Chapter 11
by @gidaniko422
*Abinda baka shiryawa ba yafi zuwar maka a bazata, misalin wannan ! Tafiyar da take gaban mai numfashi, tafiyar bai San inda yake jefa kafa ba, dare daya Ubangiji kan sauya komai, in nace komai to ina nufin komai,*
*Mai bukatar complete din littafin GARWASHI dubu daya ne,1k ****
.............Muna tsaye a filin nan dab da wutar da aka hada idanun kowa yana kan ango da amarya da son ganin abinda zai faru, Ina tsaye hagun Onye yayin da kawayen ta biyu suke daman ta duk muna sanye da ankon bikin cikin kwalliya ta burgewa, fuska ta kuwa tankar farin wata don kyau, Yayin da su yarima Gibson shi da abokan sa suka tsare ni da idanu suna magana a tsananin su har dai na gane akaina suke maganar su, nayi maza na hade fuska ta na kawar da kaina zuwa ga Onye dake Rike da tantabarar ta yayin bici ke ke damanta yayin da shima Ango Peter yake tare da abokanshi su yarima Gibson Yayan Amarya Wanda ya zuba min ido Yana kallo na abinda na tsana kenan
Hatta Ahalin gidan igwai duk sun fito filin wasan don su ga yadda Wannan taro zai Kare Amma fa fuskar Uwar Amarya Onye cikin tsoro da zullumi take, don in har ya kasance yarta ta taba sanin wani namijn to karshen abin kunya ne a garesu Kuma abin kunya ga sarki da Ahalin gidan sa ace Yar gidan shi ta lalace kafin Aure, don Haka kowa ke cikin taraddadi domin ko in har aka samu akasi shima Angon ba zai taba Auren ta ba, duk da akwai wata banzar al'ada kuma ga yayan gidan sarautar maza suma idan zasuyi aure sai matan da zasu aura din sun haihu da su kafin aureb wai don kar su auri macen da bata haihuwa, abinda na kira da banzar al'ada, in haka ne meye na binciken mace in ta lalace da wani? don Haka acikin filin ma ba iyayen Amaryar ne kawai ba har da Ahalin gidan su Ango Peter kowa zuciya na bugawa musamman uwar amarya
A gefe na kuwa bana tare da komai sai nishadi don bikin ya kayatar Dani Kuma wannan Al ada tana burgeni ko Babu komai dai zai zaburar da Yan Mata kame kansu ko don irin wannan Rana da suke gudun fallasa a gabab dubun dubatar mutane, ban sani ba ko don Ina tare da kewaye hausawa ne masu nuna min watsewar da ake a Jami'a iskanci ne marar amfani da Kuma na cikin gida yasa wannan Al adar ta burgeni? Ko ko dai don bana Ra'ayin watsewar ne ? Oho dai Amma Kuma da yawa daga cikin yaren namu suna tur da Allah wadai da wannan tonon Asiri don suna ganin ba ta lalacewa da namiji kawai mata ke rasa mutuncin su ba, dayawa daga cikin Yan Matan dake Rasa budurcin nasu ma ta hanyar lalacewarsu Samarin ne ke batasu da Romon bakan su zasu Aure su wasu Kuma Yan uwan su ne na jiki ke karbe musu budurcin da ko mu a yaren mu da addinin mu muke girmama matar da takawo wa mijinta shi a gidan shi batayi saken da ta Rasa shi tun a waje ba
Kuma shi wannan tonon Asirin ba Wai sai a irin gidan sarauta ake yin shi ba ko a gidajen talakawa suna alfahari da shi don suna ganin hanyace da ake wanke zukata daga zargi. Ango zai karbi matar shi babu zargin ta zaga yawo ko wani ya Rigashi samun budurcin da suke wa kulafuci. Suma Kuma iyayen ta zasu San basu bawa yarsu tarbiyar banzaba, kowa dai zai Gane Babu cuta a cikin Auren su bare zargi.
Sai dai kuma a gefe guda akwai wata Al ada da akeyi ga Ya'yan gidan sarauta musamman namijin da ke jiran gado wato yarima shi Kam idan zaiyi Aure Koda kuwa Yar gidan talaka ce zai aura sai anyi wannan banzar Al'adar wacce nake ta tsinewa a raina , don ba karamin haushi take bani ba har nake ganin in da nice matar da yariman zai Aura ba zan taba yarda ba sai dai komai zai faru ya faru
Wannan al'ada kuwa da na Kira banza kuwa itace ba za a taba daura Auren su da matar da Yake so ba sai sunyi gwaji Wai shi Dan sarki ba zai Auri mace ba sai wadda aka tabbatar da zata haihu don Dole ne yadda aka haife shi shima ya Haifa Kuma kamar yadda zai gaji mulkin gidan su shima sai ya bar Wanda zai gajeshi shiyasa ma ake ganin Dole ne ma ya haihu Kuma ba zai taba Auren matar da bai sani ba ko ba zata haihu ba shiyasa ma suka bullo da Al adar ba za a taba daura Auren su ba sai an kawo yarinyar da zai aura din Koda kuwa tana wata kasa ne sai an kawowa yariman ita ya kwanta da ita tsayin wata uku zata yi a dakin shi tamkar matar shi idan tayi ciki a cikin wannan lokacin na watanni uku to shikenan sai maganar Auren su ta mike a Dora sanwar Aure ana musu murna zasuyi Aure mai albarka da rabon baby, ya danganta da yadda suka tsara bikin wata ta haihu a dakin yariman wata Kuma ta haihu a gaban iyayen ta, kai wata ma sai ta tara yara biyu ko uku kafin ayi shagalin bikin su, wasu ma har haihuwa biyar suna yi kafin Auren.
Idan kuwa mace tayi wata uku a dakin yariman Bata samu ciki ba to sai akara Mata wata uku wata shida kenan idan tayi wata shida babu ciki to wannan ba zata haihu ba Kuma duk yadda suke son juna Dole zasu hakura ya Nemo wata Ni kuwa sai nake ganin kamar ba ayi hikima ba wurin yin wannan banzar Al ada shiyasa ma naji na tsaneta ba kadan ba Ashe ban sani ba kaddara ta lissafo Dani a cikin wadan da wannan lamarin zai faru dasu, nima an sako dani a ciki,
Muna tsaye a wurin wutar da na Gama tabbatar sai da aka Gama tsafeta don in ba tsafi ba ta Yaya daga kawai mace ta Rasa budurci don an Bata wata tantabara ta Rike ta zo gaban wuta ba Cass ba ass ba kuma saka tantabarar akayi a wuta ba sai Kawai tantabarar ta mutu? Yadda wutar take ci na kadai zai nuna maka Dole ne akwai tsafi da sihiri acikin Lamarin
Wata tsohuwa me amsa sunan kakar onye ta wurin Uwa ta fito tana sanye da murjanai hannu da wuya har ma da kanta duk murjani ne mai daraja wanda shine karshen ado a sarautar mu, hannun ta da wata yizga ta gashin doki ta Soma zagaye su onye amarya da Ango Peter dake gaban wuta tana rera wakoki tana kada yizgar hannunta me kama da jelar doki sai da ta kewaye su sau ba adadi kafin Suma suka Soma zagaye wutar dake ci harshen ta na kokarin lasosu yayin da kakar Onye take yafa musu wani irin ruwa dake cikin Goran duma, sai kawai gani mukayi jikin Onye da Peter ya dauki kyarma, taci gaba da yafa musu ruwan nan suna kyarma sai ga hannun Onye yana sakin tantabarar hannun ta wanda ya mace mus! Allah ya fidda Onye kunya ya kuma fidda ahalin ta na Bata taba sanin wani namijn ba, inda tantabarin hannunta ya mace aka Kuma cilla shi sama Amma ya dawo kasa a matsayin matacce, amma ita tantabarar hannun Peter da aka cillata sama sai ta tashi sama firrr abinta sai wuri ya kaure da tafin murna da sowa inda Ango Peter ya cika da murna da farin ciki ya kuma daga Amarya onye sama Yana juyi da ita inda Uwar Amarya tafi kowa murna da Jin dadin fita kunya, don haka ta fito filin barorin ta suna take mata baya ta soma watsa kudi saboda murna, da ace an samu matsala to da har gidan sarkin Sai sun fice sun barshi, amma yanzu har kyauta sai iyayen Ango da shi kanshi sarkin Sai sun Mata kyauta kuwa ta girma da kasaita Wai ta iya tarbiya
Ango Peter Yana Rike da onye Yana juyi da ita a sama kafin ya sauke ta aka saki kidan wani fitaccen mawakin yaren mu ya soma wake igwai da da matar sarki har da onye da peter, inda Kuma fili ya kaure da Rawa sai dai wani abun mamaki ina tsakiyar fili ina rawa don gwanar rawa ce ni sai dai in banji wakar da tayi min dadi ba, Ango Peter Yana rike da hannu Onye ni muna rawa na soma jin ana lika min kudi masu daraja duk da ban dago naga mai min likin ba, Amarya onye ta ruko hannu na sai kawai naji an sure ni anyi sama Dani ana juyi Dani inda naji wani tsoro ya kamani inda na Soma laluben wanda yayi min wannan Aikin, idona ya fada Akan yarima Gibson Yayan onye wato yarima me jiran gado sai Kuma fili ya Kuma daukar wata sabuwar waka ana tafi da sowa me tsanani abinda yayi matukar bata min Rai ya Kuma yi matukar faranta Ran Amaka da Maazi Nkem ganin Gibson ya nunawa duniya yadda na keta zuciyar sa har ya daga ni ya nuna...
Kan kace me? Sai ga sarki da kanshi da matar shi mamar su yarima Gibson har ma da su Maazi Nkem da Amaka har ma da mutanen Arziki sun Rufu Akan mu suna zaba Mana Ruwan nairori yarima Gibson Yana sabe Dani ana zuba Mana kudi wuri na Kara kaurewa da sowa da tabi
Aguje Naga wasu mata dake hidimtawa a gidan sarautar sun karaso a gareni dauke da wasu murjanai na garari suna daura min a hannu da wuyana har da kafafuna
Abunda ya Kara bani haushi wai duk na meye wannan abun da suke min ? Kuma meye dalilin wannan dagawar da yarima Gibson yayi min alhalin Amarya ce kawai akewa hakan kamar yadda Peter yayiwa Onye? Amsar da ke shirin bayyana a gare ni ba wacce zuciya ta take muradi bace, sai dai yaya zanyi ?.........
Kar ku Bari ayi tafiyar nan babu ku don wannan Labari daban yake da sauran, kuma book one ne free amma book 2 da 3 sune paid,
*Masu sharing na labarin nan kun cancanci yabawa da jinjinawa, ina ganin Ku Allah ya saka muku da mafi alherin da yake wurin Ubangiji*🥰
Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI❤🔥
_Masu Neman labarin GARWASHI daga farko su duba cikin channel din mu na gidan iko zasu samu labarin daga farko_