SAWU BIYU

Page 22

by @khadijahsulaiman406

SAWU BIYU 

BY 

Khadijah Sulaiman 

Young Talented Writers Association (YOTA)

Book 1

Page 22

Bilal na tsaye yana bin wurin da kallo ya ji an dafa kafaɗarsa,da sauri ya juyo,ganin Sadauki ya sa ya sauke wani wawan ajiyar zuciya ya ce"ka tsorata ni gaskiya".
A hankali ya tako ya tsaya kusa dashi ya ce"tun asali kai matsoraci ne,me kake anan?"
Ba tare da ya kalle shi ba ya ce"iska nake sha".
Sadauki ya gyaɗa kai ya ce"yeah,akwai iska sosai gaskiya".
A hankali Sadauki ya ce"me ka fahimta a kan wannan case ɗin?"
Ya sauke numfashi ya ce"sincerely speaking shiga makarantar bai musu wahala ba,kamar dai sun gama sanin komai a kan makarantar kafin su shiga".
Sadauki ya gyaɗa kai ya ce"exactly,nayi tunanin hakan,sun san makarantar babu isasshen security,sunyi targeting lokacin da komai zai zo musu da sauƙi,ka ga it's late already,babu yawaitan zirga zirgan jama'a a wannan lokacin".
Motsin da ya ji yasa ya juya da sauri,ya taka a hankali ya haska wurin da wayar hannun shi,sojan dake wurin ya ce"sorry Sir,fitsari zanyi".
Ya kashe wayar ya taka a nutse ya bar wurin Bilal ya bi bayan shi.
A ƙarƙashin wani bishiya suka tarar da Emmanuel yana tashi sana'ar,ya gama baɗe wurin da warin sigari.
Ko kallon shi Sadauki bai yi ba ya bar su a wurin.
Bilal ya toshe hanci ya ce"what is this nonsense Ema?"
Ya ɗago jajayen idanuwan shi ya ce"chill guy,idan kana so ne zo ka ƙarba".
Ya watsa mishi harara ya ce"You dey craze".
A jam'i su kayi sallahr Isha tare da musulman cikin su,bayan sun idar sojojin da ke musu girki suka miƙawa kowa abinci,suna zuwa kan Sadauki ya ɗaga musu hannu ya miƙe ya bar wurin.
Ƙarƙashin bishiya ya koma ya zauna ya fitar da wayarsa,ganin babu network yasa ya mayar da wayar cikin aljihu.
Yana wurin har ƙarfe sha ɗaya na dare sannan ya miƙe ya shiga ciki,Bilal na kwance yana danna waya ya shigo.
Bayan ya zauna ya nuna mishi wani leda dake kusa dashi ya ce"Adeyemi ta kawo maka".
Ya share shi tamkar bai ji mai ya ce ba ya kwanta,Bilal ya taɓe baki ya ce"na san yunwa ka ke ji Mallam,is better ka cire wannan girman kan ka ɗauki ledar nan don zai maka amfani".
Ya masa banza ya ja zani ya rufe jikin shi,a haka bacci ya ɗauke shi saboda gajiyar dake tattare da shi.
Cikin dare wani mahaukacin yunwa ya tashe shi,ya yaye zanin ya kunna torch ɗin waya ya haska ɗakin,kusan kowa yayi bacci sai munshari ke tashi from different angle.
Ya ja tsaki ya mike ya nufi ƙofa,har zai fita idon shi ya sauka a kan ledar Idayat,ya juya ya kalli Bilal,ganin sai bacci yake shararawa yasa ya durƙusa ya ɗauki ledar ya fita.
Bilal ya buɗe ido ya bishi da kallo,ya taɓe baki ya ce"munafiki".
Ko'ina yayi tsit sai hasken farin wata da ya haska wurin,ya samu gefe ɗaya ya zauna ya buɗe ledar.
Manyan cakes ne kusan guda goma sai doughnuts suma haka,sai drinks mara sugar sosai saboda sanin bai cika son abu mai zaƙi sosai ba.
Ya daɗe yana bin kayan da kallo sannan ya sauke ajiyar zuciya ya cire cake guda ɗaya da drink ɗaya ya maida ledar gefe.
A nutse ya gama ci ya cigaba da zama a wurin,lokaci ɗaya tunanin Sani ya faɗo mishi,yana da rai ko ya mutu?
Tambayar da ya kan yiwa kan sa kenan kusan kowane rana,babu ranar da zata fito ta faɗi bai yi tunanin ɗan uwan shi ba,Allah ya sani yana matuƙar son ɗan uwansa.
Motsin da ya ji ya sa ya dawo daga tunanin da ya tafi,bai juya ba har ta ƙaraso gaban shi sanye da riga da wando sai ƙaramin mayafi da ta ɗora kan kayan,ta sauke numfashi a hankali ta zauna nesa dashi.
Ya ɗan juyo ya mata kallo ɗaya ya ɗauke kai,tayi murmushi ta ce"ba ka ji tsoro ba?"
A hankali ya ce"sai kace ba soja ba?"
Wani blushing tayi jin ya bata amsa,kafin tace komai ta ji yace"Thank you".
Ko bai karasa ba ta san godiyar me ya ke,wai da wani irin sa'a ta tashi yau ita Idayat?
Tsabar farin ciki kasa cewa komai tayi,ya sake juyowa ya kalleta,bai taɓa natsuwa ya ƙare mata kallo ba duk tsawon lokacin da suka kwashe tare.
Gaskiyar Bilal da yake cewa tana da kyau,sai ya sami kanshi da tuno fuskar Zarah,wani murmushin da bai shirya masa bane ya suɓuce a kan fuskarsa,Idayat ta kalle shi da mamaki,ganin yana kallonta kuma yana murmushi at the same time ya sa abin ya bata mamaki.
Da sauri ya miƙe tsaye ya barta a wurin,ta bi bayan shi da kallo har ta daina hango shi.
Yana ganin Bilal ya dakata da sauri ya zuba mishi ido da mamaki, Bilal ya fashe da dariya ya ce"kun gama soyayyar?na fito taya ka hira na ga kallon love kawai ake shi yasa na dawo bakina alekum".
A fusace ya ce "You must be out of your senses Bilal".
Bilal ya gyaɗa kai ya ce"yeah,sure".
Ya ja wani wawan tsaki ya bar shi a wurin, Bilal ya bishi da kallo yana dariya ya ce"finally,ashe akwai jini jikin wannan bawan Allahn".
Washegari as early as possible suka koma Rafi Secondary School,basu tsaya ɓata lokaci ba suka cigaba da bincike.
"Akwai visitors record book a School ɗin nan?"
Yayi tambayar yana kallon Principal.
Principal ya gyaɗa kai ya ce"eh akwai, wannan aikin record officer ne,shi ke kula da shige da fice na visitors".
Sadauki ya ce"waye record officer?"
Duk aka juya ana kallon shi,jiki na rawa ya matso kusa ya ce"ni ne ranka shi daɗe".
"Zan iya sanin sunan ka?"
Da sauri ya ce"Sunana Nasiru ranka shi daɗe".
"Ina son ganin record book dake hannun ka Mallam Nasiru".
Ya juya da sauri kana ganin shi ka san a rikice ya ke ya bar wurin Ademola ya bishi a baya.
Tare suka dawo ya mikawa Sadauki,yasa hannu ya ƙarba ya fara buɗe pages ɗin ɗaya bayan ɗaya yana duba informations dake jiki.
Har zai miƙa mishi bayan ya gama sai kuma yayi saurin buɗe book ɗin ya nemi wuri ya zauna.
Ya ɗago ya kalli Mallam Nasiru da zufa ya gama wanke mishi fuska ya ce"ranar goma ga wannan watan,akwai baƙon da ya shigo wannan makarantar,haka ne?"
Yasa hannu ya share zufa ya ce"baƙi da yawa sun shigo ranar ranka shi daɗe,ba zan iya tantance wanda kake nufi ba".
Sadauki ya ce"haka ne,a nan akwai inda naga an rubuta JJ,babu cikakken suna,babu telephone number,babu address kamar yadda naga haka tsarin record book ɗin yake,sannan mutum zai rubuta dalilin shi na zuwa amma duk a nan babu,ko zan iya sanin dalili?"
"Ƙarfe goma na safe mutumin ya shigo ranka shi daɗe,ya ce yana son ganin Principal,na tambaye shi ko ya na da appointment da shi,ya nuna min bai da appointment amma abu mai mahimmanci ya kawo shi,na ce gaskiya dole sai na nemi izini kafin in bar shi ya shiga".
Yana kaiwa nan a zancensa yayi shiru,Sadauki ya ce"ina jin ka".
Ya haɗiye abinda ya tokare mishi wuya ya ce"hannu yasa cikin aljihun wandon sa ya zaro bindiga,wallahi ranka shi daɗe tun da nake ban taɓa ganin bindiga ido da ido ba sai ranar,ya sa min ita saitin wuya ya ja takardar kan tebir ya rubuta wannan sunan da kake gani,bayan ya rubuta ya ce wallahi ko tari nayi a kan shigowar shi yau sai na baƙunci lahira".
Lokaci ɗaya wurin ya rikice da hayaniya, sai da Emmanuel ya zare musu ido sannan duk su kayi tsit.
Kasa cewa komai yayi ya cigaba da musu tambayoyi,har bayan la'asar suna makarantar, ƙarfe shida da rabi suka koma tent.
Ƙarfe sha ɗaya na dare ya bar tent ɗin ba tare da kowa ya lura ba, makarantar ya koma inda ya cigaba da zagaye ko'ina cike da nazari.
Har lokacin akwai officers ɗinsu dake patrol a wurin,can bayan makarantar ya zaga inda ya hango wani siririn hanya da mutum zai iya bi ya shiga cikin makarantar.
Har zai kutsa kai ya hango kamar inuwar mutum,da sauri ya koma jikin bishiyar dake kusa dashi ya laɓe,sai da ya ga an wuce shi sannan ya fito,cike da taka tsantsan ya fara bin bayan shi.
A mugun tsorace yake tafiyar,idan yayi taku biyu zai juyo ya kalli baya.
Tsakanin bishiyoyi Sadauki ke biye dashi,sunyi tafiya mai nisa sosai sannan ya ga mutumin ya dakata,a nan ya sami daman ganin fuskar sa sosai,Labaran,wanda ya kamata yayi duty a ranar amma ya roƙi alfarmar Mallam Shuaibu ya taimaka masa saboda zawon dake damunsa.
Bai jima da tsayuwa a wurin ba wani sanye da bakaƙen kaya ya rufe fuskar shi da mask ya iso wurin.
Duk yadda yaso jin abinda suke faɗa hakan ya faskara saboda tazarar dake  tsakanin su kuma ƙasa ƙasa suke magana.
Yana nan laɓe Labaran ya juya ya bar wurin,ya jira har wancan ya juya sannan ya fito ya bi bayan shi.
Suna cikin tafiya mutumin ya tsaya cak,da sauri Sadauki ya laɓe jikin masara,da yake ɗanye ne,shi yasa kwata kwata babu wani sound.
Ya juyo ya sake dudduba bayan shi har da kunna torch ya haska amma bai ga kowa ba.
Ya kashe torch ɗin ya cigaba da tafiya,tafiya mai nisan gaske su kayi sannan suka isa wani tsohon gida,tsohon gini ne sosai don hatta roof ɗin gidan sun gama fita sai kaɗan dake nan.
Mutumin ya juya ya sake bin koina da kallo sannan ya sa key ya buɗe ya shiga.
Sadauki ya kwanta cikin ciyayi yayi crawling ya isa har jikin ginin ya miƙe tsaye.
Can ya ji an buɗe kofar an fito,kuka ya dinga ji ƙasa ƙasa daga cikin ɗakin.
Mutumin ya zauna kusa da kofar ɗakin ya ciro waya yayi danne danne yayi dailing number.
Ta speakern wayar ya ji ance"kai, Babaa ya ne?"
Mutumin dake zaune ya zuƙi sigarin hannun shi ya ce"kai oga,yaushe za ku fitar damu a wannan dajin ne,lokaci na ƙurewa fa?"
"Babaa,kwantar da hankalin ka,oga ya bada mota muna nan isowa gobe da sassafe,babu wata matsala dai ko?"
"Babu wata matsala,shegun yaran dai baƙin taurin kai garesu,sun ƙi kwantar da hankali sam".
"Kar ka damu da wannan Babaa,sai na zo goben".
Daga haka suka yanke wayar, Sadauki ya cije baki da ƙarfi ya koma ya kwanta cikin ciyayi ya bar wurin.
Sai da yayi tafiya mai ɗan nisa sannan ya zauna ya ciro wayar shi ya duba time,ƙarfe ɗaya saura na dare
Yayi dailing number Bilal,bugu ɗaya ya dauka,Bilal ya ce
"Kana ina Falcon,na fito ban ganka ba,ko yauma soyayyar ....."
“Bilal, I've located the children,mobilize the team and proceed to the coordinates I'm sending. Keep the approach quiet,bring the vehicle and necessary equipment,no engagement until my signal. Do you copy?” 
“Loud and clear, Sir.”
“Move.”
Yana kashe wayar ya tura mishi address yadda ya san zai fahimta ya maida wayar cikin aljihu.
Bayan kusan minti arbain wayar tayi vibrating,ya sa hannu ya ciro wayar tare da answering call ɗin.
“Falcon, this is Bilal. We are at the designated coordinates. Team is in position and standing by. Over."
Sadauki ya ce“Copy that. Hold your position. Maintain silence and wait for further instructions. Over.”
Yayi tafiya mai ɗan nisa sannan ya isa inda suke,su ashirin har masu patrol a School environment.
Bilal yayi saluting ɗin shi ya ce“Sir. Team is in position.”
Ya gyaɗa kai ya ce“Good. Maintain your positions.”
Cike da zafin nama da taku irin na zaratan maza masu cikakken lafiya ya koma wurin motar ya canza kayan jikin shi zuwa uniform,ya ɗauki bindigarsa ya zuba bullet ya saita ta da kyau.
Ya kalli Emmanuel ya ce"remain with the vehicle,Keep the extraction route clear and be ready to move the children once they're secured.”
"Yes,Sir"
Ya ƙirga sojoji guda biyar ya haɗasu da Emmanuel,guda biyar yace suyi gadin wurin da kewaye.
Sauran goma da suka rage ya ce su bi bayan shi.
Da sanɗa suke tafiya har suka isa wurin,mutumin na zaune har lokacin a bakin ƙofa amma wannan karon bacci yake har da minshari sai bindigan da ya ajiye kusa dashi.
Da hannu ya musu alamar mutum biyar su zagaye wurin sauran su bi bayan shi har da Bilal.
Taku ɗaya biyu ya buɗe ido da sauri,ganin sojoji zagaye dashi ya sa ya hantsilo daga kan kujerar ya ɗauki bindigarsa da saurin gaske.
Sadauki ya ce"ka ajiye makaminka".
Mutumin ya sake gyara bindigar ya saita Sadauki da shi,cikin kaushin murya ya ce"if you move any further, I'll shoot".
Yayi wani irin supa ya faɗa kan shi,Allah ya bashi sa'a ya murɗe hannun ya fincike bindigar a hannunsa.
Ya saki wani ihun azaba saboda ba karamin riƙo ya masa ba.Bilal da wasu guda biyu suka isa wurin.
Ya miƙa musu bindigar ya miƙe tsaye da mutumin,sojoji biyu suka karasa suka riƙe shi.
Ya isa gaban mutumin ya sa hannu ya lalube aljihun shi ya fitar da key,shi da Bilal suka isa kofar ɗakin ya buɗe.
A zaune suka tarar da yaran suna kuka kowannen su an manne bakin sa da seletop,suna ganin an shigo suka sake fashewa da kuka.
Bilal ya kunna torch ɗin hannun shi mai haske sosai take haske ya gauraye ɗakin.
A hankali Sadauki ya durƙusa kusa dasu ya ce"calm down please,you're all safe".
Duk su kayi tsit tare da zuba musu ido,a hankali suka kwance daurin hannun da aka musu da seletop dake nane da bakinsu.




***