THE UNWINDING PATH
*KADDARAR ZUCIYA*
*CHAPTER TWENTY: 20*
*THE UNWINDING PATH *
*JIDDAAH BARKUM*
—————
Ranar barin birnin Lagos ta zo da wani irin sanyin safiya mai taushi, gari ya yi luf, sararin samaniya ya lulluɓe da wasu ƙananan gizagizai, tamkar ana shirin saukar ruwan sama, sai dai iska mai sanyi ce kawai take yawo a sararin, a babban filin jirgin sama na Murtala Muhammed, hayaniya da hargitsewar fasinjoji ba su hana su jin wani nannauyan abu ya zauna a ƙirjinsu ba, lokacin komawa gida ya yi, Farida ta duba agogon hannunta, sannan ta mayar da dubanta ga Inteesar, idanunta sun riga sun yi ja saboda hawayen da take ƙoƙarin dannewa, ta matso kusa da ita, ta kamo hannayenta biyu, tana matse su cikin nata kamar tana son ta riƙe ta na wasu mintuna kafin su rabu, “Intee…” ta kira sunanta a hankali, muryarta tana rawa, “Ban san yaushe za mu sake samun irin wannan damar mu zauna tare ba, amma ina so ki sani, wannan satin da muka yi tare ya buɗe mini wani sabon ɓangare na rayuwa, na ga kina dariya, kina sake walwala, kuma gaskiya hakan ya faranta mini rai sosai,” ta ɗan dakata, tana ƙoƙarin haɗiye abin da ya tokare mata maƙogwaro, “Don Allah, kada ki bar abin da ya wuce ya kashe miki farin cikin gobenki, you’ve suffered enough, Intee, ki ba kanki damar sake yin farin ciki, kin ji?” Inteesar ta ji wani irin ɗumi ya bazu a zuciyarta, ta tilasta wa kanta yin murmushi, duk da cewa nata idanun ma sun cika da ruwa, “Farida…” ta furta a hankali, kafin ta rungume ta sosai, “Na gode ƙwarai da gaske, you don’t even know how much this trip meant to me, na zo nan da tunani iri-iri a raina, amma na tafi da wasu abubuwan da zan daɗe ina tunawa da su,” ta ɗan ja numfashi, tana ƙara matse ta a jikinta, “Allah Ya bar zumunci, kuma Allah Ya ba mu damar sake haɗuwa a cikin farin ciki,” “Amin, ya Rabb,” Humaira, wadda take tsaye a gefe tana ƙoƙarin goge hawayen fuskarta, ta kasa daurewa, “Haba dai! You people will make me miss this flight!” ta faɗa tana turo baki, Farida ta saki Inteesar kaɗan, tana kallon Humaira, “To, ai ke ce kika fara kuka tun kafin mu iso airport,” “Excuse me! I wasn’t crying, I had something in my eyes,” Inteesar ta fashe da dariya duk da hawayen da ke cikin idanunta, “Something in your eyes for the past twenty minutes?” Humaira ta juya ta kalleta, “Ke kuma ki yi shiru! Don’t expose me on my last day in Lagos,” su ukun suka yi dariya, amma dariyar ta kasance mai ɗan gaurayawa da baƙin cikin rabuwar, Humaira ta goge fuskarta da bayan tafin hannunta, sannan ta ɗaga wayarta, “Okay, enough! Let’s take one last picture before they announce boarding again,” suka matso kusa da juna, suka rungumi juna suna ɗaukar hotuna, a wasu hotunan suna dariya sosai, a wasu kuma murmushinsu ya kasance mai laushi, wanda ya nuna cewa kowannensu yana ƙoƙarin riƙe wannan lokacin a zuciyarsa, Inteesar ta kalli hoton da suka ɗauka na ƙarshe, ta yi murmushi tana kallon fuskokinsu a screen ɗin, wannan satin ya kasance kamar ɗan ƙaramin hutu daga nauyin rayuwarta, a nan ta sake yin dariya, ta sake jin daɗin kasancewa tare da mutane, ta kuma fara fahimtar cewa akwai rayuwa bayan duk abubuwan da suka faru da ita, sai dai duk lokacin da ta tuna cewa za ta bar Lagos, wani ɓangare na zuciyarta yana jin kamar tana barin wani sabon yanayi da ta fara sabawa da shi, sanarwar shiga jirgi ta katse tunaninta, “Passengers travelling to Katsina, please proceed to your boarding gate…” Humaira ta sauke ajiyar zuciya, “Well, that’s our cue,” Farida ta sake rungumar su biyun, tana ƙoƙarin yin murmushi, “Safe journey, girls, please call me when you land,” “We will,” Humaira ta amsa, Inteesar ta gyada kai, “Thank you for everything, Farida,” Farida ta yi mata murmushi, “Anytime, Intee, and remember what I told you,” Inteesar ta san abin da take nufi, ta gyada kai a hankali, “I will,” daga nan suka juya zuwa hanyar shiga jirgi, kowaccensu tana ɗaga hannu ga ɗayar har sai da taron jama’a ya raba tsakaninsu, kuma fuskokin juna suka ɓace daga ganinsu, a wannan safiyar, Inteesar ba ta bar Lagos da kaya kawai ba, ta tafi da wasu sabbin tunani, wasu kyawawan abubuwan tunawa, da kuma wata ƙaramar fata a cikin zuciyarta cewa watakila, a hankali, rayuwarta za ta iya sake zama mai kyau.
Bayan sun sauka a filin jirgin sama, Inteesar da Humaira suka ɗauki motar haya kai tsaye zuwa gidan Mommy da ke cikin garin Katsina, zaman motar ya kasance cikin natsuwa, kowacce tana kallon bishiyoyi da gidajen da suke wucewa ta taga, yayin da tunaninta yake yawo a wasu wurare daban-daban, Humaira tana tunanin komawa gidansu da kuma yan uwanta da suka daɗe suna kiranta, Inteesar kuwa tana tunanin komawa Katsina, inda za ta samu ɗan hutu kafin lokacin komawa Abuja da fara sabon zangon karatunta, da suka isa gidan, Mommy ta fito da sauri tana tarbarsu da fuskar farin ciki, “Alhamdulillah! Ga su nan, my daughters!” Ta rungume Humaira, sannan ta juya ga Inteesar, tana shafa fuskarta cikin ƙauna, “Yauwa, Inteesar! Sannu da zuwa, na yi kewarku sosai,” “Mu ma mun yi kewarki, Mommy,” Inteesar ta amsa, tana murmushi, Mommy ta yi musu kallon kulawa daga sama har ƙasa, sannan ta danyi dariya, “Amma dai na ga kun ƙara kyau, Lagos ɗin nan ta yi muku dadi kenan!” Humaira ta yi dariya, “Mommy, you should have seen the food we were eating!” “Allah Ya ƙara muku lafiya, ai muddin kun dawo cikin ƙoshin lafiya, shi ne abin da ya fi komai,” bayan sun shiga gida, sun ci abinci, suka ɗan huta a babban falon gidan, Mommy tana ta tambayarsu yadda suka yi tafiyar, wuraren da suka ziyarta, da kuma abubuwan da suka fi jin daɗinsu, Humaira ta ba ta labarai da yawa, tana ƙara wasu barkwanci a ciki har Inteesar ta kasa daina dariya, bayan ɗan lokaci, Humaira ta gyara zamanta, ta kalli Mommy sannan ta kalli Inteesar, “Mommy, gaskiya tafiyar nan ta yi daɗi sosai, amma yanzu kam lokaci ya yi da zan koma gida, su Yasmin sun kusa cika mini waya da kira!” Ta fashe da dariya, Mommy ta girgiza kai tana murmushi, “Haka ne, Humaira, mun gode ƙwarai da gaske da kulawar da kika ba wa ƙanwarki, Allah Ya saka miki da alheri, Ya miki albarka, Ya kuma kai ki gida lafiya,” “Amin, Mommy, thank you,” Humaira ta tashi, ta nufi ɗakin da Inteesar take zaune, sannan ta dawo kusa da ita, “Intee, yanzu kam kin zama babbar yarinya,” ta faɗa tana ɗan ɗaga gira, “Final year is waiting for you, madam, wannan shekarar ba wasa ba ce, so you have to be serious,” Inteesar ta yi murmushi, “Yauwa, teacher Humaira,” “Exactly! Ki maida hankali sosai, ki yi karatunki, ki fito da sakamako mai kyau, no distractions, okay?” Ta ɗan dakata, sannan ta karkata kusa da Inteesar ta rage muryarta, “Kuma…” ta kashe mata ido ɗaya, “ki buɗe zuciyarki,” Inteesar ta zaro ido, “Humaira!” “What? I didn’t say anything!” Mommy ta kallesu daga inda take zaune, “Me kuke raɗa-raɗa a nan?” “Babu komai, Mommy!” Humaira ta amsa da sauri, kafin ta fashe da dariya, Inteesar kawai murmushi take tana kallonta, Humaira ta sake rungumarta, “Seriously, Intee, I’m happy you’re doing better, kuma ina so ki ci gaba da haka, don’t let your past steal the beautiful things that may still be waiting for you,” Inteesar ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta rungume ta sosai, “Zan yi kewarki ƙwarai, Humaira, nagode da komai, thank you for standing by me,” Humaira ta shafa bayanta, “Always, silly girl, you know I’m only a phone call away,” bayan ɗan lokaci, Humaira ta yi sallama da Mommy, sannan ta tattara kayanta ta tafi, Inteesar ta tsaya tana kallon motar da ta ɗauke ta har sai da ta ɓace daga ganinta, sai ta koma cikin gida a hankali, yanzu gidan ya yi shiru, bayan kwanakin da ta yi tare da Humaira da Farida, komawar wannan natsuwar ta sa ta ɗan ji wani irin kaɗaici, amma ba kaɗaici mai tsanani ba ne, wataƙila kawai tana kewar yanayin da ta saba da shi a Lagos ne, ta koma ta zauna kusa da Mommy, wadda ta miƙa mata hannu ta matso kusa da ita, “Kin gaji ne, Intee?” “Kaɗan, Mommy,” “To, ki huta, za ki samu lokaci mai yawa na shakatawa kafin ku koma makaranta,” Inteesar ta jingina kanta a kafaɗar Mommy, “Okay, Mommy,” a wannan lokacin, tana jin daɗin samun wani wuri da za ta iya zama ba tare da ta yi ƙoƙarin bayyana duk abin da ke cikin zuciyarta ba, wani wuri da za ta iya yin shiru, kuma a fahimce ta.
A cikin ɗakinta a garin Katsina, Inteesar tana tsugune a gaban babban akwatinta, tana gyara kayan da za ta yi amfani da su a wannan shekarar ta ƙarshe a Jami’ar Nile, ta ware kayan makaranta a gefe guda, sannan ta fara duba littattafanta da takardun karatu, tana tabbatar da cewa babu abin da ta bari a baya, duk da cewa tana farin ciki da za ta ci gaba da karatunta, akwai wani ɓangare na zuciyarta da yake cike da fargaba, final year, shekarar da take buƙatar cikakken nutsuwa, jajircewa, da kuma ƙoƙari fiye da shekarun baya, sai dai tunaninta ba ya tsaya a kan karatu kaɗai, akwai Abuja, akwai gidan Yaya Umar, akwai abubuwan da suka faru a baya, waɗanda take ƙoƙarin kada su sake mamaye rayuwarta, ta zauna a gefen gadon, tana kallon kayanta da ta riga ta shirya, “Ya Allah, Ka sa na gama wannan karatun lafiya,” ta furta a hankali, a daidai lokacin, wayarta da ke kan gado ta yi vibrating, ta miƙa hannu ta ɗauko ta, tana tsammanin saƙon Amira ne, amma da ta duba screen ɗin, number Aliyu ne ya bayyana, ta buɗe saƙon, Aliyu: Ina fatan kin tashi lafiya? Tare da fatan ana shirin komawa karatu lafiya, Inteesar ta tsaya tana kallon saƙon na ɗan lokaci, ta san Aliyu yana ƙoƙarin nuna kulawa ne kawai, tun lokacin da suka haɗu a jirgin sama, bai taɓa matsa mata da tambayoyi ko tilasta mata yin wani abu da ba ta shirya ba, amma duk da haka, wani lokaci tana jin tsoron yadda take fara sabo da kasancewarsa, ta cije leɓenta a hankali, a kwanakin baya, ta fara lura da yadda take murmushi idan ta ga saƙonsa, wani lokaci ma tana jin daɗin hirarsu fiye da yadda take son ta yarda, kuma wannan ne ya sa ta fara ja da baya, what if I get too comfortable? What if I start expecting more than I should? Ta sauke wayar a kan gado ba tare da ta ba shi amsa ba, “Not now, Aliyu,” ta furta ƙasa-ƙasa, kamar yana gabanta, ta san ba laifinsa ba ne, shi bai yi mata komai ba, amma ita har yanzu tana ƙoƙarin gyara wasu ɓangarorin zuciyarta da suka daɗe suna ciwo, ba ta son shiga wata sabuwar dangantaka kafin ta fahimci kanta sosai, ba ta son wani ya zama mafakar da za ta fake da ita kawai don gudun fuskantar raɗaɗin baya, ta ɗauki littafinta, ta buɗe shafin da take karantawa, tana ƙoƙarin mayar da hankalinta kan karatu, a hankali, ta fara tsara abubuwan da za ta yi kafin komawa makaranta, ta yanke shawarar cewa wannan shekarar za ta ba kanta fifiko, karatunta, kwanciyar hankalinta, makomarta, kuma duk wani abu da zai zo daga baya, za ta fuskance shi ne idan ta shirya, ta sake kallon wayarta sau ɗaya, amma ba ta buɗe saƙon ba, ta juya ta ci gaba da karatu, wataƙila Aliyu zai fahimta, ko kuma aƙalla, tana fatan zai ba ta lokacin da take buƙata.
A can Abuja kuwa, yanayin Umar ya fara sauyawa idan aka kwatanta da watannin baya, ya fara samun ɗan ƙarin kuzari, fuskarsa ta fara samun hasken da ya rasa a baya, kuma ba ya yin shiru har na tsawon sa’o’i kamar yadda ya saba, Nana ta lura da wannan sauyin a hankali, ta lura da yadda yake fara shiga tattaunawa da ita, yadda yake tambayar ta game da aikinta, da kuma yadda wani lokaci yake sauraron labarunta har su yi ɗan dariya tare, a wannan rana, suna zaune a babban falon gidansu, Nana tana ba shi labarin wani abu da ya faru a wajen aikinta, tana kwaikwayon yadda wata abokiyar aikinta ta yi magana har Umar ya yi murmushi, “Wait, you’re telling me she said that in front of everyone?” ya tambaya, yana kallonta da ɗan mamaki, Nana ta gyada kai, “Wallahi! And the way she said it, you’d think she was announcing breaking news,” Umar ya yi dariya a hankali, Nana ta tsaya na ɗan lokaci tana kallonsa, murmushin da ke fuskarsa ya sa ta ji daɗi fiye da yadda take tsammani, domin a watannin baya, ta saba ganin shi cikin damuwa, kamar tunaninsa yana wani wuri da ba zai iya komawa gare ta ba, yanzu kuwa, aƙalla yana ƙoƙarin kasancewa tare da ita, Umar ya lura da yadda take kallonsa, “What?” Nana ta yi murmushi, “Nothing,” “Then why are you looking at me like that?” Ta ɗan girgiza kai, “Can’t I look at my husband?” Umar ya ɗaga gira, “Oh, so now I’m not allowed to ask questions?” Nana ta fashe da dariya, “You’re allowed, Your Highness,” ya yi murmushi, sannan ya miƙa hannu ya dauki ruwan da ke kan tebur, duk da cewa har yanzu akwai inuwar Inteesar a zuciyarsa, Umar yana ƙoƙarin fahimtar cewa ba zai iya ci gaba da rayuwa a cikin abin da ya wuce ba, ya san kuskurensa, ya san nadamarsa ba za ta goge abin da Inteesar ta fuskanta ba, kuma ya san cewa idan yana son ya gyara wani ɓangare na rayuwarsa, dole ne ya fara da abin da yake da shi a gabansa, Nana ba ta cancanci a mayar da ita wata mace da za ta jira a gefen rayuwar mijinta ba, ita ma tana da zuciya, ita ma tana da burinta, kuma ita ce matar da ya aura, ya kalli Nana, wadda ta koma duba wani saƙo a wayarta, “Wife,” ta ɗago kai, “Hmm?” “Thank you,” ta ɗan daure fuska, “For what?” Ya yi shiru na ɗan lokaci, yana neman kalmomin da za su bayyana abin da yake ji, “For being patient with me,” murmushin Nana ya ɗan lafa, ta kalleshi a hankali, tana ƙoƙarin fahimtar abin da ke cikin idanunsa, “Babe, I’m your wife, I don’t expect you to be happy every single day, but I do expect you to let me be part of your life, even when things are difficult,” ya gyada kai, “I know,” “Kuma ba na son ka ji cewa dole ne ka ɓoye min duk abin da ke damunka, but I also need you to remember that I’m here, too,” Umar ya yi shiru, sannan ya gyada kai a hankali, “I’ll try,” Nana ta yi murmushi mai laushi, “That’s all I’m asking for,” ta koma ci gaba da abinda take, kuma a wannan karon Umar ya saurare ta da cikakken hankalinsa, ba wai ya manta da Inteesar ba ne, ba wai ya daina nadamar abin da ya faru ba ne, amma yana fara fahimtar cewa nadama kaɗai ba za ta gyara komai ba, dole ne ya koyi rayuwa da sakamakon abin da ya aikata, ba tare da ya ci gaba da jawo wa wasu ciwo ba, kuma wataƙila, wannan shi ne farkon matakin da ya kamata ya ɗauka.
BACK TO ABUJA, lokacin da Inteesar ta dawo Abuja, ta shiga gidan Yaya Umar da wata sabuwar niyya a zuciyarta, ta yi wa kanta alƙawarin cewa wannan karon, ba za ta bari abubuwan da suka faru a baya su hana ta samun nasarar da take nema ba, tana da final year a gabanta, tana da burin da take son cimmawa, kuma tana da rayuwar da take son ta sake gina wa kanta, a hankali, bayan ta isa gidan, Nana ta tarbe ta cikin fara’a, “Inteesar! Finally, you’re back!” Ta rungume ta, tana murmushi, “How was the journey?” “Alhamdulillah, it was fine,” “Good, kin gaji ko? Ki je ki huta, daga baya za mu zauna mu yi magana sosai,” Inteesar ta yi murmushi, “Okay, yaya Nana, thank you,” a hankali, Inteesar ta fara sakin jikinta a gıdan, ba wai ta manta da abubuwan da suka faru a baya ba ne, amma ta yanke shawarar cewa ba za ta ci gaba da rayuwa cikin shakku da tsoro ba, Nana ma ta yi ƙoƙarin ba ta yanayi mai sauƙi, ba tare da ta matsa mata da tambayoyi ko sanya ta jin cewa tana ƙarƙashin kulawa ta musamman ba, kwanaki suka fara wucewa, Inteesar ta fara shirya komai da take buƙata domin sabon zangon karatu, ta duba jadawalin lectures, ta tsara lokutan karatu, a gidan kuwa, ta fara zama da Nana cikin walwala fiye da da, wani lokaci za su zauna su yi hira, wani lokaci su yi dariya a kan wani abu da suka gani a waya, wani lokaci kuma su yi girki tare, a hankali, gidan ya fara samun wani sabon yanayi, kuma Inteesar ta yi ƙoƙarin riƙe wannan natsuwar, wata rana da yamma, Inteesar da Nana suna tsaye a cikin kicin suna shirya abincin dare, Inteesar tana tsaye a gaban gas, tana juya miya a cikin tukunya, yayin da Nana take gefe tana yanka ganye a kan chopping board, suna ta hira a kan abubuwa daban-daban, wani lokaci har su fashe da dariya, “Intee, ki rage wutar nan, miyar za ta ƙone!” Nana ta faɗa, tana kallon tukunyar, Inteesar ta sauri ta juya ta rage wutar, “Ah-ah! Aunty Nana, as if I don’t know how to cook,” Nana ta ɗaga gira, “Really? To, bari mu gani,” Inteesar ta yi dariya, “You’re underestimating me,” “Okay, chef, we’ll see,” suna cikin wannan hirar ne wayar Inteesar da ke kan teburin kicin ta sake haskawa, tare da yin vibrating, Inteesar ta juya da sauri ta kalli wayar, saƙo ne, daga Aliyu, ta goge hannunta da towel ɗin gefen ta kafin ta ɗauki wayar ta buɗe saƙon, Aliyu: Na tashi kawai kika faɗo min a raina, na ce bari na duba lafiyarki, though na kira, ba ki ɗauka ba, I hope you are doing well there in Abuja? Inteesar ta tsaya tana kallon saƙon, wani ɗan murmushi ya bayyana a fuskarta ba tare da ta shirya ba, sai dai da ta lura da Nana tana kallonta, sai ta yi saurin sauya yanayin fuskarta, ta fara ƙoƙarin nuna kamar babu wani abu na musamman, amma ya yi latti, Nana ta riga ta lura, ta ajiye wuƙar da ke hannunta, ta matso kusa da Inteesar tana murmushi, “Intee…” Inteesar ta ɗago kai, “Yes?” Nana ta yi mata wani irin kallon tsokana, sannan ta tambaye ta cikin fara’a, “New catch ko?” Inteesar ta zaro ido, “What?” Nana ta fashe da dariya, “Na ce, new catch?” “Yaya Nana!” Inteesar ta faɗa cikin kunya, tana saurin ajiye wayar a kan tebur, Nana ta jingina da gefen teburin, tana ci gaba da murmushi, “To, wai wanne mutumin ne? Tun da kika dawo, wani lokaci idan na ga kina duba wayarki, sai na ga kin yi murmushi, yanzu kuma ga shi, saƙon ya shigo kin fara sauya fuska,” Inteesar ta ɗan juya ido, “Haba, yaya Nana, babu wani abu, aboki ne kawai,” “Aboki?” “Eh, aboki ne a makaranta, he’s just a friend, yana taimaka min da wasu littattafai da abubuwan da suka shafi final year,” Nana ta ɗan karkatar da kai, tana kallonta da alamar ba ta gamsu da wannan bayanin gaba ɗaya ba, “Okay…” Inteesar ta ɗan daure fuska, “Me kike nufi da okay ɗin nan?” Nana ta ɗaga hannayenta, “Nothing, nothing, na karɓi bayaninki,” Inteesar ta gyada kai cikin gamsuwa, “Good,” Nana ta ɗan dakata, sannan ta ƙara da murmushi, “But we’ll see,” Inteesar ta buɗe baki tana kallonta, “Yaya Nana!” Nana ta fashe da dariya, “, ban ce komai ba ai!” “Kin ce we’ll see!” “To, ai we’ll see ne kawai!” Inteesar ta girgiza kai tana dariya, sannan ta koma gaban gas, “Honestly, you people won’t let me rest,” Nana ta koma ci gaba da yanka ganyen, har yanzu tana murmushi, “Rest, my dear, nobody is disturbing you,” “Really?” “Absolutely,” Inteesar ta kalleta da gefen ido, “You’re smiling again,” Nana ta sa hannu a bakinta tana ƙoƙarin danne dariya, “Okay, okay, I’ll behave,” Inteesar ta girgiza kai, sannan ta juya tana ci gaba da juya miyar, amma bayan wasu seconds, ta kasa danne murmushin da ya sake bayyana a fuskarta, Nana ta lura, sai ta juya a hankali ta kalleta, “Intee…” Inteesar ta ɗaga ludayin miya a hannunta kamar tana yi mata gargaɗi, “Yaya Nana, don’t even start!” Nana ta fashe da dariya, “Okay, madam, na yi shiru,” Inteesar ta kashe gas ɗin da ke ƙarƙashin tukunyar, tana girgiza kai cikin dariya, amma a cikin zuciyarta, saƙon Aliyu ya ci gaba da yawo, na tashi kawai kika faɗo min a raina… Ta san bai kamata ta ɗauki kalmomin da wani babban abu ba, mutum zai iya tunawa da wani, ya tambayi lafiyarsa, ba tare da hakan yana nufin wata soyayya ta fara ba, at least, that’s what she kept telling herself, ta ɗauki wayarta, ta sake kallon saƙon na ɗan lokaci, yatsunta suka yi kamar za su fara rubuta amsa, amma sai ta tsaya, ta kulle wayar, ta ajiye ta a gefe, ba ta san abin da za ta yi da irin wannan kulawar ba tukuna, ba ta san ko ya kamata ta buɗe masa ƙofar tattaunawa sosai ba, ko kuma ta ci gaba da kiyaye tazarar da ta ɗauka za ta taimaka mata ta samu kwanciyar hankali, abin da ta sani kawai shi ne, ba ta shirya ba, ba yanzu ba, Nana ta kalleta, amma a wannan karon ba ta sake yi mata tambaya ba, ta koma shirya rice din da ta dora, tana barin Inteesar da tunaninta, domin wataƙila, Inteesar za ta buƙaci lokaci kafin ta iya fahimtar abin da take ji, kuma ba kowane sabon farawa ne yake zuwa da sanarwa ba, wasu lokutan, yana farawa ne da saƙo guda, ƙaramin murmushi, da kuma zuciyar da take ƙoƙarin fahimtar ko za ta iya sake amincewa da farin ciki.