THE HIDDEN TRUTH
Pg 31
KIRAN QADDARA🔥
By: The Unnamed Writers
CHAPTER 31: THE HIDDEN TRUTH
A kwana a tashi yau su maryam sukayi end of the year exam dinsu kuma zasu fara hutu daga gobe, zayd na dawowa gida seda ta tuna mishi alqawarin da yayi mata chewa zasuyi sati daya a cruise ship idan tayi hutu
“Haya Bakida mantuwa, Toh zanyi clearing schedules dina se musaka lokaci muje”
Taji daadi sosai har seda ta tashi ta rungume shi tana yimishi peck a kumatu
Yayi murmushi shima yayi kissing dinta a baki, daga nan dai abun ya chnja salo wanda dama tasan zaa rina, ita kanta tana mamakin yadda ynzu ta saba da zayd sosai ba kamar da datake jin tsoro da shakku ba, a ynzu kam ta riga tasan duk wasu abubuwa da zayd keso, ta sakar mishi dukkan ragamar rayuwar ta, kuma har intimacy classes maman susan tasata wa’inda akeyi online kuma tana koyon abubuwa daban daban har tana yima Safiyya forwarding, itama safiyya inta samu abu me anfani tana turo mata.
SOKOTO
Rayuwa na tafiya cikin hukuncin ubangiji da tsarinsa, Imran ya fara sabawa da sabon sauyin rayuwarsa. Bayan ya sayi motarsa Peugeot 406, ya ƙara himma sosai wajen aiki da kuma neman gidan da zai saya wa Inna da Baba. Yana son su daina zama gidan da suka daɗe suna gadi, su samu nasu gida inda za su more rayuwarsu cikin kwanciyar hankali, ya samu wani gida Wanda ke kallon gidan su maryam, wata uku da suka wuche me gidan ya rasu, shine magadan keson su saida su raba gado
Anyi ma gidan kudi cikin ikon Allah ya samu ya saya sedae akwae yan gare garen da zaa yi ma gidan saboda tsohon gida akwae buqatar penti da chanja toiletries, da dan abunda baza’a rasa ba.
Hauwa Koulou ta maida hankali sosae kan karatun ta, bata da wata damuwa, mama tana bata kudi ta dan saye abunda zata ci idan taje school, transport ma ya mata sauqi sosae Saboda wurin aikin Imran bai yi nisa da jami’ar ba, sau da yawa yakan ɗauke ta da safe, sannan su dawo tare idan lokacin dawowar su ya yi daidai.
Wata rana bayan imran ya dauko hauwa suna hanyar gida, se ta dan kalleshi
“Yaya Imran, na gode sosai, ba don kai ba, da na wahala kafin in Saba da yadda zan rinqa zuwa school, amma ta dalilin ka na samu sauƙin zuwa school kusan koda yaushe, Allah ya saka da alheri”
Imran ya yi murmushi.
“Babu komai, Ki dage da karatu, Allah ya bada saa”
Ta amsa da “Ameen”
A dd nan suka iso gida ta fita motar tana mishi sallama ta shige gida shima ya matsa zuwa gidan su ya shiga.
Inna tana lura da yanayin É—anta kwana biyu
“Imrana, kana ganin be kamata ache ka gayama hauwau abnda ke cikin ranka ba yanzu?”
Imran ya É—aga kai daga abincin da yake chi sora kadan ya sarqe
“Inna, me ya sa kika ce haka? Me ke cikin rai na?”
Baba na gefe yana jinsu, ya yi dariya sannan ya amsa ma imran
“Saboda duk ranar da kuka dawo gida tare fuskar ka tana nuna muna alama”
Imran ya yi ƙoƙarin ɓoye murmushinsa.
“Baba bincike fah ba kyau”
Inna ma ta yi murmushi.
“Ba mu ce komai ba ai, addu’a kawai muke Allah ya daedae ta.”
Imran bai ba su amsa ba, amma a zuciyarsa ya san Hauwa ta fara samun wuri na musamman. Har yanzu bai kira abin da yake ji da sunan so ba, amma ya fara fahimtar cewa lallai yana jin wani abu gameda ita.
BAYAN SATI BIYU
Wata rana da yamma, bayan imran ya dawo daga aiki, ya tarar da Baba yana zaune a tsakar gida yana shan iska, ya shigo da sallama, baba ya ansa mishi yana tambayar shi aiki, da alhamdulillah ya amsa sannan ya zauna kusa da baba
“Baba ya kasuwar?”
Baba ya É—ago kai yana murmushi.
“Alhamdulillah, kaima ya naka aikin fa? Kana ta fama kullum ba hutu”
“A qara samu cikin Addua Baba, Ina so in ga kun samu kwanciyar hankali sosae da jin dadi, mun riga mun qare magana da masu wancan gidan da na saye, sunche nan da sati daya zasu kwashe kayan ciki su bada key, zan fara gyara shi, idan na qare gyaran se mu koma chan, kuma ku samu natsuwa da kwanciyar hnkali”
Baba ya kalleshi na É—an lokaci, sannan ya numfasa.
“Allah yayi maka albarka imrana, kuma yasa ma neman ka albarka, a koda Yaushe inaso ka tuna chewa ba kuddi kaɗai suke sa mutum farin ciki ba, zamowar ka ɗa a gare mu yafi muna farinciki fiye da komai a rayuwa, ka sani chewa abin da ya fi muhimmanci shi ne ka kasance mai gaskiya, kuma ka gina rayuwa wadda ba za ka yi nadama a kanta ba.”
Imran ya gyada kai.
“Na sani Baba, kuma ina iyakacin qoqarina na ganin na kiyaye hakan, ina son kuma ku samu abin da kuka cancanta akan wahalar da kukasha, nasan bazan taba iya biyan ku ba, shiyasa nike muku addua kullun”
Baba ya É—ora hannu a kafaÉ—ar dansa
“Allah ya saka maka da alheri, kuma dai kada ka manta da kanka yayin da kake ƙoƙarin faranta mana imrana, kaima ka gina kanka dan goben ka”
Kalaman Baba sun tsaya a zuciyar Imran. Ya san yana da abubuwa da yawa da yake son chimma a rayuwar shi, amma a kwanakin nan akwai wani abu da ya fara samun wuri a cikin tunaninsa wanda bai da alaƙa da aiki ko neman kuɗi.
Hauwa Koulou! houwa koulou che!
A take kwakwalwarsa ta fara tunano masa baya, Tun lokacin da yake daukarta ya kaita wurin JAMB lesson ya dawo da ita, har zuwa ynzu da yake kaita makaranta su dawo tare mafi yawan lokuta, kuma a hankali, hirarsu tanata faÉ—aÉ—a, ya tuna shekaranjiya da safe, lokacin da Hauwa ta shigo motar da sallama tana É—auke da wasu littattafai a hannunta, bayan ta gaida shi ta fara magana
“Yaya Imran, yau muna da test.”
Imran ya kalleta kafin ya maida hnkali kan titi
“Toh kinyi karatu? Kin shirya?”
Ta yi murmushi, amma akwai É—an damuwa a fuskarta.
“Ina ganin na shirya, amma lecturer ɗinnan yana bada tambayoyi masu wahala, banda tabbacin abnda ze faru”
“Anya kin yi karatun kuwa?”
“Na yi fah”
“To, ki yi iya ƙoƙarinki, kiyi addua, kuma Kada ki bari tsoro ya hana ki tunawa da abin da kika karanta.”
Hauwa ta kalleshi, sannan ta yi murmushi.
“Kana bada postive energy, Da ace kai ne lecturer ɗinmu, da zamu samu confidence.”
Imran ya yi dariya.
“Ni lecturer? Ai kuwa da kin daina zuwa class saboda tsoron tambayoyina.”
Tayi dariya.
Haka suka ci gaba da fira har suka isa makarantar, kafin ta sauka, ta dan kalleshi
“Yaya Imran, qarfe nawa zaka tashi daga office? Tare zamu koma?”
“Maybe, Idan kin qare abnda kikeyi before 5pm ki sanar da ni se mu san yadda zaayi.”
Ta gyada kai.
“Thank you.”
“Allah ya bada sa’a”
Da ta sauka ta nufi cikin makarantar, Imran ya tsaya yana kallonta na ɗan lokaci kafin ya juya ya nufi hanyar fita daga school din. Ya lura cewa ya fara jin daɗin hirarsu fiye da yadda ya zata. Ba wai taimaka mata kaɗai ke sashi farin ciki ba, yana jin daɗin ganin yadda take ƙoƙari, da kuma yadda take ɗaukar karatun ta da muhimmanci.
Koda yaje office ya tarar da aiki dayawa, tunda yaje be natsu ba, yanata fama, kamar wanda aka tsikara ya tuna da test din maryam
Ya ɗauki wayarsa ya rubuta mata saƙo.
Imran: How was your test?
Bayan É—an lokaci, ta amsa.
Hauwa: Alhamdulillah, I think I did well. Thank you for asking.
Imran ya yi murmushi.
Imran: Good. Keep working hard, Allah ya bada saa
Hauwa: I will in shaa Allah, And don’t forget you promised to teach me how to drive one day.
Imran ya ajiye wayar kawai yana murmushi. Ya fahimci cewa waɗannan ƙananan hirarrakin sun fara zama wani ɓangare na rayuwarsa. Yana samun kansa yana tunanin abin da zai gaya mata ko abin da za ta ba shi labari a lokacin da za su haɗu.
Da yamma, ya samu damar zuwa ya ɗauke ta. Hauwa ta fito tana murmushi, tana riƙe da littattafanta.
“Yaya Imran!”
Ya É—aga gira.
Ta yi dariya tana shiga motar
A hanya, Hauwa ta bashi labarin test ɗin. Ta yi ta yimishi bayanin tambayar da ta fi ba ta wahala, da kuma yadda ta tuna amsar a minutes din ƙarshe ana gab da qare test din
Imran yanata sauraren ta, yana mata tambayoyi lokaci lokaci har suka isa gida, ta tattara littattafanta sannan ta juyo gare shi.
“Na gode sosai, Allah ya saka da alheri”
Imran ya yi murmushi kawai
“Ba komai, Allah ya bada saa”
“Ameen ya Allah”
Har ta bude qofa se kuma ta tsaya
Ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta ce cikin sanyin murya, “yaya imran, da gaske zan iya chimma burina na rayuwa har in rinqa taimaka wa jamaar musulmi?”
Imran ya juyo ya kalleta sosai da mamakin tambayarta qarara a fuskar shi, dauki dan lokaci kafin ya bata amsa
“Ba se kin san yadda za ki cimma komai tun yanzu ba, kiyi abin da yake gabanki a ynzu kawai, ki yi ƙoƙari, sannan ki nemi taimako idan kina buƙata, kar ki kuskura ki manta da addua, with Allah everything is possible, take your time and don’t be in rush”
Hauwa ta kalleshi, murmushi na bayyana a fuskarta.
“Na gode, Wani lokaci kana yimin magana kamar babban yayana”
Imran ya yi dariya a hankali.
“Wataƙila saboda na fara tsufa ne”
“A haka ka fara tsufa? Ai baka ma kama hanyar ba”
“Baba da inna sunche na fara tsufa, inda gabansu kika fadi haka da sun miki dariya.”
Hauwa ta sake dariya, sannan ta sauka daga motar
“See you tomorrow Yaya Imran.”
“See you tomorrow, bye”
Anya kuwa hauwa ba wani wuri na musamman take samu a zuciyar shi ba? Shi yaushe ya fara tsayawa yayi fira da wata bayan maryam? Kuma tun lokacin da maryam tayi aure be sake kula kowa ba
Amma dai baya so ya yi gaggawar sanya wa wannan abin da yakeji suna, ze jira yaga abunda Allah zeyi
A dd lokacin yaji an dafa shi, ya dago kai yaga inna
“Imrana Inata yimaka magana shuru tundazu, ina hnkalinka ya tafi?”
“Naam inna ina wuni, ya gida?”
Baba yayi dariya don shima tundazu yayi mishi magana amma be amsa ba, ya lura yayi zurfi cikin tunani
Baba ya É—auki kofin da inna ta kawo mishi na fura ya kai baki yasha sannan ya fara mgana
“Imrana kada ka yi gaggawar shigar da kanka wani abu saboda kawai kana jin daɗin kasancewar yanayin, Ka fara sanin zuciyarka da abin da kake son ginawa.”
Imran ya gyada kai “in shaa Allah baba”
Ba su tilasta masa ya amsa tambayar da sukayi masa kai tsaye ba, amma kalamansu sun sa shi yin tunani.
Tashi Yayi ya wuche ɗakinsa, ya buɗe wayarsa nan yachi karo da saƙon Hauwa.
Hauwa: Thank you for today yaya imran, mama tache in maka godiya”
Imran har ya rubuta reply, ya tsaya ya karanta, se ya goge wasu kalmomi kafin ya sake rubuta
Imran: You’re welcome, Get some rest, You have more work ahead of you.
Ta amsa da sauri.
Hauwa: You too. And Don’t work too hard.
Imran ya yi murmushi kawai ya ajiye wayar.
Wataƙila wannan shi ne farkon wani sabon abu. Amma kamar yadda Baba ya ce, ba sai ya yi gaggawa ba. Abin da yake buƙata shi ne ya kasance mai gaskiya ga kansa da kuma Hauwa, ze karanci zuciyar ta da kuma tashi in shaa Allah
ABUJA
A Gidan Margayi Rahman Balarabe, ana rayuwa kamar yadda aka saba a kullun.
A ido, gidan yana cike da natsuwa da kwanciyar hnkali, Amma a bayan wannan kamala, akwai wasu tsoffin al’amura da har yanzu ba a gano gaskiyarsu ba, ko ma dai ache ba’asan dasu ba
Mammi che zaune a É—akinta tana duba wasu tsofaffin takardu da ta daÉ—e tana ajiya wanda batasan amfanin su ba, tun bayan rasuwar mijinta, hajiya raliya da a lokacin itache COO ta company din northern crest ta tattaro su ta kawo mata, Ba wai tana neman wani abu na musamman a cikin su ba, so kawai take ta duba idan akwai masu amfani, idan kuma babu tayi watsi dasu.
Sai dai yayin da take tsakiyar duba su, sai ta ci karo da wani tsohon envelope mai launin ruwan kasa. An rubuta sunan Bashir Misalati a jiki da rubutun da ya tsufa sosae, wannan rubutun mijinta ne, ta tabbata
Mammi ta tsaya, gabanta na faduwa “Bashir me Salati?” Ta fadi da mamaki
Ta san sunan sosai, baban maryam ne, kuma tasan Bashir ya kasance abokin kasuwancin Rahman Balarabe na kusa, kafin rasuwar sa, har dalilin yadda suke kasuwanci cikin mutunci da amana yasa mijinta ya bashi aiki a northern crest, A lokacin, dangantakar su ta kasance mai ƙarfi, amma lokacin da Rahman Balarabe yake kwance gida yana rashin lfya, aka samu wata yar hatsaniya a aiki abubuwa suka fara chanzawa har ya rasu, kuma ana kan bincike Bashir me salati shima Yayi accident ya rasu, bayan rasuwar Bashir, abubuwa da yawa sun sauya, Wasu bayanai sun ɓace, wasu takardu ba a sake magana a kansu ba, kuma akwai tambayoyi da Mammi ta taɓa yi a lokacin game da binciken amma ba ta samu cikakkun amsoshi ba, daga qarshe akayi watsi da maganar tunda Bashir din ma ya rasu
Ta buÉ—e envelope É—in a hankali.
A ciki akwai wasu tsofaffin takardu da copies na letters. Wasu rubuce-rubucen sun dusashe saboda shekaru, amma sunan Rahman Balarabe ya bayyana a shafi na farko na wata paper, Mammi ta zauna sosai, ta fara karanta dan abin da za ta iya fahimta.
A tsakiyar shafin akwai wani paragraph dake magana akan wani tsohon haÉ—in gwiwa tsakanin Rahman Balarabe da Bashir Misalati. An kuma ambaci wasu kadarori da yarjejeniya da za a aiwatar idan É—aya daga cikin abokan haÉ—in gwiwar ya rasu
Mammi ta daÉ—e tana kallon takardar.
“Ya Allah…” ta fadi a hankali.
Ba ta da tabbacin abin da takardar take nufi gaba É—aya, Amma ta fahimci cewa akwai wani abu da bai kamata ache anyi watsi da shi ba.
Ta É—auki wayarta ta kira Hajiya Raliya, ringing biyu ta É—auka.
“Assalamu alaikum, Mammi.”
“Wa alaikumus salam, Raliya, Yaushe zaki dawo?”
“Zuwa next week in shaa Allah, lfya dai mammi?” Ta tambaya saboda jin yanayin muryar ta
“Ina son in tambaye ki wani abu ne”
“Mammi, lafiya kuwa?”
“Lfya alhamdulillah, Na samu wasu tsofaffin takardu na Bashir Misalati cikin wasu papers da kika taba bani da dadewa tun bayan rasuwar babansu zayd, kuma na ga sunan babansu zayd a ciki, tare da wasu bayanai game da haɗin gwiwarsu, kina iya tuna wani abu game da wannan? Sunyi wani hadin gwiwa ne?”
A ɗayan ɓangaren, Hajiya Raliya ta yi shiru na ɗan lokaci har mammi taji shirun nata yayi yawa
“Raliya?”
“Naam, Inaji mammi, Na tuna wasu abubuwa, amma ba zan so in muyi magana a waya ba. Al’amurran sun daɗe, kuma akwai abubuwan da ban tabbatar da su gaba ɗaya ba.”
Mammi ta gyara zamanta.
“To, ya kamata mu duba su tare.”
“In shaa Allah idan na dawo, na dade sosai ina neman takardun nan bnsan ke naba su ba, ki yi hankali da waɗannan takardu kafin in dawo, Kada ki bari su shiga hannun wanda ba ki yarda da shi ba, kar ma dai kiyi maganar da kowa ki bari kawai se na dawo”
Mammi ta kalli envelope É—in da ke hannunta.
“Me kike nufi? Akwai matsala ne?”
Hajiya Raliya ta numfasa.
“Ina nufin idan waɗannan takardun suna da alaƙa da abin da nake zargi, to akwai mutanen da zasu iya damuwa idan aka fara bincikensu.”
Mammi ta ji wani sanyi ya ratso ta bayanta.
“Kin san wani abu da ban sani ba, Raliya?”
“Mammi, ba abun tashin hnkali bane, kawai nasan akwai wasu tambayoyi da ba a taɓa samun amsarsu ba lokacin da ina aiki a northern crest, Amma ba zan so in yi miki bayani ba tare da na sake duba abin da nake da shi ba. Ki ajiye takardun a wuri mai aminci. Idan na dawo za mu tattauna.”
“Allah ya dawo dake lfya” kawai mammi ta iya fadi kafin ta kashe wayar
Ta mayar da takardun cikin envelope ɗin, Amma se ba ta mayar da su cikin tsohon akwatin ba. Ta saka su cikin wani ƙaramin file, ta saka shi a cikin bedside table dinta
Fahad Rahman Balarabe ne zaune a office dinshi na gida yana duba wasu saƙonni a wayarsa, tun bayan da wasu tsofaffin bayanai suka fara bayyana, ya rasa gane abnda ke faruwa, Kwanakki ya samu wani saƙo daga Ali, amintaccen shi, abnda kuma ya rubuta shine
Ali: An sake requesting wasu takardun tsohon haÉ—in gwiwar Rahman da Bashir, Ban san dalilin da ya sa ba, amma yana da kyau ka sani.
Fahad ya karanta saƙon sau biyu.
Fuskarsa ba ta canza sosai ba, amma hannunsa ya matse wayar.
“Wai waye ya fara tono wannan magana?” ya furta a hankali.
Ya ajiye wayar, ya tashi ya taka zuwa window. Ya daɗe yana kallon waje, tunaninsa yana komawa ga abubuwan da ya daɗe yana ƙoƙarin ɓoyewa.
A gare shi, tsohon haÉ—in gwiwar wani tarihi ne da be kamata a tado dashi ba. Akwai takardu, akwai sa hannun da aka canza, akwai bayanan mallakar kadarori da aka gyara, kuma akwai mutuwar Bashir da bai kamata a sake bincikarta ba.
Ya É—auki wayarsa ya rubuta message
Fahad: Find out who has access to the old files. I want to know immediately.
Ya aika saƙon, sannan ya zauna yana kallon wayarsa. Bai san wanda ya fara binciken ba, amma ya san ba zai iya ɗaukar wannan maganar da wasa ba.
Domin idan tsoffin takardun suka bayyana a hannun mutanen da suka dace, abubuwan da ya ɓoye na tsawon shekaru za su iya fara fitowa fili.
WASHEGARI
Hajiya raliya tun da tayi waya da mammi jiya ta kasa baccee, ta yanke shawarar yau da safe kawai zata dawo Abuja, dama program ne taje yi a Lagos se kawai ta dauki excuse ta dawo, Da yamma se gata ta shigo, mammi nata mamakin ba tache se zuwa next week ba
Bayan taje dakinta ta kimtsa tayi sallah se ta fito ta tarar da mammi tasa an hada mata abnci, Bayan tachi abnci suka wuche dakin mammi, ta fito mata da envelope É—in ta bata
Raliya ta karɓa, tanata duba shafukan ɗaya bayan ɗaya. Yayin da take karantawa, fuskarta tana ƙara nuna damuwa.
“Wannan shi ne abin da nake tsoro,” ta faɗa a ƙarshe bayan ta qare dubawa duka
Mammi ta kalleta.
“Me kika sani, Raliya?”
Raliya ta É—ora takardun a kan gadon da suke zaune
“Na san cewa Bashir da Rahman suna da wani babban haɗin gwiwa wanda shi ya assassa haihuwar northern crest holdings, Akwai yarjejeniyar da ta shafi kamfanoni da kadarori. Amma bayan rasuwar rahman, abubuwa sun rikice. Wasu sun ce an riga an warware komai, wasu kuma ba su yarda ba sunche Bashir ma’aikaci ne kawai, wasu suka fara zargin chewa Bashir yana diverting company funds masu yawan gaske”
Mammi ta sake rikicewa
“Amma me ya sa ba a taɓa yin cikakken bincike ba?”
Raliya ta yi shiru na É—an lokaci.
“Saboda akwai mutanen da ba sa son a yi binciken, kuma akwai wasu da suka ji tsoron abin da za’a gano, ni kaina bnsan meyasa aka dakata da binciken ba, amma lokacin bnda ikon inyi wani abu tunda na riga na aje aiki a kampanin, kawai external auditor nike, sedai inje inyi supervision in dawo”
Mammi ta ji zuciyarta ta yi nauyi.
“Ynzu yana iya yiwuwa Maryam da ahalinta suna da alaƙa da wannan maganar, ko ba haka ba?”
Raliya ta kalleta kai tsaye.
“Hakane, shi ya sa nake ganin dole ne mu yi hankali, kuma musan yadda zaayi ayi muna bincike a boye, Idan Bashir yana da haƙƙin wani ɓangare na kadarorin, to iyalinsa na iya kasancewa an hana su abin da ya kamata su samu tun tuni”
Mammi ta sunkuyar da kai, tana tunanin Maryam da Zayd, Ba ta son wani abu ya shiga tsakaninsu, amma kuma ba ta son a bar wani abu a ɓoye saboda tsoron rikici.
“Ba zan so Maryam ta shiga wani haɗari ba,” Mammi ta faɗa a sanyaye
“Ni ma ba na so,” Raliya ta amsa. “Amma idan za mu taimaka mata, dole ne mu fara da gaskiya. Kuma dole ne mu tabbatar cewa duk wani abu da muka samu muyi kwakkaran bincike gudun kar mu shiga hakkin su dan yanxu maganar gado akeyi”
Sun amince cewa za su fara duba takardun a hankali, ba tare da sun sanar da kowa ba tukuna, ta tambayi mammi ko tanada mukullin wannan qofar da ke bayan garden, ta amsa mata da tanada shi amma se ta bincika don bazata iya tuna wurin da yake ba.
Hajiya Raliya kuma tace za ta sake binciken mutanen da tasan sunyi aiki da northern crest a da lokacin da aka fara bude kampanin
Har ta tashi, ta juyo ta kalli Mammi.
“Kada ki yi wa Fahad maganar komai game da waɗannan takardun tukuna.”
Mammi ta kalleta da mamaki, Tana tunanin toh ai tunda shi yasan komi gameda kampanin a ynzu ba wanda ze taimake su kamar shi
“Me ya sa?”
Raliya ta yi shiru na É—an lokaci kafin ta amsa.
“Ba komai, gara dai kada kowa yaji zanchen ynzu tukunna tunda babu tabbacin komae”
Kalaman sun bar Mammi cikin tunani, Toh Fahad ai baza’a sashi cikin “Kowa” ba da za’ache ba’ason kowa ya sani, ai shi ba kowa bane, danta ne, kuma shi ke riqe da kampanin a ynzu
A wannan daren, da mammi ta shigo daki ta kwanta, ta kalli tsohon envelope É—in da ke kan table, ta dauka ta maida shi cikin drawer
Ta yi addu’a a hankali.
“Ya Allah, idan akwai gaskiyar da aka ɓoye, ka bayyana ta. Ka kuma kare waɗanda abun ya shafa”
Ba ta san cewa a wani ɓangare na cikin gidan, danta Fahad ya riga ya fara ƙoƙarin gano wanda yake binciken tsoffin takardun.
Kuma ba ta san cewa waÉ—annan takardun za su iya zama farkon hanyar da za ta kaisu ga amsar wasu tambayoyi da suka daÉ—e suna damun Maryam da Zaid.
A Amsterdam, Maryam che a kwance kusa da zaid a daren, tana jin daɗin tunanin hutunta da tafiyar da suke shirin yi. Zaid ya tambaye ta ko akwai wani abu da take buƙata kafin su kwanta.
Ta girgiza kai.
“A’a, Ina dai tunanin hutun da zamuyi a cruise”
Ya yi murmushi.
“In shaa Allah it’ll be a memorable time”
Maryam ta matso kusa da shi, ta ɗora kanta a ƙirjinsa
Zaid ya sumbaci goshinta.
Ta lumshe idanunta, tana jin wani irin kwanciyar hankali da take samu koda yaushe idan tana jikin shi.
Yayin da a Sokoto Imran yake fara fahimtar abin da yake ji game da Hauwa, a Abuja Mammi da Hajiya Raliya suka fara tono wani tsohon sirri, Maryam da Zaid kuwa suna gab da samun labarin da zai sauya rayuwarsu gaba É—aya.
Domin wani lokaci, ƙaddara tana fara canza rayuwar mutum ne ta hanyar ƙananan abubuwan da bai ɗauka da muhimmanci ba❤️
Join our WhatsApp group
Follow this link to join my WhatsApp group: ***