Page 11
by @oumamani
*TASWIRAR KADDARA*
DijahAM(Oum Amani)
Page 11
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Maida dubansa kanta yai haka yasa ni bude baki a hankali nace "Good Morning Sir"
Tabe karamin bakin sa yai ya zuba mata ido yana mamakin rashin kunyar yarinyar ashe ma level 1 take lallai bata gama balaga ba.
Dan dago idona nai caraf idonmu suka hadu, yamutsa fuska yai cikin husky voice dinsa yace "me ya kawo ki office dina?"
Cikin dauriya nace "sir assignment din da Ka bamu jiya ne, tun jiyan na gama sir yau ban samu abin hawa da wuri ba kuma da nazo already lecturer ya shiga”
Dage gira daya yai yace "so?"
Hadiye wani yawu nai nace “shine shine nazoo nayi submitting sir”
Kallon Cilla yai cikin hade rai yace “kai mai kazo yi kuma”
Da sauri cilla ya dan zaro ido sannan yace “sir rakota nai”
Sai da ya dan saci kallon ta sannan ya maida dubansa kan cilla yace “fyn zaka iya fita tunda ba abinda ya kawo Ka”
Da sauri na kalli cilla daya juya zai fita cikin saurin magana nace "Sir Abba ya hana fa yace kar na dinga zuwa office dn lecturer ni kadai"
Kankance ido Azlan yai yana bin ta da wani mugun kallo cikin zuciyar sa yace “lallai yarinyar nan bata da man kai ni Azlan take fadawa haka, bata san yadda nake tattalin budurwarcina ba ai ni ya kamata naji tsoron kebewa da ita ko dan yadda ake kawowa budurcina Hari ta kowanne bangare”
Tabe baki yai cikin husky voice yace “ki koma class ki bawa class rep dinku, duk Wanda bai submitting ba yayi kafin 1 yazo ya min submitting and ki fada masa this should be the last da zan bada assignment na ce ayi submitting aki yi akan time” daga haka ya maida kansa jikin kujerar ya lumshe idonsa.
Sai da na maka masa harara sannan nace "thank you sir"
Muna fitowa daga office din nida Cilla a tare muka saki ajiyar zuciya sai kuma muka sa dariya, muna tafiya muna gulmar sa har muka isa hall din.
Assignment din na bawa class rep din sannan nai masa bayanin abinda ya fada min muka juya nida Cilla don yunwa nake ji ko breakfast ban yiba.
Cikin lokaci kankani karatu ya fara daukar zafi sam bana wasa don sosai abubuwa sun dau zafi har Dan ramewa nai, har lokacin banyi wata kawa ba don bana son shiririta, duk inda zani tare muke zuwa nida cilla kuma shine yake rakani.
Yau ma kamar ko yaushe na nutsu fiye da yadda nake nutsuwa saboda physics din da muke da shi yanzu Wanda Mr Wicked yake mana kamar yadda nasa masa suna, ina cikin duba joter dina sbd yace yau zai mana test shiyasa duk a rikice nake don malamin mugu ne baya mana Wasa ko kadan, sallama naji a kaina hakan yasa na dan dago don ganin wace, murmushi nai ganin Asma'u Hamza course mate dita ce kuma mun dan fi shiri a cikin class din don itama da dukkan alamu karatu ne ya kawota ba shirme ba.
Zama tai a gefena tace sannu "Batul sarkin karatu"
Dan dariya nai nace "sannu Malama Asma'u kinga laifina yanzu karatun ya dau zafi sai kana yi kullum kana dubawa in ba haka ba kazo karatun exam kanka yai bombing"
Dariya tai tace "kuma hake ne, ke ba ruwan ki baki shiga cikin mutane"
Dan murmushi nai nace "toh in shiga in batawa kaina lokaci, time din da bamu da lecture nafi gane wa in zanci abinci naci, in kuma bana Jin yunwa na duba papers dina in na koma gida ba lallai na duba ba saboda gajiya"
Murmushi tai tace "haka ne shiyasa Nima nace bara dai na dawo gurinki na dinga Zama naga serious student ce keh in ba damuwa"
Dan murmushi nai nace "laa ba komai Allah mu dinga zaman tare nima wani lokacin zama haka yana damuna"
Zatai magana kenan Mr Wicked ya shigo hakan yasa ta yin Shiru, Nima bakina naja nai Shiru duk muka nutsu muka zuba masa ido......
************
Cikin shesshekar kuka tace "yanzu Mummy me na rasa da Ya Azlan zai bude baki yace baya sona, ina da kyau na Mummy kuma yadda Maza suke bibiyata shi Mai yasa baya min haka"
Kwafa Mummy tai tace "goge hawayen ki Zainab in ina raye sai kin auri Azlan, shegen yaro ya kalli tsabar idona yace baya son ki ni bansan dalilin Baffa na goya masa baya ba wallahi"
Hawayen zainab ta goge cikin shagwaba tace 'Mummy ai kema kinsan Baffa yafi sonsa akan kowa nidai ki taimake ni Mummy ki shawo kan Baffan ya amince In ban aure Saba mutuwa zan yi Allah"
Da sauri Mummy ta rufe Mata baki tace “kiyi min shiru kedai kawai ki hada kayan ki kamar yadda na tsara Miki, kije gidan Ya Muhammad din ai gidan babanki ne, kuma in kinje bangaren Hajia Maryam zaki sauka, ina Kara fada Miki kiyi duk abinda zakiyi don jawo hankalin sa gare ki sannan ki daina sa bra guda 1 ki dinga sa biyu kuma masu push sosai badai kwaila yake ce Miki ba in kika koma sa biyu ai sai ya dawo miki kallon mai abubuwan arziki, sannan kije kasuwa ki siyo abin cikin duwawu haka ni dai Wallahi bani kuka gado ba da ace ni kika gada ai karyar Azlan ya kiraki da kwaila.
Dafe kumatu Zainab tai tace "Mummy ai yasan bani da boobs din in nayi ciko bazai gane ba kuwa”
Tsaki Mummy tai tace "ke dallah rabu da shi bai wani san yadda kike ba kawai yafada ne shi Azlan din har wani ganin ki yake da zai San yadda kike, kedai kiyi abinda nace sannan in kinga Yana guri kidinga dan karairaya kina turo kirji"
Dariya suka saki suka tafa kamar kawaye Saida Mummy ta gama fada mata duk yadda zatai sannan ta mike ta bar dakin tana jaddada Mata tai hanzarin shiryawa don yau take son ta tafi gidan Abie.
Bin bayan Mummy da kallo tai sannan ta mike ta nufi gaban Mirror tana karewa kanta kallo, tana da kyau sosai don fara ce tass kuma kasancewar ta yar gayu Mai gyara fatar ta da lura da ita yasa skin din nata Kara wani haske.
Kallon kirjin ta tai da yake kamar lemon tsami don bata da kirji sosai kamar wacce ta fara kirgan dangi sai duwawun ta da yake shafe, a takaice dai bata da body structure a tsaye take number 1, ajiyar zuciya tai tana tunanin yadda zata dinga ciko tana masa karairaya, wani tsallen dadi tai tana jin kamar ta aure sa ta gama ne donfa ita tayi alkawarin auren Azlan ko ana ha Maza ha Mata........
*********
Cikin aji ta waina manyan idonta ta kalli kawayen ta tace "Nana kinsan Allah gayen ya mugun tafiya dani, tun ranar dana fara ganin sa na kamu da mugun sonsa" sai ta sauke ajiyar zuciya tana dafe saitin zuciyar ta tace "kinsan ya hadu ne koh"
Murmushi Nana tai tace "Ai ni Zuby mamaki kike bani ashe zaki fada soyayya ta gaskia"
Hararar nana tai tace"gashi kuwa ni har na fadawa Dad na samu mijin aure"
Zaro ido Hafsa tai da tunda suka fara maganar bata ce komai ba tace "Zuby are u serious? Mutumin nan fa ko sanin zaman ki baiba amma har kin fadawa dad kin samu miji"
Dan bata fuska tai tace “kina tunanin bazai soni ba kome” mikewa tsaye tai tana dan gyara budaddaiyar abayar jikinta Wanda ya fallasa Riga da wandon dake jikin ta da suka kamata sai mayafi data yafa a kanta, juya jikin ta tai tace "meye baiji ba anan"
Bin ta da kallo sukai tana da diri dai dai gwargwado kuma tana da boobs madaidaita sannan tana da kyaun fuska don fara ce duk da dai farin hadda na bleaching, gyada kai Hafsa tai tace "komai yaji kawata"
Wani Murmushi tai tace "toh kunga ai kawai nasan zaima fada tarkon Sona don wallahi sai na aure sa haba wannan daga gani ba karamin haukata mace zaiyi a bed ba" ta wani lumshe ido tana lasar Baki
Wani ihu suka saki har saida mutanen dake gefen su suka juyo suka kalle su, dariya Nana tai tace "Zuby me ya kamata mu farayi ynxu toh da zai sa yasan da zaman ki"
Hafsa ce tai caraf tace "abu Mai sauki ai gurin sa zaki je kina karairaya kice kinzo ya koya miki abin da yai mana dazu baki gane ba"
Tafawa sukai suna shewa inda ta mike tana kara fesa turare a jikin ta ta nufi Office din Mr Azlan Muhammad Abdullah.
*Wacece Zuby*
Ya daya tilo ce a gurin Alh Ahmad Muktar da kuma Hajia Badiyya, ita kadai Allah ya basu haka yasa suke nuna mata soyayya mai tsanani dukkan abinda take so Shi take yi hakan yasa ta taso sangartacciya ta riga ta saba duk abinda take so Shi zatayi ba Wanda zai kwabe ta, tana da girman kai sosai ynxu haka tana level 3 a BUK inda take karantar Architecture.
Tun suna level 1 suke tare da Nana da kuma Hafsat haka yasa suka zama aminai sosai, ba laifi tana da kokari kodan kasancewar ta mara son raini a gurin course mate dinta hakan ke sata dagewa tayi karatu don kar ta samu carry over...
Tana da tarin samari sosai wadanda kawai cin kudin su take sai kuma irin wadanda ake soyayyar shan minti ayi romance amma ba'a zarcewa.
******
Yana zaune yana shan drink aka yi knocking kofar sai da yai kamar baxai amsa ba sai kuma yace "yess come in"
A hankali ta turo kofar ta shigo tana yin sallama, a hankali ya amsa mata kallo daya yai mata ya kauda kansa saboda yadda jikinta yake bayyana.
Karasowa tai ta tsaya daga dan nesa da shi cikin kissa tace "Good Afternoon sir"
Gyada kai kawai yai yana cigaba da duban system dinsa, cikin kwarewa da iya seducing namiji ta dan janye mayafin ta saman kirjin ta da ya taso yadan bayyana, sai da ta daidaita kanta sannan ta matso kusa da table dinsa ta sunkuyo yadda kirjin ta zai bayyana tace "Sir dama abinda Ka mana dazu ne ban gane ba shine nazo ka min bayani plz in ba damuwa"
Dagowa yai zai Mata magana caraf idonsa suka fada kan kirjin ta da suka dan bayyana ta sama...........
****
Da Mamaki na kalli Asma'u nace "da gaske wai Matar aure ce keh"
Dariya tai tace "wallahi Amma auren wata 2 kenan"
Ajiyar zuciya nai nace "tab amma baku more amarcin ku ba"
Dan bude ido tai sai kuma tai dariya tace "Ashe kina magana haka nifa da kallon da nake miki san baki magana"
Murmushi nai nace "ina yi mana saidai bada kowa nake ba gaskia"
Murmushin tai itama tace "kinga Baby yana kira nasan yazo dauka ta ko zaki zo muje ku gaisa daga nan sai mu rage Miki hanya"
Hararar ta nai nace "wallahi ki shiga hankalin ki, kawai baki san halina ba kina cewa nazo muje mu gaisa da mijin ki tab, lallai da sauran ki ai kuwa in haka kike ki chanja don ynxu yaudara tayi yawa a duniya"
Murmushi tai tace "duk da bansan halin kiba Batul amma na yadda dake ai shiyasa nace Miki kizo ku gaisa din amma Nima ina kiyaye wa fah"
Gyada kai nai nace "better dai"
Dariya tai tace "tab kice haka kike da kishi wannan za'a sha kallo"
Nidai ban mata magana ba sai hannu dana daga mata kawai, murmushi nai don naji dadin yau din sosai ko dan sbd hirar da mukai da Asma'u ne, Nima fita nai na samu abin hawa don Cilla bai zo na yau...
Toh fans ga Zainab nan fah ta danno da karfin ta zata gidan Abie farauto zuciyar Azlan🤞 koya zata kasance zatayi nasara ko kuwa🤔
Ga kuma zuby fa itama tace bata yadda ba sai ta aure sa Don ita ta gama fadawa Dad dinta ma ta samu miji aure kawai za'a daura🏌️♀️🏌️♀️🏌️♀️
Ku kawo dauki za'a yiwa Oga Azlan fyaddd*****
***