NURI

SCARS BENEATH HER STRENGTH 5

by @saddiqahhh



Wannan shine last thing data kawowa ranta... Sai taji kanta kamar ya toshe kwakwalwarta ya kasa assimilating mata abinda Inna ke nufi. hakan yasa kawai ta bita da kallo har ta kammala fada bata iya ce mata qala ba.. idonta yana kan Inna kuma tana sauraren sanda ta cigaba da bata labarin abinda ya faru......

Flashback 

Bayan Rabe ya gudu da kudin da Alhj Labaran ya basu ba qaramin tashi hankalin Inna yayi ba saboda yadda ta kwallafa rai da kudin nan. Rashin kudin yasa ta zama desperately in need of money gashi taje can gidan Alhj Labaran din ya mata fata-fata hakan yasa bata sake gigin zuwa wajensa ba. Akwai wata hajiya Rahma da suke mutunci da Inna. Ko nace da Inna take liqe mata saboda kudinta (yes nasan many of you haka zasu ji Kamar son kudin Inna yayi yawa..son kudinta yayi yawa amman tana stage din da take son kudi ne... Tsofaffi normally arayuwa suna da masifar son kudi sai dai na Inna ya ninka na kowa. Lol)

Hjy Rahma ce ta fadawa Inna akwai wasu da yarinyarsu bata da lafiya suna neman kodar da za'a saka mata zasu biya maqudan kudade. A time dinne Inna bata tsaya tayi wani lissafi ba tace zata bayar, hjy Rahma sai data matamagana tace taji ta gani zata bayar.

Ita ta shige mata gaba suka je gidan masu neman kodar Inna ta sake jaddada musu zata bayar da kodar nata especially da taga gidan nasu na masu shi ne sai ta sake rikicewa. Babu wanda ya sani... Haka da aka saka ranar da za'a yi aikin sai hjy Rahma ce ta tsaya a matsayin 'yar uwar Innar sannan su kansu masu asibitin suna da son rai, ya dace suce ba zasu karba na Inna ba tunda ta manyanta sosai. Ranar da akayi aikin bata dawo gida ba ta bar Nuri da Aunty Zakiya wadda tazo kamin ta damfari Inna ta gudu cikin zullumi da tashin hankali. Kwana biyu kawai tayi a asibitin tace a sallameta suka rabu kan zasu bawa Hjy Rahma kudin ta bata.

Ranar data dawo gida hatta Nuri taga qauna kawai gani take kakarta ta yanke saqa tayi kudi don suma ba qaramin kudi suka ce zasu bata ba, worth 40M. Zakiya har tambayar Inna take lafiya ta ganta cikin farin ciki bayan an nemeta an rasa? Bata kulata ba Inna sai cewa tayi Allāh ya yanke mata qashin wahala.

Kwana daya biyu uku shiru Hjy Rahma bata nemeta ba itama kuma bata nemeta ba saboda tana dan qarasa jinyarta ne har bayan sati biyu shine Lokacin da Zakiya ta gudu bayan ta siyar da dan gidan da suke ciki.

Wannan tashin hankalin ne ya saka Inna ta nemi Hjy Rahma ta bata kudinta zata sai gida bata da wajen zama ita da jikarta. Hjy Rahma tama Inna wani kallo kamin tace "hjy Inna ai aikin nan ba'a dace ba gashi dai anyi dashen amman yarinyar ta mutu kuma bincike ya nuna daga kodarki ne iyayen ma yanzu jiya suka zo wajena wai zasu kamaki da 'yan sanda nace musu ban san gidanki ba.. yanzu dai ke suke nema ruwa a jallo zasu daureki..." Kunsan tsofaffi da tsoron yan sanda. Hankalin Inna bai taba tashi irin na ranar ba ko ranar data rasa Abdullahi bai tashi kamar haka ba.

Ta dora hannu akai tana hawaye shabe-shabe ta tambayi Hjy Rahma "ynzu ya zanyi.?"

Kai ta girgiza mata yana cewa "hqri zaki yi Inna su kamaki kawai gashi daurin rai da rai za'a yi mki don haka akeyi.." gaba daya ta gama kunna Inna banda kuka babu abinda take "na shiga uku ni Laure.. na shiga uku daga taimako.. na shigesu na lalace Ina zan saka kaina..."

Tabe baki Hjy Rahma tayi tana yiwa Inna wani kallon gefen ido tana danne dariyarta don tun ranar da aka sallami Inna iyayen yarinyar suka turo mata kudin Inna a account dinta ita kuma gani tayi tana buqatar kudin kamar tafi Inna buqata.

"Shawara daya ce kawai Inna.." da sauri tayi shiru tana share hawayenta tace "fadamin shawarar?"

"Ina tunanin ku bar garin nan for now zuwa sanda komai zai lafa sai ki dawo don gaskiya bana jin zasu iya yafe miki..." Kai kawai Inna ta hau gyadawa da zallar qaryar da Hjy Rahma ta fada mata mai cike da son rai ta miqe jiki babu qwari ta mata godiya ta fita.

Da harara Hjy Rahma tabi Inna aranta tana ayyyana bata taba haduwa da tsohuwa mai masifar son kudin da ta kai Inna ba yau ai tayi maganinta.

Wannan shine dalilin da yasa Inna tana komawa gida dama ga tashin hankalin gidanta da aka siyar ta saka Nuri dake kuka agaba tace barin garin zasuyi kawaj. Nuri ba'a son ranta ba don bata da yadda za tayi yasa tabi Inna suka je tasha suka hau motar Kaduna. Farkon zuwansu Kaduna was hectic, sun sha wahala sosai kamin suka samu matsuguni na rana daya kawai. Canjin rayuwa da tashin hankalin da suka fuskanta yasa tunda suka dawo kaduna lafiya ta rabu da Inna. Dole Nuri ta fara neman aikatau ta samu da kyar a wajen wata mai sai da abinci wadda tayi mata hanyar gidan hayar da suke ciki yanzu and life was never smooth to Nuri and Inna, basu taba jin dadin rayuwar ba tunda suka dawo Kaduna. Nuri ba wani sakewa take da ita ba sbd tana ganin kamar itace sanadin rabata da Mami da Karatunta. While Inna har lokacin tana jin damuwar kudadenta data rasa....

Back to the main story.

Banda kallon Inna dake bawa Nuri labarin nan babu abinda take. Tasan Inna nada son kudi amman ba tayi zaton ya kai haka ba irin like what the heck.. yanzu mai son kudin nata ya jawo mata. Right from the start Inna have never succeeded akan kudi. Bata taba yin arziqi da kudaden da take samu ba sannan bata taba haqura da neman kudin ba. A time din Nuri ji tayi gwara ma da hakn ya faru don ta tabbatar da Inna ba zata yi hankali ba. Maybe akawo mata wani offer din aikin da baya da kyau which for sure tasan da gudu Inna zata amsa tayi.

Miqar da ita tayi tana juyawa ta kira Nabeela dake qofar dakin da ta tabbatar ta gama jin komai da Inna ta fada. Bata damu ba don wannan ba shine agabanta ba yanzu tana buqatar lokaci enough da zata zauna ta maimaita komai da Inna ta fada mata.. kamar dai Inna ta gama kasheta da mamaki.

Gashi ko sau daya bata ji tausayin yadda aka riqa damfarar Inna kudi ba kawai gani take kamar haqqinsu ne yake kamata. Or maybe ita nata jarabawar kenan na kudi.

Nabeela ta kama mata Inna suka fita zasu kaita asibiti. Maman Nabeela ta kalli Nabeela tana cewa "rakasu zakiyi ne Nabeela?" Kai ta gyadawa Mamanta da ta sake cewa "to ki kula kinji... Allah ya bada lafiya." Ta qarashe referring to Nuri data amsa mata da kai.

Abakin kofar gida suka tsaya Nabeela tace zata je taga ko zasu samu napep. Da kallo Nuri ta bita sai for the first time tunda suka zo Kaduna almost two years taji zuciyarta ta fara aminta da wani. Dama ta dade da lura da yadda Nabeela ta damu da ita kawai tana shakkar shiga sabgarta ne. Kawar da tunanin tayi bayan ta tuna ba wannan ne abinda ke gabanta ba alokacin.

Zama Inna tayi kan dan dakalin dake wajen tana maida numfashi. Nuri ta bita da kallo wanda ita kanta bata san na mene ba, tausayi ne ko kuma akasinsa kawai dai zuciyarta a lolacin was blank akan Inna. Bama Inna ba gaba daya Lokacin sai taji kamar anyi wiping emotions dinta ne gaba daya babu abinda take ji.

Suna nan tsaye sai ga Nabeela ta dawo tare da mai napep da yana zuwa suka taimakawa Inna ta shiga ciki suma suka shiga sannan suka tafi. General hospital din dai Nuri tace a maida su, tunawa da bata da kudi ya sake sakar mata da jiki amman bata sare ba dai har suka je asibitin Nabeela da kanta ta sallami mai napep. Da kallo Nuri ta bita dashi bayan ya tafi ta bude baki da wannan muryar nata da rayuwa ya qara sanyaya mata shi ta furta "Why did you pay Nabeela?"

Murmushi kawai Nabeela tayi mata tana kamo Inna suka tafi. Nabeela tausayin Nuri ne ya sake kamata bayan taji labarin da Inna ta bayar kuma kamar ta fahimci yanayin raywuar da suka yi saboda many times tana jin wayar da take da Afif don yawanci tafi aron wayar Nabeela akan na Nusaiba. Ganin Nuri ta tsaya tana kallonta har sannan yasa ta jawo hannunta suka nufi cikin asibitin with Nuri following her absentminded Kuma har sannan bata dena kallonta ba.

Nabeela da kanta tayi musu hanya basu bi wannan dogon layin ba don anan take aiki suka sanu ganin likita daya fada musu Inna na buqatar ayi aiki acire mata stones din dake cikin kodarta. Da kallo Nuri ta bishi kamin a sanyaye ta tambayeshi kudin aikin ya fada mata da tests, anesthesia and admission will cost a total of ₦1.5M.

Kai kawai Nuri ta gyada masa tana dauke kanta taji wani hawaye ya cika mata ido. Dakin da aka kwantar da Inna ta shiga ta tarar da Nabeela tare da ita da sauran patients dake dakin. Wajenta Nabeela ta nufo tana tambyarta "What did he say?"

Qoqari sosai tayi wajen mai da hawayen fuskarta ta amsa mata da "The total cost of the operation is ₦1.5M..." Idanu sosai Nabeela ta waro tana kallon Nuri da ta mugun dake sam bata so aga rauninta. Hannunta Nabeela ta kamo tana yin qasa da muryarta ta furta "Where will you get the money Nuri?" Hannu ta yarfe mata alamar bata sani ba kamin ta kalli Inna dake bacci ta qarasa wajenta.

Hawayen da take hana kanta ne suka biyo fuskarta. Tayi saurin kai hannu ta share tana kallon Inna ta furta "This is what your love for money has cost us Inna! Where will I get the money?" Sai tayi shiru kawai ta kasa magana jin kuka yazo mata. Duk qoqarin dannewar da take yi taji ba zata iya ba hakan yasa ta juya da gudu da fita daga dakin da ward din ma gaba daya don yanzu ta dena bari kowa yaga rauninta, kuka Kuma rauni ne!

Can wani waje ta samu da babu kowa kamar isolated building haka a asibitin ta tsugunna ta toshe bakinta tana fashewa da kuka. Irin kukan nan da yake tahowa from the bottom of the heart dinnan. Yau ina kudaden da Inna ta samu suke duka? Tun daga kan na gidansu data siyar zuwa na bikin Mami alongside with wannan data saida qodarta babu wanda ta mora aciki!! Qarewa ma banda wahala babu abinda ta jawo musu. Atime din Nuri ji tayi dama bata san Inna ba, dama ba itace kakarta ba, dama jini bai hadasu ba sai dai ko ina za'a je jinin Inna dai shi ke yawo ajikinta... The proverb "Blood is thicker than water!!" 

To be continued...

like, comment and share