OMRI HAYATII

4

by @asmybaliyu

OMRI HAYATII 

by
Asmy b Aliyu 

4....
har bayan magrib mami tana ta zuba ido taga fitowar mu'azzam shiru takeji haka yasa
ta daga waya ta kirasa.har ya katse bai daga ba Sai a kira na biyu ya daga Kuma daidai lokacin yagama sallar magrib cikin dakinsa,dan Sai bayan da aka gama sallar magrib din ya farka.duk da alarm din da ya saka a wayarsa.bai sa ya farka ba
yadda Mami taji muryarsa ciki ciki tasan bacci yayi.
hope kayi sallar magrib mu'zzaam???
tambayar da ta farayi masa kenan,
yanxun nan nagama Mami.Yana jin ajiyar zuciyar da ta sauke.katse Kiran tayi batareda ta Kara fadar komai ba.
bai shiga cikin gida ba Sai bayan sallar ishaai,a massalaci ya hadu da abbansa
bai samu magana dashi ba har ya baro masallacin shi Kuma Abban nasa ya tsaya gaisawa da mutanen arzikinsa da wayandda suke neman taimako,
saboda Alh.ibrahim marafa mutum ne mai tausayin gaske,da taimako sosai,
dan haka jama'a ke kaunarsa.musamman mutanen dake zagaye dashi na cikin unguwar.
Yana shiga bangaren Mami direct 
wani dogon corridor ya nufa mai dauke da wasu irin dakuna masu tsari da kyan gaske,a hankali ya tsaya kofar farko
yayi knocking, Ayusherh dake zaune gefen kaka tana duba wani homework na tajweed da aka basu islamiyya ta kalli kofar a hankali ta aje littafin hannunta ta nufi kofar.
ta bude kofar  idonsa cikin nata.kallonta yake daga sama har kasa wannan qaron kayan bacci ne ajikinta kalar maroon riga da Wando. Wanda suka zauna ajikinta sukayi mata matuqar kyau.sai manyyan kalaban da bazasu wuce kwara goma ba dake reto 
a tsakiyyar bayanta.hannu ya daga zai Kai mata rankwashi a tsakiyyar Kai,
ta noke kasa tana fadin"wayyoni yayanmu yi hakuri dan Allah.
kaka tayi kwafa tana fadin ai kaine maganinsu itada fareeda ayi mutum Sam bayason hula akansa Sai kace ya'yan arna,
tura baki kawai Ayusherh tayi ta koma cikin dakin,Kai tsaye doguwar wardrobe ta nufa dake cikin dakin wacce take tun daga saman har kasa,bangaren huluna ta yamutsa ta dauko hula daya,ta saka
karasowa mu'azzam yayi cikin dakin
ya xauna kan rug din dake tsakiyyar dakin Yana gaisheda kaka,ta amsa cike da kulawa da soyayya tana tambayarsa 
gajiyar hanya ya amsa da Alhmdullahi.

ya karfin jikinki??"
Alhmdullahi da sauki irin namu."
ta fada da murmushi a fuskarta,
bai jimaba a dakin yayiwa kaka Sai da safe ya fita,Kai tsaye ya nufi ainahin bangaren Mami,
tura kofar falon Mami yayi dauke da sallama a bakinsa,Mami ta daga Kai 
tana kallonsa ta amsa.
zama yayi kusa ga Mami Yana dora kansa akan kafadar Mami ,
Mami ta shafa sumar kansa mai tsantsi 
tamkar ta larabawan marocoo.harka dawo massalacin kenan?"
na dawo Mami ,meyasa baka jira kuka taho da Abba ba.?"Mami kema kin San Abba idan ya fara gaisawa da mutane Sai ayi awa biyu baa gamaba.,zan dai jirasa ana kafin ya dawo.

"kaje ga abincin can akan dinning kaci."
girgiza Kai yayi Yana fadin"na koshi Mami 
ya kalli bangaren da fareeda ke zaune
tayi nisa a kallon Indian series din da take ko kiftawa batayi kwata kwata 
hankalinta baya kansu ,da mamaki yake kallonta ya mayar da hankalinsa kan TV
daidai lokacin da jarumin ya kamo kugun jarumar Yana binta da mayen kallo,
a hankali yake hade filin dake tsakaninsu
Kara kallon fareeda yayi Sai yaga tana ta murmushi..... 

"keeeeeee!!!
ya fada a tsawace
itama Mami dake danna waya ta dago tana kallonsa da wani irin yanayi kwance akan fuskarta,Kashe TV nan
fareeda ta bude baki Zata fara yimasa gardama ya wani daka mata tsawar da ta gigitata right now??"
a fusace fareeda ta miqe tsaye tayi switch off din kayan kallon Sai huci take ,
rai bace ya juya Yana kallon Mami
Mami meyasa xaki riqa barin yaran nan na kallo irin waya'nnan movies din haka??"
duka shekarunsu nawa dan Allah."
Kai kullum kallon yara kake yiwa yarana 
Meye acikin kallon,
ransa yaji ya Kara baci kan maganar Mami,
daidai nan aka shigo falon da sallama
Ayusherh CE ta shigo falon tunda ta shigo take kallon fareeda wacce ta harde hannu a kirji ta cika Sai hura hanci take 
mu'azzam ya sauke idonsa akanta
"kema kallon series din kika shigo kiyi?"
gaban Ayusherh ya fadi ,da sauri ta shiga girgiza kanta jin tayi ma kafafunta Suna son kasa daukarta ganin irin kallon da mu'azzam din ke mata.

karka firgita mun yara dan Allah mu'azzam........Mami ta fada da roko a muryarta.fareeda tabar falon a mugun fusace ganin haka Ayusherh tabi bayanta,
can dakin fareeda ta cimmata
ta xauna a bakin bed kamar zatayi kuka take kallon Ayusherh din.dan Allah meyasa yaayanmu kullum yake ganin mu wasu kananun yara fisabillahi anya kuwa idon yaayanmu basu rufe ba,ya kuwa San 
size din bra dinmu."da sauri Ayusherh ta Bude ido tana Kai hannu ta rufe bakin fareeda dan ganin take ko daga falon
zai iya jin fareedar,fareeda ta kwabar da hannun Ayusherh din tana fadin
karya na fada wannan shekarar zamu zana ssce yayi tamana kallon wasu kwailaye Ina cikin nishadina ya wani batamun mood."
Haka fareeda tayi ta mita ita daya 
ranta a mugun bace addu'a kawai take
ayi baikonsa shida Aunty malaak daga nan a saka ranar biki ayi biki kowa ma ya huta.


######
Sai da Abba ya gama cin abincin dare har lokacin Yana zaune a falon abbansa
Yana jiransa Sai da ya Kammala,
suka shiga tattaunawa akan business din abban din,dan Abba Yana cikin manyyan masu kudin garin kaduna,Wanda suka ci suka koshi suka tada Kai da naira.
dan ko clinic din da Mu'azzam din ke aiki ta Abban ce ,duk da Shima ba kullum 
yake zuwa ba duk da Yana son aikinsa kamar me Amman Abban karfi da yaji 
Yana son ya jawosa ya turasa cikin kasuwancin da ko kadan baya gabansa,
Sai wuraren qarfe 10 na dare ya baro 
bangaren Abba a gajiye dauke da wasu files a hannunsa da zaiyi signed,
koda yazo ya tarar da miss call din malaak har biyu,
wanka ya sakeyi yabi lafiyar gado
kafin ya jawo wayarsa ya kira malaak din,
hira suka farayi irin ta masoya kamar koda yaushe hirar tata tafi tasa yawa......


######
washegari wuraren qarfe 9 ya shiga bangaren Abba da shirin fita clinic
a wurin Abban yayi breakfast din da Mami ta hado masa.Yana gamawa yayiwa iyayen nasa sallama ya nufi clinic.a clinic din ma bai jimaba ya shiga theater.
bai samu kansa ba Sai karfe biyu na rana,
wani irin ciwo kansa keyi masa,
Yana zaune a office Yana dan hutawa
yaji ana knocking kofa.
ya dan yi mamakin haka saboda babu patient din da zai duba,
tura kofar office din tayi 
idanunsa suka sauka akanta.
da murmushinta take ta kowa 
zuwa cikin office din,tuni kamshin turarenta ya cika wurin Wanda ya hade da nasa Yana saukar da wata irin natsuwa a zukatansu batayiwa kanta mazauni a koina ba Sai akan cinyoyinsa.
har lokacin kallonta yake da idanunsa masu saukar mata mugun kasala,

"kin lalatawa Mami ni lokaci daya malaak!"""Ya fada da wani yanayi a muryarsa Yana sakin murmushi.
itama murmushin tayi tana dan dukowa gamida shigewa cikin kirjinsa
hannunta duka ta saka tana zagaye kugunsa ,da wata irin murya mai Jan hankalin duk wani da namiji take fadin"ka manta ni din rainon turai ce."
lumshe idonsa yayi Yana jin wata irin kasala na saukar masa,
gabadaya kamshinta ya cikasa.
daga Ina haka??"
daga gida nayi kewarka wallahi.
ta fada tana dan dagasa,
meya samu idonka?"naga sunyi wani iri ko baka da lafia ?"a rude take jera masa tambayayoyin  tana taba kansa da cikin 
dogon wuyansa,

Hiii relax!!!
ya fada a hankali,.
ciwon kaine kurum
nasan da nasha magani zai daina,
tashi muje eatry muyi lunch nima banci abinci ba na fito."tare suka fita
a reception Sai kallonsu ake
ana gaisheda doc.mu'azzam Cike da girmamawa jin tayi kanta Yana qara girma da wani irin alfahari tasan ko matan dake wurin tayi masu wani irin nisa 
Dan ita din mai tsananin sa'a ce doc.mu'azzam marafa zai zama nata ita kadai har karshen numfashinsu,
da motarta suka fita Yana zaune front seat 
Yana kallon yadda take sarrafa sitiyarin motar cikin kwarewa tun kafin su isa
tayi waya.mafi tsadan eatry dake cikin garin kaduna ,a tanadar masu abubuwan da Zasu bukata a vip inda babu hayaniya itada masoyinta.kasancewar an Santa a wurin ko kafin su iso an tanadar masu komai.

ita ta riqa lallabasa tana basa abincin a baki  tamkar wani Karamin Yaro,haka Shima ya riqa diba Yana bata cikin tsantsar son junansu da kulawa,
bayan sun Kammala cin abincin 
ta dubesa tana fadin"gida zan kaika ko office??"
office zan koma kin manta motana na office."ta girgiza Kai da sauri tana fadin"
ban yadda ba gida xan kaika 
idan kana bukatar motar Sai ka tura driver ya dauko maka."Allah beb na fara kishi da motar nan ka nanewa mota daya 
tamkar bakada motoci."Allah watarana xaka wayi gari kaga na kyautar da motar nan."

Murmushinsa Mai natsuwa da aji ya sauke mata kafin ya furta really???
Yana dage mata girarsa duka biyun....
anan ta ciro kudin da bata San yawansu ba ta aje masu kafin subar wurin,
Kai tsaye gidansu ta nufa........


#OMRI HAYATII 
#HOTE LOVE/ROMANCE
#MU'AZZAM MARAFA
#MALAAK FAROOK RANO
#ASMY B ALIYU...
#***