GARWASHI

Chapter 13

by @gidaniko422

*A lokacin da wani yake dariya a lokacin kuma wani kuka yake, wani yana murnar ya samu wani kuma yana bakin cikin rasawa da yayi, dukkan su hikimar Ubangiji ce ta nuna su, da sannu kuma masu hakuri zasu cimma babban rabo, sai dai hakurin yana da wahala*


_Akwai complete na littafin nan garwashi akan 1k ***_


...........Ina zaune cikin tafasar zuciya da Bakin cikin wannan Al amari dake shirin faruwa dani, Wanda su Amaka da Maazi Nkem ke ta fama yaya ta maganar cikin dangin mu da ahalin mu, musamman Amaka da take ta faman Kiran waya tana fadin a taya ta murna wai zanyi Aure a gidan igwai wato gidan sarauta, ko da ya ke ba Amaka kawai ba hatta Maazi Nkem ma sanar da mutane Yake Aure na a gidan igwai din, yayin da ni Kuma nake ta ganin abinda ba zai yuwu bane don ban hango auren mu da Gibson ba, shiyaasa nake ta ganin  wautar su amaka da suke murna da yayata zancen.

Nasha mamaki da aka bude akwatunan da yarima Gibson ya Rako ni dasu, domin kuwa kayane irin na gidan sarauta tare da tarin murjanai wanda na gama gane sune karshen adon kure adaka a gidan sarautar, sai Kuma tarin kayan Ado da burgewa, Amaka sai kakabin kayan takeyi tana murna ita da Maazi Nkem

Da ranar Sunday tazo wato ranar  zuwa coci Amaka ba ta boyewa fastor komai ba ta sanar dashi aure na gidan igwai har ta nemi a yi mata addu a yarta ta SHIGA gidan igwai da kafar dama,   faston kuma ya tambayi Amaka sun sanar da igwai lalurar  matsala ta ta aljanu ko? Tace A a ba su fada ba yace to su fada musu don Kar suce an cuce su, idan Gibson yana sona a haka ko acan sai suyi min magana tunda lalura ce, amaka tayi maza tace tana tsoron ta fadi cewar Ina da lalura gibson ya fasa aire na, amma fastor yace dole ta sanar da su amma amaka tayi gum da bakin ta don tana ganin igwai ba zai yarda Gibson ya auro mai lalurar aljannu ba, ita kuma yadda ta dora rayuwar ta a kan auren nan in aka fasa shi ai har suma zata yi,

Da Amaka ta dawo Bata boyewa Maazi Nkem yadda sukayi da fastor ba inda su duka cikin su ya duri ruwa don suna ganin idan Gibson yaji ba zai Auri me cutar aljanu ba sai kawai sukayi mursisi suka ki fada 

Ni kuwa tunda na kudurtawa Raina da zuciya ta ba zan Auri Gibson ba auren da nake ganin kamar ba aure ba tunda naga yadda hausawa suke auren su cikin tsabta da tsari mai burgewa, sai naji ba zan iya aure irin na yaren mu ba, to Haka nake nufi banayi bana kamar inayi sai na shiryawa zaman jiran inji wata magana da ta danganci batun Auren mu da Gibson don in fashe fashewar da komai zai tarwatse


Zuwa wannan lokacin na gama yarda matsalar ciwo na tana saga Alkur ani kamar yadda sumayya ta fada min sai kawai na SHIGA laluben ta Yaya hakan zata faru? 
Sai kawai naga tunda tace rufe jiki yana daga cikin kariya sai na soma da Rufe tsiraici na tunda ta fada min harda shigar tsiraici ke jawowa mutum aljanu,
Dama Ina da less less da atamfofin ma kawai dai nafi son shigar kana Nan kayan ne irin su English wear da sauran su, don haka sai na Fara da saka less da atamfa Ina yafa gyale wanda nake sakawa cikin jaka ta idan na fita makaranta na yafa, don na san ban isa saka shi a gaban amaka ba, lokaci zuwa lokaci kuma ina sirkawa da English wear shiysaa nayi nasarar rufe amaka bata lura ba

Wata Rana na dawo daga makaranta Ina tafe a mota ta bayan na sauke sumayya wacce sau tari tare muke tahowa daga makaranta, ina tafe a motar sai na kunna Redion motar abinda ban faye yi ba ko da kuwa zn kunna din to CD ne zan saka naji cred debit ko 2 pac ko dangogin su amma a yau sai na latso cenal din FM inda Kuma najiyo ana rera K'ira'ar karatun nan  cikin wata murya Mai dadin sauraro sai dai ba muryar ce ta ja hankali na ba irin abinda naji Yana ratsa zuciya ta sannu kan hankali  wato karatun kanshi  naji Ina so,

Gaba daya na bawa karatun Nan hankali na da nutsuwa ta har na karaso gida Ina muradin karatun nan wanda banso aka janye shi ba, haka Kuma naji bana bukatar sauraron komai a yanzu sai karatun, cikin wata irin sa'a aka sake sanyo shi naji wani irin dadi, don haka da na zo parking space din gidan mu ban fito daga motar ba sai nayi zamana A motar nayi shiru Ina sauraron karatun Ina Kuma Jin wani Abu na keta zuciya ta Yana SHIGA har Yana sauko min da wata nutsuwa ta musamman wadda ban San abinda ya kawo min ita ba, ko da yake ba zance ban San abinda ya kawo min ita ba tunda Bai wuce wannan karatun ba

Sai da karatun nan yayi awa daya kafin aka janye karatun Wanda banso ba dole na hakura, na Kuma kashe Redion na fito na SHIGA gida na samu Amaka tana fadin Ina na tsaya yau ban dawo Kan lokaci ba?  Nace Mata a makaranta ne aka tsaida mu wani gwaji

Washe gari da ma sai da na kunna Redion ko zanji karatun nan amma sai na Tara's suna want program Wanda yasani Jan tsaki na kashe Redion

Bayan mun fito daga lacca ne na fadawa sumayya dadin karatun su da naji jiya shine nake tambayar  ko tana da karatu a wayar ta ta tura min? Fauziyya Ta tambaye Ni wane irin karatu nake so? Nace Mata na Alkur ani nake so. Ta Jima tana kallo na kafin tace min Ina dashi amma me zakayi dashi? Na fada Mata jiya ne naji shi a mota Kuma yayi min Dadi shine nake so don nayi ji duk lokacin da nake so

Sai tayi murmushi tana fadin 
''Justina lamarin ki fa yazo da mamaki, sai ta shiga yi min bayani akan Alkur ani, akan masu sauraren sa da masu karanta shi, da maganin da yakeyi wai har maganin kunci da damuwa sa Bakin ciki yakeyi, Kuma shi din waraka ce ta maganin kowace irin cuta ce Kuma waraka ne wanda babu shakka akan sa,
Nayi shuru ina kallon ta da mamakin wannan littafi nasu, lallai yaci sunan sa mai tsarki

''Ba zan karyata hakan ba don Ni da kaina naji ajikina don Haka sai na ce mata kwarai na yarda da hakan don Nima naji hakan. Nafisat Rabi u Umar itama duk muna tare a wurin Kuma taji duk abinda muke magana akai sai tace 
Amma kuwa Justina iyayen ki ba zasu damu ba idan sukaji kina Jin karatun Alkur ani? A garin mu fa gombe akwai wata yarinya da iyayen ta suka kashe ta don kawai tace tana son hijabi tana kuma Sha awar yadda ake sallah sai kawai suka kashe ta wai gara ta mutu da dai tace salla tana burgeta kenan zata iya shiga wata Rana.
Nabi nafisa da kallo don ni nasan nafi waccan yarinyar da aka kashe hadari don Amaka ko taraiya da masu salla bata son nayi bare kuma addinin su ya burgeni. ai idan akwai abinda yafi kisa to sai Amaka tayi min shi. Amma sai nayi maza na cewa nafisat babu wata matsala
Aka tura min karatuttukan da yawa na kumayi hikimar nemo hearphon nake sakawa a kunne na in saurari Kira'ata yadda nake so babu Wanda yasan me nakeji

Abin mamakin da na kula dashi shine wata irin nutsuwa da na samu, ni da kaina shine na gane alfarmar alkur'ani ce, sai kuma yawan mafarkai da nakeyi wai gani Ina kallon mutane suna salla, wani lokacin ma zan ganni a cikin sahun salla anayi tare dani cikin irin kayan su summayya wato hijabi, kuma wai wani gari ne da ba Legos ba don mafi yawan mutanen da muke sallar tare dasu farare ne tas masu dogon gashi Matan su Sanya da hijabi da Nikabi mazan kuwa sanye da fararen doguwar Riga sun Kuma yafa wani farin mayafi ko ja ko Baki kowa dai da kalar dake kanshi
Idan na farka sai inji Ina begen wannan wuri da na ganni in Kuma ji muradin inyi salla amma Kuma Ina tsoron Amaka ta ganni Dole nayi shiru 

Kwana biyu Ina sauraren karatun Nan Ran Nan sai tsautsayi ya samu waya ta ta lalace  gashi Kuma muna cikin strike wato yajin aiki bare fauziyya ta sake tura min karatun Alkur ani Dole na wuce kasuwa na siyo CD masu yawa na kawo mota na zube idan fita ta Kama Ni na saurara idan kuwa babu kowa a gidan sai na dawo mota na kunna na saurara

Tsautsayi Wai in ya wuni baya kwana Ranar Nan Yaya na Sony ya dawo gida babu kowa ya iskeni na kure volume cikin Kira a ta malamin da har na hardace sunan shi wato sudais na kasa kunnuwa Ina saurare har ban San lokacin da Sony ya shigo ba sai da Naga inuwar mutum akaina na farga dashi a tsaye ya zubo min idanu Yana Huci tamkar zai hadiye mu Ni da motar tawa inda Kuma na San kashina ya bushe don gashi can ma ya kwarmatawa Amaka da Maazi Nkem kafin Nan ma nasan shima ba kyale Ni zaiyi ba sai naji a jikina............


Kar ku Bari ayi  tafiyar nan Babu ku don labarin GARWASHI daban yake da sauran


Gidan iko shine sunan ke cewa saduwar ALHERI💃🏿

_Masu Neman farkon labarin su duba duba cikin channel din mu zasu samu dukkan labarin_