3
by @asmybaliyu
OMRI HAYATII
by
Asmy b Aliyu
3.....
Karfe goma sha daya na safiya Suna kofar gidan haisam cikin wata tsadaddiyyar unguwa dake cikin Kano,daman Sun shigo su gaisa da amarya suyi masu sallama,
tunda haisam ya qaraso wurinsu suke binshi da tsokanar shakiyanci irinta abokanin ango.banda murmushi babu abunda Haisam din ke sauke masu,
ango kasha mai!""Anas ya fada da wata irin murya,
still wearing a big smile kwance a fuskan Anas din.idan Zaku xo kuyi aure kuzo kuyi
bakusan rahamar dake cikin yin aure ba wallahi.allah nagode maka da ka nuna mun wannan ranar."
wani dariya Omar ya fashe daita Yana buga kafarsa kasa.acikinsu mu'azzam kawai ne yaki magana.
yanxu bikinwa zamu sha anan kusa?
mu'azzam in sha Allahu!"Anas ya fada Yana kallon gefen mu'azzam din,still baice komai ba,daman yasan Anas din yayi magana ne dan suji bakinsa,
a babban falonsa Omar ya saukesu,
ya wuce bangaren Yasmin din.baa fi minti goma ba ta fito cikin shigar alfarma,
tayi masu sannu da zuwa da gaishesu.
babu jimawa Haisam din
ya shigo dauke da babban tray da aka jero drinks Kala -kala komawa yayi
ya dauko wani tray mai dauke da snacks
Shima ya aje gabansu,Banda kallo a tsakaninsu babu abunda sukeyi,
suna son magana babu dama saboda matar Anas din na falon...........Haisam ya zauna gafda amaryarsa mai Suna
Yasmin haka ya kama hannunta Yana sarqewa cikin nasa,caraf acikin idanun mu'azzam wani shegen kallo yayiwa Haisam din da yasa ya dan bude idonsa akansa.gamida Kashe masa ido daya,
hakan da yayi yasa mu'azzam din saurin dauke kansa.
basu jimaba sukayiwa Yasmin din sallama kowa ya aje mata envelope mai dauke da kudi aciki godiya tayi masu tana fadin Allah ya tsare hanya,haka suka fito
nan ma su Anas suka sakasa gaba tamkar Zasu cinyesa ,Sai da suka ga mu'azzam ya
tada motar Yana yimasu wani mahaukancin horn dukansu suka shiga motar Suna dagawa Haisam din hannu,
####
kusan 3 na rana harda mintuna goma suka shiga garin kaduna,Sai da ya sauke ko wane a gidansu,sa'annan ya juya kan motar zuwa gidansu malaak duk da Anas din ya karbi driving din har suka shigo kaduna.bata ma San zaizo ba ,Yana gafda kawowa layinsu ya kirata ya fadamata
Yana kusa ga gidansu ta fito........wani irin farin ciki taji ya lullubeta ,dakin mum dinta take zaune.da sauri ta baro dakin mum din,Abuja boubou ce ajikinta wacce tayi mata wani irin kyau dinki ya xauna ajikinta
na cikakken asalin Yan gayu,
dakinta ta koma ta fesa turarrukkanta
ta gyara fuskanta dan qaramun veil ta
yafa ta nufi kofa zuciyarta taji tana wani irin bugawa.....
dan dakatawa tayi ta lumshe ido
a hankali ta furta Ya Allah Ina sonsa dayawa......."!!!tana fita ta hango motarsa,
da wani irin aji ta fara takawa zuwa wurin motar cikin motar Yana hangota ya kafeta da ido,duk takun da takeyi tana qarasowa wurinsa jin yake tana narka zuciyarsa,
still Yana zaune cikin motar batareda
yayi yunkurin fitowa ba,
saboda baxai jimaba gida kawai yakeson zuwa shiyasa ma bai shiga gidansu malaak din ba.dan idan ya shiga dole Sai yaje sun gaisa da mum dinta.
Kai tsaye ta bude murfun motar ta shiga
gamida rufe kofar nan take kamshinta
ya cika motar,rungumesa tayi
zuciyarta na bugawa take fadin."I really miss you."shafa bayanta kawai
yayi batareda yace komai ba,Sai da suka dauki mintuna a haka kafin
ta dago tana kallonsa,
ta wani rike hannunsa tana murxawa
kafun tace ya hanya ?"
ka gaji ko?"
kallonta kawai yake batareda yayi magana ba .dogon hancinsa ta kama taja
lumshe idonsa yayi
ya Kara budewa still Yana kallonta,
jin tayi jikinta na qara mutuwa da wani irin sonsa dake qara Kashe mata zuciya,
a hankali ya zagaye hannunsa ta daidai kugunta ya kwantar da seat dinta lokaci daya ta tafi baya,kwantar daita
yayi Yana kallon cikin idanunta.
fuskarsa ya dora gafda tata ,
a hankali ta runtse idonta.
daidai ya dora bakinsa a nata
Yana sauke mata numfashi mai dumi,
a hankali ya fito da harshensa
Yana zagaye bakinsa da nata
wani irin kamshin cool mint bakinsa ke fitarwa,a hankali ya hade bakinsa
da nata Yana yimata wani irin deep kiss,
sun dauki minti biyu a haka
kafin ya cire bakinsa cikin nata,
tana kallonsa lokaci daya idonsa suka shige suka kankance gamida canja
kala.dora kansa yayi akan sitiyari
sai da ya samu nutsuwar minti biyar kafin yace zan wuce gida ki gaida mum!"
hannunsa ta rika tana manna masa kiss
akan hannun ,ta kallesa tana fadin"
kasan Ina sonka ko??"
daga mata Kai kurum yayi,
ka kula da kanka dan Allah."
ka gaisheda Mami a huta lafia
ta fada lokaci daya Kuma tana sakin
hannunsa,ta balle murfin motar,
ta juya ta fara tafia dan tasan bazai tafi ba sai yaga shigarta gida,Sai da ta shiga din
sa'annan ya tada motar yabar cikin unguwar da wani irin cool speed.........
######
tana tsaye a dakin Mami tana gyaran kayan Mamin da suke a goge tana shiryarsu cikin wardrobe taji ana knocking kofar dakin,da dan mamaki take kallon kofar shiru tayi tana jin kamshin dake cika mata hanci tun kafin ya bude kofar ya bayyana,kamshinsa ne ya fara bayyana.
jin shiru mu'azzam ya riqa handle din kofar ya tura idonsa suka sauka cikin nata.
kyakkyawar yarinyya ce wacce bazata wuce shekara goma sha biyar ba a duniya,
fara ce tas haka siririya ce sosai dan ko kadan bata da jiki,tana da wani irin kyau Mai fisgar hankali.gashin girarta ya hade dana kanta Wanda kallo daya xakayiwa
gashin girar nata zaka San tana da baiwar gashi sosai.....tun daga sama har kasa
yake kallonta english gown ce a jikinta
Sai half hijab.
"Ina wuni yaayanmu,sannu da zuwa."
ya Kara kallan agogon hannunsa,
batareda ya amsa gaisuwar da take yimasa ba yake fadin"yau babu islamiyya ne."dan shiru tayi tana saukar da kanta
kasa kafin tace."Mami tace a bari Sai gobe jikin fareeda har yanxu bai sauka ba,
har ya bude baki zaiyi magana Sai ga Mamin ta bayyana,da murmushi sosai cikin fuskarta take kallon yaron nata,
Rungume Mamin yayi tamkar karamun
yaro,na sameku lafia Mami?"
ya fada cikin sanyin muryarsa mai dauke da natsuwa,ta dagosa daga rungumar da yayi mata tana dan shafa bayansa,
lafia kalau ya hanya?"
ya langabe Kai Yana fadin"babu dadi Mami
Duka jikina ciwo yake,
kwafa Mami tayi kafin tace waya aikeka,
ka wuce bangarenka ka huta duka,
zan hadawa Ayusherh abincinka ta kawo ma."gyada Kai yayi
Yana furta thank you Mami."
da haka ya bar dakin mamin ya nufi bangarensa,mamin ta kalli Ayusherh da ta gama gyaran kayan mamin tsaf tace ta biyota kitchen ta hada abincin yayansu ta Kai masa.
Ayusherh na biye da Mamin har kitchen,itada Mamin suka hada abincin
ta saka komai akan babban tray ,taba Ayusherh ta nufi bangarensa.
koda ta isa bangaren mu'azzam din iya falo ta tsaya ta dora masa tray din akan dinning table,tana ajewa ta juya tabar bangaren,
daman Yana shigowa part dinsa Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa kayan jikinsa ya rage ya fada bathroom.a shirye ya fito cikin farar jallabiyyar da tayi masa kyau,
Sai wani sanyayyen qamshi ke tashi
ajikinsa mai sanyaya zuciya da ruhi
ya fito falonsa kenan ya hango abincinsa da Mami ta shirya masa kan dinning,
murmushi jin dadi ya saki Yana jin kaunar Mami na qara cika zuciyarsa ta koina,
jin an tada sallah yasa ya fice zuwa massalaci.
koda ya dawo sallar komawa part dinsa yayi duk da yasan baccin yamma babu kyau ya dibi abinci kadan yaci ya hada da coconut juice yasha testing din abinci kawai da yaji yasan Ayusherh tayisa dan
idan tayi girki kamar mami tayisa .babu wani banbanci saboda training din mamince tun tana da shekara 7 da kakarta tazo daita aiki gidansu ,ta horu da kowane irin aiki dan babu kalar girkin da bata iyaba kusan sa'annin juna suke da fareeda,
yadda Ayusherh ta shiga ran mami farkon zuwansu gidan ,Kai tsaye Mamin tasa ka
mu'azzam ya samar mata makaranta
ta fara duk da kakar tace ta fara a can
garin zaria inda suke da zama,tun tana da shekara biyar iyayenta suka sakata makaranta,bayan rasuwarsu ,sanadin gobarar da aka wayi gari baa San inda ta fara ba ta canye daga uwar har uban.
mahaifin Ayusherh shine Wanda kaka ta haifa ,asalin Yan niger ne cirani ya kawo su a Nigeria inda suka yadda xango
a garin zaria .tun tasowar kaka da ahalin nata watau danta da mahaifiyar Ayusherh,
bata da wasu dangi Sai su haka sukayi
rayuwa Wanda anan Nigeria aka haifi
Ayusherh,suka cigaba da kula daita cikin tsananin so da soyayya.mahaifin Ayusherh mutum ne Mai zafin neman gaske bai yadda ya kwanta ba haka yake fadi
tashi akan iyalinsa da Kuma mahaifiyarsa wacce ake kira kaka indo,bayan rasuwarsu
mahaifan Ayusherh rayuwa ta juyawa kaka baya da Ayusherh,gidan da suke hayama korar Kare akayi masu.sanadin wata
dillaliyyar dake shigowa gidansu sukayi wani irin sabo da kaka indo itace tayi mata hanyar aikatau a garin kaduna
gidan babban mutum mai karamci
irin Alh.ibrahim marafa,da wani irin Alkhairi ta shiga gidan dan lokacin da karfin inna indo tasamu Mami mutunniyyar kirki
Mai hannu a sake hakama ya'yanta sam sam basuji kyankyamin su ba
musamman Ayusherh da sukaji ta shiga ransu lokaci daya musamman da sukaji sunanta ,watau sunan mahaifiyarsu
farkon zuwansu gidan Sam mu'zzaam
baya iya fadar sunanta ,duk da ita ba Aisha ake kiranta ba kamar Mami,
shine farkon Wanda ya fara kiranta da Queen. sannu a hankali sunan ya fara binta.
#OMRI HAYATII
#LOVESTORY2026
#ASMY B ALIYU
#***