ƘYAURE KARIYAR GIDA

BOOK ONE CHAPTER 18

by @hindatuauwal



Zainab ta mike tsaye tana kallon fuskokinsu. Ba suce da ita komai ba, ta fahimci wani abu daban da basu san da shiba yasamu Khadijah.



Doctor yagyara tsayuwa. Acikin aikinsa ba abinda ke bashi wahala kamar wannan, rasa kalaman sa yake, komai ya ƙwace masa, bayada yanda zeyi adole ya tattaro wasu kalmomi ya furta su ga Zainab dake tsaye zuciyar ta na rawa.



"Ki ya hakuri kui mata addu'a, muna cikin aiki ta warke."



Ji tayi kanta ya kulle. Ranta yai tsam. Idanuwanta na cikada rashin fahimta.



"Ban fahimta ba." Dakakkiyar muryanta ta tambaya.


"Tarasu...!"


Idanuwanta ta lumshe kalaman na zama a kowani sashi na jikinta. Da ciwo mara misaltuwa ta ɗaga idanunta ta kalli gadon da aka gunguro Khadijah akai.




Batasan meya riƙe taba awannan lokacin amma jinta tayi kamar ba ita ba. Ƙwaƙwalwanta ta natsa, zuciyar ta tsaya. Emotions, feelings and pain duk sun kauce sun barta ita kadai akaran kanta.




Tana kallon Ramlat da Anis suka je suka fada kan gadon suna sumbatu. Nurse ta kawo mata takadda tai sining.



Aka ɗauki gawar zuwa motar asibiti. Suma suka shiga ciki zuwa gidan su.



Ana saukowa da gawar mutane na fitowa daga masallaci sallhn la'asar. Dayike la'asar ta shiga shiyasa kusan duk ma'aikata suna gida.



Cike da tausaya wa ake kallon su. Duk wanda yasan faruwar accident din da safe zuwa gudun wanda ya kaɗeta se bada labari su keyi.


*


Bayan sa'a guda. 


Gidan cike yake dan ƙam da mutane maƙota da dangin Ahmed waɗanda Zainab ta kira.



Zuwa yanzu an shirya Khadijah tsaph acikin suturanta na ƙarshe a gidan duniya.



Yaya Yusha'u da sauran ƴan uwansa nata kai komo akan gawar. Ahmed na veranda shida sauran mutane, dama ko sau daya bai shigo ɗakin ba. 



Zaliha na can gefe ara kuɓe tana sharɓan hawaye. Ramlat na cikin bedroom asume. Anis na gefe yana kuka har yanzu.



Khalid dake zaune kusada gawan Khadija yana kallon ta babu ko ƙiftawa sannan hawaye basu saukar mai ba samm. Numfashi kawai yake shaƙa yana fitarwa batareda yasan abinda ke damunshi ba ayanzu. Abu dai ɗaya yasani shine zuciyar sa ciwo take masa, wanda yakeda yaƙinin akodayaushe nashi mutuwar zata iya rizƙanshi.



Yaya Yusha'u ya umarci Zainab da taje kan gawan Khadija tai mata sallama.



Sanin ko ta miƙe ƙafafunta bazasu iya ɗaukan nauyin taba yasan yata rarrafawa zuwa kan gawan.



Ta kalleta a kwance sanɓall acikin annashi. Bayan likafanin da aka sanya mata aka rufe ta da zani kanta na tallafe da wani sabon zani saboda har yanzu jini bai daina zuba daga cikin kanta ba. Ƙamshin tirarika masu sanyi da aka sanya mata na tashi ajikinta.




Zainab ta runtse idanunta hotunan Khadija na kara kaina acikin kanta. Sai ta jita kamar an ɗauketa ɗungurungun an maidata can wasu lokuta na baya.



Tun daga ranar da ta haifi Khadija. Yadda ta rai neta. Maganganunta masu cike da hikima, da wasu motsika da take yi cike da ciwon rai.



Da wata murya da tafi ƙarfin raɗa mai sanyi ta furta"na yafe miki duk wani kuskure da kika min arayuwa. Ubangiji shi yafe miki. Ya amshi baƙun cin ki. Mala'ikunsa su sanda zuwan ki...!"




Haka ta dingi jero mata addu'oi masu taɓa zuciya da sanya ɗaukacin jama'an dake wurin zubar da ƙwalla.




         *ZALIHA*
Jiki a matukar mace ta janye jikinta daga ɗakin. Yaraph ta zube akan kujera tana jan iska ta bakinta, zuciyarta ta karye wasu hawaye masu zafi suka ciko idanunta.



Hotunan Zainab da yaranta ne ke mata yawo in different sheets. Idan tace ba taji mutuwar Khadija ba tayi ƙarya. Dagaske taso yarinyar tamkar Nusy data haifa. Hatta ita kanta Zainab taso ta da dukkan zuciyar ta. Soyayyar jini da jini take mata. 



Sedai tun ranar da Ahmed ya furta mata kalmar so komai yasauya. Sa 'ilinda zuciyar ta tai na'am dashi yasoma fifita Zainab akanta taji bazata iya ɗauka ba.



"Zuciyar ki da nashi ahaɗe suke duk abinda kika ji shima zai ji." 


Maganar ta ratso ta cikin tsakiyar ma'adanan tinaninnikanta masu muhimmanci.


Ta runtse idanunta"Yana sonki amma soyayyar da yakema matarsa mai girma ce. Idan zan baki ban-banci atsakanin ku zance ke farin cikin shice, ita kuma rayuwarsa ce, za'a iya sadaukar da farin ciki saboda rayuwa."


Taji diran maganar a tsakiyar kwanyanta. Zata iya rantsuwa tana jin amon muryansa acikin kunnuwanta, tare da kashe din dayake mata acikin ƙwayannin idanunsa dake kallonta babu ko ƙiftawa.


Takai hannu ta goge hawayen ta. afili ta furta"ko da yaushe Zaliha ce agaba da Zainab."




JAMILA

Misalin ƙarfe 4:30pm ta buɗe ɗakinta tafi to. Cikin ƙwarinda bata jinsa aduk jikinta taje dining taci abincin da cakalansa tayi ta cika cikin ta da drinks ta dawo ɗakinta ta zauna abakin gado tana kallon wayanta.




Ƙofar ɗakin aka turo. Ta ɗago kanta tana jin takaicin rashin rufe ƙofan da tayi asanda ta shigo.



Dama sallama ba ɗabi'ansa bane. Haka ya tako cikin ɗakin yana kallon Jamilar tare da karantan yanayin ta.



Akusa da ita ya zauna yana tambayar ta lafiyan ta. Jamila ta ɗan ja jikinta tana ƙoƙarin dai-dai ta kanta da bashi amsar "lafiya ta ƙalau..."



Hannunta ya kamo. Ta ɗago ƙwayannin idanunta ta kallesa da dukkan wani yanayi da take ƙoƙarin binnewa acan ƙasan ranta.




Fuskarsa ya matso daph da nata. Ya hura mata iskan bakinshi na sauka ahankali. Zuciyarta tai tsam!da yanayin da take ciki.




Ƙwayannin idanunta basa aiki sedai zuciyar ta na iya hasko mata yanda Raihan ya karkata kansa gefe, tsinin hancinsa na sauka agefen fuskar ta, laɓɓansa suka sauka anata cikin wani yanayi mai nauyi.




Idan ƙaddara ta iso babu wanda ya isa ya dakatar da ita. Kuma aduk lokacin da zuciya taci galaba akan mutum to haƙiƙa danasani zai biyo baya.




Adai dai wannan lokacin Jamila na iya kiran abinda ya faru atsakanin ta da Raihan da sunan ƙaddara.



Inko zata fadi abinda yake dai-dai to son zuciya ce ta jawo mata fadawa cikin wannan yanayi.



Ko acikin munanan mafarkan da take yi arayuwa bata taɓa hango kanta awannan yanayin na aikata zina ba.




Sai gashi ayau ta aikata. Kuma mafi muni ta aikata ne da igiyoyin aurenta akanta tare da yaron daya kasance mafi soyuwa ga mijinta.



Hannu kawai ta sanya ta ture Raihan dake kwance asamanta yai laƙwass tun bayan kammaluwan komai.




Tana ƙoƙarin sauka daga gadon taji yariƙo tsintsiyan hannun ta. Batareda ta juyo ba ta fizge hannunta tana soma magana da wata busashshiyar murya mai zafin amo.



"Kaine mutum na farko da nai danasanin kasancewa dashi acikin rayuwata. Kamin alfarma guda kada ka ƙara yarda naga fuskar ka arayuwa ta."



Wani murmushi mai sauti yayi, da sautinsa ya sauka acikin gudan tsokan naman dake cikin ƙirjinta kamar ɗanyen ruwan dalma mai zafin gaske.



Kalaman sa agareta suka sanyata tsayawa cak tana waiwayowa ta kallesa da wani irin yanayi da bayada suna agareta.



"Daƙiƙi shike maimaita aji. Mata da university duk daya nake kallon su. Zanyi aiki tuƙuru na ɓata lokacina na sami attention din duk macen da naga dama. Ina spending moment ɗaya rak da ita na rufe babinta.



Nayarda bazaki ƙara ganin fuskata akurkusa dake kamar acan baya ba. Kema ki manta Ni dake mun hade airin wannan lokacin."


Yana rufe bakinsa ya miƙe. Tananan tsaye tana kallon sa kamar zombie har ya sanya kayansa ya fice daga dakin.



Ƙafafuwanta dake riƙe da ita suka soma rawa suna lauyewa. Bata damu da abinda take jiba balle ta bashi muhimmanci ta jasu dakyar ta shige bathroom.



Da ruwan sanyi ƙalau tai amfani wajen wankan tsarki. Seda tagama ta ɗauro towel ta fito sai tai tsaye tana kallon ɗakin.



Sai alokacin ƙwalla masu zafi suka ciko idanunta. Ta lumshe su hawayen na sauka a tsakiyar zuciyarta, dake cike da wuta mai zafin gaske.