutane, kuma watakila… wannan ba ƙarshen labarinta ba ne.
Suna shiga cikin jirgi suka zauna a mazaunansu, Humaira ba ta ɓata lokaci ba ta juya tana fuskantar Inteesar, idanuwanta cike suke da sha’awar jin labari, kuma murmushin da ke fuskarta ya nuna cewa ba za ta bar ta ta huta ba sai ta samu abin da take so, “Gaskiya Intee, yanzu kam ba ki yi tsirfa ba, dole ki gaya mini gaskiyar lamarin mutumin nan,” Inteesar ta lumshe idanunta, ta ɗora kanta a kan kujerar jirgin, “Humaira, please, what now?” Humaira ta matso kusa da ita, ta rage muryarta, “Wato ashe tun a jirgin farko kuka haɗu, kuma har yanzu yana nuna wannan juriya? Kalli yadda yake magana da ke cikin mutunci, even the way he looks at you…” Inteesar ta buɗe idanunta ta kalleta, “Humaira!” “Okay, okay! I’m just saying,” ta ɗan yi dariya, sannan ta ci gaba, “Amma gaskiya, I like his approach, bai yi kamar wanda yake tunanin dole ne ki amince da shi ba, kuma kin ga yadda ya ce zai jira?” Inteesar ta juya zuwa ga tagar jirgin, tana kallon yadda ma’aikatan airport suke ta motsi a wajen, “Humaira, ba wani abu ba ne mai girma, kamar yadda na gaya miki ne, haɗuwar jirgi ce kawai ta faru sa’ilin da nake kuka ranar da zan tafi Katsina,” ta yi ɗan shiru kafin ta ci gaba, “Shi kuma ya nace akan lallai yana son sanin halin da nake ciki,” Humaira ta gyada kai, “Na gane, amma wani lokacin, abubuwa masu muhimmanci suna farawa ne daga haɗuwa ta bazata,” Inteesar ta yi murmushi kaɗan, “You’re beginning to sound like a relationship coach,” Humaira ta fashe da dariya, “And you’re beginning to sound like someone who’s trying too hard to deny something!” “Ina zan musanta me?” “Nothing!” Humaira ta amsa da sauri, tana ɗaga hannayenta sama, “I’m innocent,” Inteesar ta girgiza kai tana dariya, jirgin ya fara motsi a hankali, sannan ya nufi hanyar tashi, Inteesar ta jingina da kujerarta, tana kallon yadda filin jirgin yake ƙara nisa daga idanunta yayin da jirgin ya fara ɗagawa sama, gizagizai suka fara bayyana a wajen tagar, suna lulluɓe sararin samaniya da wani irin kyau mai ban sha’awa, ta yi shiru tana kallonsu, a cikin ranta, tana jin wani irin ɗumi daga kalaman Aliyu, amma a can ƙasan zuciyarta, tsoron tsohon raunin da ta sha yana nan, yana tunatar da ita cewa ba duk abin da yake fara da murmushi ne yake ƙarewa da farin ciki ba, ta san ba za ta iya barin zuciyarta ta yi saurin yanke hukunci ba, ba yanzu ba, she needed time, time to heal, time to understand herself again, kuma mafi muhimmanci, tana buƙatar ta koyi yadda za ta iya amincewa da kanta kafin ta sake amincewa da wani, sai dai ba ta san cewa a Abuja, wani mutum yana zaune shi kaɗai, yana kallon hotonta a wayarsa, yana ƙoƙarin koyon yadda zai rayu ba tare da kasancewarta a kusa da shi ba, Umar, mutumin da har yanzu yake son ta cikin shiru, duk da cewa ya san ba shi da damar neman komai daga gare ta, kuma a wannan lokacin, wani mutum daban ya fara samun gurbi a cikin zuciyarta, Aliyu, mutumin da bai san irin yaƙin da yake shirin shiga ba, domin zuciyar Inteesar ba filin da aka buɗe wa kowa ba ce, wannan shi ne farkon wani sabon babi, farkon gwagwarmayar zuciya, yaƙin da babu wanda ya shirya masa.
THE LASGIDI VIBE AND WARM WELCOME, saukarsu a filin jirgin sama na Murtala Muhammed Airport a birnin Lagos ya kai su wata sabuwar duniya ta daban, da suka fito daga cikin jirgin, Humaira ta fara nuna farin cikinta, tana kallon ko’ina cikin sha’awa, “Finally! Lagos, here we come!” Inteesar ta yi dariya, “Humaira, we just landed, calm down!” “Calm down? Ke ya kamata ki nutsu, ni kam, I’m ready to enjoy myself!” Suna tafiya zuwa inda ake karɓar kaya ne suka hango Farida, ɗiyar Yaya Adamu, tsaye kusa da motar da aka zo ɗaukar su da ita, Farida tana ta ɗaga musu hannu cikin tsantsar murna, fuskarta cike da annashuwa, “Intee! Humaira!” Humaira ta ɗaga hannunta sama, “Farida!” Farida ta rugo ta rungume su gaba ɗaya, tana dariya, “Welcome to Lasgidi! Kun riga kun san babu zaman banza ko?” Humaira ta yi murmushi mai faɗi, “That’s exactly what we came for!” Inteesar ta rungume Farida, tana jin daɗin sake haɗuwa da ita, “Na yi kewarki sosai,” “Ni ma na yi kewarku! Gaskiya yau kam za mu more, no boring moments, no unnecessary stress, just good vibes!” “Oh Allah na,” Inteesar ta faɗa tana dariya, Farida ta karɓi ɗaya daga cikin jakunkunansu, sannan ta nuna musu motar, “Come on, girls, let’s go home,” tafiyar motar ta kai su cikin wani yanki na gidajen alfarma a Lagos, inda manyan gine-gine suka yi layi cikin tsari, kuma yanayin wurin yake nuna irin rayuwar alfarma da ake yi a yankin, gidan Yaya Adamu babban gida ne na zamani, mai faɗin fili da kyakkyawan tsari, wanda yake kallon wani ɓangare na tekun Atlantika, da suka isa, Inteesar ta tsaya na ɗan lokaci tana kallon gidan, Farida ta yi murmushi cikin alfahari, “Welcome to your home away from home!” Humaira ta juyo tana kallon Inteesar, “See? I told you this trip was going to be worth it,” Inteesar ta yi dariya, “Okay, okay, you’ve made your point,” a babban falon gidan, Yaya Adamu da matarsa Anty Zainab suna jiran su cikin farin ciki da annushuwa, da suka shiga, Anty Zainab ta miƙe ta tarbe su, “Ku zo, ‘ya’yana! Sannu da zuwa,” “Anty!” Inteesar ta faɗa tana rungume ta, Anty Zainab ta shafa kanta cikin ƙauna, “Sannu da zuwa, my daughter, kin yi kyau, amma gaskiya na ga kamar kin ɗan rame,” Inteesar ta yi dariya, “Anty, wannan maganar ramewa fa ta zama kowa ma Haka yake fada !” Kowa ya fashe da dariya, Yaya Adamu ya ƙaraso ya rungume ta, “Princess, welcome! Ya karatun? An gama exams lfy?” “Alhamdulillah, Yaya, mun gama lafiya,” “Masha Allah, Allah ya sa albarka,” “Amin,” ya juya ya kalli Humaira, “Ke ma sannu da zuwa, ku ji daɗinku, gidan nan naku ne,” Humaira ta yi murmushi, “Thank you, Yaya,” Anty Zainab ta nuna musu inda aka tanadi abinci iri-iri, sannan ta ja Inteesar kusa da ita tana shafa kanta, “Intee, gaskiya kam kin canza gari, amma a nan Lagos za mu dawo miki da dukan kyawunki,” Inteesar ta yi dariya, “Anty, even you?” “Of course! Someone has to take care of you properly,” Humaira ta ɗaga hannu, “Anty, please include me too!” Anty Zainab ta yi dariya, “Ke ma kina ciki, Humaira, ku ci abinci sosai, ku huta, sannan ku yi barci, gobe za ku fara jin daɗin tafiyar,” Yaya Adamu ya jinjina kai, “Haka ne, ku huta yau, domin gobe Farida za ta fara kwashe ku zuwa zagayen gari,” Farida ta yi murmushi mai faɗi, “Already have a plan!” Humaira ta bata hannu suka tafa, “Now we’re talking!” Inteesar ta kallesu tana dariya, “Allah ya ba ni ikon jurewa halinku,” Farida ta ɗaga gira, “You’ll thank us later.”
Kamar yadda aka tsara, kwanaki kaɗan suka juya zuwa shagali da nishaɗi, Farida ta zama jagorarsu a duk wuraren da suka ziyarta, tana tabbatar da cewa kowace rana tana da wani sabon abu da zai sa su yi dariya ko su more lokacinsu, a rana ta farko, ta kwashe Inteesar da Humaira zuwa manyan shopping malls, inda suka yi ta zagayawa daga shago zuwa shago, Humaira kuwa, kamar wadda aka saki daga wani dogon zaman gida, ta kasa zama a wuri ɗaya, “Farida! Come and see this bag!” “Humaira, you said that five minutes ago!” Inteesar ta faɗa tana dariya, “Because there are so many beautiful things here!” Farida ta ɗaga gira, “Don’t worry, we have the whole day,” Inteesar ta tsinci kanta tana zaɓen sabbin kaya, takalma, da wasu ƙananan abubuwan da ta daɗe tana son saya, da farko, ta yi niyyar kallon kaya kawai, amma daga baya ta fara jin daɗin sayayya tare da yan uwanta, Humaira ta ɗauko wata riga ta nuna mata, “Intee, this would look so good on you!” Inteesar ta kalleta, sannan ta yi murmushi, “Really?” “Absolutely, go and try it!” Farida ta goyi bayanta, “She’s right, that colour would suit you,” Inteesar ta karɓi rigar, tana murmushi, “Okay, let me see,” a cikin shagon, tana gwada kaya tana kallon kanta a madubi, ta lura cewa fuskarta ta fara ɗaukar wani irin annashuwa da ta daɗe ba ta gani ba, she was slowly returning to herself, ba wai ta manta da abubuwan da suka faru ba ne, amma a wannan lokacin, ba ta bar tunanin abubuwan baya ya hana ta jin daɗin abin da ke gabanta ba, bayan sayayya, suka je wasu wuraren cin abinci, suka ɗauki hotuna, suka yi dariya, har Humaira ta fara korafin cewa ƙafafunta sun gaji, “Please, can we sit down? My legs are officially on strike!” Farida ta fashe da dariya, “Madam, we haven’t even finished!” Inteesar ta kama hannun Humaira, “Come, let’s sit before she finishes us!” Dariya suka sa gaba ɗaya, a wasu ranakun kuma, sun ziyarci kyawawan rairayin bakin teku na Lagos, iskar teku mai daɗi tana kaɗa tufafinsu yayin da suke tafiya a kan yashi, suna jin sautin kukan ruwa yana bugun bakin teku, Farida da Humaira sun haɗe wajen yin rashin ji da tsegumi, suna ta ɗaukar hotuna da yin poses iri-iri, “Intee, come here! Let’s take a picture!” Inteesar ta juya gare su, “Again? We have taken like fifty pictures already!” Humaira ta ɗaga wayarta, “And we’re not stopping!” Farida ta yi dariya, “Just one more!” Inteesar ta girgiza kai, amma daga baya ta ƙarasa wajensu, “Fine, one more,” Humaira ta kalleta da sauri, “Say cheese!” “Cheese!” Inteesar ta amsa tana dariya, suka ɗauki hoton, sannan suka ci gaba da tafiya a bakin teku, a hankali, Inteesar ta fara jin cewa wannan hutun yana taimaka mata fiye da yadda ta yi tsammani, tana sake koyon dariya ba tare da ta ji laifi ba, tana sake koyon jin daɗin abubuwa ƙanana ba tare da tunanin abin da zai iya faruwa a gaba ya hana ta ba, kuma tana sake fahimtar cewa rayuwa tana iya ci gaba, ko da mutum ya taɓa fuskantar wani babban ciwo.
A daren ranar da suka dawo daga beach, Inteesar tana zaune a farfajiyar gidan, tana kallon ruwan teku da ke haskawa a ƙarƙashin hasken farin wata, iskar dare tana kadawa a hankali, tana ɗauke da ɗan sanyi da ƙamshin ruwan teku, a nesa, ana iya jin sautin ruwan, ya na samar da wani irin natsuwa mai daɗi, Inteesar ta jingina da kujerarta, ta lumshe idanunta na ɗan lokaci, ta daɗe ba ta samu irin wannan kwanciyar hankali ba, ba ta tunanin jarabawa, ba ta tunanin abubuwan da suka faru, ba ta tunanin abin da za ta ce ko yadda za ta kare kanta daga wani abu da zai iya sake cutar da ita, a wannan lokacin, tana nan kawai, enjoying the silence, wayarta ta yi vibrating a gefenta, alamar saƙo ya shigo, ta buɗe idanunta, ta ɗauko wayar, number Aliyu ce, har yanzu ba ta yi saving ɗin number ɗin ba, ta kalli saƙon da ya shigo, “Assalamu Alaikum, Intee, ina fatan kina jin daɗin Lagos, ki yi enjoying ɗinki sosai, kuma ki ci abinci sosai, don bana son jin cewa kin sake ramewa,” Inteesar ta tsaya tana kallon saƙon na wasu seconds, sai wani ɗan murmushi ya bayyana a fuskarta, “Even from here?” ta furta ƙasa-ƙasa, tana girgiza kai cikin nishaɗi, ta sake karanta saƙon, sannan ta ajiye wayar a gefenta ba tare da ta ba da amsa ba, ba don tana jin haushinsa ba, a’a, sai dai ba ta san abin da za ta ce ba, kuma ba ta ga dalilin da zai sa ta tilasta wa kanta yin magana ba, ta koma kallon teku, amma a wannan karon, murmushin da ke fuskarta bai ɓace ba, a hankali, ba tare da Inteesar ta sani ba, Aliyu ya fara zama ɗaya daga cikin mutanen da suke kawo mata natsuwa bayan watanni masu tsawo na kuka, tsoro, da ciwon zuciya, ba wai saboda ya matsa mata ba, ba wai saboda ya tilasta mata ta karɓe shi ba, a’a, sai dai saboda ya ba ta sararin da take buƙata, ya girmama shirunta, ya fahimci cewa ba dole ne ta amsa duk saƙonsa ba, kuma ba dole ne ta yi murmushi a duk lokacin da yake magana da ita ba, he was giving her something she hadn’t experienced in a long time, space without pressure, care without demands, and patience without conditions, wasu raunuka ba a warkar da su da yawan kalaman soyayya ba, wani lokaci, ana fara samun sauƙi ne ta hanyar kasancewar wani mutum da ba ya sa ka ji dole ne ka yi wani abu don ka cancanci kulawarsa, Inteesar ta ɗaga kanta tana kallon farin wata da ke haskakawa a sararin samaniya, a hankali ta lumshe idanunta, a karon farko cikin lokaci mai tsawo… ba ta jin tsoro, ba ta jin ana bibiyarta, ba ta jin kamar wani yana ƙoƙarin ƙwace mata numfashinta, sai dai wata nutsuwa da ta daɗe tana nema, kuma ko da yake ba ta shirya ba wa Aliyu wani matsayi a rayuwarta ba, a hankali tana fara yarda cewa watakila za ta iya sanin shi ba tare da ta rasa kanta ba, watakila za ta iya ba da dama ga wani mutum ya nuna mata ko wanene shi, ba tare da ta yi gaggawar yanke hukunci ba, but for now, she was content with the little peace she had found.
A can Abuja kuwa, Yaya Umar yana zaune shi kaɗai cikin duhun falonsa, riƙe da wayarsa a hannunsa, falon ya yi shiru, gidan ya yi shiru, rayuwarsa ma ta yi shiru, sai ƙamshin turaren Oud da ya mamaye gidan, da kuma hoton Inteesar da ke kan screen ɗin wayarsa, ya zauna a kujerar da ya saba zama a kai, yana kallon hoton ba tare da ya motsa ba, a hankali ya lumshe idanunsa, yana jin wani irin ciwo mai nauyi da nadama da ba ya iya bayyanawa, tun da Inteesar ta bar Abuja, gidan ya zama kamar ba gida ba, kafin ta tafi, akwai lokutan da yake jin muryarta daga ɗakinta, ko yana jin tana magana da Nana a falon, wani lokaci kuma zai gan ta tana tafiya da sauri, tana ƙoƙarin guje masa, kuma duk da yadda hakan yake masa ciwo, aƙalla yana ganin ta, amma yanzu? Babu komai, babu muryarta, babu takunta, babu fuskarta a ko’ina cikin gidan, sai dai tunaninta da ya ƙi barin zuciyarsa, ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi, sannan ya ɗora wayar a kan cinyarsa, “How am I supposed to do this, Princess?” ya furta ƙasa-ƙasa, ba wanda zai ba shi amsa, ya san ya yi kuskure, ya san cewa ta rasa amincewarta da shi, kuma babu wani abu da zai iya faɗa a yanzu da zai sa komai ya koma yadda yake a da, ya yi alƙawarin ba zai sake takura mata ba, ya yarda cewa ba shi da wani matsayi a zuciyarta da zai ba shi damar neman wani abu daga gare ta, amma akwai wani abu guda ɗaya da zuciyarsa ta kasa koya, yadda ake rayuwa ba tare da Inteesar ba, ya ɗauki wayarsa ya sake kallon hotonta, a wannan karon, bai yi ƙoƙarin murmushi ba, sai ya sauke kansa, yana jin yadda nadama take ƙara nauyi a zuciyarsa, domin wasu kuskure ba sa karɓar gafara cikin sauƙi, kuma wasu soyayya suna makara ne lokacin da komai ya riga ya lalace, ya rufe screen ɗin wayar, ya jingina da kujerarsa, sannan ya lumshe idanunsa, a can Lagos, Inteesar tana fara samun nutsuwa, tana sake koyon dariya, tana sake koyon rayuwa, kuma a hankali, tana fara fahimtar cewa watakila akwai wata sabuwar dama a gabanta, a can Abuja kuwa, Umar yana koyon yadda zai rayu da sakamakon kuskurensa, yana ƙoƙarin cireta daga zuciyarsa duk da cewa bai san ko zai iya yin hakan ba, biyu daga cikin mutane masu alaƙa da juna ta hanyar abubuwan da suka faru a baya, amma yanzu, suna kan hanyoyi biyu mabambanta, ɗaya tana neman healing, ɗayan kuma yana fama da nadama, kuma babu wanda ya san abin da ƙaddara ta tanadar musu a gaba.